Showing 102001 words to 105000 words out of 105295 words

Chapter 35 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6104

cirko suna tsokanar megida matarda zatayi yaye da yan mata ma duk suna iya Amfani dashi . 2, A Dakin amarya munada mayyukan kamshi da gyaran jiki haka kuma muntanadi mayyukan gyaran gashi akwai hadin buzaye mesa gashi taushi laushi da kuma santsi 3 hakama bangaren kayan mata suma ba'a barmu a baya muna hadin kaya masu inganci akwai hadin kinfi Amarya akwai zumar karya gado akwai hadin sabuzu kuwa akwai hadin dan bagigita akwai kalolin kaza dakuma tsimi da kuma kalolin san matse domin karin bayani sai ku tuntubi wanam Lambar 0805 086 4183 kokuma sakon karta kwana ta wanam lambar a man hajar WhatsApp 08164714675 kokuma saadatusadik@gamil.com sayen nagari maida kudi gida muna aikewa da sako gari gari kuma inganci kayanmu ke sayar dasu da ikon Allah ku garzayo dakin amarya muna nam garin sokoto
.............. Bayan an tattara mutanen Nahara, an tsallaka da su sai da Abid ya raka su da kayan gudummawar abinci da na sha, aka raka su da shi a lokacin da suka isa abin ya basu mamaki, domin basu tab'a zaton zasu sami haka ba, shirun Abdullahi da yayiwa Kyautah ba kome bane yaso ya bata haka a matsayin kyautar Haihuwar da zata yi mishi, yasa aka gine musu ana haka kuma yasa aka musu noman rani, kasancewar suna kusa da ruwa, an cire musu abincin farko, wanda Uzairu ne akan al'amarin, yanzu kuma ana shiga damina aka fara musu nomar damina, wanda dakarun Deehar suke haka ba dare ba rana, har zuwa yau da suka dawo nahara, cike da mamaki.
"Wannan shi ne abin da Kyautah ta muku, kuyi hakuri da rashin da kuka yi, akwai wasu suna cikin nahara, daga cikin su waɗanda suka a bayan tsibirin nahara. Sarki Abdullahi ya bada wannan alkhairin ne saboda yar ku da yake aurenta, da fatan zaku amshi haƙa a matsayin alkhairi daga Kyautah."
"Mun gode sosai, shi kuma ka bawa Sarki Abdullahi Noye hakuri yayi bikon matar shi mun san ba shi zai kashe su ba, laifin su da kwadayi ya ja musu, muna godiya muna kara godiya, ko ba kome mun samu yanci mun dawo muhallin mu, ita kuma Nahara ya bata hakurin fuskarta mijinta"


Da haka Abid suka juya, bayan an saka musu dakarun da zasu kula da garin, suma Abid suka dawo, har zai wuce gida sai ya fasa ya dawo fada, ya same shi zaune zugum.
"Abdullahi!" D'ago kai yayi, "har zuwa yanzu kana fada?"
"Tow ina zanje?" Sai ya bawa Abid tausayi, "gida zaka mana" Abid ya fada, "A'a bani da me kula da ni, me zanyi da gidan?"
"Me kake bukata" "taso muje dan uwana" a hankali ya taso, suka nufi gidan Abdullahi, suna shiga Aaliyah ta shiga basu kulawa, salolin kan shi ma a gidan yayi, sai da dare yayi ya koma gidan shi, ɗakinta ya nufa ya samu kome a birkice, sannan ya shiga tattara kome ya kintsa dakin, ya dauki wani rigar ta, ya zubawa idanu. Sannan ya nufi dakin shi da rigar, kamar yadda yaga rana haka ya ga dare, da ya kasa barci alola yayi ya fara sallah dare, yana gayawa Allah kukan shi. Har yanzu asuba, ya shirya ya tafi masalaci.
Itama a ɓangarenta haka ta ga dare, sai kuka da kukan zuci, a tunaninta zata iya rabuwa da Abdullahi ne, sai gashi tana nisa da shi zuciyar ta, yana kuntatta mata, har suka yadda zango, bata iya barci ba haka tayi ta juyi.
***
Washi gari haka suka tashi da bayan sun karya lokacin itama ta fara barci, uwar bayi da ladi basu tadda ita ba, tun daga lokacin zata kwana idanunta biyu, gari na wayewa zata fara barci, haka suka cigaba da tafiya, tana nisa da shi tana kara jin wani irin kunci bata walwala, bata cikin farin ciki da jin dadi
..... Haka shima ya zubawa Ya Musa idanu, bai mishi magana ba, har zuwa lokacin da suka hadu a fada, suna kallon juna irin ina sane da kai, a lokacin Kamilu dan gidan Chiroma da suke zuwa fadan, domin Abdullahi ya bukaci su shigo ayi da su, inda ya mai da musu matsayin su na iyayen su, ya cewa Abdullahi. "Allah ya baka nasara yana da kyau ka bi sawun iyalinka, domin zama haka babu dad'i"
"Tunda ta iya tafiya da kafarta, a bar kawai ga Mulikah da Radiah ga kuma Raudah" sai lokacin Abid ya ce musu.
"Mulikah da Radiah, Abdullahi ya sake su tun bayan rantsar da shi domin haka babu batun dawo da su, kuma batun Raudah ina ga tuntuni aka manta da batun."
Shafa gemu Ya Musa yayi, sannan ya ce.
"Idan kuma mace ta guje mijinta,.akan wani dalili mara tushe fa? Ai sai ya kara aure."
"Tabbas ita tayi haka ne domin tana son mijinta, wasu ƴaƴan su, watsa musu kasa suka yi a idanun su." Abid ya fada yana kallon Ya Musa. "Abid" ya kira sunan Abid rai a bace, "Ya Musa wani abu ne?" Ya tambaye shi yana tsatsare shi da idanu. Shiru suka yi, haka aka gama fadancin aka tashi. Abid yana zaune suna cin abinci da Abdullahi Uzairu ya shigo, ganin shi suka mike. Fita suka yi can Abid ya dawo suka fita da Aaliyah, lokacin ana wanke gidan su, Khamilah kawai ta rage da sauran numfashi itama an jimata rauni sosai, dafe tsohon cikin ta, tayi tana ja da baya. Rike ta yayi, ta fasa ihu tana dukar kirjin shi.
Dakyar aka samu Zinaru tsohuwar kwarkwaran sarki hayatudeen ta rike ta, su kuma aka shiga dasu ana musu sutura, aka wuce da Khamilah gidan me magani, ita kuma Aaliyah haihuwa ce tazo mata bazata, haka suka shige da ita cikin gidan ta bangaren ta na da. "Ya kamata mu dakatar da Ya Musa!" "Ih, kiyayyar Sarki Hayatudeen ne yake fitar da ita, idan muka ce zamu yi amfani da karfi mun yi asara, ka saka a ɓatar da Raudah har abada, yadda babu yadda zata kuma dawowa, ka ɗauke ta ku tafi da ita, can sahara inda babu wanda zai kuma jin labarin ta, kafin ta samu wanda zai bata ruwa da guziri ta jikatta, kunama da macizan sahara sun ishe ta. Shi kuma uban a bar shi da jiran samun labarin ta har karshen rayuwar shi"


"An gama" haka aka yi jana'izar Yarima Shehu da matar shi da Fure, sannan aka zauna jiran tsammanin haihuwar Aaliyah, ta sha wahala kafin ta haifi danta namiji me kama da Ubanshi, sosai aka shiga bata kulawa, inda Abid ya dauke su, suka koma gida. Lokacin da Abdullahi ya dauki Yaron, Kyautah ce ta zo ran shi. Murmushi ya sake yana sumbatar goshin Yaron.
*In sha Allah, sai na dawo maka da ita gare ka* Abid ya fada, yana me ɗaukar alkawarin dawo da Kyautah ga Abdullahi.


Haka suka kwashe kwanaki bakwai, kafin aka wayi gari Raudah ta b'ata, aka nime ta sama da kasa babu labarin, karamin hauka ne ya Musa bai yi ba, amma yayi kuka ya kuma kuka, domin duk abin da ya aikata yaso ita ta amfana shi yasa yake yi koda an kashe shi ita zata rayu da mahaifiyar ta, bakin cikin haka yasa Uwar da bata san lokacin da ta fadi ba, sai gawarta yana ji yana gani aka Kore shi a fadar domin ya tona asirin kan da kan shi da kan shi, zaa kashe shi Abdullahi ya ce a a abar shi yayi ta jiran dawowar Yar shi, Abid da kan shi ya kaita Wurin da taimakon abokin Abdullahi Aljani, suka ajiye ta a wurin suka juyo tana ihu da kuka, tana ji tana gani suka tafi ita kuma tayi ta gararanba a cikin sahara, tun dare har gari ya waye babu inuwa sai rana ko tsillin bishiya babu, haka tayi ta tafiya har rana ta fadi itama ta fadi a wurin. Babu shakka abin da suka shiga suka girba.
***
Jafar Abid Jafar, wanda suke kiran shi da Wazir, suka rad'a mishi suna ranar bakwai din shi da kuma Addu'oin bakwai, haka Abdullahi ya dauki soyayyar duniya ya daura akan Baba Waziri, Domin soyayyar da Baba Waziri ya mishi, Kyautah da alkhairi babu iya, ya kuma gayawa Aaliyah da Khamilah basu da Uban da ya wuce shi.


***
Sai da suka kwashe wata biyu a hanya kafin suka isa Habasha, wanda tafiyar ya saka kara fahimtar wani cikin da Abdullahi ya dirka mata, ta hanyar zuba da yawu da amai, koda suka isa garin Adrin dawa, sun isa bata da lafiya sosai, haka aka yi ta bata kula, tarban da aka musu ya kara sakawa Uwar Bayi fahimtar cewa mahaifiyar Kyautah daga babban gida ta fito, domin bangaren Kyautah da su kawai babba ne, wannan karon ita da kanta ta fahimci ciwon ta har da kamar wani abu da bata fahimta ba, watan su Uwar bayi daya, suka kama hanya domin zasu koma deehar kamar yadda Abid ya umarce su, haka suka barta da kewar su. Wani lokaci sai taji kamar tayi tsuntsuwa ta nufi wurin Abdullahi domin cikin ya saka mata bukatar shi kamar tayi hauka.


Bayan wata biyar cif, Uwar bayi suka isa Deehar, inda suka bawa Abid labarin cikin Kyautah, ai kuwa a ranar ya yanta su tare da hana su shiga ko ina aiki, bayan sati Uku ya tafi habasha dan murna ko yadda zango baya yi, kwana da wuni yake a hanya sai sallah da yake tsayar da shi, a cikin kwanaki arba'in ya isa, lokacin cikin ta yana wata biyar da wasu kwanaki, ya samu ganinta, a lokacin tana kewar su sosai. Domin da tabawa Mahaifiyar ta labarin abin da ya barota can, fada suka mata tare da sauran dangin Maman, sai kuma taji bata Kyauta ba. Koda Abid yaso kuka ta saka mishi.
"Tow ya isa mana, dama nazo ganin ki ne." Ya sake murmushi yana share kwalla, idan ta tuna su haihuwar Baba Waziri suka yi amma har fada Abdullahi daukar shi.yake su shiga yana kan cinyar shi, shima yaron yana son Abdullahi kamar me.
"Kin tafi kin bar shi da kadaici, maraya ne bai da kowa sai Allah sai ke, kece kwarin gwiwar shi amma kika juya mishi baya, Abdullahi ba shi ya kashe Wabi da Uwa ba, shi me son farin cikin ki ne, yana kewar ki sosai wanda baki ba zai iya furta wa ba."
"Kace mishi ya yafe min, nayi mishi kuskuren fahimta, idan Allah ya bani aron kwanaki zan zo gare shi, idan ban rayu ba, ya zo ya dauki ajiyar shi na gode. Kace ina son shi."
Share kwalla yayi shima sannan ya ce mata.
"In sha Allah, zai zo gare ki nan da sati biyu zan koma yau"
"Akwai nisa hanya"
"Sakon ki zai isa kafin gobe in sha Allah "
Haka suka yi sallama, ya ga Mas'udul qaryatu. "Ka biyo ni" murmushi yayi sannan ya ce mishi. "Shugabana ya ce na nimo mishi ina kaje." "Ina son sakon ya isa gobe, shi kuma nan da sati biyu ya tawo"
"An gama shugabana" sannan suka nufi hanya, dafa dokin Abid yayi suka isa wani gari da yake kusa da Deehar, sannan suka cigaba tafiya, sai dare suka shiga Deehar, tunda ya isa gida, ya shiga hutawa da gyaran jikin shi sannan ya nufi dakin matar shi, wacce ta tarbe shi kamar yadda ya dace, bayan sun nutsu ya gaya mata sakon Kyautah. Washi gari suna karyawa da Abdullahi Baba Waziri sai ya rigima yake mishi ya bata mishi kaya, shi kuwa sai kara bashi abinci yake.
"Tace na gaya maka tana sonka sosai, ka yafe mata idan ta samu damar dawowa gare ka, tow idan bata samu ba ka yafe mata" murmushi yayi yana kallon baba waziri.
"Dama waye ya ce maka ina fushi da ita?".
"Dama Uban waye zai ce kana fushi da ita,.naga dai rabon da ka min dariya na manta sai da wannan me sidadden kan" ya zungure Baba Waziri.
"Matsalata da ku,.kishi kai da kanwarka halin ku daya"
"Tabbas shi yasa naji labarin ka saka a fasa nima min auren Yar Fulani ko!"
"Ih, ba zaka tab'a yiwa yata kishiya ba. Tunda kai ma ka hanani yin kwarkwarah "
"Mayen mata"
"Mayun mata zaka ce"
Haka suka koma raha, kowa yaga Abdullahi yasan yana cikin farin ciki, bayan sati biyu ya kama hanyar habasha, ita kanta bata san zai zo ba, amma ta kasance cikin daukin zuwan shi. Da la'asar sakaliya ya isa kofar gidan, ganin shigar shi yasa su fahimtar mijin Kyautah ne, cikin girmamawa aka tarbe shi da kulawa, sai da yaci abinci sannan ta fito ita da Mahaifiyarta da kakanta, dakyar ya rike kanshi suka gaisa, idanun shi yana kanta. Zama tayi a gaban shi, ta dauki hannun shi ta daura akan cikinta. "Ga amanar ka da ban san na tawo da shi ba"
"Sannu na barki da wahala ko?"
"Ranka shi dade, kayi hakuri da abin da tayi"
"An yafe mata" ya fada yana kallon ta, ganin haka yasa suka bar musu wurin, janyota yayi ya shiga sumbatar bakinta.
A hankali ta zare bakinta ta nufi dakin ta, tana rike da hannun shi. Suna shiga ta fara kuka tana gaya mishi ta'asar da ajiyar shi yake sata. Ai kuwa ya shiga rarrashinta,daga nan suka lulla sama jannati. Kwanan su biyar, suka kama hanyar Deehar. Domin iyayen ta basu da matsala Abdullahi ya gaya musu idan ta Haihu da kan shi zai zo ya gaya musu.


***
Kwana goma da dawowan su, aka yi bikin Mulikah da Samir dan Sarkin Musulmi Umar na Sokoto, Radiah kuma ta auri abdulrahman jikar Sarkin rano, Har lokacin Ya Musa yakan tafi bakin kofar Deehar ya zauna jiran yar shi, yawan kukan da yake ya makantar da shi, yana jin labarai akan Abdullahi da Abid da kuma matar Abdullahi da ta dawo.


Bayan wata hudu Kyautah ta sauka lafiya, ta samu Yaranta mace da namiji, a ranar Abid ya nufi habasha, washi gari ya dawo sakamakon kai shi aka yi. Aka dawo dasu da mamanta da kakanta.
Ranar suna Yara sun ci sunan Kubrah da Hayatudeen, an bar su da sunan haihuwar su. Inno tazo ta mata wankar jego, mutanen nahara sun zo suna, bayan sun tafi aka cigaba da kula da ita, sai da suka yi arba'in Maman Kyautah ta koma nahara, ta cigaba da zama, a can haka ya.mata dadi. Ita da Abdullahi suka nufi nahara, kwanan su biyar suka dawo, inda aka kafa sabuwar rayuwa ga Inno kakar shi a tare da shi. Ga Abid Aminin kwarai.


........ Ya Musa har tsufa ta cimma shi babu labarin Raudah haka yana ji baya gani karshen shi bata yi kyauta ba, domin yana shan tozarci a wurin jama'a.


Abdullahi ya gayawa Al'ummar Deehar babu wani tsinuwa da take tab'a al'ummar su, domin sun haifi yara lafiya camfi ne.
Inno ta saka su a daki tana gyara musu jiki.
"Ku dai kula da kyau mazajen su suna bukatar hadin kai ban da gardama" tashi Kyautah tayi tana saka mayafinta ta ce mata.
"Yo Inno ban da abin ki mazan kabilar Noye ai basu daukar wargin mace a shinfida"
"Ja'ira ya koya miki jaraba."
"Inno nima tafiya zan yi Waziri yana jirana "
"Au har dake me hankalin?"
"Hmmm! Mazan kabilar Noye basu da hakuri "


***
Bayan shekara biyu.


Arshan ya dawo Deehar, sakamakon kiran da Abdullahi ya mishi, ya bashi sarautar mahaifin shi na galadima, garkuwa da ya rasu a inda Abid ta ajiye shi Namir dan shi aka bawa muƙamin su, masarautar Deehar ya koma karkashin jagorancin Ƙabilar noye kamar yadda Rana yaso.
A shekarar Kyautah ta kuma haihuwar da namiji, a wannan karon da kanta ta bukaci addinin Musulunci, ta kuma bawa mahaifiyar ta da al'ummar nahara shawaran su musulunta, ganin dibun dukiyar da take zuba musu yasa suka musulunta,.inda Aka sakawa garin Darul Khair. Garin Kyautah ita kuma Abdullahi ya ce a gyara sunanta ya koma Ummul khair domin ita din alkhairi ce.


Zamanta da mijinta gwanin ban sha'awa, haka a bangaren fada kome ya tafi, Fulani Babba haka yaranta suka dauke ta. Kilishi dama ta jima da rasuwa sakamakon jinya. Deehar ya koma kamar yadda Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ya rubuta a wasiyyar shi, na garin ya zama me yanci da ilimin addinin musulunci.


***
Yau ma rakiyar kura suka yi Ya Haruna ya raba su, shima da yake tare da matar shi Uwar bayi.
"Ya isa haka muje na raka ku,"
"Tow" haka ya raka su sannan ya wuce gidan shi.


Yana shiga cikin gidan ya ji tsit, yaran sun yi barci kawai ya nufi ɗakinta tana shan zuma da Madara. Kallon shigar ta kawai yasa shi sussuce ya manta yau fada suka yi dan ta yaye Abid karamin danta, shi ne har da ɗaukar yaron ya kaiwa Abid dazun aka dawo mata da danta. Itama ta shirya bashi ciwon kai.
"Ummul khair" d'ago fararren idanunta tayi, sake sussuce mata yayi.
"Abin da ya faru sharrin shaidan ne"
"Haba tow Allah ya Kyauta" ta ajiye kofi zata wuce ya fincikota.
"Kar ki min horo da jikinki bani da karfin ganin ki haka ina hakuri."
"Cewa kayi dan Allah ya bani haihuwar su bani daya bace me wurin fitar su, Abdullahi ciki nake da shi sai ya sha nonon ciki?"
"Nayi laifi don bani damar na goge laifina" kuka ta saka mishi, daga nan zance ya kare. Tunda macijin shi ya shige ramin shi(🙈🙆🏾‍♀️🙈😹 lolz) shi kenan zance ya kare.


Tammati bihamdalillah in sha Allah ba zaku kuma jina ni daya ba, koda zaku ji ni sai dai da Tawagar Top-notch zamu waiwayen ku bayan sallah idan da nisan kwana. Ku yiwa Shatu fatan Alkhairi watan bikinta kenan,. Allah yasa ayi a Sa'a mu kuma masu abin 🙈🙆🏾‍♀️ Allah ya sauke mu lafiya thank you, musamman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login