Showing 72001 words to 75000 words out of 105295 words

Chapter 25 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6127

ne kika kawo Kanki?"
"A'a"
"Tow meye? Jeki lokacin sallah yayi"
Takowa tayi gaban shi tana me, sunkuyar da kanta a daidai kirjin shi, d'ago kanta yayi yana kallon fuskar ta a cikin duhu, bakin shi ya kai kan nata kamar zai sumbace ta, kuma sai ya fasa.
"Jeki gida ko"
Ya juyar da ita, suka fita har bakin kofar ya tura ta. Ya rufe kofar, yana jin tafiyar ta. Juyawar da zai yi yaji an yanke shi da wuka bayan shi, tafiya yayi kamar zai fadi ya dafe kofar ya tsaya cak. Kashe wutar fitilar dake zauren aka yi, bau motsa ba aka sake tawowa da gudu za a caka mishi. Cikin zafin nama ya kaiwa mutumin mangari.
Can ya hantsila, ya dake zuwa ya shure shi ta daku da bango, sannan ya cigaba da take shi, sai da ya suma kafin ya koma ban daki ya daure ciwon da kyau, buga mishi kofa Abdullahi yayi ya je ya bude mishi kofar.
"Lafiya ya wutar a kashe?"
"Hari aka kawo min, kuma da hadin gwiwar Aaliyah yau sai ta gaya min uban da ya turo ta "
"Idan kuma bata sani ba fa?"
Abdullahi ya tambaye shi, "kasan abin da zaka yi ma tukun? Kunna wutar naga waye?" Kuna wutar suka yi,karshe a gidan suka yi sallah magariba,Abid suka ga ba wani Babba bane yaro ne kuma hannun damar Barde.
"Rabilu ko?"
Gyada kai yayi sannan sunkuyar da kan shi.
"Waye ya aiko ka?"
"Ku kashe ni da son sanin waye ya aiko ni."
"Tare da Aaliyah kuka shigo " ganin yana niman mafita da sauri ya ce.
"Ih, ita ta bude min kofar ma" naushin iska Abid yayi.
"Karya kake Aaliyah ba zata bude maka kofa ba, ka shigo bayan ta mai da kofar ta rufe amma bata san da kana abin bayanta ba."
"Abdullahi idan kuma da hadin bakinta fa?"
"Ba wani fa"
"Tow shi kenan"
"Na bar ka amma tabbas da hannunta."
"Babu hannunta, sharri zai mata "
Take suka hargitsa mishi lissafi ta ha yar musun da suka saba.
"Bata san kome ba" ya furta kallon juna suka yi.
"An bani damar kashe ne, amma bata san ina bibiyar ta ba."
"Waye ya turo ka"
"Idan ba gaya maka wanda ya turo ni, karya ta ni zaku yi dukkan ku rayuwar ku tana cikin hatsari"
"Allah da gaske?" Abdullahi ya tambaye shi yana daukar wukar da yake yashe can, daukar mayafi yayi ya rufe bakin shi. Cikin rashin mutunci Abdullahi ya kama yatsun kafar shi ya yanke su baki daya. Yana jin yadda yake ihu har ya suma. Murmushi yayi sannan ya ce "watsa mishi ruwa."
Abid ya watsa mishi,ai kuwa ya farka yana ihu.
"Gaya min na sake wanke wancan biyar din?"
"A'a wallahi sako aka bani"
"Waye?"
"Barde"
"Dan banza" ya fada yana wurga da wukar, suka fita da Abid.
"Me zamu yi?"
"Uzairu, kaje ka same shi ka gaya mishi ya watsa mana masu bakaken kaya. Kana dawowa kuma zamu shiga cikin gidan."
"Tow"
Tafiya Abid yayi har gidan Uzairu, ya gaya mishi sakon Abdullahi.
"Tow an gama"
Dawowa yayi ya gayawa Abdullahi, murmushi yayi sannan ya ce mishi.
"Mu shiga"
"Tow"
Kashe wutar zauren suka yi, ai kuwa suka kaure da fata har da yankar jikin juna. Garin fadar suka kunce shi, ya fita da gudu bai tsaya ba. Riko hannun Abid Abdullahi yayi suka sake kunna wutar zauren. Waje suka fito ya bace.
"Subhanalillahi sannu" Abid ya fada yana kallon cikin Abdullahi da ya yanka da wuka.
"Kar ka damu aikin ne dole mu dauki kasada"
Rungume shi Abid yayi yana faɗin.
"Na gode"
"Sake ni karka sumbace ni"
Dariya yayi yana jan gashin kanshi. Haka suka sakawa juna magani, suka nufi masallaci.
"Kasan me? Dole zaka sake amfani da wannan damar, domin sake jefa kuri'ar mu inda ya da ce"
"Me fa?"
Tab'a jijjiyar wuyar shi yayi, aikuwa Abid ya zube a wurin, saka hannu yayi ya cire daurin da ya mishi a saman ciwon shi, sannan ya saka hannun shi sai da ya tab'a fatar jini ya fara zuba, shima ya fama na shi ciwon.
"Kayi hakuri dan uwa ba koda yaushe, ake nunawa makiya nasara ba. Kamar yadda suke a haukace haka zamu bi dasu."
Daukar Abid yayi ya wuce masalaci, daidai za a fara sallah kawai aka ga Abdullahi dauke da Abid. Shima kuma ya zube a wurin wanwar, ai a take hankalin mutane ya tashi musamman talakawan da suke zuwa masallacin fada sallah.
"Innalillahi wa'inna alaihil raju'un, hari aka kawo musu? Sun mutu ne?"
"A'a, Ina Ya Musa da Haruna?"
"Lafiya?"
"Su nan" ai hankali tashe aka dauke su zuwa gidan me magani, koda suka isa. Abdullahi yana jin su. Haka suka gama bawa Abid kulawa, Ya Haruna yana tsaye ya Musa kan fita yayi abin shi.
Tashi yayi zaune, me maganin ya ce.
"Ranka shi dade"
"Yallabai!"
"Shii!"
"Ku rufe ciwon Abid ba matsala, ya farka daga gajeriyar suma. Ya Haruna"
"Na'am"
"Ka kula da kyau"
"Tow" haka suka kula da Abid har ya farka, a tare suka yi sallah isha kafin suka koma suka kwanta.
"Meye nufin haka ranka shi dade?"
"Zaku gani "
..........500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
lbishirinku mata masu Duniya mata masu Abin Atata dake nake hajiya idan kinaso kayan gyara yan gaske tau kina da damar ziyar (Dakin Amarya )domin dawo da martabarki kimarki a gurin megida har ma da Aboka huldarki A dakin maryan nane zaki samu 1, garin sabaya me kyau haka kuma Akwai garin lakuse wanda zai gyaraki ciki da wajenki ki koma tamkar halwa jikinki yi luwai luwai fatarki ta goge haka nonuwanki zasu ciko suyi cirko cirko suna tsokanar megida matarda zatayi yaye da yan mata ma duk suna iya Amfani dashi . 2, A Dakin amarya munada mayyukan kamshi da gyaran jiki haka kuma muntanadi mayyukan gyaran gashi akwai hadin buzaye mesa gashi taushi laushi da kuma santsi 3 hakama bangaren kayan mata suma ba'a barmu a baya muna hadin kaya masu inganci akwai hadin kinfi Amarya akwai zumar karya gado akwai hadin sabuzu kuwa akwai hadin dan bagigita akwai kalolin kaza dakuma tsimi da kuma kalolin san matse domin karin bayani sai ku tuntubi wanam Lambar 0805 086 4183 kokuma sakon karta kwana ta wanam lambar a man hajar WhatsApp 08164614675 kokuma saadatusadik@gamil.com sayen nagari maida kudi gida muna aikewa da sako gari gari kuma inganci kayanmu ke sayar dasu da ikon Allah ku garzayo dakin amarya muna nam garin sokoto
....... Hawaye ne ya zubo daga idanun shi, ya gyada mata kai yana faɗin.
"Sun san cewa, kin san abin da suka aikata"
Girgiza mishi kai tayi itama hawaye na zuba mishi, ta ce mishi.
"Babu wanda ya sani, sai ku da nake baku labarin"
"Mu shiga cikin gidan" Abid ya fada yana dafa Abdullahi. Rike hannun juna suka yi, suka shiga cikin gidan. Jin motsin an shigo yasa ta fitowa ganin su tare da Uwar bayi yasa ta sauke ajiyar zuciya.
"Zo nan" Uwar bayi ta kirata, kallon shi tayi taga shima ita yaƙe kallo, idanun shi na zubda kwalla, a rud'e ta isa gaban shi.
"Basamude" janyota yayi jikin shi ya rungume ta, yana kuka kamar Yaro. Duk yadda ka kai da rashin imani idan kaga yadda Abdullahi yaƙe kuka rungume da Kyautah zaka fahimci ya rasa mafita.
"Ya isa haka" itama ta fad'a cikin kuka.
"Nifa an gaya min samudawa basa kuka, me yasa kai kake kuka? Ka tuna da Mama ne?" Sake k'amk'ame ta yayi yana jin kamar tana tuna mishi abin da ya ke mishi kaikaayi, a hankali ta kai hannunta bayan shi ta fara shafa bayan shi har ya fara sauke ajiyar zuciya.
"Tun jiya kake kuka, kanka zai yi ciwo." Ta fada tana janye shi a jikinta, ta dan tab'a goshin sa.
"Zauna na nimo maka magani, zaka yi zazzaɓi." Ta juya da sauri ta nufi ɗakinta.
"Mahaifiyar ka, ta roki Allah ya baka macen da zata kula da kai, Allah sai ya baka wacce ita kanta bata san lokacin da ta samu kanta da fadawa rayuwar ka ba, Abdullahi me ya fi haka dad'i?" Ta tambaye shi, magani ta kawo mishi, ta ajiye tana kallon shi.
Riko hannunta yayi ya zaunar da ita a gefen shi.
"Bude" ya mika mata kunshin kayan, a hankali ta bude tana kallon kayan Kwalliyar matan sarakuna ita a wuyar Fulani Babba ta tab'a ganin irin wannan abin. Dauka yayi ya cire mata na kunnenta, a hankali ya saka mata kome saka mata yake. Jin kunnen ta ya fara nauyi ta ce.
"Basamude waɗannan fa?"
"Kayan Kwalliyar Umman shi ce, ta ce a baki." Uwar bayi ta fada tana kallonta. Wani irin abu ne ya tsaya mata a rai, kafin ta janye jikinta a na shi tana kallon shi.
Hannunta ta kai fuskar shi tana faɗin.
"Idan na mutu, haka zaka yi kukan kewata?"
Rufe mata baki yayi yana faɗin.
"Zan sab'a miki, hakkina nima miki lafiya." Ya fada yana kara rike hannunta.
"Uwar Bayi, yanzu muna shirin kai farmaki ne meye tunanin ki?" Shiru tayi kafin ta ce musu.
"Yaki dan zamba ne, idan kuka bisu da karfin gaske ba zaku yi nasara ba, domin duk da basa shiri da juna zasu taimakawa juna, don haka a shawarce. Ku zama irin su ku koyi halin su ta nan ne zaku fanshe abin da suka muku, ga damar haka ta same ka, domin haka sai ka kara himma "


Ta mike tana faɗin.
"Mahaifiyar ka tana da saka rai akan zaka iya, ni kuma ina da saka ran samun nasarar ku don Allah kar ku fadi domin sauran sun fadi sau babu adadi kafin suka yi nasarar samun ku. Abid Mahaifinka yasan zaka dawo zaka taya shi kar yarda haka ya kwace tsammanin shi." Gyada mata suka yi, tana fita kusan sai suka bawa Kyautah tausayi, bayan tafiyar Uwar bayi ta shiga madafi dauko abinci.
"Itama Uwar bayin ba abin yarda bace, domin zata iya nuna mana tausayawa daga baya ta koma jikin su."
"Sai dai ko babu kome ta nuna mana hanyar daukar mataki, me ka gani?" Abid ya tambaye shi.
"Ih, da haka amma kuma ba zama nata zamu yi aiki da shi ba."
"Me ka shirya "
"Makirci "
Kallon juna suka yi, sannan ya mike tare da cewa.
"Da gaske?"
"Ka shirya?"
"Na shirya " fitowa tayi da tire, dauke da kaza gefe madara ce.
"Gashi zaku tafi na kawo "
"Zauna kaci Abid"
"Sai dai ka zauna muci "
"Tow shi kenan "
Zama suka yi suna ci Abdullahi yana bashi labarin abin da zasu aikata, sai gyada yake yana murmushin mugunta.
***
"Barde da sauran su, sun b'ata sakamakon harin da aka kai Ya Haruna kai da Me magani ne a wurin, taya suka b'ata babu alamar su?"
"Ni ban san me ya faru ba, kuma dama an kai musu hari ne su Abdullahi kenan dama."
"A'a ba yadda kake tsammani bane"
"Tow, gaskiya daga ni har me magani muna wurin domin anan na kwana"
"Ikon Allah, shi kenan tashi ku je"
Haka suka tashi suka bar shashin Fulani Babba. Wacce hankalinta yake tashe.
Suna zaune Abdullahi da Abid suka shigo cikin gidan, zama suka yi suna kallon Fulani Babba.
"Fulani Babba!"
Abid ya kira sunanta sannan ya ce mata.
"Abdullahi yana son a bashi auren Radiah "
Shiru suka yi domin basu kawo kome a ransu ba,kuma Abdullahi shammatar su yayi a lokacin.
"Auren Radiah? Tow Mulikah fa?"
"Ita ai ba cewa yayi yana sonta ba, cusa mishi ita aka yi"
"Tow mun fahimta ai dama dole wata rana ya dawo Niman ta, tunda yar uwar shi ce."
"Tow an bashi ita an bashi amma ya zaka yi da Mulikah?" sai lokacin Fulani Babba tayi magana.
"Ni kawai Baba Galadima ya shiga maganar ya gayawa Garkuwa na fasa"
"Aikuwa tunda baka so, babu dan iskan da zai maka auren dole dan haka ka tafi zamu ji da Garkuwa. Kaji kar ka damu, kuma zamu saka a baka tsaro yadda babu me cutar da kai"
gyada kai yayi suka sannan kafin suka bar gidan.
A hankali suke tafiya suna tattaunawa, suka hadu da Ya Musa.
Sam fuskar shi bai nuna alamar damuwa, firgicin shi a cikin idanun shi zaka hango ba a kan fuskar shi ba, domin ya iya boye b'acin ran shi.
Shi kuma Abdullahi kuntatta musu yake son yi, domin haka ba tare da sun kawo kome a ransu ba, suka tsaya suka gaisa, sannan suka wuce abin su.
"Idan na ga mutumin nan ko? Hmm"
"Me zaka mishi?"
"Kashe mara mutunci mana" ya fada yana jin kamar ya kamo ya musa ya mishi yankar rago.
"Tow a danna kiyayyar ka, in sha Allah wannan zuwan zai zame musu tashin hankali"
Haka suka iso gidan, tun a bakin kofar Abid suka ga Ya Haruna.
Shiga cikin gidan suka yi sannan suka ce.
"Sun tambaye ka ba?"
"Ih, tow yanzu ma wai garkuwa da Chiroma suna nima na a fada"
"Kar ka razana, nima hujja suke kuma dole sai an samu gawarwarkin ai ko? Su kuma Uzairu ya kai su inda ya da ce, koda sun samu gawarwarkin kawai zasu gani ne amma babu yadda za su yi damu,domin basu da hujjar kama mu"
"Yawwa Yaran albarka bari naje"
"A'a muje dai"
Haka suka kuma Fitowa suna nufi fada, inda ake zaman jiran su. Har suka isa hankalin shi kwance, kamar ba su ba.
Sai da ya shiga kafin suka bi bayan shi, suka zauna suna masu mika gaisuwa.
"Ya Haruna, jiya mun samu labarin an kai muku hari da fatan babu abin da ya same muku, domin mun saka a kamo maharan?"
A rikice Abid ya mike yana rawan jiki.
"Mu za a kashe? Me muka yi musu? Innalilahi Abdullahi mu bar Deehar kar a kashe mu"
Murmushi Abdullahi yayi yana faɗin.
"Tow kai tsoron me kake ji?"
"Tsoron kar na mutu, tuzuru ban yi aure ba"
Shiru fadar ya dauka.
"Ya Haruna, baka ce kome ba"
"Gaskiya daren jiya ina tare da su, babu inda na tafi har asuba yayi suka koma gidajensu."
"Tow kuwa su Barde..."
"Kenan daga fadar deehar aka tura su, kashe mu?" Abid ya tambaye su.
"Saurin me kake Abid"
Abdullahi ya riko hannun shi yana kallon Chiroma.
"Kenan daga nan aka tura su?"
"A'a Abid ba daga nan bane, kawai ba a ga Barde da tawagar su bane, kamar yadda ya faru lokacin da aka tura su kashe Kubrah da Ya Musa da D'anta? Sannan anya Kubrah mutuwa tayi a ranar?"
Kallon jjna suke a rikice, kamar yadda ba su zata maganar zata fito daga bakin shi ba.
"Koda yake a wancan lokacin nasan za ayi bincike a nime mutanen da suka kashe su, amma ai naji labarin Waziri Jafar a gaban jama'a aka kashe shi, shima babu tabbas ko? Tow jibi za a daura auren mu, daga yau a fara binciken inda Barde da tawagarsa."


Kamar waɗanda aka watsa musu ruwa suka yi jungun-jungun, haka kasance kafin Abdullahi ya mike zai tafi sai ga Garkuwa da Galadima, sai zagin juna suke,


"Abdullahi wai da gaske baka son Mulikah?" Garkuwa ya tambaye shi,
"Wai kai wani irin jahili ne, ana yi dole ne tow ba zai auri Yarka ba, matukar ina raye, na gaya maka kai tashi ka tafi kar a sauya maka ra'ayi"


Kiri-kiri galadima ya hana Garkuwa magana da Abdullahi, domin Galadima gani yake matukar garkuwa yayi magana da Abdullahi zai fasa auren yar shi.
"Abdullahi kar ka min haka, ka haɗa su dukkan ka aura" shiru suka yi yana kallon yadda fuskar Abdullahi take, kawai Abid ya ce.
"Tow ai ba matsala tunda shi din jinin Noyewa ne yake yawo a jikin shi, dan haka biyu lokaci guda duk Allah zai taya shi riko, tunda halaliyar shi ne, ba matan mutane zai bi ba. Dan ma sun rika da yawa amma ai yadda ake bamu labarin Fulani Umma Kubrah yarinya ce shakaf kamar Kyautah ga kyau ga yan matanci"


"Ni gaskiya ba zan auri mata biyu lokaci guda ba, sai dai dukkan su. Su hakura."
Wayyo Allah garkuwa kamar zai fashe da kuka ya ce.
"Abdullahi kar ka min haka, duk da bamu yin Hayatudeen amma wallahi mutum ne me nagarta bai taba sauya ra'ayinsa ba."


"Eyye domin ya amince ya auri Yarka shine zaka gaya mishi labarin Hayatudeen tow kayi a banza domin ba jin ka zai yi ba na gaya maka"
"Mahaukacin kare kawai"
"Waye mahaukacin kare? Tow wallahi ba za ayi auren da Yarka ba, tawowa matar cushe kawai"
"Galadima Ya ishe ka, ba da kai nake ba da Abdullahi nake"
"Na sayi fadar da ni kake"
"Banza Mugu mara imani"
"Ni kake zagi Garkuwa? Banza maciyi amana"
Take fadar ta kaure da balalin fada kowa sai.zagin dan uwansa yake, su kansu Chiroma abin ya sha kansu, dakyar Abdullahi ya shiga tsakiyar su ya ce musu.
"Ku bani yau da gobe" ya fada bayan ya mike a hankali, Abid ya ce.
"Duk da haka bai hana wasu kashe shi ba." Suka fita abin su. Idanun kowa yayi waje. Kowa a ranshi tambaya yake a ina yaran suke samun magana haka suke fada musu.
Suna fita aka fara sa'in'sa a fadar baki dayan su fada suke, kamar zasu kashe junan su. Domin rayukan su ya b'aci garkuwa yana ganin kamar Galadima ya tona musu asiri ne.
Abid da Abdullahi kuwa tafawa suka yi suna faɗin.
"Mahaukata domin rufe hujja shi ne suke fada kamar zasu kashe kansu."
"Yanzu aka fara....
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
lbishirinku mata masu Duniya mata masu Abin Atata dake nake hajiya idan kinaso kayan gyara yan gaske tau kina da damar ziyar (Dakin Amarya )domin dawo da martabarki kimarki a gurin megida har ma da Aboka huldarki A dakin maryan nane zaki samu 1, garin sabaya me kyau haka kuma Akwai garin lakuse wanda zai gyaraki ciki da wajenki ki koma tamkar halwa jikinki yi luwai luwai fatarki ta goge haka nonuwanki zasu ciko suyi cirko cirko suna tsokanar megida matarda zatayi yaye da yan mata ma duk suna iya Amfani dashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login