Showing 24001 words to 27000 words out of 239422 words
Chapter 9 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
kunya haka suke lodawa cikinsu abinci, sam baruwansu da wani surkuntaka, saboda sunaganin duk suɗin ƴan uwan junane, haka kuma Ummi mahaifiyace agaresu, saboda haka babu wani batun noƙe-noƙe, duk da cewar ansan fulani da kunya, saidai sabo da kuma zumuncin dake tsakaninsu ya goge wannan kunyan.
Cikin mamaki yake kallonsu don sam basu sanar dashi zuwansu ba.
Ƙarasowa cikin falon yayi, inda yakai hannu ya zunguri Ishaq wanda ke ta faman suɗe hannunsa wanda yaci masa dashi, bakomai yasashi suɗe hannunba kuwa face daɗin miyar masan, shikam har yau baiga macen da takai Ummin Saifuddeen iya girki ba.
Ishaq kuwa cikin gane wanda ya zungureshi yace. "Banason wulaƙanci fa Saifuddeen, wato wulaƙanci zaka mana saboda mun riga mun damƙa maka amaryarka a hannunka ko?."
Gaba ɗayansu sukayi murmushi inda Saminu yace.
"Manta dashi da Allah, nasan bazai wuce haushinmu yakeji ba, kasan dai Saifuddeen sakaline baison wani ya raɓi masa Umminsa, kuma mumadai Ummin nan nasonmu."
Saminu yaƙare maganar yana me kai loman gandar fatan saniya, wanda yaji haɗi sosai, sai ƙamshin su kanumfari yake.
Kai Ahmad ya girgiza tare da duban Saminu cikin yanayi na tsokana yace.
"Surkinka nefa Yayan matarka."
Hararansa Saminu yayi tare da cewa.
"Kamanta tare mukai wasan ƙasa."
Dukansu suka saka dariya, banda Saifuddeen wanda shi kullum murmushine aikinsa, da haka yasaba kuma hakan yafi yi masa kyau, aduk sanda yayi murmushi idan kumatunsa da tsakiyar gemunshi da goshinsa suka lotsa, sai yayi wani irin fitinannen kyau.
Dai-dai lokacin Ummi da Goggo Dada suka fito daga cikin kitchine, bayansu kuwa Raliya ce riƙe da plate, wanda samansa ke shaƙe da yankakkun kayan fruits, agabansu ta dire musu plate ɗin, duban Ummi Saifuddeen yayi tare da shagwaɓe fuskarsa, cikin body language ɗinsa yayi mata alama da cewa.
"Shine kika wahalar da kanki wajen haɗawa waƴannan ƙattin abun karin kumallo ko bayan ga matansu!."
Gane abunda yake nufi yasanya Ummi sakin murmushi, ƙarasowa cikin falon tayi tare da sanya hannu ta shafi lallausan suman kansa, cikin kulawa tace.
"Ae duk al'barkacin aurenka sukeci."
Jin abun da Ummin nasa tafaɗa yasanyashi sakin murmushi, idanunsa ya ɗan lumshe, ahankali ya dubi Goggo Dada nan yayi mata alamun gaisuwa, da fara'a ɗauke akan fuskarta ta amsa, tare da ƙarayi masa murnar biki.
Nan suka zauna inda suka shiga ɗan taɓa hira kaɗan, su Hisham na gama kammala cin abincin Goggo Dada tasanar dasu cewa zasu buɗe kan ango da amarya tunda dai jiya bata samu taje wajen diner ɗinba, nan dukansu sukayi na'am, inda Aunty Meenat ma da fitowarta daga ɗakin Ummi kenan tace itama zata yiwa ango nasa liƙin, su Adda Rahama da Raihana ne suka firfito falon, nan fa Ummi tace da Raihana taje ta ƙirawo amarya.
Zaleeha kuwa har zuwa yanzu suna tare da Balkeesu, inda Balkeesu ke ƙara fomfata tana kuma kunnata akan kada ta gudu ta tsaya ta fetsarewa mutanen gidan ta yadda uwarshi da kanta zatasa ya saketa shi kuma ta nuna kasheshi zatayi, ita dai Zaleeha abun daya dameta ne ya isheta don wannan karon dai zugar bilkeesu ba abar ɗaukar mai hankali bane, to bare kuma asirin Mama ya riga zugar tasiri.
Ƙoƙarin kwanciya take, sukajiyo knocking door, azaton Zaleeha Zaheera dake kallo afalo ne hakan yasa tace.
"Yes come in."
Ahankali Raihana tatura ƙofar ɗakin tashiga, ganin Raihana yasa Zaleeha ɗan sakin fuskanta, duk da batasan wacece ita ba, amma kallo ɗaya tayi mata ta hango matsanancin kaman da sukeyi da Aljanin gurgun da tsanarsa tayi mata tsaye acikin rai sosai ta yaba da kyan Raihana kuma har ranta taji tana sonta.
Balkeesu kuwa baki tasake tana ƙarewa Raihanan kallo, gaba ɗayama hankalinta yatafi ga tsadadden zanin dake jikin Raihana'n, domin kuwa babban Chiganvy ne ɗan ubansu.
Murmushi Raihana tayi tare da duban Zaleeha cikin kulawa tace.
"Idan babu damuwa muna buƙatarki afalo, za'a ɗanyi muku buɗan kai ne!."
Dammm haka Zaleeha taji ƙirjinta ya doka, sam batason abun dazai ƙara haɗata dashi, musamman idan ta tuna da abun daya shiga tsakaninsu jiya saitaji kanta kamar zai buga gaba ɗaya tsoro lamarinshi ke bata.
Cikin baƙinciki da takaici Balkeesu tace.
"Mezai hanamu zuwa kuwa, ai zamuzo yanzun nan." tafaɗa tana me miƙewa tsaye dan samawa Zaleeha mayafi, ɗan murmushi Raihana tayi tare da cewa.
"Badamuwa, ai bama sai kunzo ku dukanku ba, itaɗin dai kawai muke buƙata!."
ta ƙarishe mgnar cikin yatsina fuska dan sam ita da Bilkeesu bata konta mataba, Zaleehan kanta a fakaice take sonta tunda ance bata son Hammanta ita kuwa duk wanda yace baison Hamma Saifuddeen ɗinta itama bazata sotaba.
Ƙasake Balkeesu tayi tare da watsawa Raihana harara ƙasa-ƙasa, tabbas maganace afakaice Raihanan ta faɗa mata, amma dai koma menene ta rantse saitaje anyi buɗan kan da'ita.
Wani tsantsareren mayafi laffaya Zaleeha ta yafa aduka jikinta inda ya sauƙo ya rufe har fuskarta, wani flat shoe kalan yadin jikinta ta sanya aƙafafunta, Raihana da kanta taƙara fesa mata turare nan Balkeesu uwar gulma tariƙe Zaleehan, Raihana na gaba sukuma suna biye da ita abaya haka suka nufi cikin gidan.
Sunanan zaune afalo suna ɗan taɓa hira, daddaɗan ƙamshin daya ziyarci hancinsa shiyafara sanar masa da zuwanta, juyawan dazaiyi kuwa ya hangota cikin wani light orrange ɗin mayafin laffaya mai tsananin kyaun gaske, sai walwali da sheƙi yake, Raihana da kanta ta kamo Zaleehan, inda ta zaunar da ita akan kujeran dake facing na Saifuddeen ɗin, tsulum Balkeesu daketa faman ƙarewa falon kallo tazo ta zauna akusa da ita, sosai Balkeesu tasha mamakin haɗuwan falon, wanda kuma yake mallakin Ummi, sam abubuwan mutanen suna shammatan ta, kwata-kwata bata taɓa tunanin yawan arzikinsu har yakai haka ba, duk abun da sukayi takan ɗauka, ƙaryane kawai da fafa, wani abun kuwa takanyi tunanin sunayinshi ne kawai don su mallaki Zaleehan, saidai kuma tunaninta ya fara sauyawa ne tun lokacin da aka kawo Zaleehan gidan, yanzu kam tagama yarda cewa suɗin masu arziki ne, duba da irin kuɗin da aka kashe wajen ƙawatawa Ummin nasu falonta, uwa uba ga ƴan uwan Saifuddeen ɗin da ako yaushe suke cikin sutura mai kyau, da shiga ta al'farma domin kab cikinsu babu wacce take sanye da ƙasa da kayan dubu ashirin, saima yayi sama, kowa kagani acikinsu masha Allah, Gaba ɗayansu cikin jindaɗi da rufin asiri suke rayuwarsu gasu kyawawane ajin forko, duban Adda Rahama wanda ke sanye da wani jan leshi mai shegen tsada tayi, taɓe baki tayi, cikin ranta tace "Ƴan iska, kowa kagani cikin farinciki yake, badai Saifuddeen shine farincikin ku ba, hmmm ai na gano lagonsa, rashin Zaleeha shine baƙin cikinsa, kukuma baƙin cikinsa shine tashin hankalinku, to kuwa kushiryawa tashin hankali, don wallahi al'ƙawari nayi sai nasa Zaleeha tasa ya saketa saki mafi muni kafin insata ta gudu daga gidannan."
ƙasa-ƙasa tayi ƙwafa, tare da cigaba da ƙare musu kallo.
ita kuwa Zaleeha shiru tayi kanta a sunkuye ta cikin mayafin ta zubawa ƙafafun Saifuddeen ido, wanda suke ƙal-ƙal kana daga ganinsu zasuyi tsananin laushi da taushi kodan hakan bazai rasa nasaba da rashin takawarsuba daga ganin fatar tiɓis zatayishi laushi, yatsunshi ta zurawa ido tana kallonsu tamkar ka taɓasu jini ya tsallo kan faratun yatsun nashi ta maida idanunta ganinsu ƙal-ƙal yasata ɗan kauda idonta, a ranta take tajjudin yawan tsabta na wannan nakasasshen aljanin yakeda shi sabida ita fa tana alaƙanta kyan Saifuddeen da iska, takalmanshi dake gefe ta kalla wanda suke na Gucci a tsiwace cikin ranta tace,
"Hmmmm gurgu kafi mai ƙafa iya shege, shi komai nashi mai tsada, wannan da lafiyarsa lau, alla'anɗi iya ƙasaitar da zai zuba.
Shi kuwa Saifuddeen kota kanta baibiba hira yake da abokanshi.
Bilkeesu kuwa sam bata tsinke da al'amarin nasu ba saida taga yanda Ummi da kuma Goggo Dada ke yiwa Saifuddeen ɗin ɓarin kuɗi, sosai suka zuba masa kuɗi, inda Aunty Meenat ma tazuba masa nata, nanfa kuma suka dawo kan Zaleeha, Goggo Dada ne tasa Raliya ta buɗe mata mayafin, nanfa suka shiga zuba mata kuɗi itama, sosai suka zuba mata nairori, Ummi ne ta dubi Raliya inda tace taje ɗaki akwai wani gift da ta ajiye akan gado ta ɗauko mata, babu ɓata lokaci kuwa saiga Raliya ta dawo, hannunta ɗauke da wani ƙaton gift wanda aka masa ado da pink flowers, sosai yayi kyau, hannun Zaleeha Ummi takamo inda ta sanya mata babban gift ɗin cikin nutsuwa tace.
"Wannan tukuici ne agareki na zamantowa matar ɗana da kikayi, Allah Ubangiji yayiwa rayuwar aurenku al'barka, sannan yabaku zuri'a ta gari tare da zaman lafiya mai ɗorewa."
Gaba ɗaya jama'an wajen suka amsa da Ameen, saidai banda Zaleeha, sai kanta data sunkuyar alamun jin kunya, kana tanata wasa da yatsun hannunta.
Sosai Ummi taji ƙaunar ƴarinyar a ranta komai da nitsuwa da kunya take yinshi.
Balkeesu kuwa da ƙarfi tafaɗi Ameen ɗin, wanda hakan kuwa da biyu tayishi, sam bataso sugane cewa itaɗin munafukace, don tafuskanci cewa kamar, Raihana ta ganota.
Haka suka gamayi musu buɗan kaiɗin cikin nuna ƙauna, Balkeesu ne tajata suka koma part ɗinta bayan duk an haɗa mata kuɗin.
Su kuwa su Saifuddeen anan falon Ummin sukaci gaba da zama.
Suna shiga cikin ɗaki, Balkeesu wanda jikinta ke mazari ta amshi gift ɗin, hannunta har rawa yake wajen ƙoƙarin buɗewa.
Zaleeha kuwa mayafin dake jikinta ta yaye, cikin ƙunan zuciya tayi wurgi da mayafin, faɗawa kan gado tayi tare da lumshe idanunta, sam batajin tsanar kowa dake cikin gidan saishi kaɗai haka nan taji tana so duk mutanen gidan sabida ta lura sunada karamci da mutunci kuma sunfi ƙarfi tijara koda da ƙwayar zarrane a wurinta.
Ihun da Balkeesu tayi shiyasanya Zaleehan ɗagowa da sauri ta dubi Balkeesun, cikin yanayin mamaki haɗi da firgita Balkeesu tace.
"Gold, Zaleeha Gold ne fa aciki da kuma turaruka masu tsada ga kuɗin duk ke akabarwa."
Wani haɗaɗɗen kwalban turare Balkeesun ta zaro tare da cewa.
"Zaleeha kinkuwa san kuɗin wannan turaren?, oh my God ashe waƴannan mutanen masu kuɗine sosai har haka!!."
Wani dan ƙareren agogo da sarƙan gold Balkeesun ta ciro, wanda aka ƙawata gidansu da wani farin glass, cike da mamaki tace.
"Lallai kuwa mutanen nan sunshiryawa auren nan, what a surprise."
Kallon sarƙa da agogon Zaleeha tayi, wanda lokaci ɗaya sukayi bala'in yi mata kyau, amma ayanda takejin zuciyarta yasa bata nuna ba, maida kanta jikin pillow kawai tayi tare da lumshe idanunta, abun daya dameta shine aranta ita kuɗinsu baya gabanta.
Balkeesu kuwa kaman Zararriya haka ta dinga yaba kayan, saida tagaji don kanta sannan tayi shiru, nan kumafa zuciyar hassadan nata ta motsa, take taji wani danƙareren baƙin ciki ya cika zuciyarta, inama da ace itace tasamu wannan kayan more rayuwa haka? wai ma shin maiyasa ita rayuwa bata zuwar mata da garaɓasa haka? lallaima dole ne taraba Zaleeha da wannan gidan, idan bahaka ba tanaji tanagani zasu maida Zaleeha millionaire girl, ita tananan zaune Zaleeha zata shiga cikin sahun manyan mata, wanda kokaɗan kuwa ita bata fatan haka, dole ne ma taƙara zuga Zaleeha akan batun a sakin kafin guduwarta, don kuwa ayau ɗin ta hango irin tsananin soyayyar da dangin Saifuddeen ɗin keyi masa, tabbas ayanda tafahimta ayanda suke masifar sonsa, to zasu iya ɓatawa da duk wani wanda ya ɓata masa, dakuwa zasu tsani Zaleeha da tafi kowa murna.
Saboda tsananin ƙyashi da hassadan dayaci Balkeesu kasa cigaba da zama agidan tayi, lokaci guda tayiwa Zaleehan Sallama inda takoma gida, zuciyarta cike da saƙe-saƙe kala-kala.
Tun wannan fitowan da Zaleeha tayi na zuwa buɗan kai, daganan bata sake fitowa ko falo ba, abincin da aka kawo mata ma har ɗaki, Raliya takawo mata ta ajiye, sam kasa cin abincin tayi, Zaheera ce taci inda tacika cikinta, itakam babu abun daya shallaketa, tanajin daɗin zaman gidan, babu wani takura, dagaci sai kallo, dama ita tanan tafi kauri, aiki ko na misƙala zarratinne basonshi take ba, wannan dalilin ma yana ɗaya daga cikin abun dayasa ta ƙi komawa gida, domin tasan da zaran takoma tofa aiki za'aita sakata kamar jaka, itakuwa sam bason hakan take ba, ga shi Ziyada ba zama take ba, always tana gidan Hajja ga Zaleeha dake yawan yin wasu aiyukan kuma an aurarta.
Saifuddeen kuwa gaba ɗaya wunin yau dasu Ishaq yayisa, don sosai suka zauna don ɗebe masa kewa, kasancewar acikinsu babu wanda baisan matsayin auren Saifuddeen da Zaleehan ba, kowa yasan baso takeyi ba, dan haka nan suka wuni sai dare suka tattafi.
Koda Yadawo sallan Isha, kai tsaye falonsa ya wuce, koda yazo falonta ko ƙofar ɗakinta bai kalla ba, dan shima yau ƴan jan ajinnasa suna kusa, duk dacewa yana da buƙatar jinta ajikinsa, amma dole haka zai daure, dan yasan koda yaje ma tofa faɗa zasuyi, shikuwa bayanzu yakeson yafara gwada mata ƴar ƙarfi ba.
Koda yashiga haɗaɗɗen bedroom ɗinsa wanka yayi, inda ya kimtsa kansa cikin kayan baccinsa, kwanciya yayi tare da jawo laptop ɗinsa, nan yayi ƴan danne danne, a hankali ya zubawa system ɗin ido, yana kallon motar nan da yasa Hayatuddeen ya liƙa mata na'ura tana tafe har gidan da ta shiga,
yaga matasan baki ɗaya sai kuma duk sukayi cikin gidan hakanne ya hanashi damar ganin abinda ke faruwa a cikin gidan. bincike yaci gaba da yi akan gidan da matasan har saida ya samu iya abinda zai samu to amman har yanzu babu ƙwaƙran laifin da za'a kamasu dumu-dumu a ciki haka dai ya haɗa abinda ya samu,
kafun daga bisani bacci ɓarawo ya ɗaukesa.
A cikin gidan Dalla kuwa,koda yaranshi suka gama yi mishi bayanin abinda ya faru,
cikin tsananin tashin hankali yace.
"To meyasa!? Waya ɓata min tsarina!? ya akayi haka ta faru?."
sai ya kuma shaƙo wuyan Lado dake gabanshi cikin rashin imani yace.
"Shekara ɗaya cur ban fatattaka ƴar kowaba, nace muku babu ƴar da zan taɓa a kanta nakeso na gwada lafiyata, meyasa zakuyi min kuskuren da har wani ya gane ya bata tsaro, nafa ce muku a buƙace nake."
ingiza Lado yayo ganin yana kakarin mutuwa, shi kuwa Lado tari ya rinƙayi ba sassauci.
yayinda gaba ɗaya sauran yaran suka sha jinin jikinsu,
shiko Dalla safa da marwa ya farayi a kansu yana wani irin numfashin masifa da tijara da ƙwarewa a dabanci cikin yaƙini da kansho murya a hargitse yace.
"Wallahi wallahi sai na girgiza zuƙatan gombawa sai kowa yaji kwatankwacin baƙin cikin da naji, na rantse da ubangijin dake busan numfashi sai na keta haddin ƴan mata huɗu a wuni ɗaya shine fansar budurcin shegiyar yarinyar nan da a kanta wannan sojan yamin dandatsan ɗan akuya."
wata iriyar wawuyar tsawa ya tamfatsa musu tare da cewa.
"Dole ku nemo min zuƙa-zuƙan ƴan mata huɗu dan na gwada lafiyata a kansu." cikin biyayya da tsoro sukace,
"An gama." shi kuwa Dalla a harzuƙe yace.
"Ku nemo min su daga yau zuwa mako biyu rak,
ita kuwa shegiyar yarinyar nan dan nasan ba namijin da za'a kaiwa ita ya kwana da ita ɗaki ɗaya bai ratsa budurcinta ba,
dan haka na ɗage neman har sai nanda wani lokacin zan nemeta in mata fyaɗe mafi muni irin fyaɗen da ban taɓa yiwa ƴar kowaba, zan kwana akanta, kuma kuma kowa sai yayi awa biyu a kanta wannan ganimar samotane."
cikin jin daɗin ganimar daya alƙawaranta musu, suka sallameshi suka tafi.
A can ɗakin Zaleeha kuwa, duk yanda taso bacci ya ɗauketa abun yaci tura, tayi juyin harta gaji amma bacci yaƙi ɗaukarta, gaba ɗaya zuciyarta cike take da tunani kala-kala, sosai soyayyarsa ke ƙara yawaita acikin zuciyarta, duk wannan rububin da akeyi da sonsa take kwana take tashi, har zuwa yau batacire rai da samunsa ba, tasa aranta cewa komin daɗewa watarana zata gansa.
Tashi zaune tayi ji take kamar korata akeyi daga cikin ɗakin sam bata samu tayi isshen bacci, gyara zamanta tayi tare dakai dubanta ga Zaheera wacce ke kwance akan kujera tanata sharar baccinta, inda tayi ɗai-ɗai da ƙafafunta, ahankali ta dawo da dubanta ga jikinta, sanye take da wata fitinanniyar sleeping gown, irin mai fitar da surar jiki ɗinnan, sosai rigan dake da kalan coffee ta amshi farar fatarta, daga wuyan rigar har zuwa kan ƙirjinta gaba ɗaya net ne irin mai showing skin ɗinnan, yayinda kwata-kwata tsayin rigar yakasance iya cinyarta ne, hannu tasa taɗan shafi dogon gashinta dake baje bisa kafaɗunta, ahankali ta zuro da ƙafafunta ƙasa, tashi daga kan gadon tayi tare da miƙewa tsaye.
gaba ɗaya jin ɗakin take ya mata ƙunci, ahankali take tafiya harta ƙarasa jikin ƙofar fita daga ɗakin, ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar tare da sanya key ta buɗe ƙofar, cikin nutsuwa tafito zuwa falo, ahankali take ɗan takawa harzuwa tsakiyan falon nan taɗan shiga ƙarewa falon kallo, sai alokacinne ma take yaba tsantsar kyawun kayan da Yaya Ahmad ɗin ya saya ma, taga masifar tsaruwar ginin falon, amma saboda yakasance mallaki ga Saifuddeen yasa, ko kaɗan bataji zata yaba tsarin falon da gidan ba, ƙarasawa jikin window'n falon tayi ta tsaya, ahankali taɗan buɗe glass ɗin window'n, take wani irin ni'inmtaccen ƙamshi haɗi da sanyin shuke shuken dake wajen suka daki fuskarta, lumshe idanunta tayi tare da sake manna jikinta da bango tana shaƙan ƙamshin...
Saifuddeen kuwa wani iri fitinannan ƙishine ya tasoshi gaba cikin baccinsa.
Ahankali Yake buɗe kyawawan idanunsa, hakanan yaji wani irin sanyi na ratsa zuciyarsa, sake buɗe idanunsa yayi tare da sauƙesu akan agogon bangon dake saƙale cikin ɗakin. 1:40 am agogon ya nuna, hakanne yasashi ɗan tashi ya zauna, mamakin farkawarsa adai-dai wannan lokacin yake, jin masifan ƙishirwa na damunsa yajawo kekensa inda ya hau, ya zauna ɗas a kai ya tura kansa har zuwa gaban ɗan madaidaicin fridge din dake cikin ɗakin, koda ya buɗe fridge ɗin gani yayi babu ruwa, gaba ɗaya drinks ne suka cika fridge'n, dolensa haka ya murɗa handle ɗin kofar ɗakin inda yanufi falonsa.
Gaban fridgen dake cikin falon ya ƙarasa, inda ya buɗe ya ɗauki goran ruwa, ahankali ya ɓalle murfin tare dakai goran bakinsa, sosai yasha ruwan saida yaji ya ƙoshi kafun ya aje goran, aƙoƙarinsa na komawa ɗakinsa ne idanunsa suka gane masa haske acikin falon Zaleeha, kansa kawai ya girgiza, har zai koma ɗaki kuma, saiya tuna da cewa baya son abar ƙwan wuta akunne matuƙar za'a kwanta yana da kyau adinga kashe ƙoyayen wuta.
Ahankali yaƙarasa jikin ƙofar falon nasa ya buɗe, kekensa ya danna inda yaƙaraso zuwa falon nata, idanunsa ne sukayi masa tozali da bayanta, inda har yanzu take tsaye jikin window.
Kallonta yasomayi tundaga ƙasa, santala santalan