Showing 6001 words to 9000 words out of 239422 words

Chapter 3 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11836

shirye-shiryen hidiman biki ne yasanya basu damu ba, don atunaninsu wani uzurine wanda ya shafi bikin zai kaita Dukkun.
Haka Ummi tayi sallama da su, inda dukansu suka rakota har compound ɗin gidan.
Saida suka ga tafiyarta kafun su dukansu suka koma cikin gida.


Kusan ƙarfe shabiyu da wasu ƴan mintuna Ummi suka iso cikin garin na Dukku me al'barka.
Kaitsaye gidan Bappa Ali suka sauƙa.
Sosai Aunty Mina tayi murnar ganin Ummin, nanfa lokaci ɗaya tacika mata gabanta da kayan ciye ciye, hadda dangin su fura da nono,
Sosai Ummi da Auntyn ke shan hiransu, kasancewar Bappa Alin bayanan, sunje gaisuwan wani abokinsu wanda bashida lafiya, shida Malam Ashiru.
Cikin ikon Allah Kuwa Ummi na idar da sallan azahar saiga Baffa Alin ya shigo, koda yaga Ummin yaji daɗi, saidai kuma zuciyarsa ta basa kan cewa ba lafiya ba, domin lafiya ƙalau babu abun da zaikawo Ummi Dukku ana tsaka da shirye shiryen bikin Saifuddeen kana kuma jiya-jiya nan sukaje amsa kiran nata.
Bayan sun gaisa da Bappa Alin ne Ummi ta gyara zama, lokaci ɗaya damuwa ya bayyana akan fuskarta, dubanta Baffa Ali yayi cikin sanyin murya yace.
"Lafiya kuwa? badai wanine bashida lafiya acikin gidan ba?."
Kai Ummi ta girgiza cikin ƙunan zuciya tace.
"Akan maganan auren Saifuddeen da yarinyar nanne, kamar yanda na faɗa muku kaida Malam Ashiru jiya cewa yarinyar nan batason Saifuddeen, tana masa barazanar matuƙar ya aureta zata kasheshi, to fa yanzu abin k'aruwa yakeyi dan bata daina ba, awancan karon kun tausasheni ta hanyar cewa nayi haƙuri nabari ayi auren, na haƙura badon raina yana soba, saidai ayanzu bazan iya haƙura ba, inamatuƙar jin tsoron abun da zai faru anan gaba, inatsoron rasa Saifuddeen, Bappa Ali kasan yanda Saifuddeen yake awojenmu dan Allah Kayi wani abu!."
Nan ta kwashe duk kan abun daya faru da kuma text message ɗin da ta karanta wanda Zaleehan ta turowa Saifuddeen ta faɗa masa.
Ajiyar zuciya maiƙarfi Bappa Ali yayi, tare da sanya hannu ya ɗan dafe kansa, tabbas zuwa yanzu yakamata yabita maganan Ummi, don kuwa tabbas ayanda Zaleehan ke faɗa da kuma bayyana tsanar Saifuddeen afili tabbas zata iya aikata koma miyene don ganin ta cutar dashi, tabbas shima zuwa yanzu kam yafara tsorata da al'amarin.
Ɗan jim yayi tare da gyara zamansa, cikin kulawa yace.
"Insha Allahu Ayau yau ɗinnan zan ɗauki Malam Ashiru mu tafi Gombe tun lokaci bai ƙure mana ba, haƙiƙa wannan lamari yayi tsaurin da dole sai manya sun shiga cikinsa, ki kwantar da hankalinki, Insha Allah zamuje mu samu shi Malam ɗin, zamuyi magana ta fahimta dashi, bakuma zamu ɓoye masa komai dake faruwa ba, tabbas nasan zai fahimce mu, shi kuma Saifuddeen Allah yabasa wata mace tagari wacce ke ƙaunarsa!."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ummi ta sauƙe tare da cewa "Ameen!."
Har cikin ranta taɗanji sanyi, haka dai suka ɗan taɓa hira kaɗan kafun daga bisani tace zata koma.
Haka suka rakota har wajen mota inda Sule driver ke jiranta.
Haka Ummi suka kama hanyar shigowa cikin garin Gombe zuciyarta wasai, tanajin kamar ta raba Saifuddeen da ƙaya.
Tafiyar 1 hour ne kacal ya kawosu Gombe, inda ta koma gida zuciyarta cike da salama, saidai kuma ta wani ɓangare, cike take da tausayin Saifuddeen, domin kuwa koda sau goma zata kalleshi, to akowani kallo ɗaya, saita hango zazzafar ƙaunar da yakeyiwa Zaleeha acikin ƙwayan idanunsa.
Amma addu'a bata bar komai ba. Zata tayi masa addu'a akan Allah Ya musanya masa da mafi alkhairi.


Su Bappa Ali kuwa ƙarfe biyar dai-dai suka kamo hanyan zuwa garin Gombe shida Malam Ashiru, daga cikin abun da Ummi ta faɗa masa, ko ɗaya bai rage ba, haka ya labartawa Malam Ashiru komai, shikansa Malam Ashiru saida yaji zuciyarsa tayi masa ba daɗi, tabbas yasan sharrin ƙiyayya, ƙiyayya bata da daɗi sam, kuma takan rufewa mutum ido, yayi duk abun dayaga dama, musamman ma ga mace da auren mijin da bata so dan haka shima ya yarda baza'ayi wannan aurenba.


Ƙiran sallan Magriba acikin garin Gombe tayi musu, nan suka tsaya sukayi sallah, inda suna idarwa suka nufi gidan Dirankaɗi, wato Baban Ishaq kenan, kasancewar tunkan su taso sunyi masa bayanin komai sun kuma sanar dashi zuwansu, inda shikuma ya ƙira Baba Malam ya shaida masa cewa da anyi sallan Isha za su zo.
Koda suka ƙarasa gidan na Dirankaɗi, anan sukayi sallan Isha, daganan suka wuce zuwa G.R.A wato unguwar su Zaleeha.
Tarba me kyau suka samu daga Baba Malam, inda ya sauƙesu acikin babban falonsa, nan yasa aka cika musu gabansu da kayan ciye ciye,
hira kaɗan suka ɗan taɓa, kafun Dirankaɗi ya gyara zama inda ya fuskanci Baba Malam, cikin nutsuwa haɗi da halin dattako yashiga labartawa Baba Malam abun dake faruwa, da irin saƙon text message din da Zaleehan ke turawa Saifuddeen wanda suke ɗauke da barazana haɗi da baƙaƙen maganganu, inda ya ɗora da cewa.
"Kayi haƙuri Malam, amatsayinmu na manya masu hankali, baikamata ace mun zuba ido hakan na faruwa ba, haƙiƙa duk auren da akace akwai ƙiyayya acikinsa to mafi al'khairi shine barinsa, tabbas babu wani uba dazai so ɗansa ya rasa iri awannan gida naka mai cike da kamala haɗi da tarbiya, saidai kuma babu yanda zamuyi ɗaukan ƙaddara ya zame mana dole, saboda hakane mukazo baka haƙuri, kayi haƙuri Malam bisa dole munjanye nemawa Saifuddeen auren Zaleeha da mukayi, fatanmu shine Allah ya bawa kowannensu abokan zama nagari!."
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da ɗanyin jigum, tabbas Zaleeha nason dasa masa ciwon zuciya, sannan tanason zubar masa da ƙima da kuma mutumcinsa a idanun jama'a, saidai kuma yayi al'ƙawarin bazai taɓa bari hakan ya faru ba, gyara zamansa yayi tare da duban su Baffa Ali, cikin dattako haɗi da tausasa zance yace.
"Babu wani abu dazan faɗa muku face haƙuri, kuyi haƙuri, haƙiƙa nine nan mahaifin Zaleeha, sannan nike da ikon bada aurenta ga koma waye, tuntuni nakuma bada aurenta ga Saifuddeen, kamar yanda Zaleeha take ƴa awajena, hakama Saifuddeen, shi ba iya ɗalibina bane kaɗai, inajinsa kamar jinina, saboda haka kuyi haƙuri, kujanye batunkun fasa auren, Zaleeha ƴatace kuma inada ikon tanƙwarata duk yanda naga dama, kuyi haƙuri ku ɗauka cewa duk waƴannan abubuwan da takeyi yarinta ne kuma zata daina watarana, tabbas nasan yanzu giyar ƙuruciya ne ke ɗibanta, nan gaba kaɗan bazatayi abun da tayi yanzu ba."
Ɗan jim yayi tare da cigaba da cewa.
"Kuyi haƙuri dan Allah, Amatsayina na Uba agareta na baku haƙuri, kuma kamar yanda kuke sha'awar haɗa zuri'a dani, haka nima nake sha'awar haɗa zuri'a daku, musamman Saifuddeen daba kowani uba bane zaiƙi son zamowarsa suruki agaresa, kamar yanda na faɗa muku tun daga farko babu abun da zan faɗa daya wuce nace kuyi haƙuri insha Allah aurennan ba fashi."
Da sauri Malam Ashiru ya fara jujjuya kai a hankali tare da cewa.
"A a Malam kayi hak'uri abar batun auren nan mu kam mun janye.....!













BY
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Murmushi Baba Malam yayi irin nasu na manya, kana ya ɗanyi jim, haƙiƙa fasa auren Zaleeha bazai rage komai ba face mutuncinsa da kimarshi, mutuƙar kuwa aka fasa auren to tabbas ita da mahaifiyarta sun samu abun da suke so, sam shikuma bazai lamunci hakan ba, gyara zamansa yayi tare da kai dubansa ga su Baffa Ali da Malam Ashiru.
Cikin nutsuwa haɗi da kamala yace.
"Haƙiƙa nafahimci me kukeji agame da wannan auren, saidai kada ku manta mu daku ɗin kamar ƴan uwa muke, dukanmu tsofaffine masu dattako da sanin ya kamata, amatsayina kuma na mahaifi ga Zaleeha zan ƙirata na zaunar da ita nayi mata nasiha, insha Allah nasan zata fahimta, dan Allah kuyi haƙuri, rashin tunanine kawai irin na yaran zamani!."
Ajiyar zuciya su Baffa Ali suka sauƙe, cikin sanyin murya haɗi da fahimtar Baba Malam ɗin, Baffa Ali yace, "shikenan Malam Basheer babu komai, Allah yasa auren ya zama al'khairi agaresu, Allah kuma ya sawa Zaleeha so da ƙaunar Saifuddeen acikin zuciyarta, don shikam yana sonta sosai, fatan mu shine auren nasu yayi al'barka!."
Da "Ameen Ameen!." suka amsa su dukansu, inda Baba Malam ya sauƙe ajiyar zuciya, sosai yaji girman na iyayen Saifuddeen ya ƙaru acikin idanunsa, nan suka ɗan tattauna maganganu masu muhimmanci, daga nan kuwa su Baffa Ali sukayiwa Baba Malam ɗin sallama, har bakin motarsu Baba Malam ya rakosu, inda bai dawo cikin gida ba saida yaga tafiyarsu.
Zama yayi akan ɗaya daga cikin tausassun royal chairs ɗin da suka ƙawata haɗaɗɗen falon nasa, bayansa ya jingina da jikin kujeran tare da lumshe idanunsa, cikin ransa haka yakejin ba daɗi, tunda yake baitaɓa sanya ranan auren ɗansa ko ƴarsa daga baya kuma akazo da maganar fasawa ba sai akan Zaleeha! duk kuma a dalilin taurin kai irin nata, tabbas Zaleeha tanason sashi yaji kunya a idanun mutanen da suke matuƙar ganin ƙimansa, amma babu komai zaiyi abun tubkar hanci tunda wuri, wayarsa dake cikin al'jihun rigarsa ya laluɓo inda ya dannawa nombern Mama ƙira, bugu uku ana huɗu Mama ta ɗauki ƙiran, batare daya jira komai daga gareta ba yace.
"Kituromin Zaleeha." kitt ya kashe wayan, don sam baison abun dazai ɓata ransa da daren nan.
Bayan kamar minti shida dai-dai Mama tashigo cikin falon hannunta ɗauke da ɗan madaidaicin tray wanda samansa ke ɗauke da flask da kuma ƙananan cup guda biyu, bakinta ɗauke da sallama ta ƙaraso cikin falon, inda ta jawo wani babban table dake tsakiyan falon ta kawosa har gaban Baba Malam ɗin, nan ta ɗaura ɗan ƙaramin tray din akan table ɗin, duban Baba Malam tayi fuska ɗauke da Murmushi tace.
"Barka da hutawa!."
Shima Baba Malam ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi, ya jinjina mata kai alaman ya amsa.


Su Baffa Ali kuwa koda suka isa gidan nasu Saifudden kai tsaye ɓangaren Ummi suka nufa, zaune suka isketa ababban falon nata, gefenta kuwa Hayatudeen ne wanda keta faman buga game ɗin Drok Stack Ball awayarsa.
ganinsu yasa Hayatuddeen ya gaishesu cikin ladabi, don kuwa hadda Dirankadi akazo, nan ya miƙe ya haura sama zuwa ɗakinsa.
Ummi kuwa tashi tayi ta kawo musu drinks masu ɗan sanyi, nan ta zauna suka shiga ɗan gaisawa, musamman da Dirankaɗi wanda suka jima basu haɗu ba.
Bayan sungama gaisawa ne, Dirankaɗi ya gyara zamansa tare da fuskantar Ummi'n, sanin cewa ita ɗin mai yawan haƙuri da sauƙin kai ne yasanyasa tausasa lafuzansa, tayanda zata fahimcesa sosai, ahankali yace.
"Kamar yanda kika buƙata da muje gidan su Zaleeha, munje munkuma sanar musu cewar mun janye batun auren!.".
Ajiyan zuciya sauƙe a hankali tare da cewa.
"Alhamdulillah".
murmushi suka ɗanyi, sai kuma Dirankadi ya ɗan numfasa tare da cewa.
"Kiyi haƙuri Hajiya.. kisa aranki cewa auren Saifuddeen da Zaleeha haɗine na Allah bawai yin kanmu ba, sannan kada ki manta ance matar mutum kabarinsa, sannan idan Allah Ya nufa cewa Saifuddeen sai ya auri Zaleeha bamu isa hanawa ba."
shiru tayi jiki a mace taci gaba da sauraronshi.
"Tabbas nasan mekikeji nakuma fahimci irin fargaban da kike ciki, ƙwarai kowacce uwa bazata taɓa son wani abu dazai cutar mata da ɗanta ba, nasan kina gujewa Saifuddeen auren Zaleeha ne badon komai ba saidan, kina jin tsoron abunda kaje kazo, da kuma irin tsananin ƙiyayyar da Zaleehan ke nuna masa, ƙwarai hakan abun tsorone to amma kada ki manta, babu wani abu dazai samu bawa me kyau ko akasinsa, face dama tuntuni anrubuta acikin littafin ƙaddaransa."
Kai ta gyaɗa tare da cewa .
"Haƙƙun".
Cikin jin daɗin tana gamsuwa yaci ga da cewa.
"Wani baya taɓa iya cutar da wani harsai Allah Ne ya tsara hakan, saboda haka inaso ki kwantar da hankalinki, munyi magana ta fahimta da mahaifin yarinyar, mutum ne shi mai tsananin dattako da kamala, kema kinsan hakan tuntuni, ya ƙasƙantar da kansa ya bamu haƙuri, ya haɗamu da Allah cewa kada a fasa auren! yakuma taushemu da lafuzza masu daɗi, saboda haka mu dai mun aminta cewa Saifuddeen zai auri Zaleeha, saboda haka yana ɗaya daga cikin ƙaddaransa, komai zai wuce kuma watarana sai labari, kema inaso
kisa aranki cewa Insha Allah auren Saifuddeen da Zaleeha al'khairine mai tarin yawa, wanda zaisa dukkanmu farinciki anan gaba, mudai addu'an al'khairi yadace munayi musu ako da yaushe!."


Baffa Aline yaɗan nisa tare da amsawa da cewa.
"Ƙwarai kuwa, abun da Dirankaɗi ya faɗa gaskiyace, haƙiƙa dukanmu nan munsan cewa ke uwa ta gari ce, munsanki da haƙuri Ummi, dan Allah inaso ki ƙara akan nada, ki-kumayi duba da irin tarin soyayyar da Saifuddeen keyiwa yarinyarnan tunfa suna ƙanana, kuma rauninki zaisa Saifuddeen fasa auren nan!."


Malam Ashiru ne yace. "Ƙwarai kuwa, ayanzu dai fatan al'khairi da sa al'barka kawai suke buƙata daga garemu."
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare dayin ƙasa da kanta, sosai taji zuciyarta tayi mata nauyi, yayinda matsanancin rauni ya bayyana acikin idanunta, haƙiƙa ita abu ɗaya take gujewa Saifuddeen shine halin dazai faɗa bayan aurensa da Zaleeha, matuƙar bata sanja hali ba, tasan Saifuddeen bazaiji daɗin zaman auren ba, wanda ita kuma duk wani fata da burinta baiwuce Saifuddeen ɗinta ya samu mace tagari, mai share hawayensa.
Hawayen dake ƙoƙarin cika idanunta ta shanye tare da ɗan sakin murmushi, cikin sanyi tace.
"Babu komai, duk yanda kukace shikenan, dama ni baƙin Zaleeha nake ba kawai dai munanan kalamai da ƙudurinta akan Saifuddeen shine ke bani tsoro, amma zantayi musu addu'a Allah yasa auren yazama alkhairi, wanda kowa zai amfana dashi!."
Cikin jin daɗin sauƙin kai irin na Ummin dukansu suka amsa da "Ameen Ameen."
Nan Dirankadi yace acigaba da shirye shiryen biki kada afasa komai da akayi niya, baiwani jima agidan ba yashiga motarsa inda ya nufi gida, su kuwa su Baffa Ali can cikin BQ suka sauƙa, saboda dare yayi babu yiyuwar komawarsu Dukku aranan, saidai gobe da safe zasu kama hanya.


Jin ƙiran da Baban nata keyi mata yasanya taji gabanta ya faɗi, take tsoro ya shigeta saidai kuma babu yanda ta iya dolenta ta amsa ƙiran nasa, zumbuleliyar hijab ɗinta ta zura, kana tanufi ɓangaren mahaifin nasu.
Da sallama ɗauke abakinta ta kutsa kanta cikin falon, cikin sanyi Baba Malam ya amsa mata, ƙarasowa tayi inda ta zauna akan lallausan carpet ɗin dake malale bisa tsakiyan falon, duƙunƙune jikinta tayi acikin hijabin, cikin ƴar siririyar muryarta dake rawa tace.
"Barka da dare Baba Malam!."
Kansa kawai ya jinjina mata alamar "Yauwa."
Aƙalla ta ɗau sama da mintuna 5 baice da ita komai ba, nanfa bugawar zuciyarta ya tsananta, don amatuƙar tsorace take.
Gyara zama Baba Malam yayi tare da fuskantar ta, cikin kulawa yaƙira sunanta.
Ɗagowa tayi ta kalleshi tare da amsa masa murya na rawa jiki asanyaye.
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da yi mata duban tsab, cikin son tausasa lafuzansa agareta dan yi mta nasihar da wala Allah imaninta zai sabunta cikin kula yace.
"Haƙiƙa kowani uba yana al'fahari da ƴarsa ko ɗansa matuƙar sukayi masa biyayya,."
Sosai lafazinshi ya ratsa jikinta,
Shi kuwa cigaba yayi da cewa.
"Bazance bana al'fahari dake ba Zaleeha saboda ke jininace, sannan kuma ko ba komai kin amshi zaɓin dana baki, kin kuma yi na am, saidai kuma labari yazo kunnena akan cewar kina rubuta saƙo irin na ɓaƙaƙen maganganu da kuma gargaɗi da barazana da kisan kai kina turawa Saifuddeen".
Tuni jikinta yake tsuma.
"Kada ki watsamin ƙasa a ido Zaleeha! Dan in kikamin haka ,wallahi Allah zan barranta dake, kada kimin fuska biyu.
tabbas nasan cewa rashin sanin wanene Saifuddeen agareki shiyasa kike wulaƙantasa, yanunamiki ƙauna da gata tun kina ƴar ƙanƙanuwan yarinya, haka kuma har kawo yanzu bai janye ƙaunarsa daga gareki ba, Saifuddeen maganarci ne wanda nayi imani samun kamarsa nada matuƙar wahala, ba'akowani gida ne ake haihuwar irin Saifuddeen ba haka kuma irinsu basu da yawa acikin al'umma, nazaɓa miki Saifuddeen amatsayin mijine saboda nasan bazaki taɓa danasanin aurensa ba, Saifuddeen bazai barki kiyi baƙinciki ba Zaleeha."
Tuni hawaye ke kwaranyo mata a ranta take faɗin.
"Wannan musakin wanne farin ciki zai samar min,mutun da bashi da bakin da zai furta min kalaman so, mutumin dake kamar dutse duk daɗin kalmar da zan masa ba ji zaiba,
haka zan rayu dashi babu so bare soyayya da ƙauna! muryar baban natane ya katse mata hasashenta. "Zaleeha kina ganin nakasasshe ne ko, to Saifuddeen da kike gani shi zai zame miki GARKUWA sannan bongo majingina na rayuwarki, shin Zaleeha menene aibun Saifuddeen dan yakasance Nakasashshe? saboda shi nakasashshene shiyasa kawai kike gudunsa? Baki san cewa Nakasa Ba Kasawa Bace Zaleeha, kuma babu nakasasshe sai kasasshe musamman nakasa irin ta Saifuddeen da bata shafi lafiyarsa ba, sannan nakasar zuci itace nakasa ba wai ta gangar jiki ba, Saifuddeen yana da kyakkyawar zuciya, kyawawan ɗabi'u, kyawawan halayya, ga wadatan zuci duk ya haɗa in kuma kyau ne tako ina Allah ya mishi kyau da haiba, haƙiƙa amatsayina na uba mahaifinki, ina matuƙar yi miki kwaɗayin samun managarcin miji kamar Saifuddeen, sanin cewa miƙa aurenki ga Saifuddeen danayi bazaisa nayi dana sani ba, shiya zuciyata ta aminta da shi sosai, dan Allah Zaleeha, ki nutsu ki dawo cikin hankalinki, ki watsar da duk wani buri ki rungumi auren Saifuddeen amatsayin ƙaddarar rayuwarki, kin kuma san idan kikayi haka Allah bazai bari ki taɓe ba, ni mahaifinki ne Zaleeha, idan ban nusar dake ba, babu wani wanda zai nusar dake, saboda haka maganan tura ɓaƙaƙen maganganu ga Saifuddeen banasonshi dan Allah ki daina kinji ko Mamana?."
A hankali ta gyaɗa kanta alamar to yayinda cikin zuciyarta kamar ta mutu dan baƙin ciki.
"Saura ƴan kwanaki kaɗan yazamanto miji agareki saboda haka yazama dole ki girmamasa kamar yanda kike girmamani harma fiye da haka domin shi mijinki ne kuma al'jannarki tana ƙarkashi diga-diginshi ,sai ya ɗaga zaki shiga".
A ranta take cewa.
"Wannan gurgun kam ai ɗaga ƙafarma ba iyawa zaiba." hannu tasa tana share hawayenta jin Baba malam ɗiɓ yaci gaba da cewa. "Saboda matsayinsa na miji agareki yazama dole kiyi masa biyayya da ɗa'a, koda wasa kada kice zaki bijirewa umarninsa, ƙin bin umarninsa tamkar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login