Showing 162001 words to 165000 words out of 239422 words

Chapter 55 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11874

yake harda kamo ƙafarshi ɗaya, har wata zufa yake haɗawa,
shafa kanshi Saifuddeen yayi cikin son yaron da ganin darajar da kumar Uwarshi,
ya juya zai fita kenan Ummi tace.
"Saifuddeen zo muci abinci tukun".
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da mata alamar.
"Ummi kuci na ƙoshi".
Murmushi Zaleeya tayi tare da cewa.
"Autan Ummi ka gani ko".
Tura baki Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Waya san me kuka ciyo a woje".
Dai-dai lokacin Raliya tace.
"Dan Allah kuzo muje muci abinci ni yunwa nakeji".
Miƙewa Zaleeha tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah wlh a ƙoshe nake, yau a gajiye ma nake zan konta da wuri".
Cikin wani irin yanayin tuhuma da zato da zargi Ameena ta bita da lallo tana fita.


A ranta tace.
"Okay duk sun ƙoshi bazasu ciba, to me suka ciyo? Ina sukaje? Me suka wuni yi da tace a gajiye take?".
Take shaidan ya fara haɗa mata zato da zargi ya kuma zauna ras dan komai da hujja yake bata.


Abincin da itama bata iya ci ba kenan dan sai ruwa tayi tasha koda Ummi ta matsamata kan taci sai tace a ƙoshe take ƙawarta Samira ce ta kai musu awara shi sukaci shine sai ruwa suke tasha.
Koda suka gama ta saɓa ɗanta a kafaɗa ta nufi side ɗin.


Zaleeha kuwa dama kai tsaye ɗakinta ta wuce, rege kayan jikinta tayi kana ta shiga wonka,
tana fita tayi shirin baccinta sannan ta konta.


Shi kuwa Saifuddeen aiki ya ɗanyi a system ɗinshi, inda ya ƙara samun damar bin diddigin Dalla dan ya dawo da niyar, rarake yan mata huɗu da yayi al'ƙawarin dan dama ya tafine dan badda sawu,
wannan dalilin yasa Saifuddeen bai bari direba ya kai Zaleeha ita ɗaya ba ko ɗaukota.


Koda ya gama aikinshi wonka mai rai da lafiya yayi dan Allah ya sani yana begen cingam ɗinshi, ya rigada ta saba mishi ko yaushe tana liƙe dashi kuma hakan na mishi daɗi yanzu tunda ya rigada ya saba.
Bayan ya gama kimtsa wa ne sai zuba ƙamshi yake,
ya nufi side ɗin Zaleeha ganin tayi bacci sui ne yasa bai tada itaba rigarta ya ja ya ɗan gyara mata a hankali ya fice ya tafi.




Ita kuwa Ameena da bata da niyar neman shi so take ya mata laifi kaɗan ta samu na ƙorafi,
haka yasa ta konta tasa ɗanta a gaba.


Jin motsinshi ne yasa ta rufe ida nunta,
kunna hasken wayarsa yayi gane ba bacci takeyi bane ya sashi ɗauke Adeel cak ya medashi kan gadonshi kana ya dawo a hankali ya sauƙa kan kekenshi ya hau kan gadon ya konta inda ya ɗauke Adeel ya meye gurbin shi kenan,
ya zama suna fuskantar juna.
a hankali yasa hannu ya jawota jikinshi,
da sauri taja baya tare da juyawa ta bashi baya.
Hannunsa yasanya ya rungumota ta baya, fusge jikinta tayi, ranta amatuƙar ɓace, ta matsa daga kusa dashi, idanunta wanda suka kaɗa sukai jajur ta watsa masa, cikin fushi da ƙunan zuciya tace. "Kada ka taɓani, dan bani da buƙatar hakan, bani kaɗai bace matarka ai, kana da wanda kake ɗauka kutafi resturant da garden ai, ni dama menene amfani na awajenka, tunda na riga dana haifi ɗa, sannan kuma bankaita kyau ba, hakanne yasa kake ƙoƙarin fifi tata akaina, saboda kun fita yawon shaƙatawa, kunje kun more rayuwarku, dole ai kace bazaka ci abinci ba, tunda kana da ƴar gold kunje kun wuni liƙe da juna harda wani cewanta a gajiye take,ai ba sai ta faɗa min haka zan gane ta wuni a kanka kuna aurataiya ba."
Taƙare maganan cikin matsanancin ɓacin rai, da kuma tafasar zuciya, Allah yasani kishin Saifuddeen yaci ƙarfinta, saboda hakane ma take yarda da duk wani abun da zuciyarta ta raya mata.
Shiru yayi tare da tsura mata tsumammun idanunsa, ƙwarai yanda idanunta suka rufe, take faɗan duk wani abu da yazo bakinta, shine abun dake matuƙar basa mamaki, dan gaba ɗaya lokaci guda ta sauya, ta tashi daga Ameenan da yasani ada, ta dawo wata irin mace me yawan ƙorafi, da kuma yarda da zargi bata da wani mugun abu tare da ita illa kishi dake son fin ƙarfinta, wato dama duk ilimin mace dole kishi na tsaburarta sai dai wasu na iya dannewa, wasu basa iya, a zahiri dai babu matar da bata da kishi,kuma yaji ya sani ya yarda zazzafan son da take mishine yasa take tsananin kishinsa.
Kansa ya girgiza tare da sa hannu ya kamo hannayenta, tabbas dole zaiyi mata uzuri saboda yasan zafin kishi ne ke ɗawainiya da ita, a wayarshi ya rubuta mata.
"Zargi bashi da kyau, kin sani ko a addinance, meyasa Ameena? meyasa ako yaushe kike yarda da abun da zuciyarki ke faɗa miki, meyasa ba zakina ƙaryata zuciyarki ba? kada ki cigaba da bari shaiɗan yayi tasiri acikin zuciyarki, tayaya kike tunanin aranan girkinki zan ɗau Zaleeha mu tafi garden ko resturant duk dan kawai na baƙanta miki, sam ba haka nake ba, ya kamata ace ke dakanki ki zama shaida, dan bana iya tauyewa kowa haƙƙinsa, sannan da kiketa ihun cewa munje resturant, ayaushe ne mukaje resturant ɗin? ya kamata ace kina kyautata mana zato, domin kuwa ba resturant mukaje ba, gidan Baba Malam mukaje, saboda yau akayi sadakan bakwai ɗin rasuwar Adda Maryam, zargi bashi da kyau, yana lalata aure, saboda haka ya kamata kina iya controlling zuciya, kishi, da kuma fushinki sabida bana so ki lalata mana zamanmu." Hannunta dake cikin nasa ta janye, kwata-kwata maganganun da ya faɗa basuyi tasiri acikin kunnuwanta ba duk da wani sashi na zuciyarta ya yarda da batunshi, sai dai zafin kishi da takeji ya danne komai hasalima jinsa kawai take, dan ayanzu kam gaba ɗaya idanunta sun rufe, wutar kishi ne kawai kecin zuciyarta, hakan yasa ba zata gane gaskiya ko akasinta ba, ganin yanda take ta sakin huci tana fitar da numfashi cikin fushi, ya sashi girgiza kansa kawai, tabbas tana ƙoƙarin ɓarar da damar da ta samu,
gyara kwanciyarsa yayi tare da kwanciya ya juya mata baya, saboda aduniya baya tunanin akwai wata mace da ta isa, yi masa fushi babu dalili, ya kuma rarrasheta taƙi ji, shiba sakarai bane, saboda haka bazai taɓa zama wawa akan mace ba, ko Zaleeha da ta kasance zaɓinsa ne takeyi masa haka, to tabbas bazai tsaya sauraranta ba, domin yariga dayasan ko awajen Allah bashi da wani laifi, tunda dai bai aikata ba dai-dai ba. Blanket ya ja ya rufa ajikinsa, tare da lumshe idanunsa. Ameena kuwa ganin yanda yayi kwanciyarsa ba tare da ya kara ce mata komai ba, yasa taji gaba ɗaya ranta ya ƙara ɓaci, can nesa dashi ta matsa tare da jawo Adeel jikinta.


Saifuddeen kuwa dama baji yake ba, kuma gashi ya bata baya, hakan yasa baimasan tanayi ba, dan baccin gajiya ne ma keneman ɗaukarsa.
Saida tayi kuka sosai kafun take maida ajiyar zuciya, jitake inama da ace Zaleeha bata dawo gidan ba, inama da ace Saifuddeen baikasance mijin Zaleeha ba, da duk hakan baifaru akanta ba, dan tanajin zata iya jure kishi da kowacce mace amma banda Zaleeha, ta jima sosai tana sheshsheƙan


Washegari da asuba kuwa antashi da ruwa, hakan yasa bai samu zuwa masallaci ba, nan cikin toilet ya shiga ya ɗauro alwala, tare da shumfuɗa darduma ya tada sallah.
Itama Ameenan miƙewa tayi, ta shige toilet ruwa ta ɗan watsa ajikinta, saboda ta tashi taji zuciyarta wasai, acikin kaso ɗari na damuwarta kaso saba'in ya ragu, hakanan taji cewar abun da tayi masa daren jiyan bata kyauta masa ba, sauda dama takanyi regreting abubuwan da takeyi mai, dan kuwa ita kanta tasan baiyi mata laifin komai ba hakama Zaleeha bata tare mata komai ba, kawai dai zafin kishi ne ke ɗawainiya da ita wanda kuma tana addu'an ALLAH ya yaye matashi tajin son Zaleeha koda al'barkacin son da takewa Adeel, nan kusa dashi ta shumfuɗa wani darduman, tare da ta da sallah, zuwa lokacin kuwa shikam ma harya idar, zaune yake akan guiwowinsa, yana gabatar da azkar, yana nan azaune harta idar da sallan itama azkar ɗin tayi, sannan ahankali ta ɗago ta kalleshi, gaba ɗaya jikinta asanyaye yake, ga kuma wani irin fitinannen ƙaunarsa da kuma sha'awarsa da takeji, hannunta takai ta dafa kafaɗansa, sarai yajita amma sai yayi kaman ma baisan tanayi ba, ganin haka yasa ta dawo gabansa suna fuskantar juna, ganin yana kallonta yasa taɗan sunkuyar da kanta, asanyaye tace.
"Ina kwana."
Kansa ya jinjina mata alaman.
"Lafiya." ƙoƙarin hawa wheelchair ɗinsa yasomayi, ganin haka yasa ta faɗa jikinsa, cikin sanyin guiwa tace.
"Dan Allah Abban Adeel kayi haƙuri, nima bansan meyasa nakejin wasu abubuwa akanku wani lokaci ba, kasan inasonka wannan dalilin yasa nakejin kishinka sosai araina, amman in sha Allah zan bari dan nacewa Mamana taita min Addu'a Allah ya yaye min kaima kaita min Addu'a kuma nima inayi." Idanunsa ya zuba mata, shi mutum ne me saurin fahimta da kuma uzuri, musamman ma ita da yasan cewa kishine ke ɗawainiya da zuciyarta. Ɗan lumshe idanunsa yayi, tare da jinjina mata kai alaman.
"Shikenan komai ya wuce."
murmushi ta sakar masa tare da sake shigewa jikinsa, bakinta har rawa yake haka ta shiga kissing ɗinsa tako ta ina, sam bai hanata ba, dan baiso ya tauye mata haƙƙi, jikinta na rawa haka ta taimaka masa ya kwanta akan gado, bin bayansa itama tayi, tare da haɗe jikinsu waje ɗaya.
Duk wani abun da takeso baiƙi yi mata ba sabida shima yana buƙatarta, haka ya bata duk wani haƙƙinta dake kansa, after 22 minute gaba ɗaya jikinsa yayi weak, gajiya ne keta damunsa, da ƙyar ya iya tashi yayi wanka, fita yayi inda yaje ya gaishe da Umminsa, yana dawo wa kuwa nan kan gadon ya kwanta yana me da numfashi, ahaka har bacci ya ɗaukesa.
Ameena kuwa jin ranta take fari ƙal, wani annushuwa takeji acikin ranta, koda ta fito daga wankan, mai kawai ta shafa sannan ta yiwa Adeel wanka, saida ta fara shirya Adeel ɗin, kafun ta shirya kanta cikin kayanta na zuwa aiki.
Ganin Saifuddeen ɗin na bacci ne yasa taɗan ranƙwafo tare da yi masa kiss agoshinsa, Adeel na ɗauke akan kafaɗanta ta fice daga cikin ɗakin, kaitsaye sashin Ummi ta nufa, anan falo ta iske su azaune, yayinda Zaleeha ke zaune anan ƙasan sofa, tasha kyau cikin simple riga da sket ɗin dake jikinta, anutse ta gaishe da Ummi sannan Zaleeha ta miƙa hannu ta amshi Adeel, yau ko breakfast ma bata tsaya tayi ba, saboda taɗan makara.
kuma tana son yau ɗin ta keɓe da ƙawarta, Samira tasan zata ƙara kwantar mata da hankali kuma zata bata shawarwarin yadda zata samu ta yaƙi wannan zazzafan kishin ta zauna da ƴar uwarta lfy.


Saifuddeen kuwa sosai yayi bacci, dan bashi ya farka ba sai wajajen ƙarfe 10, bathroom ya shiga ya sakeyin wanka sannan ya kimtsa kansa cikin, wasu haɗaɗɗun riga da wando, sai baza ƙamshi yake haka ya nufi sashin Ummi, dan yunwa yakeji sosai.
Ummi ce da Zaleeha kaɗai zaune afalon, Ummi nakan kujera, ita kuwa Zaleeha tana ta kaikoma acikin falon, sai faman jijjiga Adeel dake kuka yake,
shigowarsa cikin falonne yasa Ummi cewa.
"Yauwa gama babansa nan, Zaleeha miƙawa babansa shi ko zaiyi shiru, tun ɗazu ya cikamu da ihu, bansan meke damunsa ba, bacin kuma ƙiwa ba halinsa bane." Ɗan kallon Saifuddeen ɗin Zaleeha tayi, sai kuma ta sadda kanta ƙasa.
Shikuwa ahankali yaɗan lumshe kyawawan idanunsa da suka sauƙa akan haɗaɗɗiyar surar jikinta, hips ɗinta wanda ya cika sket ɗin jikinta, yayi masifar kyau da tsaruwa yake kallo, jiyayi tsikar jikinsa sun mimmiƙe, asanyaye Zaleeha ta karaso inda yake, ɗan sunkuyawa tayi daniyar ajiye masa Adeel ɗin akan cinyarsa, hakanne yasa beautyful breast ɗinta suka ɗan bayyana ta saman wuyan rigar, ganin kyawawan saman breast ɗin nata yasa yaji wani abu na yawo ajikinsa, wajen miƙa masa Adeel ɗin ne kuwa, hannunta ya gogi nasa, take sukaji wani irin shock, hakanne yasa cikin sauri ta zare hannunta tare da komawa gefen Ummi ta zauna,
ɗaga Adeel ɗin yayi yana yi masa wasa, take kuwa yaron yasoma sakin murmushi, harma da ɗan dariya,
Ummi ne tace.
"Kuji ja'irin yaro, wato yaga Babansa shine harda dariya, dama kenan mu kakewa ƙiwa." Murmushi kawai Saifuddeen ɗin yayi, yana riƙe da Adeel ɗin, ya ƙarasa dinning area, ganin haka yasa aɗan kunyace Zaleeha ta tashi, ta ƙarasa dinning table ɗin, cikin nutsuwa take seving ɗinsa haka nan take jin kamar ta zauna kusa dashi, shikuwa idanunsa ya zuba mata, dan sosai tayi masa kyau, yau ɗin zallan yarintarta ya bayyana sosai, gashi kayan jikin nata sunyi mata cif-cif, har gabansa ta kawo masa plate ɗin abincin, ɗan ɗagowa tayi, hakanne yasa idanunsu sarƙewa acikin na juna, rolling eyes ɗinsa yayi, take taji wani irin yaarrr yaarrr ajikinta, saboda yanda abun ya ƙarawa fuskarsa kyau, wani irin kallon shauƙin daya bita da shine yasa, takusa yin tuntuɓe wajen barin dining area'n,
wani ƙawataccen murmushi ya sake, tare da ɗauke kansa ya maida hankali kan abincinsa. Nan kusa da Ummin ta dawo ta zauna, suna ɗan taɓa hira da Ummin, har ya kammala cin abincin, koda yazo fita, akan cinyanta ya ajiye Adeel ɗin, sannan ya fice. Yana fita kuwa Adeel yasa musu kuka, haka suka dinga rarrashinsa ita da Ummi, saida yayi bacci kafun suka samu salama, Zaleeha kam tuni kukan Adeel din ya ruɗata, har tanajin ƙwalla sun cika idanunta, sam batason kukan Adeel ɗin.


Saifuddeen kuwa yana fita daga part ɗin Ummi'n, kaitsaye gidan ya bari, dan suna da meeting ɗin da zasuyi.


Adeel kuwa wunin yau gaba ɗaya kuka ya dinga musu, da ƙyar suke iya rarrashinsa.


Ameena kuwa yau da wuri suka tashi, a hankali suke tafiya ita da ƙawarta Samira, har suka iso bakin harabar inda suke aje motocinsu, shiru Ameena ta ɗanyi tare dacewa Samira.
"Yau baki fito da motarki bane?".
Murmushin Samira tayi tare da cewa.
"Eh yau a napep nazo, ƴar uwatace motarta na wurin gyara, kuma sunada biki a danginta, shiyasa na bata nawan".
Cikin fidda numfashi Ameena tace.
"Uwar gidanki ko?".
Kai Samira ta gyaɗa mata alamar eh,
cikin sanyi Ameena tace.
"Kinji dadi Samira inamw ace nima Allah zai yaye min kishi in samu in saki jikinda uwar gidana, dan wlh ita dai irin kice."
Murmushi Samira tayi tare da cewa.
"Uhum Ƙawata ai abin mai sauƙine muddin kika sauƙaƙawa kanki to Allah zai sauƙaƙa miki in kuwa kika tsananta wa kanki zakisha wuya, ni da uwar gidana wlh ko ƴan uwa sai haka, bamu da matsalar komai sabida mun sawa ranmu haƙuri, bawaifa bama kishin bane, no ai kishi kumallon matane, amman kishinmu mai tsari mukeyi, ina gaya miki ki saki ranki da abokiyar zamanki zakuji daɗin zama, tunda keda kanki kin shaida min ita bata da kishinki asalami ke gani kike wai kamar bata son mijin nakune, to wlh Ameena bawai bata son mijinku bane ba mamaki ma ta fiki sonshi kawai dai ta iya takunta ne, babu mamaki ma ta fiki sonshi sai dai wata ƙil ita sonta irin son nanne da zaka so miji ka kuma so duk abinda yake so, kawai dai ta iya sarrafa kantane."
Cikin sanyin jiki Ameena tace.
"Shiga motata muje in sauƙeƙi dama ina son muyi mgna".
kai ta gyaɗa mata kana suka shiga Mota,
shiru sukayi saida Ameena ta dai-dai ta hancin motarta kan titi kana ta juyo ta ɗan kalli Samira cikin sanyin jiki tace.
"Wato ko Samira ni kaina nasan zuciyata bata min adalciba akan Ammin Adeel, na yarda na gane tana masifar son ɗana so kuma na gaskiya, kana tana kawar da kanta akan harkata da mijinta tamkar bata san me mukeyi ba, bawai ina jin na tsaneta bane a a wlh ni kaina ina sonta sai dai ina masifar kishinta,ina son Abban Adeel wani irin son da ni kaina bansa adadinshiba shiyasa nake kishinsa bana son yayi nesa dani, kinga tsabar zugar kishi wallahi yanzu sai yayi ta bina yana son haƙƙinshima sai inji to ai yanada wata matar."
Juyowa Samira tayi ta fuskanceta da kyau cikin wayewa da iya salon kishi na Musulunci tace.
"Kin wahala kin ɗorawa kanki dala ba gammo, ke ƙawata in banda tsaurin ido

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login