Showing 111001 words to 114000 words out of 239422 words

Chapter 38 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11845

komawa inda ya fito.
Ƙarasowa kusa da Ummin nasa yayi, haɗe hannayensa biyu yayi, kana cikin body language ɗinsa ya gaida
ta.
Amsa masa gaisuwar Ummi tayi tana ɗan sakin murmushi.
Asanyaye Zaleeha ta ɗago kanta, cikin wata irin murya me ɗauke da sarƙewa, akaron farko kenan na tarihin rayuwarta da zata fara gaida shi, cikin sheshsheƙan kukan daya taso mata tace.
"Ina kwana." kasancewar yana iya kallonta ta gefen idanunsa ne,yasashi fahimtar abunda tace, amma sai ya share yayi kamar baigani ba, saima sake haɗe fuskarsa da yayi, tare da ƙoƙarin soma ciro wayarsa, daga aljihun rigarsa. Ganin hakane yasa Ummi sa hannu taɗan taɓashi, ɗago da kansa yayi ya kalli Ummi'n.
Da idanu tayi masa nuni da Zaleeha kana tace. "Bakaga Zaleeha na gaisheka bane."
Ai tunma kafun Ummi ta gama rufe bakinta, yasake maida kansa ƙasa, dan bama yaso ya fahimci abunda Ummin ke ƙoƙarin faɗa, ahankali ya tura wheelchair ɗinsa, ya nufi hanyar fita daga ɗakin, ko inda Zaleehan take bai kuma kallo ba. Baki buɗe Ummi ke kallonsa har ya fice daga cikin ɗakin, kanta kawai ta girgiza, tare da sakin ɓoyayyen murmushi, sarai tasan gano ƙasan zuciyarsa cewa wannan fushin nasa da yakeyi da Zaleehan hukunta yakeyi har cikin zuciyarsa, kuma yanayi ne dan ya gwada mata ɓacin ransa, akan abun da ta aikata, sannan kuma ya nuna mata kurenta ta kuma sani shima mutunne kamar kowa yanada zuciya kuma zai hukuntata muddin ta ɓata mishi.
sanin irin zazzafar soyayyar da Saifuddeen ɗin keyiwa Zaleeha yasa Ummi sanin cewa bazai taɓa iyayin haƙiƙanin barranta da ita ba.
Itakuwa Zaleeha asanyaye ta miƙe, cikin sanyin da ayanzu ya zama tamkar ɗabi'arta tace.
"Ummi ina Raleeya, da Hayatuddeen."
ɗan murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Raleeya na kitchine, Hayatuddeen kuma kinsan yau weekend yanacan yana baccin nasa da baya gajiya dashi."
Kanta taɗan jinjina, sannan tace.
"To bari inje kitchin ɗin in taya Raliya aikin".
Da sauri Ummi tace.
"A a jeki kwanta". Zata kuma yin mgna Ummi tace.
"Nace kije ki konta ki huta".
ganin yadda Ummi tayi mgnar cikin bada umarnine yasata cewa.
"To Ummi bari naje na ɗan kwanta."
Kai Ummi ta jinjina mata, saboda duk wani koke koken da tayi adaren jiya, Ummin najinta, hakanne ma yasa tasan cewa Zaleehan bata wani samu ishashshen bacci ba. Tana fitowa daga ɗakin Ummin kuwa, sukai karo da Hayatuddeen wanda da dukkan alama yanzu tashinsa, dan sai hamma yake ta zubawa tare da miƙa.
Ganin Zaleehan yasashi sakin murmushi, ƙarasowa yayi tare da kamo hannunta, cikin kulawa yace.
"Good morning my beautyful Aunty, ya jikin naki?"
Kanta taɗan jinjina masa alaman da sauƙi, idanunta ne suka sauƙa akan Saifuddeen wanda ke zaune akan kekensa ya basu baya, yana ta faman aikin danna wayarsa, saurin ɗauke idanunta daga kansa tayi, tare dayin ƙasa da kanta.
Dai-dai lokacin Raleeya ta fito daga cikin kitchine, gaisawa sukayi cikin kulawa kuwa Raleeya ke tambayarta jikinta, nan tace mata da sauƙi. Hayatuddeen ne ya kamo hannun Zaleehan, tare da zaunar da ita akan ɗaya daga cikin kujerun falon, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha dan Allah minti biyu, ki jirani anan ina zuwa."
kai ta jinjina masa tare da sadda idanunta ƙasa tana wasa da ƴan yatsun hannunta.
Ameena ce ta buɗe ƙofar falon ta shigo bakinta ɗauke da sallama, shirye take tsab acikin kayan aikinta, ga kuma kekyawan ɗanta Adeel da ke riƙe ahanunta, shigowarta falon kuwa yayi dai-dai da fitowan Ummi daga ɗaki.
Jin ƙamshin turaren Ameenan ne ya sashi ɗago kansa ya kalleta.
ƙarasowa cikin falon tayi, da ganin Zaleeha kuwa sai taji gaba ɗaya ranta yayi ƙunci, ɗan durƙusawa tayi, aladabce ta gaishe da Ummi', fuska ɗauke da fara'a da kulawa Ummi ta amsa tare da miƙa hannu ta karɓi Adeel dake ta yi mata dariya irin tasu ta yara.
Ɗago kai Zaleeha tayi, karab kuwa suka haɗa idanu da Ameena'n, kasancewar dama idanun Ameena'n akanta suke, ta tsareta da idanu kamar ta samu tv. Cikin sanyi Zaleehan ta janye idanunta, tare da cewa Ameena'n'.
"Ina kwana." zazzaƙan muryar Zaleehan da Ameena taji shiya sanya bugun zuciyarta tsananta, wanda har yasa ta kusa daburcewa, cikin in ina ta amsa da "La fi..ya." dan zata iya rantsewa cewa bata taɓa jin murya me daɗin a zahiri irin ta Zaleehan ba.
Kallon Adeel dake hannun Ummi Zaleeha tayi, cikin sa'a kuwa yaron shima kallonta yake, murmushi tayi masa sai kawai ya buɗe baki yana mata dariya, wani irin kyau yaron yayi mata, musamman ma yanda dimples ɗinsa suka lotsa da yana dariyan, lokaci guda taji ya shiga ranta, hakan yasa ta miƙa hannu dan ta ɗaukeshi, babu ƙiwa kuwa yazo wajenta, karɓansa tayi tana sakin sassanyan murmushi. Ummi ne itama tayi murmushi cikin kulawa tace.
"Lallai Adeel yaga ɗiyarsa, tunda dai baiyi mata ƙiwa ba." Kallonta Zaleehan tayi da ɗan mamaki, kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Ai me sunan Baba Malam ne."
Wani irin farinciki ne ya cika zuciyar Zaleehan, sai kawai ta rungume yaron ajikinta tanajin sonsa sosai aranta haka nan sai takeji kamar itace ta haifeshi in ba gizo idonta ke mata sai takega kamar yaron yana kama da ita, musamman dimples ɗinsa irin nata ne sak.
Dai-dai nan Hayatuddeen ya fito daga kitchine hannunsa ɗauke da cup, wanda aka zuba yoghurt acikinsa, akusa da Zaleehan ya zauna tare da miƙa mata yoghurt ɗin, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha amsa kisha, al'ƙawari nayiwa Zakariyya cewar yau sai nasa kinci abinci, saboda haka dan Allah kisha kafun agama break fast." ɗan marairaice fuska tayi, sai dai kuma ita kanta tasan cewa tana matsanancin jin yunwa, hakanne ma yasa ta amsa, tare da ɗan sha kaɗan, kan Adeel da har yanzu ke kan cinyarta take shafawa, sosai yaron ya shiga ranta tana jin sonshi da ƙaunarshi har cikin ranta.
Duk wannan wainar da ake toyawa Ameena idanu kawai ta zuba musu, itakam Allah yasani bata gajiya da kallon Zaleeha, to itama da take mace, bata gajiya da kallonta, inaga kuma Namiji haka yasa kishinta kuma ninkuwa a ranta.
Hayatuddeen ne ya ɗago kansa ya dubi Ameena'n, murmushi yaɗan saki cikin kulawa da girmamawa ya fuskanceta tare da cewa. "Aunty Ameena ina kwana."
itama murmushi'n ta mayar masa tare da cewa.
"Lafiya Auntan Ummi, ya rigima." murmushi kawai yayi, batare da yace mata komai ba, ya maida hankalinsa wajen Zaleeha tare da kissing goshin Adeel dake kan cinyar Zaleeha, wanda da dane kuma ta tabbatar tsayawa zaiyi yayita mata rigima, amma yanzu gaba ɗaya hankalinsa naga Zaleeha.
Hakanne yasa asanyaye ta juyar da kanta ɓangaren Saifuddeen, ai kuwa idanunsu ne ya haɗe, dan dama kallonta ya keyi, murmushi ta sakar masa, domin tuni haushin nasa da takeji ya gushe, ayanda take matsanancin sonsa batajin zata iya dogon fushi dashi bare ta ɓata rawanta da tsalle, shiɗin ma murmushi yayi mata tare da miƙa mata hannunsa, ganin Idanun su Ummi baya kansu yasa ta kama hannun nasa, gamamakinta sai gani tayi yajawota dab dashi, har jikinsu na gogan na juna, kasancewar jiyan ba'a ɗaki ɗaya suka kwana ba, hakan yasa bata gaishesa ba sai yanzun, ahankali tace.
"Ina kwana." Kansa ya jinjina mata alaman lafiya, sannan ya tallafo haɓarta, kiss ya ɗaura mata akan kumatunta da kuma bakinta, baruwansa da wani jin kunya wai dan su Ummi na falon bare yasan idon Ummi baya kansu.
Gaba ɗayansu sunga abun da Saifuddeen din yayiwa Ameena hakan ne yasa suka janye idanunsu gefe, Zaleeha ma da tsautsayi yasa ta ɗago, idanunta sun gane mata abun da ya faru, kawar da kanta gefe tayi, tare da ƙara manne Adeel ajikinta, ko ajikinta itakam, bata ma ji wani abu adangane dasu ba, saidai zuciyarta ta tsegunta mata cewa. "Halan Ameenan matarsa ce kenan." Ummi kuwa, tashi tayi gaba ɗaya ma tabar falon, dan ta gano cewa wannan sabuwar kulawan da Saifuddeen ɗin ya fara bawa Ameena agabansu wani salone, kawai yayi ne saboda wata manufarsa ta daban. Ameena kuwa da gangan ta kamo lips ɗinsa itama ta tsotsa, cikin sanyin murya tace. " I will miss you dear" sake manna masa wani kiss ɗin tayi, sannan ta ɗan janye daga jikinsa, Hayatuddeen kuwa baki ya sake yana kallon ikon Allah,
Zaleeha kuwa sam bata ƙara ɗago kanta bama sai wasa takeyiwa Adeel wanda da ka gani kasan tana jin son yaron har cikin ranta.
Ƙarasowa inda suke Ameenan tayi, tare da sanya hannu ta ɗauki Adeel, tana sakin murmushi me ɗauke da ma'anoni kala kala, haka ta saɓa Adeel akafaɗanta ta fice daga cikin falon, wani irin farinciki takeji acikin ranta, wannan kiss ɗin da Saifuddeen yayi mata agaban Zaleeha ji take kaman kyautar zuciyarsa ya bata a gaban Zaleeha ji takeyi ya gama mata komai dan ko ba komai ya nunawa Zaleeha itama matarsa ce kuma yana sonta murmushi kawai take tayi.


Tashi Zaleeha tayi ta wuce ɗakinta, kusan rabin cup tasha yoghurt ɗin sannan ta kwanta. Acan falo kuwa Raleeya ce ta gama shirya musu abinci akan dinning area, Ummi ne tace da Hayatuddeen yaje ya ƙira Zaleeha tazo suyi beak, koda yaje ɗakin nan ya isketa tana bacci. Dawowa yayi ya faɗawa Ummi'n, hakan yasa Ummi tasa Raleeya ta ɗeba mata nata break fast ɗin daban.


Saida suka kusa kammala break fast ɗin, Ummi ta ɗago kanta ta dubi Saifuddeen wanda yake tsakalan chips yana kaiwa bakinsa, ahankali yake tauna abincin, yanayin komai nasa cikin nutsuwa.
Gyara zama Ummi tayi tare da ɗan muskutawa ta kamo hannunsa, ɗago kansa yayi, tare da sakarwa Ummin nasa murmushi.
Itama Ummin murmushi tayi masa, cikin kulawa tace.
"Ka bani key ɗin side ɗin Zaleeha,"
Fuska ya ɗan kwaɓe tare da mata alamu.
Shiga baisan inda key ɗin yakeba".
Kwaffa tayi tare da cewa.
"Uhumm yayi kyau." Fuska ya ɗan kele,
tsareshi da ido Ummin tayi tana mai nazartanshi kana tace.
"To Inaso kashirya anjima ka raka Zaleeha ta bawa Baba Malam haƙuri, ko kuma shima car keys ɗin naka duk baka san inda sukeba."
take yanayin fuskarsa ya sanja, kansa ya girgiza, tare da aje spoon ɗin hannunsa. Idanu Ummi ta zuba masa ganin ya mata alamun dan Allah tayi haƙuri, sai kuma yaja wheelchair ɗinsa yayi baya, tare da juyawa yabar wajen baki ɗaya,
da idanu Ummi ta bisa har ya fice daga cikin falon.






Wasa farin girki sannu sannu dai bata hana zuwa sai dai a dadde ba'a jeba






Littafina na kuɗine. in kina buƙata ga number 09097853276 katin mtn zaki turo na ɗari 300 ko kimin transfer ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.








By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Sbpejtt Kai kawai Ummi ta girgiza tare da tashi kaitsaye ta wuce ɗakinta, Hayatuddeen ma dake zaune ji yayi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, sam baiso hakan ba, yaso ace Hamman nasa ya amince, saboda shima ya gamsu cewa, da taimakon Hamman nashi ne kaɗai Baba Malam zai iya haƙura ya yafewa Adda Zaleeha'n.
Haka dai suka kammala cin abincin nasu duk jikinsu asanyaye, acan ɓangaren Saifuddeen kuwa yana barin falon nasa, kaitsaye ɓangarensa ya nufa, sauƙa daga kan wheelchair ɗinsa yayi, tare da haurawa saman ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun falon ya kwanta, idanunsa ya lumshe yana jin zuciyarsa nayi masa wani iri, maganganun Ummin ne ya dawo cikin tunaninsa, ahankali ya girgiza kansa, cikin zuciyarsa yace.
"Ada ni ba komai bane awajenta, bata ɗaukeni matsayin komai ba, kullum idan akwai wata magana da zai fito abakinta, wanda ta shafeni to baiwuce kalmar ƙiyayya ba, matsalar da ta faɗa ayanzu, shiyasa ta ɗaukeni wani me mahimmanci agareta, ta gudu ne saboda batason aurena, yanzu kuma gashi ta dawo tana zaune aƙarƙashin inuwata, ahaka kuwa shine har da wani neman alfarmarta."
wani murmushi me ciwo yayi tare da girgiza kansa, shiba sakarai bane, ita tayi amanta saboda haka ita kaɗai zata lashe.
Yana gama tunanin ya gyara kwanciyarsa, tare da sake lumshe idanunsa, yana sakin ajiyar zuciya.
Acan ɓangaren Part ɗin Ummi kuwa baccin Zaleeha baiyi wani nisa sosai ba ta farka, Hayatuddeen ne ya kawo mata abinci, haka ya sakata gaba dolen ta saida taci, tana kammalawa kuwa ya miƙo mata ruwa da magungunanta tasha, nan ƙasan carpet ya zauna, ita kuwa tana kwance akan gado, ganin cewa akwai damuwa atattare da itane yasa shi, soma bata labarai wanda yasan dole zasu ɗebe mata kewa, suna zaune ahaka Raleeya ta shigo, akusa da Zaleehan ta zauna, cikin kulawa tace "Aunty Zaleeha ya jikin naki?".
ɗan jinjina kanta tayi, asanyaye tace.
"Da sauƙi." Murmushi Raleeya tayi, tare da faɗin.
"Masha Allah, Allah Ya ƙarasa sauƙi."
Da "Ameen" Zaleehan ta amsa, haka dai suka ci gaba da hiransu, Ita dai Zaleeha idanu kawai ta zuba musu, sau dayawa dramer'n Hayatuddeen da Raleeyan na burgeta. Duk dama har yanzu akwai damuwa kwance aƙasan zuciyarta.
Suna ahaka Ummi tashigo cikin ɗakin, ganinsu atare ne yasata sakin murmushi, sake gaisheta Zaleehan tayi, ta amsa mata fuska asake, har cikin ranta kuwa taji daɗin ganin Zaleehan cikin ɗan yanayi me kyau, kallon kayan dake jikin Zaleehan tayi, take wani tunani yazo mata hakan yasa tace da Hayatuddeen yazo zata aikeshi.
Babu musu ko ya tashi yabi bayanta.
Kaitsaye ɗakinta suka wuce, nan kan gado ta zauna, tare da jawo jakarta ta zage zip ɗin, duban Hayatuddeen tayi, cikin kulawa tace. "Makay zan aike ka ne, ko San Hussain Super Market?".
ta tambayesa da yanayi na ɗan tunani, zama yayi akusa da ita, tare da cewa.
"Wani abu za a sayo miki ne?".
"Kaya nakeson kasayowa Zaleeha, kaga dai bata zo da kayanta ba, part ɗin ta kuma akulle yake, na kuma ce Hammanku ya bada key yayimin biris, dama daya ba da key ɗin sai nasa ko Raleeya ne ta ɗebo mata sauran kayanta." cikin zumuɗi Hayatuddeen yace. "Ummi Makay zanje, wallahi dama ina kwaɗayin strowberry cake, kinga kawai sai na shiga Makay shawarma na saya, nasan itama Adda Zaleehan idan na sayo mata zataci." Hararansa Ummi tayi tare da cewa.
"To sarkin kwaɗayi, an faɗa maka cewa dama kowa irinka ne, koko ance maka kowa kwaɗayi kawai yasa agaba?."
Murmushi yayi, cikin zaƙuwa yace.
"Hmm Ummi bakisan wacece Adda Zaleeha ba kenan, ai shan zaƙinta ko shazumami sai haka, yanzu kawo kuɗin naje na sayo mata kayan."


Kai kawai Ummi ta girgiza tare da zaro Kuɗin da aƙalla zasu kai 70k, acikin jakanta ta miƙa masa, cikin kulawa tace.
"Kanutsu dan Allah Hayatuddeen, dogayen riguna nakeson kasayo mata masu kyau, ni hankalina ma kwata kwata bai kwanta da aikanka ka ba, dan tunda ka iya mota kuma shikenan ka zama ayawo, dan ma ana zaman makokin nan ne da da Zakariyya zakuje, saboda hankalina zaifi kwanciya, saboda ya fika nutsuwa wani lokaci'n."
Ɗan bakinsa ya turo gaba, cikin halin sakalcinsa yace. "Yanzu Ummi dan Allah Zakariyya'n

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login