Showing 18001 words to 21000 words out of 239422 words
Chapter 7 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
irin na masu sunan naka_
A hankali ya lumshe Kyawawan idanunshi, tare da furta.
"Masha Allah!." a cikin zuciyarshi sosai tayi masa kyau acikin shigar wedding gown ɗin nata, har wani ƙyallin kyau take kamar wata tauraruwa, komai nata yazama wani na musamman, cikin nutsuwa haɗi dajan aji irin na amare suka ƙaraso wajen motar Saifuddeen ɗin, da sauri Sule driver ya ƙaraso inda ya buɗe murfin motar da kansa, idanunta dake cikin wani ɗan siririn mayafi ta rumtse sakamakon ƙamshinsa da yadaki hancinta, sakamakon buɗe marfin motar da akayi, da taimakon Balkeesu tashiga cikin motar, ƙasa-ƙasa Balkeesu ke kallon Saifuddeen, sosai yayi bala'in yin kyau, saikace wani balarabe, komai nasa is perfect, sosai Saifuddeen ya haɗu, haƙiƙa musamman a irin wannan rana ko maƙiyinsa bai isa kushesa ba.
Zaleeha na gama shiga cikin motar Sule driver ya maida murfin motar ya rufe.
wata muguwar hararan Balkeesu ta abkawa Sule driver, cikin takaici tabi Rasheeda suka shiga wata mota ta daban.
Ahankali Sule driver ke tafiya dasu acikin motar, idanu Saifuddeen ya lumshe tare da jingina bayansa da jikin kujeran motar, sosai yake shaƙan daddaɗan ƙamshinta, hakanan haɗewar ƙamshin turarensa da nata suka ba da wani irin yanayi me daɗin gaske, irin yanayin ƙamshin nan mai sauƙar da kasala uwa uba ga sanyi Ac da motar ke busa musu, cikin nutsuwa ya ɗaura hannunsa ɗaya akan nata hannun, take haɗuwar lallausan fatar jikinsu waje ɗaya ya ƙara sauƙar masa da kasala, cikin ƙunan rai da hatsala Zaleeha tayi yunƙurin janye hannunta baya, amman sai ta gaza hakan jin ya rumtse tafin hannunta cikin nashi sosai zuciyarta ke tafasa, gefe guda kuwa ga ƙamshin turarensa wanda gaba ɗaya yabi ya cika mata hanci yana birkita mata kwanya sai shaƙar daddaɗan ƙamshin nashi takeyi, wanda tsabar tsanan da tayiwa mai turaren yasa take ta son cusawa ranta tsanan ƙamshin turaren nasa har wani abu me ɗaci-ɗaci take rayawa kanta takeji acikin maƙoshinta, zuwa yanzu har rasa yanda zata misalta tsanarsa aranta takeyi, komai bayayi mata daɗi, tana daurewa ne kawai don plant ɗinsu da suka shirya yakai ga ci, ga kuma gargaɗin ya Habu wanda tasan ba mitunci ne dashi ba, bacin haka babu wani abu da zaisanyata zuwa wannan banzan diner'n toma da wanne angon zata taka ta shiga.
Ganin tajanye hannunta daga cikin nasa yasanyashi maida kansa jikin lallausan kujeran motar, numfashi yake fitarwa ahankali, yayinda wani irin kasala ke sake lulluɓe masa jiki.
Kowannensu zuciyarsa ɗauke take da tunani kala-kala shi ji da gani yake kamar bata tsiraba daga sharrin masu son saceta da haryanzu hidimar bikin bata barshi ya gama bincikosu ba,
ita kuwa ji take da zama kusa dashi gwara zama kusa da bakin kura.
A haka suka ƙaraso babban wajen wanda aka ƙawatasa iya ƙawatuwa, wato Gombe International Hotel, sosai wajen ya haɗu komai gwanin burgewa ga kuma tsaron da dole yasa yaran Dalla barin wurin.
Acan cikin babban hall din da za'a gudanar da diner ɗin kuwa, kowa zuwan ango da amarya kawai yake jira, gaba ɗaya mutanen dake wajen zuciyarsu awanke take da farinciki, yayin dasu Hayatuddeen keta ɗaukan pictures, suma zuwan ango da amarya kawai suke jira kafun nan abasu filin cashewa, don al'ƙawarine yau sai gaba ɗayansu sunnu nawa Hamma Saifuddeen ɗin gata, wannan rana itace ranan da Hayatuddeen dakuma gaba ɗaya dangin da abokan Saifuddeen ke jira, hakan yasa suke fata da burin faranta ran ɗan uwannasu tahanyar ƙawata masa bikin nasa yanda zaiyi armashi.
Labarin isowar ango da amarya da MC yajine yasanyashi soma labartawa jama'an wajen cewa.
"Allah yayiwa ango da amarya isowa."
Nanfa kowa ya zubawa ƙofar hall ɗin ido, gaba ɗaya mutanen wajen sun zaƙu dason ganin amarya da angon.
Ishaq wanda yasha dakakkiyar shaddarsa blue tare da wani haɗaɗɗen glass, wanda idan baka san shiba bazaka taɓa shaida cewa makaho bane, don kuwa komai nasa irin na masu gani yakeyi, Ishaq da kuma Ahmad haɗi da Hisham da kuma Aziz wanda yana ɗaya daga cikin abokan Saifuddeen wanda sukayi Gombe State University tare sune suka fita don zuwa taro ango da amarya, wanda dama tuni su Balkeesu da Rashida suna da ƙannan Ya Aminu yaran Yayan Baba malam da yara Goggo Maryam da dai sauran ƴan uwan amarya waje, don kuwa sune suka riƙewa amarya Zaleeha ƙasan rigarta dake da matsanancin tsawo, wanda dole ya zama sai an riƙe mata shi.
Sule driver ne ya ya buɗewa Saifuddeen ƙofar motar tare da ware masa sabuwar kekensa mai azabar kyau, har wani ɗauke ido da ƙyallinta keyi
Cikin azama da alamun iya sarrafa kai da cikar nitsuwa ya hawa kan keken Saifuddeen ya dai-daita zamanshi hakan kuwa sai yayi bala'in ƙarawa kwalliyar tasa armashi, don kuwa wani irin kwarjini ne yasake bayyana atattare dashi, zamansa akan wheelchair ɗin nasa sai ya ƙara masa girma da wani irin kima, ya fito tamkar jinin sarauta sule driver ne ya buɗewa Zaleeha murfin motar, ahankali ta zuro da kyawawan ƙafafunta wanda sukaji tsadaddun takalma masu kalan pitch, tana gama fitowa daga cikin motar, su Rasheeda suka tattaro ƙasan rigar nata inda suka riƙe mata shi, ahankali Saifuddeen ya danna madannin wheelchair ɗin, take yasoma tafiya dashi, cikin nutsuwa yaƙaraso inda Zaleehan ke tsaye, kasan ceqarshi dogo, kuma wheelchair ɗin yafi sauran tudu, kana tanada maddan da za'a ƙara tunda ko a rage sai ya zama yayi tsawo in ka hankosu zakayi zaton a tsaye yake hannunshi yasa ya kamo nata ya ɗan haɗe tafukan hannunsu ya rumtse.
Ahankali suka soma takawa inda yake sarrafa wheelchair ɗinsa cikin nutsuwa, wani irin haɗuwa da burgewa tsarin tafiyan tasu ya bada, duk dacewa shi yanakan wheelchair ne, amma kuma sai hakan yaƙarawa kwalliyar tasu armashi, don kuwa zamansa akan wheelchair'n ya bayyana tsantsar ajinsa da kuma kwarjininsa da kima da kamala uwa uba ƙasaita, hakan yasa mutane da yawa zasuyi masa kallon zallan ajine da kasaita yasanyashi naɗewa akan kujeran, wanda saima ka lura sosai zaka iya gane cewa wheelchair ne don kuwa kujera ce mai tsananin tsadan gaske, musamman aka kawo masa ita daga Germany.
Ishaq da Ahamad ne ke biye dasu, saikuma su Rashida dake riƙe da jelan rigarta, bayansu kuwa Aziz da wasu matasa wanda sune zasu bada tsoro a wurun dan yanzuma akwai mashunan UD da suke zargi a wurin.
Jabeer ne da kuma Hisham ke biye dasu Ahmad ɗin a baya, sosai tsarin nasu yayi kyau, cikin nutsuwa suka kutso kansu cikin hall ɗin.
Lokaci guda mutane suka somayin hanmdala sakamakon ganinsu, dan sunyi bala'in burgesu, nanfa Diamond Photograpgy suka soma aikinsu na ɗaukan hoto, sosai akeyi musu hoto, ga wani sassanya kiɗa dake tashi. Ahmad da ishaq da Salisu da Aziz kuwa da yayyafin kuɗi suka biyo bayan ango da amrya,
yayinda rashida kuwa ke fesa wani abu mai ɗan karen ƙamshi kana yana bada kalan wal-wali.
ɗaukansu hotuna tako ina, don sun bala'in yin kyau da dacewa, yanayin yanda Saifuddeen ke hakimce akan kujeransa shiya ƙara zautar da mutane, don hakan ya masifar ɗago ajinsa, sosai yayiwa kowa kwarjini, take ƴan matan da suka samu halartan wajen diner'n suka mato akansa, sosai dayawan mutane ke hamdala da godewa Allah, don kuwa tabbas Saifuddeen ya cika cikakken namiji kuma ingarma, maiji da tashen kyau haɗi da kwarjini, haka kuma mutane da yawa ke yaba tsananin kyawun da amarya Zaleeha tayi, don kuwa kowa na iya hango beauty face ɗinta ta cikin wani ɗan abun da aka ɗiga mata akanta wanda yaɗan rufe gefen fuskarta kaɗan, sosai su Adda Rahama ke yaba kyawu da haɗuwar Zaleeha, tabbas sai yanzu suka tabbatar da cewa bawai abanza Saifuddeen ya nace akan cewa sai ita ba, haƙiƙa Zaleeha tacika mace abunso ga kowani irin ɗa namiji, sannan kyawunta ya isa kyau, sosai kowa yaga dacewarsu da Saifuddeen ɗin, don kuwa kyaune ya gauraya da kyau.
Wani irin cool music na Ed sheeran mc ya sakar musu irin mai taɓa zuciyar nan, hakanne ya ƙara bawa tafiyar da sukeyi armashi, Hayatuddeen da abokansa ne suka zo sunayi musu live vedio,
Ahaka har suka ƙarasa wajen da aka ƙawata domin zaman ango da amarya, wajene wanda aka ƙawatasa da decoration mai kyaun gaske, wanda akayi amfani da colours irin na kayan dake jikin ango da amarya, cikin nutsuwa Saifuddeen yayunƙura ya sauƙa daga kan kekensa cikin nutsuwa haɗi da salon mai armashi ya hau kan wata rantsatstsiyar royal chair wanda tagaji da haɗuwa, Rasheeda ne ta zaunar da Zaleeha agab dashi har takai ga jikinsu naɗan gogan na juna.
Kamar yanda aka saba ango da amarya na zuwa wajen diner ake fara gudanar da shagulgula hakanne yasanya babu wani ɓata lokaci MC yabuƙaci da babban abokin ango akan yazo yaɗan basu biography na ango.
Ishaq wanda fuskarsa ke ɗauke da murmushine yataso inda ya ratsa cikin yawan jama'an tamkar wanda yake gani haka yaƙarasa gaban MC, mike ya karɓa inda yayi gyaran murya, cikin nutsuwa haɗi da kamala yasoma bada ɗan taƙaitaccen tarihin Saifuddeen ɗin, sosai biography'n na Saifuddeen ya taɓa zuciyar kusan gaba ɗaya mutane dake wajen, duk da cewa in brief Ishaq ɗin yayi komai, amma tabbas rayuwar Saifuddeen cike take da al'amura masu sosa zuciya, dayawan mutanen da basusan Saifuddeen ɗin ba, sai alokacinne ma suka san da cewa shiɗin kurmane, koda Ishaq yagama bada ɗan taƙaitaccen tarihin na saifuddeen, take jama'an wajen suka soma tafi, sosai aka jinjina gwarzantaka irin na Saifuddeen don haƙiƙa yacika Namiji. Ishaq na komawa, still Mc yasake buƙatan babbar ƙawar amarya don tazo ta bada biography na amarya.
Tsulum Balkeesu tasoma ƙoƙarin miƙewa zuciyarta cike da mugunta, don kuwa dama tuni tagama kitsa kalaman da zata faɗa agame da amaryan, haka kuma tashirya gasawa Ango magana afakaice, saidai kafun ta farga sai tsintar muryar Rasheeda tayi acikin kunnuwanta, wanda sanin halin Balkeesun da mugun nufinta ne yasanya Rasheeda rigata zuwa, don tabbas tasan balallai abun da Balkeesu zata faɗa yazamanto al'khairi ba, wannan ranan kuwa ta farinciki ce, sam batason aɓata ran kowa, sudai da suka ɗaukawa kansu dala ba gammo sai suyita fama.
Cikin nutsuwa Rasheeda ta ɗan bada taƙaitaccen tarihin Zaleeha, wanda kuma iya abun da ta sani ta faɗa, nan mutane da yawa suka ƙara gaskata cewa lallai Amaryar Saifuddeen ɗin ƴar ƙwalisa ce, don aɗan biography ɗinnata da Rasheeda ta bayar, zaka fahimci cewa, itaɗin ƴar ƙwalisa ce, sannan mai aji da kuma wayewa, uwa uba ƴar gidan hutu ce, sam bata wani san baƙin cikin rayuwa ba kuma ƴar gidan mutunci ce.
Koda aka gama gudanar da biograpy nanfa mc yasake musu music mai daɗi da taɓa zuciya, inda aka ɗan soma ƴan ciye ciye wanda aka kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tsara abunci dana sha.
Haka suka shiga gudanar da diner ɗin cikin nutsuwa, bayan ankammala ciye ciye ne, mc ya sanya wata waƙa mai daɗin gaske, nanfa ya buƙaci da ƴan uwa suzo don nunawa amarya da ango ƙauna.
Aunty Rahama, Raleeya, da kuma Raihana, Aunty Kubra sune wanda suka fara miƙewa tsaye, don filin nasune na musamman, cikin yanayin taku haɗi da ɗan rawa mai burgewa suka ƙarasa kan step ɗin da ango da amarya suke, sosai suka burge kowa musamman shigar alfarman dake jikinsu tunkan su ƙaraso Saifuddeen ya miƙowa Adda Rahama hannunsa, cikin nutsuwa Adda Rahama takamo hannun nasa ta riƙe tana murmushi, hannu tasa ta shafi gefen fuskarsa take ta buɗe wata ƴar purse ɗinta, fararen ƴan dubu-dubu miƙaƙƙune suka cika cikin jakan, haka suma su Raihana da Raleeya da Aunty Kubra gaba ɗayansu jakakkunansu suka buɗe, kuɗaɗen suka ciro inda suka soma yiwa ɗan uwannasu da amaryarsa ɓarinsu, kuɗi suke zuba musu sosai har kaman basason kuɗin, yayinda wajen ya cika da kiɗa haka masu vedio da kuma photo sunatayi, abun sosai yake ƙayatarwa, shikansa Saifuddeen saida yasha mamakin yanda ƴan uwannasa ke ɓarar da kuɗi wajen yi masa liƙi, suna cikin yi musu liƙinne, Dr Adnan da kuma Ahmad, haɗi da Saminu da General Abbas mijin Aunty Kubra suka ƙaraso.
Hohoho idan bakwayi kuban waje, domin kuwa sosai suka shiga taya matansu likin, nanfa abun yaƙara girmama mutane da yawa sai sakin baki sukayi suna kallonsu, Ahmad kuwa har kamo Raleeya yake suna ɗan taka rawa atare, sosai suka nunawa Saifuddeen ɗin ƙauna, kafun daga bisani mazajensu suka janyesu inda sukabar kan dandamalin, nanfa mc yabawa gaba ɗaya abokan ango dama.
Nanfa akeyinta rigiji rabgi , domin kuwa gaba ɗayansu da rawa suka shigo cikin filin, hakanne yasa gaba ɗaya hall ɗin aka ɗau sowa, don sosai abun ya ƙayatar, babuma kamar ishaq, Aziz, Ahmad, Salisu, Warisu tumbuleƙe, Mudassir, Jabeer, Hisham, kai baki ɗayansu dai wanda suke rawa sosai, babu wani kunya ko ɗar, acewarsu ranan da suke jirane tazo, Ibrahim, Wareesu, Saleesu, Saminu, da kuma Aziz da sauran school friend ɗin Saifuddeen ɗin kuwa suma sosai suka taka, Ishaq ma da ba gani yake ba haka ya gwada basirarsa wanda ya burge kowa, Ahmad ne ya jawo Saifuddeen zuwa cikinsu, har tsakiyarsu ya jawosa bisa kan wheelchair ɗinsa, nanfa suka kewayesa sukayi mishi zube suna rawa tare dayiwa junansu ɓarin kuɗi, ko ina dake cikin hall ɗin tafi haɗi da shewane ke tashi, domin sosai salon na abokan Saifuddeen ya tafi da kowa, sun bala'in burgewa.
Koda suka gama bidirinsu suka koma, nanfa mc yayi gyaran murya tare da ƙiran masu gayya da aiki, ginshiƙai kuma ƙannen ango.
Hohoho inji hausawa sukace abu namu maganin akwaɓemu.
Su Hayatuddeen da Zakariyya Imran da Sulaiman kana isma'il da Faruq ɗan Adda Rahma.
Manyan ƙanne, yara matasa masuji da ƙarfi ajikinsu, ƴan matasan da suke ji da tashen tasowarsu, salon rawar tasuma ta dabance don kuwa saida ango da kansa yashiga tafa musu, don da wani irin ƙayataccen rawa suka shigo cikin filin, nanfa aka somayi musu ihu ana ƙara zugasu kansu na ƙara girma, harta Isma'el ɗan Alhji Kaburu dayake kurma saida ya taka, sosai Hayatuddeen da abokansa Imran, Sulaiman, Isma'il da ƙanin amarya Zakariyya rawa irin ta zamani sukeyi mai ɗaukar hankali, hakanan jama'an wajen sukaji kwaɗayin yi musu liƙi, don kuwa rawan nasu yayi kyau sosai, nanfa jama'a suka soma yi musu ɓarin kuɗin.
Ango Saifuddeen kuwa sai wani ƙasaitaccen murmurshi yaketayi hannunshi rike da hannun Zaleeha daketa mutsutsun kwacewa, yayinda hawaye ke zubo mata tabbas taron ya haɗu iya haɗuwa irin haɗuwa na kece raini da nunawa sa'a taso ace da wanda take sone take zaune a yanzu ,domin har tsikar jikinta tashi yakeyi yadda hall ɗin ya ricaɓe aketa ɓarin kuɗi, ita da kanta tasan babu ƙaranta a bikin ta kuma yarda komai na alfarma akeyi ta gamsu da ranta mijinta kuma kekyawane irin kyau na kece raini da nunawa sa'a ta kuma gamsu mai cikekkiyar tsabta ne da gayu, kuma masoyine na gaskiya dan taga salon zazzafar soyayyarshi to amman mijinfa bashi da maraba da ginennen taɓo kuma duk haka tasan yazo a ƙirerren lokacine wlh da yazo kafin haɗuwanta da wanda ya taimaketa tabbas yanada nagartar da dole ta soshi to amman a makere yazo, kuma sai takeji can cikin zuciyarta kamar wani abu ke sarrafa mata zuciya,
bata dawo daga duniyar tunaniba taji sauƙan tattausan yatsunshi kan haɓarta da sauri ta ɗan juyo ta kalleshi sai kuma tayi maza ta lumshe idanunta ganin ya ɗaga mata girarshi ɗaya tare da kashe mata ido kana ya ɗan kaɗa mata harshe alamun,
ya dai, kana ya ɗan nago hannunta dake tsarke da nashi bayan hannun nata ya juya tare da manna mata wani irin sassanyan kiss.
wow nanfa masu hoto suka koma kansu.
Cikin farinciki Hayatuddeen yaƙarasa wajen Hammansa nanfa yasanja salon rawarsa, hannun Hamman nasa ya kamo, ahankali yake juya kujeran Hamma Saifuddeen ɗin nasa, hakan yasa abun yaƙara armashi, murmushin farinciki kawai Saifuddeen ɗin keyi, haƙiƙa ƴan uwa da abokansa sun nuna masa tsananin gata, nanfa Hayatuddeen da abokansa suka ciro kuɗaɗen al'jihunsu suka soma zubawa Saifuddeen da Amarya Zaleeha, Zakariyyane yaƙarasa jikin ƴar uwartasa ahankali ya kamo hannuwanta tare da jawota tsakiyan filin, tayi matuƙar mmkin ganin Ya Aminu Ya Ahmad Ya Habu Aunty Shatu Aunty Lubna da Adda Maryam dasu Amira ƙannen ya Aminu sun mata zobe ita da ango Saifuddeen suna mata yayyafin kuɗi, Zakariyya kuwa nan ya riƙe duka hannuwanta, cikin tsananin ƙaunar ƴar uwartasa yasoma ɗan jijjigata hakanne yasa Zaleeha taɗan saki murmushi, nan taɗan soma ƙafafunta, ganin haka yasa gaba ɗaya su Hayatuddeen suka ke wayeta suna rawa, bisa dole Zaleeha ta biyesu suka ɗan soma takawa,don kuwa ansanya musu wata daddaɗan waƙa, wanda ko baka da niyar yin rawa saika taka, bare ita Zaleeha uwar son waƙa da kiɗi haka yasa taɗan saki jikinta bayan anyi musu ɓarin kuɗi sosai takoma kan kujeran ta zauna tana me maida ajiyar zuciya.
Haka dai akayita shagulgula masu ƙayatarwa yan ƙungiyar jonapwd sunyi matuƙar bada mmkin irin kuɗaɗen da suka liƙawa ango, nairori kam awannan rana sunyi kuka sosai, an ɓarnatar dasu baɗan kaɗan ba, sai wajen ƙarfe 10:00 pm, aka kammala gudanar da diner'n, nan kowa yasoma ƙoƙarin tafiya gida, don dayawan mutane amatuƙar gajiye suke, babuma kamar Saifuddeen, wanda dama shi sam bai iya jure wahala, abu kaɗan ke gajiyar dashi, sai yaji duk yazama very weak bare kuma ga hidimar da yasha, yanzuma babu wani abu dayake buri da fatan gani kamar Umminsa, so kawai yake yaje yayi mata complain ɗin gajiyar dake damunsa, kamar yanda sukazo amota ɗaya haka komawarsu ma takasance amota ɗaya, saidai har suka iso gidan ko ƙala baice mata ba, gaba ɗaya gajiya ke damunsa, itama Zaleehan agajiye take hakan yasa ta lafe jikinta ajikin kujeran motar tare da lumshe idanunta da suke cike da bacci.
Jin isowarsu yasanya dakanta ta buɗe murfin motar ta fice, ko tsayawa batayi ba, riganta na sharan ƙasa haka tanufi ɓangaren nasu, don ta zaƙu da ta cire rigan, sam bata wani iya zama da kaya mai nauyi ba, musamman ma wannan dayake wedding gown.
Shima Saifuddeen saita wheelchair dinsa yayi tare da hawa kai, kaitsaye yanufi cikin gidan nasu.
Kasancewar