Showing 96001 words to 99000 words out of 239422 words
Chapter 33 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
Murmushi Zaleehan tayi, tana ƙoƙarin cewa wani abune taga screen ɗin wayarta ya kawo haske, hakanan taji ƙirjinta ya buga, zuciyarta ta tsinke, jawo wayartata tayi tare da dubawa, text message ta gani da sunan Zakariyya, nan ta cire wayan a key, tare da shiga cikin message ɗin.
Hannunta na ɓari jikinta na rawa, haka tashiga karanta message ɗin, maganansa na kusa da na ƙarshe shine abun dayasa taji gaba ɗaya duniyar ta tsaya mata kanta yayi wani irin mugun sarawa duhu ya wulgawa ganinta, azabure ta miƙe tsaye, cikin wani irin gigita haɗi da kiɗima da tsananin tashin hankali ta dannawa numbern Zakariyyan ƙira, bugu biyu kuwa ya ɗauka, yana kara wayar akan kunnensa ya saki kuka, abun dayasa hankalin Zaleeha tashi kenan, lokaci guda bakinta ya soma ɓari, murya asarƙafe tace. "Zak....kar iya, ina Adda Maryam, meya sameta, mekakeson faɗamin Zakariyya?"
Cikin matsanancin kuka Zakariyya, yace.
"Adda Maryam tarasu Zaleeha, Adda Maryam ta rasu tun daren jiya, tatafi inda bazata ƙara dawowa ba, tayi nisa nisa irin na har abada....."
Kuka ne ya ci ƙarfinsa hakan yasa ya kasa ƙarasa maganan.
Tun afaɗan maganganunsa na farko, ta dainajin komai, duk wani abu najikinta tsayawa yayi, wayar hannunta ne ta sulale inda ta faɗi ƙasa, wani irin ƙara ta saki take kuma ta faɗi awajen sumammiya, cikin matsanancin tashin hankali, Aisha tayi kanta tana jijjigata, haɗi da ƙiran sunanta, ihunta da su Elizabet sukaji ne yasasu shigowa aguje, ganin Zaleehan asume yasa Elizabet dafe ƙirji cikin ɗaga murya tace.
"Innalillahi, a madadin tace Oh jesus meya ke faruwa?" Uncle solomon ne ya fita da gudu, bajimawa ya shigo hannunsa riƙe da kofin ruwa, ƙarasowa yayi inda ya ɗan yayyafawa Zaleehan ruwa afuskarta.
Azabure tatashi, cikin wani irin tashin hankali, damƙo Aisha tayi tana me jujjuya kanta, take kuma sai ta fashe da wani irin kuka mai matuƙar tada hankali, cikin kukan take ja da baya, tana me sake girgiza kanta, hankalinta amatuƙar tashe tace.
"Aisha Adda Maryam, Adda Maryam ɗina ta rasu, Adda Maryam tabar duniya batare da na sake sanyata a idanuna ba, wayyo Allah na wayyo ni, kaicon rayuwata, kaicona !!!" Wani irin azababben kuka ta saka kukane mai cushe zuciya da numfashi, lokaci ɗaya ta miƙe tsaye wayarta kawai ta ɗauka tare da buɗe jakanta, kuɗi ta ɗauko wanda batamasan ko nawa bane, takalmi ta zura aƙafafunta, ƙoƙarin fita daga cikin ɗakin take Elizabet ta riƙota cikin kulawa tace.
"Zaleeha ina zakije, dan Allah kitsaya ki nutsu tukun"
Faɗawa jikin Aishan tayi tana wani irin kuka, kanta ta girgiza cikin kuka tace.
"Adda Maryam ɗina Uncle Solomo Addana, Adda Maryam ɗina ta rasu"
Hawayen tausayin Zaleehan ne suka kwaranyo daga cikin idanun baki ɗayansu cikin sanyin murya Aisha tace.
"Muje to na rakaki ki hau mota, amma kafun nan ki kimtsa tukunna."
Kai Zaleeha ta girgiza cikin matsanancin kukan dake neman shiɗar da ita ya tafi da rants.
Hannunta Aisha ta kama suka nufi ƙofar fita daga gidan Solo da martasa na biye dasu a baya.
Gaba ɗaya Zaleeha bata cikin hayyacinta, hakanne yasa Aisha mannata da jikinta, domin kukan da Zaleehan keyi yasa bata ko iya ganin gabanta.
Suna kawo bakin titi kuwa sukai sa'a nan suka samu wata mota, wanda kaitsaye Gombe zata taho, da kwai ma mutane cike acikinta, Aisha ce tayi mata komai, tasata acikin motar, hannun Zaleehan dake kuka ta kamo, nan ta ɗan ɗaga mata hannu, itama hawayene ke zuba akan fuskarta, murya asanyaye tace.
"Allah yajiƙanta yasa al'janna tazamo makoma agareta, kiyi haƙuri kinji Zaleeha, dukkan me rai dama mamaci ne, kowa lokacinsa yake jira, dayazo kuma babu jinkiri."
Kai Zaleeha ta jinjina, tare da sakin sabon kuka, nandai Me motar yaja suka tafi, kowa dake cikin motar kallon yanda Zaleeha ke kuka suke, wasu kukan nata ya damesu, wasu kuwa matsanancin tausayinta ne ya kamasu, domin kukan da take irin kukan nanne me karƴar da zuciya, kukan da take, kukane me fitar da irin tsananin tashin hankalin da take ciki, kukane da duk me imani dole zaiji tausayinta.
Littafina na kuɗine in kin gashi yana yawoma na satane, in kina buƙatan saya ga no ɗina 09097853276
By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Sbpejg Acan gidan Baba Malam kuwa, kamar yadda Maryam ta buƙata kafun rasuwarta, Ya Ameenu da kuma Baba Malam ne sukayi mata wanka, wanda da ƙƴar suka iya daure zuciyarsu, nan ma Ya Ameenu saida ya durƙushe awajen yayi kuka sosai, har saida yaji numfashinsa na ƙoƙarin cushewa a ƙirjinsa, Baba Malam ma hawaye ne keta tsiyaya daga cikin idanunsa, haka dai suka kammala yi mata wanka, Ya Ameenu ne ya zura mata likkafani, sannan yayi mata duk wani abun daya dace, sosai jikinsa yake rawa, sakamakon kukan da yakeyi, ga wani irin jiri dake neman kadashi.
Bayan sun kimtsa ta ne suka koma gefe suka zauna, dan kuwa da sauran lokaci, ƙarfe goma ne za a sallaceta, yanzu kuwa ƙarfe 9 ne dai-dai.
Can ɓangaren Zaleeha kuwa, tunda ta shiga cikin motar, ta tura kanta tsakankanun cinyoyinta har zuwa yanzu bata ɗago ba, kuka take sosai harsaida numfashinta ya soma ƙoƙarin ɗaukewa, sosai motar tasu ke tsula gudu akan titi, hakanne yasa cikin abun dabai wuce awa uku ba suka iso cikin garin Gombe, nan cikin tashan gombe line aka sauƙe su, zuwa lokacin idanunta sun kunbura sunyi luhu-luhu dasu,
kaitsaye bakin titi ta nufa, wani mai adai-dai ta sahu wato keke napep ne, ya tsaya agabanta tare da ɗan leƙo kansa, cikin kulawa yace. "Ranki ya daɗe tafiya ne?".
Bata iya cewa dashi komai ba, kawai faɗawa cikin keke napep ɗin tayi, nan ta jingina kanta da jikin keken, kana ta rumtse idanunta, wasu hawaye masu ɗumi ne suka silalo daga cikin idanunta, dubanta me adai-dai-ta sahun yayi, cikin yanayi naɗan mamakin ganin hawaye akan fuskarta, yace.
"Hajiya ina zamu ne?".
Kasa amsa masa tayi domi , bakinta yayi mata nauyi sosai, batajin bayan kuka zata iya motsa laɓɓanta dan tace wani abu, wayarta dake hannunta ta kunna, cikin text message ta shiga, ataƙaice ta rubuta masa.
"New G.R.A, da kuma layin da zai sauƙe ta."
miƙa masa wayar tayi, amsa yayi ya karanta, yana gama karantawa ya miƙa mata wayar, cikin ransa yace.
"Masha Allah wannan gata kyakkyawa amma kuma da dukkan alama kurmace bata magana, amma dai Allah yayi baiwar kyau anan, ko me yasata kuka kuma oho?" Ganin zancen zucin bazai kaisa ko ina ba, ya sashi tuƙa keken nasa yaja sukai gaba.
Kamar yanda ta rubuta masa arubuce kai tsaye cikin G.R.A ɗin ya nufa da ita, har kuwa cikin layin da tayi masa kwatancen ya kawo ta, gaba ɗaya bata cikin hayyacinta saboda haka batasan da cewa sun iso ba, dawani idanu zata kalli ƴan gidansu? da wani bakin zata basu haƙuri? mezata ce dasu? da wani idanun zata kalli gawan Adda Maryam ɗinta? Da wanne ƙafar zata shiga gidansu da wanne ido zata kalli Baba malam me zata ce mishi?.
waƴannan tambayoyin sune abun da suka cika zuciyarta, juyowa me adai-dai-ta sahun yayi, cikin kulawa yace.
"Ranki ya daɗe mun iso fa."
Sai alokacin ta buɗe idanunta da suke alumshe, gaba ɗaya kuɗin dake hannunta ta damƙa masa, wanda ita kanta bata masan ko dubu nawa bane, idanunsa ya waro waje, cike da mamaki, dai-dai lokacin ita kuma tafice daga cikin napep ɗin, ƙofar gidan nasu cike yake da jama'a wanda suka fara taruwa danyin sallan jana'iza, tsaye tayi tana kallon tankamemen gidan nasu, lokaci guda kuma wasu hawaye masu tsananin zafi suka fito daga cikin idanunta, da ƙyar take iya jan ƙafanta haka ta nufi cikin gidan, bataji bakuma ta ganin kowa agabanta, hakan yasa tafiya kawai take, sai faman cin tuntuɓe take tayi, amma bata ko kulawa, da wani dutse ta buge har saida babban ƴar yatsar ƙafarta ta fashe, amma koda kaɗanne bata ji zafi ajikinta ba, domin kuwa zafin dake cikin zuciyarta, ya zarce na wannan ciwon, wannanne yasa wasu daga cikin mutanen da suka zo jana'izan suka tsura mata idanu, saboda yanayinta ya gama nuna cewa bata cikin hayyacinta.
Tana jefa ƙafanta acikin gidan taji wani irin abu ya daki zuciyarta, kaitsaye sashin Baba Malam ta nufa, sai faman gauraya hanya take, tana zuwa dai-dai bakin ƙofar shiga falon Zakariyya yazo zai fito sukayi karo da juna, amatuƙar mamakance Zakariyya yasoma ja da baya yana komawa cikin falon, dai-dai lokacin kuwa nan cikin falon Baba Malam ne zaune yana kuka mai tsananin taɓa zuciya, kuka yake sosai wanda hakan yasa gaba ɗaya mutanen falon suma suka fara zubda ƙwalla, cikin kuka murya na rawa Baba Malam ke cewa.
"Ya Allah ka jiƙan Maryam kayi mata rahama,ya Allah ka ƙara mana haƙurin rashinta.
Tabbas mutuwa ta yanke mana ƙauna, mutuwa ta nesantani da ƴata me tsananin biyayya agareni."
Sai ya kuma saki shessheƙan kuka mai cike da ciwo a zuciya murya a disashe yace.
"Inama ina ma da ace mutuwa tana bada zaɓi.
To wallahi dana bata zaɓi ta ɗauki min Zaleeha a doron duniya tabarmin Maryam, dana bata zaɓi ta nesantamin Zaleeha daga wannan duniyar ta barmin Maryam! Da ta ɗauke Zaleeha dana huta da baƙin cikin da take ƙunsamin."
Ya ƙare maganar yana kuka sosai.
Waɗannan maganganun sune suka dira acikin kunnuwan Zaleeha, Zakariyya kuwa bakinsa na rawa, cikin ɗan ɗaga murya yace.
"Adda Zaleeha!." Ƙiran sunan Zaleehan da yayi, shiya sanya gaba ɗaya mutanen falon suka kai dubansu ga ƙofan shigowa, ae kuwa tabbas suka ga Zaleehan ce tsaye, hawaye na shatata akan fuskarta kaman an buɗe famfo, dai-dai lokacin kuwa aka fito da gawar Adda Maryam daga ɗakin Baba Malam, angama kimtsata tsaf saura ai mata sallah kawai akaita makwancinta na gaskiya.
Cikin wani irin gigita Zaleeha ta ɗaga ƙafanta da niyar ƙarasowa cikin falon, Baba Malam ne ya ɗaga mata hannu, alaman dakatarwa, kanta ta shiga jujjuyawa tana kallon gawar Adda Maryam ɗin, take ta saki wani irin firgitaccen kuka mai tsananin ƙarfi, tare da sulalewa anan jikin ƙofan falon, tana wani irin kuka mai tada hankali.
Daga Ya Ahmad zuwa kan sauran ƴan uwanta kuwa babu wanda ya dubeta, dai-dai za afita da gawan Adda Maryam ɗinne, Ya Ameenu yasake sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya, take kuma sai wani irin jiri ya ɗebesa haka yatafi luuu, ya faɗi ƙasa sumamme, abun daya ƙara ɗaga hankalin su Baba Malam kenan, Cikin kuka Baba Malam yace amiƙo masa ruwa, Zakariyya wanda ke kuka sosai ne ya miƙowa Baba Malam ɗin ruwa, nan Baba Malam ya ɗan yayyafa ruwan akan fuskar Ya
Ameenu'n, saida ya ɗauki kusan mintuna 7 bai farfaɗo ba koda ya farfaɗo kuwa da wani irin kuka mai tsanani ya tashi, kuka yake sosai tare da rirriƙe Baba Malam yana nuna masa gawar Adda Maryam, Wannan abun shiya ƙara sanya gaba ɗaya mutanen falon kuka, cikin kuka Baba Malam yasanya hannu ya dafa kafaɗan Ya Ameenu'n, cikin matsanancin tausayawa yace.
"Muyi haƙuri Ameenu, kada rasuwar Maryam yasa imaninmu gushewa, tabbas duk wani me rai mamaci ne, mutuwa bata barin wani dan wani, da ace tana bari kuwa da ta barmana Maryam, kayi haƙuri ka tuna da wasiyan da ta barmaka, kacika mata wasiyarta, katashi muje asallace ta, kasata acikin kabarinta kamar yanda ta buƙata."
Zaleeha dake durƙushe tana kuka, duk abun dake faruwa akan idanunta, hakanne yasa ta ƙara gigicewa, kuka take jikinta na tsuma, ko ina na jikinta rawa yake.
Ya Ahmad dake kuka sosai idanunsa gaba ɗaya sun kunbura sunyi suntum, shi ya riƙo Ya Ameenu, Haka duk jama'an dake cikin falon suka mimmiƙe, Zaleeha dake durƙushe bakin ƙofa ganin za a fita da gawan Adda Maryam ɗin yasa,ta sakin wani irin gigitaccen ƙara me ɗauke da kuka, zubewa tayi awajen takama ƙafan Yaya Fahad, da kuma na Yaya Sudais, wato ƙannen Ya Ameenu kenan, wanda suke ɗauke da gawan, sai kuma wasu abokan Baba Malam na kusa, cikin fusata Ya Fahad da Sudais suka ƙwace ƙafafunsu, dan kuwa gaba ɗaya family'n cike suke da baƙin cikin ta, haka tanaji tana gani suka fita da gawan Adda Maryam, Wani kukan kuma ta sake wanda yafi kowanne zafi, haka Baba Malam da kuma sauran jama'an dake cikin falon suka tsallake Zaleeha suka wuce, Ya Ahmad ne yayi fitan ƙarshe, cikin matsanancin kuka Zaleeha ta kama ƙafan Ya Ahmad ɗin tana wani irin kuka, cikin matsanancin kukan da yake cinsa ya ƙwace ƙafarsa, tare da wucewa ko waiwayenta baiyi ba. Wannan dalilin yasa ta soma buga kanta ajikin bango tana kuka, mai ɗauke da fitar hayyaci.
Acan waje kuwa ana fita da gawan nata, jama'a suka soma kimtsawa, Baba Malam shikansa ya shiga mamakin irin yawan mutanen da sukazo sallan jana'izar Maryam ɗin, saboda mutanene da yawa kamar ƙasa, ga wanda baisani ba ma zai iya cewa wani babban malami ko kuwa babban ɗan siyasa ne ya rasu, dan jama'an sun zarce tunaninsa, daga gidan su Saifuddeen kuwa babu wanda baizo ba, kama daga kan Saifudeeen, Ahmad, Dr Adnan, Bappa Ali Malam Ashiru Hayatuddeen, Harma dasu Wareesu abokan Saifudeen gaba ɗaya sunzo, ga Ishaq ma da Babansa Dirankadi da ƙananinsa Imran duk sunzo.
Haka akayiwa Maryam Sallah, nan aka ɗauketa aka sata acikin motan gawa, Dayawansu kuka suke me tsuma zuciya, haka dai waƴanda zasu rakata zuwa maƙabarta suka shiga cikin motocin da zasu tafi, ciki kuwa harda Ahmad da Dr Adnan da kuma Hayatuddeen, Saifuddeen kuwa anan ƙofar gidan suka zauna, saboda shi bazai samu zuwa maƙabartan ba, saboda larurarsa.
Acan cikin gida kuwa, Zaleeha har yanzu na zaune anan bakin ƙofar falon na Baba Malam, tana wani irin kuka, tariga da ta zauce, gaba ɗaya ta shiɗe bata wani cikin hayyacinta, wani irin kuka take wanda duk wani wanda ke cikin hayyacinsa dole ya tausaya mata, tun muryarta na fita har ya zamana kukan kawai takeyi, idanunta sunyi wani irin kumbura, fuskarta tayi jajur, cikin haka numfashinta ya soma ƙoƙarin ɗaukewa, duhu ne ya soma rufe ganinta, take kuwa ta sulele ƙasa daga durƙushen da take, lokaci guda numfashinta ya ɗauke, haka dai takejin kanta kamar ba aduniya take ba.
Sama da mintuna 20 ta ɗauka batare datasan inda hankalinta yake ba, harzuwa wannan lokacin kuwa babu wanda yazo yabi ta kanta, zafin ranan dake dukan jikinta shine abunda yasanya taɗan buɗe idanunta wanda suka wani irin ƙanƙancewa, hawayene suka kwaranyo daga cikin idanun nata, ahankali ta tashi inda ta jingina bayanta da jikin ƙofan falon, kuka ta fashe dashi tare da dafe saitin ƙirjinta wanda keyi mata zafi.
Aunty Lubna da tazo wucewa ne taga Zaleehan ahaka, ɗan tsayawa tayi tana meyi mata kallon mamaki, ganin Aunty Lubna yasa tasoma yunƙurin tashi dan zuwa ga Aunty Lubna'n, cikin sauri Aunty Lubna taja baya, hawayen dake cikin idanunta ta share, ɗauke kanta tayi daga kallon Zaleehan taci gaba da tafiyanta.
Abun daya ƙara sautin kukan Zaleehan kenan, nan ta zube akan guiwowinta tana kuka, gaba ɗaya aduniya babu inda zata shiga taji sanyi, kowa fushi yake da ita, gaba ɗaya danginta sun ƙita, harma da wanda take tunanin zasuji tausayinta, sun nuna mata fushi alokacin da take tsananin buƙatarsu.
Acan maƙabarta kuwa, Baba Malam da Ya Ameenu ne suka sanya Adda Maryam cikin ramin ƙabarinta, shikuwa Ya Ameenu zuwa yanzu gaba ɗaya hawayensa sun kafe, idan kuwa ya maka kallo ɗaya bazaka so ya ƙara ba, saboda gaba ɗaya idanunsa sun rune, sun zama jajur kamar wanda aka watsa masa garin barkono, zuwa yanzu yadaina tunanin komai, haka ya zama kaman mutum mutumi wato, statue, hatta da buɗe bakinsa baya iyawa, lokaci ɗaya yazama wani iri dashi, cikin rana ɗaya yayi wani irin muguwar rama, suna gama bunneta suka soma ƙoƙarin barin maƙabartan, amma me Ya Ameenu zama yayi anan bakin kabarin nata, da ƙyar su Malam Adam da Dirankadi suka lallashesa, Ya Ahmad dake wani irin kuka ne ya kama hannun Ya Ameenun suka fito daga maƙabarta'n, dan kuwa Ameenun yazama kamar wani ƙaramin yaro, ba ya um baya um um saidai shiru kawai, harkuwa suka shiga cikin mota bai daina kallon kabarin Maryam ɗin ba.
Dahaka suka nufo gida. Suna ƙarasowa ƙofar gida kuwa suka samu ankakkafa manyan runfuna, nan suka zauna ko cikin gida basu shiga ba, dan amsar gaisuwa, Baba Malam wanda da taimakon addu'o'in da yakeyi, yaji zuciyarsa ta ɗan samu salama, duban Zakariyya, dake zaune abayansa yayi, cikin muryarsa dake nuna