Showing 45001 words to 48000 words out of 239422 words
Chapter 16 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
da sanya hannunta, kasancewar kowa yasan cewa, ita ɗince ke zugata akan wasu abubuwa itace ke gurɓata komai na Mamansu.
Ya Ameenu kuwa yanzu damuwar rashin lafiyar matarsa ne ya damesa, don kuwa tun randa Zaleeha ta gudu, Maryam ta kwanta zazzaɓi da ciwon kai, kasancewar bata da wani aiki kullum sai kuka, sosai ɓatan ƴar uwartata ya shiga jikinta, gefe guda kuwa ga Baba Malam daya shiga halin baƙin ciki, kowa ya gansa yasan da cewa yana cikin damuwa, kasancewarsu Yara masu biyayya hakan yasa basa ƙaunar ganin damuwar mahifinsu, uwa uba ga Mama da ta bar gidan, wannan abu na damun Maryam sosai, ganin lokaci ɗaya zuri'arsu naneman watsewa komai ba daɗi ga ɓatan ƴar uwa ga saɓani tsakanin iyayenta ga ɓacin ran mahaifinta damuwa dai ta taru ta cika zuciyar baiwar Allah.
Ƙarfe 10 na safiyar ranan dai-dai Ya Habu ya kama hanyar zuwa Doho.
Zaune yake akan wheelchair ɗinsa mai kalan silver gold, sanye yake da wani army jeans, sai kuma wata farar long sleeve wanda ya nannaɗe hannun rigar zuwa guiwar hannunsa, aƙafansa kuwa, wasu fararen bedroom slippers ne masu kyau, kamar koda yaushe laptop ɗinsa ne, ɗaure akan cinyarsa, sosai ya bata hankalinsa gurin binciken da yakeyi.
Gefensa Ummi ne wanda tayi jigum, duk damuwan ɓatan Zaleeha ya isheta, kusa da ita kuwa Hayatuddeen ne zaune yana ta faman latsa wayarsa, inda ya ɗan kaucewa ganin idanunsu ya matsa can gefe, chatting yake sosai, da wani sabon abokinsa da yayi acikin G.S.U, wanda yakasance department ɗinsu ɗaya, sunan abokin nasa Khamis, sosai Hayatuddeen yasoma shaƙuwa da Khamis, wanda yake kuma Khamis, yaro ne wanda bayajin magana sam, babansa mai kuɗin gaske ne, gidansu yana nan cikin New G.R.A, gaba ɗaya Khamis asangarce yake, kasancewarsa shine ɗa namiji agidansu, hakan yasa gaba ɗaya iyayensa suka sakar masa yarda, tare da bashi daman yin duk abun da yake so, shikuwa Khamis tun da yaga Hayatuddeen, yaji cewar yana sonsa da abota, kasancewar Hayatuddeen ba laifi yana shiga mai kyau da burgewa, sannan yana ɗan chilling ɗinsa, da sabuwar iphone ɗinsa, makaranta kuwa kaisa ake amotar gida sannan driver ya ɗauko sa, shikuwa Khamis jibgegiyar motace ahannunsa, hakan yasa ko zaman school ɗin bayayi, da yazo sai yawo kawai, kamar da wasa kuma suka fara abota da Hayatuddeen wanda gashi kuma zuwa ayanzun abotan nasu ya soma ƙarfi.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe tare da lumshe kyawawan idanunsa, buguun zuciyarsa ne ya ɗan sassauta ahankali, hannunsa yasanya inda ya kama ƙasan haɓarsa, numfashi ya sauƙe, tare da fesar da wani irin iska mai zafi ta bakinsa,
*"NUMAN"* shine abun daya faɗa acikin zuciyarsa, sake duba inda location ɗin ya tsaya, kansa yajinjina tare da ɗan cije laɓɓansa, tabbas tana can Adamawa cikin Numan domin kuwa, haka sakamakon tracker ɗin da yayi ya nuna mishi.
Ɗan jim yayi tare da lumshe idanunsa,
"Tabbas tana can Numan, amma kuma waye nata acan, da zata je ta zauna?."
Tambayar da yayiwa kansa kenan, sanin cewa bashi da amsa yasa shi, sakin ɗan guntun murmushi, wato da zama dashi ne ta gwammace rayuwa a wancan ƙauyen mai cike da yawan ƙabilu arnataku, hmmmm shikuwa zai zuba mata ido ya gani, bakuma zai faɗawa kowa inda take ba, sannan zaiyi duk yanda zaiyi wajen ganin, ya cire Umminsa adamuwa, dan tasanya ɓatan Zaleeha'n, sosai acikin ranta.
Ta gigita mishi ƴan uwa da abokai gaba ɗaya, Ishaq Salisu Warisu Mudassir Aziz hatta Saminu Hishsm, Jabeer, da baya garin duk ta tashi hankalin kowa.
Yasan ko ahaka Allah bazai bar Zaleeha ta zauna cikin farin ciki ba, saboda yasan ta ɗauki al'hakin iyayenta, sannan ga igiyar aurensa dake kanta, wanda take ta walagigi dashi.
Wheelchair ɗinsa ya danna inda ya ƙarasa har gaban Umminsa, hannunsa ya ɗaura akan na Ummi'n, cikin kulawa ya karyar da kansa, tare da ɗan marairaice fuska, anutse yayi mata alama, cikin body language cewa.
"Ta daina sa kanta adamuwa, Zaleehan zata dawo nan bada jimawa ba."
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe, cikin rauni ta dubeshi, murya asanyaye tace.
"Banajin daɗi Saifuddeen, idan na tuna da cewar sanadiyar aurenka Zaleeha ta gwammace barin iyayenta, yayunta, ƙannenta, aikinta, mahaifanta, da duka danginta, wannan abun shine abun danake ta gudu tun farko, shiyasa naso afasa auren, gashi yanzu an nemeta an rasa, babban tashin hankalina ma, shine bamu da tabbacin cewa ko lafiya take!."
Kansa ya girgizawa Ummin nasa, tare dayi mata alaman cewa.
"Zaleehan tana nan lafiya ƙalau aduk inda take."
Kai kawai Ummi ta jinjina masa don bata iya cewa komai.
Can Doho kuwa, Ya Habu na isa gidan Aunty Ruda yayiwa tsinke, Aunty Ruda na ganinsa ta taɓe baki, don tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, first abun da Ya Habu ya fara tambayarta shine.
"Ina suka kai Zaleeha?."
Shewa tayi tare da cewa.
"Ae baku bani ajiyan Zaleeha ba, balle kuce zaku zo nemanta, abu mafi sauƙi ku shiga uwa duniya ku nemeta kawai, tun da kune kuka salwantar da rayuwarta."
Wannan abun shiya ƙara harzuƙa Ya Habu, nan take ransa ya ƙara baci, haka yayiwa Aunty Ruda'n tas, inda ya wanketa soso da sabulu, ya ɗora da cewar.
"Ita ke zuga mamansu akan komai, kuma wallahi su fito da Zaleeha, duk ma inda suka kaita suka ɓoyeta, kuma ta daina zuga musu uwa tana tura mata halinsu na arna ya ƙara da cewa kada tayi zaton basu gane ita ke zuga Mamaba."
Haka yabaro Doho'n ransa amatuƙar ɓace, domin yasan da cewa sunsan inda Zaleehan take faɗa ne kawai bazasuyi ba.
Bayan kwana 5 da dawowan Ya Habu daga Doho, Baba Malam ya kwanta rashin lafiya, inda ciwon hawan jininsa ne ya tashi, nanfa gaba ɗaya ahalin suka sake shiga cikin tashin hankali, ga jikin Maryam ma da yaƙi daɗi, bata da wani zance saina ƙanwarta Zaleeha.
Saifuddeen dake zaune afalon Ummi ne, ya kwantar da kansa ajikin kujera, yanzu labarin rashin lafiyar Baba Malam ya iskesa, hakanne yasa yaji babu daɗi acikin ransa, sam ada baiyi niyar faɗawa kowa inda Zaleehan take ba, yaso barinta ne idan tagaji don kanta zata dawo, amma ayanzu yazama dole ya faɗa, kodan saboda rashin lafiyar Baba Malam ɗin ma.
Computer ɗinsa ya ɗauka, inda yayi rubutu mai ɗan tsawo, sannan ya nunawa Ahmad, bai jirayi Ahmad yagama karanta saƙon ba, ya ciro wayarsa inda ya turawa Ya Ameenu saƙo, wanda ya rubutashi ataƙaice.
Ahmad nagama karanta saƙon ya ɗago ya dubi Saifuddeen, kai Saifuddeen ɗin ya jinjina masa, ajiyar zuciya Ahmad ɗin ya sauƙe, nan yakai dubansa ga Ummi, sai kuma Adda Rahama dake zaune, cikin nutsuwa Ahmad yace.
"Ummi Saifuddeen ya ganno inda Zaleeha take fa."
cikin mamaki Ummi tace.
"Ta ina? Tana ina? ko wani abune ya sameta?."
Kai Ahmad ya girgiza, cikin nutsuwa yace.
"Uhmmm Ummi kenan wato dai kuna ganin kaman Zaleeha ɓata tayi ko, hmmm to wlh Zaleeha ba ɓata tayi ba, guduwa tayi da ƙafafunta, sannan yanzu haka tana can Numan, halan akwai wasu ɓoyayyun ƴan uwanta acanne, wanda tunanin su Ya Ameenu da Habu baije can ba, amma dai yanzu Saifuddeen ya faɗawa Ya Ameenu'n."
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare dayin hamdala acikin ranta, tabbas ta ɗanji sanyi acikin ranta,don dama ɓatan Zaleehan yayi mata tsaye acikin rai, itakuwa Adda Rahma shiru tayi tana meyin wasu nazari, hakanan Zaleehan ta soma sanewa acikin ranta, tabbas ita duk wani wanda baison Saifuddeen, to fa itama bata
ƙaunarsa ko kaɗan. Raihana kuwa da dama can bata wani sake da Zaleeha a rantaba, sai taji ta fice mata a rai haushinta kawai takeji har ita waye da zatace bata son Hammanta me ya rasa dame sauran maza suka fishi haka dai taketa ƙunƙuninta.
Ƙiran Ya Ameenu ne yashigo wayan Ahmad, da sauri Ahmad ya ɗaga wayan.
Daga ɓangaren Ya Ameenu, wanda ke zaune acikin falon Baba Malam, kasancewar dukaninsu suna cikin falon, hakan yasashi sanya wayar a speeker, yanda kowa zaiji, tambayar Ahmad yayi akan saƙon dayaga Saifuddeen ya turo masa, nan take Ahmad yayi masa bayanin dukkan abun da Saifuddeen ya faɗa masa, inda yace ta hanyar yin tracker Saifuddeen ɗin ya gano inda take.
Nan take gaba ɗaya suka cika da mamaki, domin koda wasa basu taɓa zaton cewa zataje Numan ɗinba, saboda su kwata-kwata ma sun manta da cewa Mama tana da ɗan uwa acan, domin kuwa ba zuwa take ba, suma kuma ba zuwa suke ba.
Ya Ameenu na kashe wayan, Baba Malam dake kishingiɗe yana shan fruit salad, ɗin da Mamy ta haɗa masa ya saki ɗan guntun murmushi irin nasu na manƴan dottijai murmushi mai cike da ma'anoni da manufa masu tarin yawa,
cikin baƙin ciki Ya Ameenu ya rusuna gaban Baba Malam ɗin cikin neman izini yace.
"Kayi haƙuri Baba idan kayimin izini kabarni naje ayau ɗinnan na taho da ita gida."
Ahankali Baba Malam ya aje bowl ɗin dake hannunsa kai ya jujjuya mishi alaman a a, cikin kulawa ya dubi Ya Ahmad, wanda yayi jigum, anutse yace.
"Ahmad ka ɗauki matarka gobe ku koma, banason zamanka hakanan, saboda haka ka koma bakin aikin ka."
Cikin salon bada umarni wa yaran nashi ya kalli Habu dake jin tamkar yayi fiffige ya fire yaje Numan cikin haiba da kamala yace.
"Kai kuma Habu nabaka izinin gobe kaje can Numan ɗin, badai kasan gidan yayan Mamar taku dake can ba?."
Kai Ya Habu ya jinjina tare da cewa,
"Eh."
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da cewa.
"To nayi maka izini kaje, duk wani abu dakasan na Saifuddeen ne wanda Zaleeha tatafi dashi ka ƙwatosa ka kawomin, sannan ka ɗauko masa kayayyakin aurensa wanda ta tafi dashi, amma kuma koda wasa kada kace zaka ɗauko ta, badai ta zaɓi guduwa da zaman can ba, shikenan kubarta ta zauna acan ɗin, da sannu duniya zata koya mata hankali, kadai ji abun dana faɗa maka ko?".
Da sauri Habu ya gyaɗa kanshi alamun eh, shi kuwa Baba Malam a kausashe yace.
"Bana buƙatar ta saboda haka koda wasa kada kayi kuskuren ɗauko min ita, kabarta acan, amma kaya dai dayake mallakin Saifuddeen kada kabar ko abu ɗaya awajenta."
Cike da gamsuwa Ya Habu ya jinjina kansa don shima, zaifison abar Zaleeha'n, ta ɗana ƙunci da baƙin ciki data ɗana musu.
Duban Ya Ameenu Baba Malam yayi cikin kulawa, ya dafa kafaɗunsa, kana yace.
"Matarka bata da isashshen lafiya Ameenu, saboda haka ku koma gida kaje ka kula da ita, saboda tana buƙatar kulawanka, in sha Allah Maryam ƴar aljannace, domin takasance ƴa mai biyayya ga mahaifinta, haka kuma ga mijinta, tabbas Maryam ƴa ɗayace tamkar da dubu, sannan itaɗin mafi soyuwa ce agareni, saboda haka bazanso ace kayi mata nisa, ka ɗauketa ku koma gida kaji!."
Cikin yanayin gamsuwa Ya Ameenu yace.
"To."
Gyara zama Baba Malam yayi, cikin nutsuwa yace.
"Kudukan ku idan kuka sake sanya damuwar Zaleeha a cikin ranku, to tabbas zanyi fushi daku, haka ta zaɓa haka kuma take ganin yafi mata, saboda haka mu ƙyaleta, ita da kanta wata rana zata dawo, kutashi kuje kowa yayi sabgogin gabansa, ko da ita ko babu ita zamu rayu."
Haka dukansu suka miƙe, inda Ya Ahmad gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, har acikin ransa yaso ace Baba Malam ya bari aɗauko Zaleeha'n, baiso ace an barta acan ba, duba da cewa ba'a cikin musulmai take ba, sannan basu san ma wani irin rayuwa takeyi acan ba.
Su Ya Ahmad ɗin nafita, Mamy ta gyara zama cikin kwantar da murya, haɗi da tausasa zance tace.
"Amma Malam kanaga barinta acan ɗin shine mafi alfanu?, da a so nane a ɗaukota, sai ayi mata koda nasiha ce, nasan gaba zata gyara."
Murmushi Baba Malam yayi tare da girgiza kansa, bowl ɗin fruit salad ɗinsa ya jawo, cikin kulawa yace da Mamy.
"Ina da babban dalilin dayasa nace abarta acan, duniya zata koya mata hankali."
Shiru Mamy tayi tare da ɗan jingina bayanta, ta shiga nazari.
Numan.
Cikin kaɗaici haka take gudanar da rayuwarta anan Numan ɗin, sosai takejin ƙyaman mutanen da take tare dasu, domin kuwa a iya arean nasu Solomon gaba ki ɗayansu christan's ne babu musulmi ko guda ɗaya, sai ita da tashigo cikinsu ayanzu, wanda kuma ba daɗin rayuwa dasu takeji ba, tana dai zaunene acikinsu bisa dole, sau da yawa Solomon baya zaman gida, kusan koda yaushe yana gona cikin lamɓunshi na shuke-shuken kayan marmari danginsu ,Ayaba, Gwaiba, Dabino, Kwakwa, Lemun zaƙi dana tsami Kankana Abarba sweet milo Aya, Gyaɗa, ɗanyar Masara, Dankalin hausa dana turawa, rogo, tumatur attaruhu albasa da dai sauransu, wanda shine sana'arsa daya dogara da ita.
Hakanne yasa basosai suka cika zama dashi ba, sabida babu salla babu salati ko yaushe yana can yana yiwa ƙasa aski don inƙanta al'barkatun gonar tasa, itakuwa matarsa Elizabet baƙin halinta ma ya isheta, wanda tun Zaleehan bata fahimta ba harta fara fahimta, hakanne yasa itama take ɗauke mata kai,
Sai dai can gefen unguwar su Solomon akwai rugar Fulani masu mutunci da tsabta,da riƙo da addini sosai Zaleeha ta fara sabawa dasu, wanda kullum sukan kawo mata Nono da Zuma mai kyau da inƙanci wanda hakan yake matuƙar taimaka mata ta samu abin sawa a bakin salati sai kuma ƴaƴan itatuwa da Solomon kan kawo mata.
Yanzuma kwance take akan ƴar katifar da suka bata, gaba ɗaya batajin daɗin gidan, babban matsalan data fara fuskanta ma shine rashin samun ingantaccen wutan nepa, acan Gombe tasaba unguwarsu kwata kwata ba'a ɗauke musu wuta, koda kuwa ma an ɗauke tsanani bai wuce 5 minute andawo dashi, haka koda ta koma gidan su Saifuddeen ma kullum cikin wuta suke, amma tunda tazo nan saita kwana ta wuni bata ga idon wuta ba, kuma koda ma sun kawota bai wuce mintuna 50 sun ɗauketa, ita da ta saba kwana cikin sanyin AC kan makeken gado na alfarma, da tattausan blanket masu taushin gaske amma sai gashi yanzu kusan kullum dare cikin zafi take kwana, hakanne yasa gaba ɗaya takejin komai bayayi mata daɗi, gashi wayarta ayanzu bata samun wadataccen caji, wani lokaci ma tanason shiga yanar gizo don ɗebe kewa, amma rashin ƙarfin network haka yake hanata, dolenta haka zatayi jigum tayi shiru, yanzuma kwanciyar da takeyi ne ya isheta, hakan yasa ta miƙe tsaye, wani ƙaton hijabinta ta ɗauka ta zura daga kanta zuwa idon sawunta dan tasan akwai igiyar aure a kanta wani flat shoe ɗinta ta zura, sannan tafito daga cikin ɗakin.
Babu kowa atsakar gidan, hakan yasa kai tsaye tanufi hanyar fita daga gidan.
Tsayawa tayi daga ɗan nesa tana me hango wani wutsinyan tafkeken kogi Numan, wanda ruwan cikinsa ke gudana da ikon Allah, sosai sanyin wajen ke shiga jikinta, kasancewar da yammaci ne, ahankali ta ƙarasa kusa da kogin, zama tayi akan yashin dake shimfiɗe awajen tare da zura ƙafafunta cikin ruwan, idanunta ta lumshe tare da sauƙe ajiyar zuciya.
Wani sabon shauƙin ƙaunarsa, wanda ke kwance a ƙasan zuciyarta ne ya taso mata, aduk tsawon kwanakin nan koda sau ɗaya ne soyayya da kewarsa, basu ragu acikin zuciyarta ba, kullum da soyayyarsa take kwana take kuma tashi, har yau bata fidda ran cewa watarana zai zo gareta ba, duk kwanan duniya soyayyarsa ƙara ninkuwa take acikin zuciyarta, zuwa yanzu kewa da muradinsa ya zamo wani sinadari na cikin rayuwarta, tajima awajen, ganin magriba ta gabato ne yasa, ta tashi inda ta koma cikin gida, a bakin fonfonsu ta tsaya ta buɗe ruwa mai tsabta, wanda dashi tayi alwala, ɗaki ta koma, koda tayi sallan Magriba, bata tashi akan sallayan ba, har saida ta sallame sallan isha.
Haka nan take jin tausayin Baba Malam na cika mata can ƙasan zuciya, ji takeyi kamar tayi fiffige ta fire ta ganta gabanshi amman bazata iyaba ta rasa meyasa ta kasa yiwa mahaifinta biyayya.
A wani yanki na zuciyarta kuwa, tana yawan tuno Ummi dasu Hayatuddeen da Raliya,
musamman uban gayyan taken haɗe fuska taja tsaki duk sanda ya faɗo mata a rai.
Yanzunma hakance ta kasance wani ɗan gajeren tsaki taja,
tuno yadda ya rinƙa tsotse mata sweet lips ɗinta,
ido ta rumtse da ƙarfi tare da cewa.
"Hmmmm gwarafa dana gudu, in na tsaya wannan zalamemmen zaimin sagegeduwa, mugu duk ya lallatseni caɓɓullena,wannan in na zauna sai ya maida min nono kamar biredi ko bolon-bolon da mutumtaka ya rinƙa wani shana, mugu kawai mai idanun jaraba."
a hankali ta miƙo hannunta ta jawon hand bang ɗinta wanda a ciki aka sa mata kuɗin fansan idonta da rafan sadakinta wanda Baba Malam ya damƙa mata lokacin da za'a kaita gidan wancan jarabebben.
zazzage jakarta tayi gaba ɗaya kuɗin ta zubesu kan sallayar,
cikin mmakin yawan kuɗin ta fara haɗe kansu,
ta daɗe sosai kafin ta gama kana ta irgasu, cikin mmki tace.
"Kai har dubu ɗari huɗu da talatin."
Taɓe baki tayi tare da cewa.
"Uhmmm kasa abokanka da ƴan uwanka zubda kuɗaɗensu a banza, ni ɗinnan dai nan gani nan bari sadakin agalawa yaseen cinye kuɗin sada kinka zanyi kuma budurcina nan gani nan bura awaran mayya ga yaji ga albasa kuma babu damar ci."
Ƙasan pillow tasa ƙuɗin sabida baccin daya fara fin ƙarfinta.
Daga nan kuma kwanciya tayi, domin yau ɗin da wuri taji bacci naneman ɗaukarta.
Washegari.
Gombe State.
Tun da sanyin safiya Ya Habu ya gama kimtsawa, inda ƙarfe 7 na safiya atasha tayi masa, kasancewar a motar haya zai tafi, saboda idan yaje can ɗin, har motar da Zaleehan ta tafi dashi zai ɗauko, domin kuwa Saifuddeen ne yasaya motar, tunda ta rufe ido ta gwada cewa bata ƙaunarsa kuwa, to bazasu taɓa bar mata komai nasa awajenta, wanda yake shiya saya mata ba.
Zaman ɗaki daya isheta ne yasanyata fitowa, kan wani benci dake aje a tsakar gidan ta zauna, wayarta ta ɗauka inda ta shiga latsawa, zuwa yanzu tagaji da ɗurawa cikinta kayan zaƙi, dangin su chocolate da biscuit, da ƴaƴan itatuwan kasancewar su suka zame mata abinci, duk da gidan fulanin nan suna yawan kawo mata abinci kuma Alhamdulilla ta yarda da tsabtansu kana sun iya girki sosai gata dama tana son man shanu.
Ɓangaren Ya Habu kuwa, lafiya ya samu