Showing 108001 words to 111000 words out of 239422 words
Chapter 37 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
magriba da akayi ne yasa Hayatuddeen tashi ya wuce masallaci, Raleeya ma ɗakinta ta koma don yin sallah, Adda Rahama kuwa shirye-shiryen tafiya ta somayi, sam bama da niyan kaiwa dare tazo ba, saidai ganin halin da Zaleeha take ciki yasa bata tafi da wuri ba.
Zaleeha kuwa babu laifi ta ɗanji sauƙin zazzaɓi da kuma ciwon kan daya rufeta.
Hakan yasa ta ɗauro alwala tazo ta gabatar da sallah, koda ta idar da sallan bata tashi akan sallayan ba, jingina tayi da jikin gadon Ummi, tare da lumshe idanunta, wasu siraran hawaye ne suka biyo ta gefen idanunta suka sauƙa akan fuskarta. Dai-dai lokacin Ummi ta shigo cikin ɗakin, ƙarasowa jikin gadon tayi ta zauna.
Cikin kulawa ta ƙira sunan Zaleeha'n, ahankali taɗan ɗago kanta ta kali Ummi'n. kafaɗunta Ummi ta dafa cikin son sake bata karfin guiwa tace.
"ki kwantar da hankalinki, Insha Allah gobe zamuje za'a bawa Baba Malam haƙuri, kuma nasan zai haƙura ya yafe miki, sannan kuma Baba Malam ba tsanarki yayi ba, hakama ƴan uwanki, kawai dai suna fushi dake ne, saboda abun da kikayi baki kyauta ba sam, bawai dan kina auren Saifuddeen bane yasa nace haka, a'a ina faɗa miki hakane dan ni matsayin ƴa na ɗauke ki, ke macece Zaleeha, duk kuwa mace me tarbiya irinki ba a santa da gudu ta bar gida ba, haka kuma ɗabi'ar guduwa ma sam bai kamata ace mace ta ɗaukesa ba, bazan tursasaki faɗamin dalilin dayasa kika gudu ba, saboda nasan dama tuntuni bakyason auren ki da Saifuddeen, bakya sonshi dole akayi miki amma kuma duk da haka bai kamata ki tsalleke iyayenki ki tafi can wata duniya ba, nasan kinyi nadama kwarai, kuma insha Allah Allah Zai karɓi tubanki, kuma Baba Malam ma nasan zai yafe miki, kawai dai yana fushi ne saboda yanda kikayi watsi dasu, amma nasan da zaran anbasa baki zai yafe miki, saidai kuma ina fatan zaki kiyaye gaba, sannan kowata kikaga zata aikata irin abun da kika aikata zaki haneta." Tuni hawaye sun gama wankewa Zaleeha fuska, tabbas tasan bata kyauta ba, kunyar Ummi ta rufeta yadda ta gane cewa bata son ɗanta ita kuma duk da haka bai hanata so taɓa. wanda dalilin hakanne kuma kowa ke fushi da ita, ƴan uwanta sun ƙita saboda abun da ta aikata, Babanta mahaifi ya koreta duk akan abun da ta aikata, tabbas Ummi ta cika uwa ta gari, abun so ga kowa, ta aikata musu laifi amma sun ƙaunace ta, alokacin da kowa ya nuna mata tsana, su kuma sunjawota jikinsu, Babanta ya koreta, su kuma sun amsheta duk da laifin da ta aika ta musu suka bata mafaka, tayaya zata fara misalta girman halaccinsu agareta? abune me girma da bazai kwatantu ba, kukane ya ƙwace mata sai kawai ta kifa kanta akan cinyar Ummi, ta saki kuka'n.
Awannan karon Ummi batayi yunƙurin hanata kukan ba, saboda ko ba komai shi kukanne zai rage mata zafi da raɗaɗin zuciya.
Saida Ummi taga kukan yayi yawa sannan tashiga ɗan bubbuga bayan zaleehan tana shafa kanta.
Sannu ahankali ta rage sautin kukan nata, shiru tayi tana sakin ajiyar zuciya.
Ganin haka ne yasa Ummi kamo hannunta suka fice daga cikin ɗakin, kai tsaye ɗakin dake gefen na Ummi'n, Ummi takaita, wanda yake ɗakin su Raleeya ne wanda sukai budurci acikinsa, kuma nanne masauƙin Goggo Dada da Aunty Meena in sun zo, akimtse ɗakin yake sannan babu wani hargitsi acikinsa, akan gado Ummi ta zaunar da ita, toilet ɗin ɗakin ta shiga ta haɗawa Zaleehan ruwan wanka me ɗan ɗumi. Dubanta Ummi tayi cikin kulawa tace.
"Kishiga kiyi wanka, zuwa gobe an gane key ɗin side ɗinki, dan yanzu na tambayi Hammansu key ɗin yace baisan inda key ɗin yakeba sai ya nema,
shiga na kiyi wonka sai kizo ki kwanta, ko za ki ci abinci nasa Hayatuddeen ya kawo miki."
Asanyaye ta girgiza kanta alaman
"A'a" jinjina kai Ummi tayi sannan ta fice daga cikin ɗakin, tana mai tuna za'ayi daga da Saifuddeen dan tasan batun wai shi baisan inda key ɗin side Zaleeha yakeba duk cikin fushine ta lura ya fusata sosai da Zaleeha.
Ita kuwa Zaleehan cikin sanyi ta tashi ta shiga toilet ɗin, wanka tayi sannan ta ɗauro al'wala'n sallan isha, rigar da ta cire shi ta sake mayarwa, wanda dama doguwar rigar atamfa ce ajikinta. Koda tayi sallan ta jima akan sallaya tana addu'o'i, har kusan ƙarfe tara na dare tana nan zaune akan sallaya'n, daga ƙarshe kuwa anan kan sallayan ta kwanta tare da lulluɓe jikinta da bargo, luf tayi tana sakin ajiyar zuciya, hawaye kuwa na tsiyaya daga cikin idanunta.
A ɓangaren Saifuddeen kuwa dawowarsa daga sallan isha kenan, kai tsaye bathroom ya nufa, wanka yayi haka ya fito jikinsa sai tashin ƙamshin turaren wanka yake, tura wheelchair ɗinsa yayi zuwa gaban dressing mirror, cikin nutsuwa ya shafawa jikinsa mai me daɗin ƙamshi, body spray ya fesa, sannan yaja wheelchair ɗinsa ya ƙarasa gaban drawer'nsa, wani 3 quater jeans ya sanya tare da wata blue ɗin t-shirt me kyau, sake feshe jikinsa da turare yayi sannan ya ƙarasa inda laptop ɗinsa yake, ɗauka yayi tare da ajesa akan cinyarsa, cikin nutsuwa ya soma ɗan daddanawa. Ahankali ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, tasha kwalliya cikin wata sleeping dress me kama jiki, kana ta sake ɗan gashinta wanda iya kansa ya kwanto kan wuyanta, tsaye tayi ajikin ƙofan tana kallonsa, sosai yayi mata kyau, akullum indai ta ɓangarenta ne ƙara kyau yakeyi tana masifar sonshi shiyasa take tsananin kishinsa ji take tamkar dan ita ɗaya aka halicceshi, shikuwa Saifuddeen sam ma baisan da zuwanta ba, saboda ya bawa ƙofar shigowa ɗakin baya sannan kuma gaba ɗaya hankalinsa akan laptop ɗinsa yake. Murmushi ta ɗanyi tare da takowa ta ƙaraso inda yake, hannuwanta tasa ta bayansa kana ta rungumesa, ɗan lumshe idanunsa yayi, tare da cije laɓɓansa, dama yasan aje azo dole saitazo ta katsesa daga abun da yakeyi.
Ameena kuwa zagayowa ta gabansa tayi ya zamana suna fuskantar juna, wani irin annuri ta hango akan fuskar tasa, take taji ƙirjinta ya buga, shikuwa Saifuddeen ganin yanda ta ƙuresa da ido ya sashi ɗan sakar mata murmushi. Itaɗinma murmushi ta mayar masa, tare da ɗan duƙowa tayi kissing ɗinsa akan forehead ɗinsa, ɗago kyawawan idanunsa yayi ya kalleta, ɗan lumshe idanunsa yayi tare da miƙa mata hannunsa, kama hannun nasa tayi, shikuwa ya jawota cikin jikinsa ya ajiyeta kan cinyoyinshi ya zama suna fuskantar juna da kyau, wani sakalin murmushi yayi mata tare zaro harshensa waje yana ɗan karkaɗa mata wani irin abu taji ya ratsa jiki da zuciyarta, ido ta zuba mishi ganin ya sanya lips ɗinsa yaɗan yiwa kumatun ta kiss, wani irin sanyi taji acikin ranta, hannayensa ya sanya ya tallafo haɓarta, haɗe fuskarsu waje ɗaya yayi, tare da kamo bakinta yana kissing, cikin jin daɗi da farin cikin da ta samu kanta ciki, ta kamo tongue ɗinsa tana tsotsa, tunaninta ne ya fara kwancewa, sakamakon irin salon da taji yanayi mata, wanda bata bai taɓa yi mata irinsa ba sai yau ɗin, wani tunani da yazo zuciyarta ne yasa ta ɗan janye jikinta baya, idanu ta ƙura masa tana me ƙoƙarin karantar yanayin da yake ciki. Kyawawan idanunsa ta kalla, wanda suka kasa ɓoye abun da ke zuciyarsa, wani irin zallan farinciki ta hango acan ƙasan idanunsa, dubansa tayi sosai shaiɗan na ingiza kishinta, har yanzu fuskarsa ɗauke take da sahirtaccen murmushi wanda ke nuni da can ƙasan zuciyarsa na danƙare da tarin farin ciki mai ratsa jiki da zuciya gashi har ya baiyana bisa fuskarsa, take wani tunani yazo ranta, nan kuwa taji wani abu me ɗaci ya tsaya a maƙoshinta, tabbas tasan cewa wannan farin cikin da ta hango akan idanunsa bawai na haka kawai bane, tasan wannan farincikin da take hangowa acikin idanunsa, bai rasa nasaba da dawowan Zaleeha abinda ranta ya saƙa mata kenan, take taji wani ɓacin rai ya zo mata, matsanancin kishin da tsanar Zaleehan ne ya sake rufeta, ahankali yasake matso da fuskarsa gab da nata, ƙoƙarin sake kamo laɓɓanta yake, cikin sauri tajanye jikinta baya, ji tayi gaba ɗaya idanunta na neman kawo ruwa, hakan yasa cikin sauri ta juya ta fice daga cikin ɗakin. Binta yayi da kallon mamaki, saboda yanda yaga yanayinta ya sauya lokaci ɗaya.
Ɗan jim yayi, yana tunanin shi dai bai mata komai ba lokaci guda kuma ya saki murmushi, maida kansa ga laptop ɗinsa yayi ya cigaba da aikin da yakeyi.
Ameena kuwa tana fita daga ɗakin nasa, kai tsaye ɗakinta ta wuce, ranta nayi mata ƙuna, akan gado ta zauna, take kuma sai taji hawaye nabin gefen idanunta, hannu tasa ta dafe kanta, ita ta sani tabbas wannan farincikin da ta gani akan fuskarsa duk dan saboda dawowan wannan aljanar tasa ne, tana sonsa shiyasa take jin kishinsa sosai, bama kamar yau da ta hango soyayyar Zaleehan acikin idanunsa, bayan kuma tasan cewa Zaleeha tafita komai, kyau, sura, dama komai da komai. Tashi tayi ta kashe hasken ɗakin nata, kana ta haye saman gado ta kwanta, gaba ɗaya ranta babu daɗi.
Sai wajajen ƙarfe 11 kafun ya kammala abun da ya keyi, harzuwa lokacin kuwa Ameena bata dawo ba, sosai abun ya basa mamaki, dan a iya saninsa baiyi mata wani abu da zai ɓata ranta ba, wayarsa ya ɗauka tare da laluɓo number'n ta ya shiga rubuta mata text message kamar haka. _"Har yanzu fa ke nake jira banyi bacci ba, kuma baki zoba, Please kiyi sauri kizo, idan zaki zo ki taho, ki ta homin da Adeel."_
yana gama rubutun ya tura mata, ƙoƙarin sauƙa daga kan wheelchair ɗinsa yayi inda ya haura saman gadon.
Dai-dai lokacin da saƙon nasa yazo mata kuwa, tana nan kwance sai-dai ba bacci takeyi ba, gaba ɗaya tsananin kishinsa ya hanata sakat, ganin wayarta ta kawo haske yasa ta ɗauka ta duba, tana gama karanta saƙon nasa ta maida wayar ta ajiye, batare da tayi masa reply ba. Saifuddeen kuwa ɗan kishingiɗa yayi, yana jiran ko zata shigo, amma shiru babu alamarta, kuma sannan babu reply, jawo wayartasa yayi ya sake tura mata wani text ɗin. Shima sama da mintuna goma aka kwashe babu amsa, ganin haka ya sashi gyara kwanciyarsa tare da jawo blanket ya rufawa jikinsa, cikin ransa yace.
"Meye hakan ke nufi kenan? fushi tayi ta tafi ko kuma me? To fisabilillahi ni me nayi mata da zatayi fushi dani? To ko dai tayi bacci ne?". kansa ya girgiza tare da ɗage kafaɗunsa, cikin ransa yace.
"Allah ya sani ban mata komaiba a iya sanina kuma banyi komai da nufin baƙanta mata ko cutar da itaba, domin nasan son da take min shiyasa nake ganin kimarta sam bani da nufin tozartata duk rintsi zan kasance mata adalin miji jagora mai tausayinta. maganar zuci ya kumayi banyi mata wani abun da ya kamata ace taji haushi ba, well zata ma kawo kanta da ƙafafunta kwadayayyi kawai cingom ɗin na."
sake gyara kwanciyarsa yayi, yana rufe idanunsa kuwa sai bacci, don dama agajiye yake.
Ameena kuwa da ƙyar ta iyayin bacci, saboda duk juyin da zatayi shaiɗan da zafin kishi na zuzuta mata kyawun Zaleeha, da kuma zallan farincikin da ta hango acikin ƙwayan idanun Saifuddeen su ke yi mata gizo, haka nan taji gaba ɗaya ta raina kanta, sannan kuma wata zuciyar na faɗa mata cewa, kada tayi kuskuren wuce matsayinta, saboda Zaleeha zaɓinsa ce, ita kuwa zaɓin iyayensa ne bana saba, kuma dama Maza irin su Saifuddeen rayuwarsu zai tafi ne da kyawawan mata irinsu, tasan kai tsaye baza a ce mata mummuna ba, amma kuma idan aka sanyata alayin su Zaleeha, bazata ganu ba, dan ko stage ɗin farko na kyawunsu bata taka ba, domin kuwa a kyau su nasu stage ɗin acan sama yake, musamman Zaleeha da ta haɗa komai da komai, haka kishi yasa ta yita kuncewa da saƙawa, daga ƙarshe dai haka bacci ya ɗauketa, ranta duk ba daɗi.
Ɓangaren Zaleeha kuwa ƙiran sallan farko na asuba akan kunnenta, kasancewar dama bata wani samu ishashshen bacci ba, duk yanda taso hana kanta kuka ta kasa, haka ta wayi garin yau ɗin ma da wani sabon kuka, cikin kukan haka taje ta ɗauro al'wala tare da zuwa ta gabatar da sallan Asuba, zama tayi akan sallayan, nan cikin muryarta me ɗauke da kuka take karanta Al'Ƙur'ani saboda tasan karantasa zai yaye mata damuwa.
Tajima tana karatun saida taga gari yayi haske, kafun tatashi daga kan sallayan, zuwa lokacin idanunta sun sakeyin luhu luhu, gwanin ban tausayi, kallo ɗaya zaka mata, kasan ta kwana kuka, ƙarasawa jikin ƙofar ɗakin tayi, cikin sanyi ta fice daga cikin ɗakin. Kaitsaye ɗakin Ummi ta nufa, abakin ƙofa ta tsaya, tare da yin knocking, daga ciki Ummi ta bada izinin shigowa, ahankali kuwa ta murɗa handle din ƙofar tashiga, Ganin Ummin na zaune akan gado, yasa cikin sanyi ta ƙarasa tare da durƙusawa, cikin muryarta dake rawa tace. "Ummi ina kwana." Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Lafiya ƙalau Zaleeha ya jikin naki dai?" Asanyaye tare da muryarta dake bayyana rauninta tace.
"Da sauki."
Kai Ummi ta jinjina cikin kulawa tace.
"Masha Allah, Allah Ya ƙara sauƙi, sannan ki ƙara kwantar da hankalinki kinji, komai yayi farko yana da ƙarshe, haka ma kuma komai yayi tsanani zaiyi sauƙi da yardan Allah, ako yaushe kina sawa zuciyarki nutsuwa, kinga ko yawan kukan nan ma da kike bashida amfani, kiyi haƙuri kinji, ƙaddara ce babu kuma yanda bata zuwa wa bawa, saidai neman sauƙi awajen Allah kawai."
Kanta ta ɗan jinjina cikin muryarta dake rawa tace.
"To Ummi, amma kullum zuciyata ƙara karyewa take, gani nake kaman Baba Malam bazai taɓa yafe min ba, tsoro nakeji Ummi, idan na mutu Baba Malam na fushi dani, samun aljanna zaiyi min wahala, kuma kowa nace ya roƙamin Baba Malam sai yaƙi, har Daddy (Malam Adam) shima nace ya bawa Baba Malam haƙuri, amma yace shi babu ruwansa, shima fushi yake dani."
Ɗan jim tayi tare da sakin sheshsheƙa, asanyaye tace. "Zakariyya yace duk wanda na ɗauko dan yabawa Baba Malam haƙuri, bazai haƙura ba, har saidai in Hamma Saif ne ya rakani.
Dan Allah Ummi ki roƙamin Hamma Saif ya yafemin, ya rakani mu bawa Baba Malam hakuri, idan Baba Malam baiyafemin ba, nasani haske bazai taɓa ziyartan rayuwata ba ." Taƙare maganar cikin yanayin ban tausayi, ga kuma hawayen da gaba ɗaya suka gama jiƙa mata fuska.
Hannayen Zaleehan Ummi ta kamo cikin yanayin kulawa haɗi da tausayawa tace.
"To kidaina kuka, insha Allah zan faɗa masa, kuma nasan zai yafe miki, sannan kuma zai rakaki kuje ku bawa Baba Malam haƙuri, ki tsaida kukan haka kinji."
Ummi ta faɗi maganar cikin lallashi. kanta ta jinjina, saboda ta ɗanji sanyi aranta. Jan jikinta tayi ta zauna anan kusa da Ummin.
Ahankali ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, dan alokacinne dawowarsa daga masallaci, kusan atare suka ɗago kansu suka kalleshi, hakanne yasa idanunsu faɗawa cikin na juna, lokaci guda ya kawar da duk wata annuri dake kan fuskarsa, itama asanyaye ta yi ƙasa da kanta, cikin haɗe fuska ya ƙaraso cikin ɗakin, dan ma Ummi ta riga da ta ganshi ne, da ace bata gansa ba babu abun dazai hanashi