Showing 201001 words to 204000 words out of 239422 words

Chapter 68 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11843

hannun Ishaq dake ƙoƙarin kamo nashi cikin tsanyi yace.
"My Ishaq gani nan kusa da kai".
Wani irin riƙo Ishaq yayiwa hannun Saifuddeen cikin tsananin farin ciki yace.
"Allahu akbar Allah mai iko da girman buwaya. Buwayi gagara misali Alhamdulillah ko yanzu na mutu Allah ya cika min burina laruran Aminina sun ragu".
Wani irin raunine ya baiyana a fuskar Saifuddeen murya na rawa yace.
"Ni kuwa ina roƙon Allah ya aramin rai da lfy, ya nuna min lafiyarka inga kaima kana gani da idanunka".
Kusan a tare Ahmad da Salisu ds Mudassir da Warisu sukace.
"In sha Allah, shima Allah zai bashi lfy".
Salisu kuwa tuni hawaye sun wonke mishi ido sai yake tuno irin gogormoya da suka sha shida Saifuddeen a cikin bulayin neman halal ɗinsu a lokacin badon ƙarfin imaniba sai su kauce hanya, sabida tsananin uƙubar talauci da wahalar rayuwa
hannu Saifuddeen yasa yana share masa hawayenshi, shi kuwa sai maimaita kalmar Alhamdulillah yake tayi.
Warisu kuwa murmushi yayi tare da cewa.
"Ya Allah ka nuna mana randa zaka tsaya da kafafunka kamar yadda ya jiyar damu mgna da muryarka".
Amin Amin yace kana ya kalli Salisu tare da cewa.
"Haba Salisu godewa Allah zamuyi ba kuka ba".
Cikin sauri duk suka rinƙa maimaita Alhamdulillah,
Ahmad ne yayi dariya tare da cewa.
"Daga dare ɗaya Zaleeha tayi sanadin dawo mana da bakinshi da kunnenshi, a dare na biyu kuma ƙugu kam zai ida ɓalgawacewa in mutun bai jira kanshi ba".
Dariya sukayi baki ɗaya dan sun gano kurman baƙin da Ahmad ya musu,
shi kuwa Saifuddeen mare ƙeyan Ahmad yayi,
lokaci ɗaya kuma ya riƙe hannun Ishaq da karfi dan sarawar da yaji ƙugunshi nayi cikin dakiya yace.
"To mugaye masu cewa Allah yasa ƙuguna ya ida ɓalgacewa, kunji daɗinku ya ɓalgace ɗin".
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Ganin alamun yana cikin ciwo ne yasa suka sarara mishi suka koma falo.


Kafun sallan Azahar tuni gidansu Saifuddeen ɗin ya cika da jama'a, ƴan uwa da abokan arziki da maƙota, harma dasu Bappa Ali da suka samu isowa, acikin gidan fuskar kowa ka kalla zaka ganta ɗauke da zallan farinciki, da kuma jindaɗi.




Kusan ƙarfe 3 na yamma, su Baba Malam suka samu isowa gidan. Tarba me kyau Ummi tayi musu, inda Baba Malam yashiga har ɗakin Hayatuddeen ya gaishe da Saifuddeen ɗin. Mama ma haka ta gaishesa tana ta faman sunne kai, dan kunyansa takeji.
Ahamad ne yaja Baba Malam gefe ya sanar dashi buɗewan kunnen Saifuddeen.
Sosai Baba Malam yaji daɗi, sam baiga laifin Saifuddeen ɗin ba kuma da yace a ɓoyewa Zaleeha hakan, dan yasa komai Saifuddeen yana yinsane cikin hikima da kuma dalili tabbas yasan yanada dalilin da yasa yace a ɓoye matan.


Jin cewar Zaleeha na kwance bata da lafiya, yasa Mamy zuwa ta dubata, Mama kam da Baba Malam basuje ba, saboda abun akwai nauyi sosai.


Har zuwa tafiyansu kuwa Zaleeha bacci take batasan ma da zuwansu ba.

Haka gidan nasu ya cigaba da amsan baƙi har kusan dare.
Sai Bayan sallan la'asar Zaleeha ta farka daga nannauyan baccin da take.
Dai-dai lokacin kuwa Adda Rahma da Raleeya suka shigo, da taimakonsu tayi wanka, dan taɗanji dama daman jikinta, sai-dai tafiyan natane har yanzu bai dawo dai-dai ba.
Da taimakon Adda Rahama ta koma ɗakinta, sallan Azahar da la'asar tayi.sanna Ta kwanta.


Ƙarfe biyar dai-dai Dr Aleeyu yaso daga Abuja kai tsaye gidan su Saifuddeen ɗin ya Adnan ya kawoshi, ya dubashi yayi da kyau kana yayiwa Saifuddeen allurai da kuma magunguna, ba laifi kuma yaɗanji sauƙi.


Bayan sallan isha ne Ya Ahmad da Aunty Lubna suka zo suma dan dubashi da jiki


Bayan sun gaishe da Saifuddeen ɗinne. Raleeya tayiwa Aunty Lubna jagora xuwa ɓangaren Zaleeha. Zaune suka sameta akan sallaya, tayi jigum, ganin Aunty Lubna yasa ta kwaɓe fuska, sai kuma ga hawaye sun soma tsiyaya daga cikin idanunta.
Ƙarasowa cikin ɗakin Aunty Lubna tayi tare da zama akan wani ɗan stoll ɗin dake gefen gado, a hankali ta kamo hannun Zaleehan cike da kulawa tace.
"Sannu Zaleeha ya jikin naki".
Kasa amsa mata tayi, saima samun kanta tayi da ɗan jan jikinta, ta ɗaura kanta tayi akan cinyar Aunty Lubna'n, lokaci ɗaya ta kwaɓe fuska cikin zallan shagwaɓa tai rau-rau da ido.
Ganin haka yasa Aunty Lubna ta ɗanyi murmushi dan tasan mai neman kukane aka jefa da kashin awaki, ahankali ta soma shafa kanta, cikin sanyi da kuma lallashi tace.
"Ya isa haka Zaleeha kada kiyi kukan, ciwon me kuma yake damunki harda kuka?" ɗago kanta daga cinyar Aunty Lubnan tayi cikin naƙe murya tace.
"Zafi nakeji Aunty duk jikina ciwo yake min, sabida muguntar da Hamma Saif yamin."
Danne dariyarta tayi tare da cewa.
"Kenan nima sai ince ya Ahmad ɗinki ma mugunta yaita min".
Kai ta jujjuua tare da cewa.
"Allah nasan da kinyi ta magiya da roƙon ya Ahmad ya barki yadda nai ta mishi jiya da dare nasan zai barki.
Shi dai mugune, babu irin kuka da roƙon da banyi masa ba, amma yaƙi jina, zafi nakeji sosai Aunty ko tafiya mai kyau bana iyawa, gashi ma harda zazzaɓi nakeyi."
Sosai Aunty Lubna ta gane sanadin ciwon Zaleeha'n, ɗan sake shafa kanta tayi.
Cikin kulawa tace.
"Kiyi haƙuri Zaleeha kowa ma yaji hakan, amma da sannu yake wucewa, banaji Ummi tace likita ta dubaki ba." Ashagwaɓe ta gyaɗa kanta, cikin lumshe ido tace.
"Amma Aunty Lubna meyasa zaimin haka, yanzu fa ko ƙarfi banaji ajikina."
Ɗan guntun murmushi Aunty Lubna'n, tayi, tare da cewa.
"To yanzu ai yayi mgnin guduwa da bakin tsiwa.
Ai haƙuri kawai zakiyi , shima dakike magana akai ai ba daɗi yakeji ba, yanzu haka ma fa shi mukazo dubawa, jikinsa babu daɗi, ciwonsa ya tashi, ko ɗazu ma su Baba Malam harma da Mama sunzo dubashi." Idanunta ta zaro waje, cikin yanayin damuwa da fargaba tace.
"Bashi da lafiya kuma Aunty, to me ya sameshi?." "Bayansa ne ke ciwo, dan ma naji ance sai an fitar dashi India, yanzu dai ki lallaɓa kije ki duba shi, yana can sashin Umminsa."
Hakanan taji wani irin matsanancin tausayinsa ya dirar mata azuciya, take taji zuciyarta ta karye taji tana son ganin shi.
Miƙewa tsaye Aunty Lubna tayi tare da cewa. "Ni kam zan wuce, dan tare ma muke da Yayanki, nace bari na shigo naɗan dubaki." Hannun Aunty Lubnan ta kama sannan ta miƙe tsaye, cikin yanayin shanye ciwon da takeji, tace.
"Aunty muje na gaishe da Ya Ahmad, tunda dai yaƙi shigowa."
A cikin ranta kuwa cewa tayi.
"Daga nan zan ganshi ai, in banda Hamma Saif kai kamin fyaɗe kuma kaima wai baka da lfy mu duka mun zama majinyata".
Murmushi Aunty Lubna tayi, tace.
"Baƙin shigowa yayi ba, suna tare da me sunansa ne."
(Wato Ahmad mijin Raleeya.) Kaita ɗan jinjina, sannan ta kama hannun Aunty Lubna'n, haka suka fito daga cikin sashin nata, ahankali take tafiya, sai faman ciccije baki take, kasancewar tana ɗanjin zafi acikin jikinta.
A compound ɗin gidan, suka iske Ya Ahmad da kuma Ahmad atsaye, suna ɗan tattaunawa, wanda kuma duk akan matsalan Saifuddeen ɗinne, kana anan Ya Ahmad ke ce mishi suma gobe zasu koma Abuja.
Ganin Zaleeha yasa Ya Ahmad ɗin sakin murmushi, cikin kulawa yace.
"Ha'a marar lafiyance da kanta, har kin warke kenan?."
Ɗan shagwaɓe fuska tayi tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, asakalce tace.
"Nidai Ya Ahmad nayi fushi, kazo har gidan nan shine kuma sai kaƙi zuwa sashina, bayan kuma kasan cewa bani da lafiya."
Murmushi yayi tare da kamo hannunta, ya shafi gefen fuskarta cikin kulawa yace.
"Sannu ko, Mangana yanzu ya jikin naki? Ko dai yanzu kam Mangan Hamma Saif ne?."
Jin yace mata manga, Hamma Saif ta sake shagwaɓe fuska, cikin mamul mamul da baki tace.
"Da ɗan sauƙi kaɗan."
ɗan murza hannunta yayi tare da cewa. "Good Allah Ya Ƙara sauƙi."
Kanta taɗan jinjina sannan tace Ameen. Bayan motarsa ya buɗe inda ya ɗauko wata leda miƙa mata yayi, yana murmushi yace.
"Gashi dama saboda ke kaɗai kawai na saya, ki kula da kanki kinji Shagwaɓaɓɓiyar Mijinta." Amsan ledan tayi tana murmushi, jin yace da ita wai Shagwaɓaɓɓiyar mijinta, yasa tayi saurin basa baya, wai ita adole taji kunya. Murmushi yayi, kawai nan sukayi sallama, Saida taga fitansu daga cikin gidan kafun suka juya ita da Ahmad suka nufi sashin Ummi. Ahmad ne ya ɗan kalli yanda take tafiya, tausayinta ya ɗanji saboda ya tuna da Raleeyansa, haka itama tayi first night ɗinsu. "Ya jikin?."
Ya tambayeta, yana ɗan sakin ɓoyayyar murmushi.
A hankali tace.
"Da sauki."
Murmushi Ahmad ɗin yayi, tare da girgiza kansa kawai, dan yasan daga Zaleehan har Saifuddeen ɗin jirgi ɗayane ya kwasosu, dan komai nasu iri ɗaya ne, sakalci, raki, da kuma zallan shagwaɓa.


Koda suka ƙarasa falon Ummi, Raleeya suka samu da Adda Rahama azaune sai Hayatuddeen. Ganin Zaleehan yasa Adda Rahama tace. "Masha Allah Jiki yayi sauƙi kenan."
Ɗan ƙasa tayi da kanta, dan wani irin kunyansu takeji, su dukansu sabisa sai take ga ai duk sun fahimci sanadin ciwonta. Hayatuddeen wanda yake kusa da Adda Rahama ne kuma shi sam bai fahimci sanadin cutar ta duba ne yace.
"Ba dole jiki yayi sauƙi ba, tunda rabin ranta ba lafiya, ae yana buƙatar kulawanta".
Daga jin maganan kasan zallan tsokana yakeson takalowa. Ɗan sunkuyar da kanta tayi tare da ɗan hararan wasa,
Daga Raleeya har Ahmad dariya sukayi, Adda Rahama kuwa cewa tayi.
"Manta da Autan Ummi kinji, jeki ɗakin Hayatuddeen ɗin ki duba Saifuddeen dan shima yana fama da jiki." Kanta ta jinjina, tare da ɗan kallon Hayatuddeen ganin yana binta da idone yasa ta ɗan haɗe fuska kana ta juya.
Cikin sanyi ta nufi ɗakin Hayatuddeen din. Murmushi Ahmad yayi, cikin zuciyarsa yace. "Marar kunyan ƙarya, lokacin da kikaji maza, ina da ga kwance saida najiyo ihunki, fitsarerriya ai yamin mgnin ki, ko yau na mutu ban mutu da baƙin cikin ba yamin dai-dai dan daga yawau bakin ya mace."


Ahankali ta tura ƙofar ɗakin Hayatuddeen, bakinta ɗauke da sallama, taɗan kutsa kanta ciki.
Kwance yake akan gadon Hayatuddeen, ya ɗan jingina bayansa da jikin pillow, dan Dr.Aleeyu yace masa yanayin hakan, zai ɗan taimaka bayan nasa ya ware. Gefensa kuwa Ameena ce, zaune tana ƙoƙarin ɓare magunguna zata bashi yasha.
Ahankali tayi ƙasa da kanta, cikin muryarta da ta ɗanyi sanyi tayi sallama.
Ameena ce ta amsa, tare da cewa.
"Masha Allah jiki yayi sauƙi kenan Ammin Adeel."
Kanta ta jinjina kana ta ɗanyin guntun murmushi, tare da kama ƴan yatsun hannunta ta shiga yin wasa dasu, Idanunsa ya ɗago ya watsa mata, wani irin so, ƙauna, haɗi da zallan tausayinta ne suka cika masa zuciya ya kamata ace a irin ya wannan ranar ta samu kulawarshi irin kulawa mai nuna jin daɗi to ciwo ya hana.
A hankali ya ɗan nago hannunsa ɗaya ya miƙa mata alaman tazo.
lumshe idonta tayi, kana ta buɗesu ganin har yanzu yana miƙo mata hannun ne sai
taji bazata iya ƙi ko musa masa ba, ahankali ta ƙaraso tare da sanya hannunta acikin nasa, jawota yayi ya zaunar da ita kusa dashi, har gaba ɗaya jikinsu na manne da juna.
Kanta taɗan ɗaura akan kafaɗansa, tare da ɗan lumshe idanunta. Wani irin ajiyar zuciya suka sauƙe atare su dukansu uku,
ganin haka yasa Ameena ɗanyin ƙasa da kanta, tana ambaton sunan Allah acikin ranta, kana sai ta kumayi ɗan murmushi jin ya kamo hannunta.
Ahankali ya kamo hannun Ameena'n, ya riƙe acikin nasa gam ya haɗe tafukan hannunsu wuri ɗaya,
Murmushi tayi, cikin son basu waje tace. "Bana bari to kuɗan gana, nasan ma Adeel nacan yana neman nono, anjima ina dawowa." Ɓuɗe idanunsa yayi, ya kalleta, tare da ɗan yi mata murmushi sannan ya jujjuya mata kai alaman "A a shi dai karta fita."
Tafin hannuntan yasa tsakanin wuyanshi da kafaɗanshi cikin yanayin mai wuyar fasalta sirrin zuciyarshi.
yayi mata wani irin kallon da taji tamkar ta faɗa jikinshi,
zaro hannun nata yayi ya ɗaura shi kan bakinshi a hankali yayi mata wani fitinenne kissing bayan hannunta,
ido ta lumshe cikin tsananin farin ciki ta ɗan janye hannunta tare da miƙewa cikin sakin fuska da zuciya tace.
"To bari inje in ɗauko Adeel kajishi can yana kuka".
Kai ya gyaɗa mata alamar to.
Tana fita kai tsaye side ɗinsu ta wuce, dan Adeel kam wurin Ummi ma yake.


Shi kuwa Saifuddeen
yana kallonta har ta fice daga cikin ɗakin. Hannunsa yasa yaɗan tallafo haɓar Zaleeha data sunkuyar da kanta tallaɓo haɓarta ya kumayi.
Hakanne yasa taɗan bude idanunta ahankali, ɗan ƙaramin bakinta ta turo, take kuma saiga ƙwalla sun cika idanunta. Ɗan rolling beauty eyes ɗinsa yayi, cikin body language ɗinsa yace. "Menene kuma?."
Ɗan hararannsa tayi, cikin muryarta da ke fidda zallan sakalcinta tace.
"Ka sani ai".
Kanshi ya jujjuya da sauri tare da waro idanunshi alamu a a ni ba abinda na sani.
Narke fuska tayi tare da cewa.
"To bakai bane kajimin ciwo".
Jin muryarta acikin kunnuwansa, ya sashi lumshe idanunsa, wani irin ni'ima da daɗi ne yakeji na ratsa sa, take daɗin muryar tata ta sauƙar masa da kasala. Shagwaɓewa yayi shima cikin body language ɗinsa yace.
"Nima bake bace, kika sa duk jikina yayi weak, ko tashi da kyau bana iyayi bayan ma ya ida golɓalewa kun huta keda Ameena baku da mijin da zai lilaku."
Hannu tasa taɗan daki ƙirjinsa, cike da wani zazzafan shauƙi tace.
"Wai ni, wallahi bani bane, kaine ai kuma sai Allah ya sakamin..." Murmushi yayi tare da jawota gaba ɗaya jikinsa, ta zauna akan cinyansa, hannunsa yasa ya kamo waist ɗinta, tare da ƙura mata ido kana ya mata alaman, kan me Allah zai saka miki?.
Tura masa baki tayi, asanyaye tace.
"Zalina da kaci mana".
Murmushi yayi tare da jawo wayar shi ya rubuta mata.
"A a ni banci zalinki ba, ni amarci da budurci naci, kuma halal nane. sadakina na amsa".
Nuna mata rubutun yayi yana mata ɗan murmushin ƙeta.
Karya wuya ta ɗanyi a hankali tace.
"Nidai Allah zafi nakeji, kuma sai na faɗawa Ummi irin ciwon da kaji min."
Murmushi yayi, cikin body language ɗinsa yace.
"Haba da gaske naji miki ciwo?".
Still baki ta sake murguɗa masa, ahankali ya ɗaura ƴan yatsunsa yana zagaye laɓɓanta.
Cikin shammata ta kamo hannun nasa ta tura abakinta, kan babban yatsansa ta ɗaura haƙorinta, tare da ɗan cizawa.
Hakanne yasashi sakin wani irin nishi da ɗan ƙarfi, tare da rumtse idanunsa, alaman zafi, ganin haka yasa ta sakin dariya har dimple ɗinta na lotsawa.
Dariya take sosai inda ta ɗaura duka hannayenta akan wuyansa ya zama suna fuskantar juna da kyau dariya takeyi sosai tare da cewa.
"Kaji ai kaida cizone ma kaɗai ni kuma kana wani cemin baka ji min ciwo ba".
Dariya ta kuma saki ganin yadda yayi mata da fuskarshi dariya takeyi sosai harda rufe Idanunta.

Sake jawota yayi, tare da matseta ajikinsa, kansa ya soma ƙoƙarin cusawa acikin wuyanta, tare da saka bakinsa yana ƙoƙarin kamo fatan wuyanta wai zai ciza shima zai rama. Hakanne yasa dariyanta ƙaruwa sosai, dan tanajin kaman cakulkuline yake mata.
Sosai take dariya tana son zillewa amma ya riƙe ta gam.
Dai-dai lokacin Ummi ta nufo ɗakin dan a zatonta Ameena na nan har yanzu shiyasa da Adeel ya fara kuka ta ɗaukoshi zata kawo mata shi.
A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin tana shiga tai saurin...!




Littafina na kuɗi ne biya ki karanta halal ɗinki turo katin mtn na ɗari uku ta wannan number 09097853276 ko kimin transfer ta asusuna na 0005388578 jaiz back Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyarki ta nan 09097853276. In kin karanta na sata 😂😂😂 yaseeen doguwa bulluƙutu baƙar mutuwa aradu🤣🤣


Allah sarki yarinta duk sanda nace yaseen doguwa bulluƙutu baƙar mutuwa, sai na tuna yarinta, Brother Usman wannan shafin nakane Dr Usman Aliyu Garkuwa ɗan uwana rabin jiki, yau da gobe mai nesanta yan uwa, in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login