Showing 123001 words to 126000 words out of 239422 words

Chapter 42 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11896

dake zaune acan gefe kaman mutum mutumi kuwa idanunsa kawai ya zuba musu, shikam aduniya yanajin cewa tunda matarsa ta rasu ta barsa, shikenan duk wani jin daɗi da farinciki sun ƙare masa. Ɗago kai Baba Malam yayi da idanunsa wanda sukai jajur, cikin sanyin murya yace.
"Tabbas kin shayar dani baƙinciki marar misaltuwa, kinyimin abun da duk acikin ƴaƴana babu wanda ya ta ɓamin, kin ƙi zaɓina sannan kika gudu kikabar gidan mijinki ɗanki aurenki ba tare da izinin mijinki ba." farin handkerchief ɗin dake hannunsa yasa, inda ya share ƙwallan dake ƙoƙarin fitowa daga cikin idanunsa. Ajiyar zuciya ya sauƙe, sannan yace.
"Bani zaki bawa haƙuriba, shi kika saɓa kika wulaƙanta aureshi, shine al'jannarki take ƙarƙashin diga-diginsa dan haka shi zaki bawa haƙuri ba niba yafiyarsa zaki nema da kika fita bada izininshi ba, sai ya yafe miki kafin ni in yafe miki".
Da sauri ta juyo ta fuskanci Saifuddeen murya na rawa kana murya a disashe tace.
"Kayi hakuri Hamma Saif ka yafe min in sha ALLAH har iya raina da mutuwata bazan sake fita ba saida izininka ko bakin gate bazan sake zuwaba saida izininka".
Haɗe hannayenta tayi alamu roƙo kana hawaye na kwaranya a fuskarsa, kanshi ya rinƙa jujjuya mata yana mai jin zazzafan tausayi ya, murya na rawa ta kuma cewa.
"Dan Allah Hamma Saif ka yafe min".
Kanshi ya kuma jujjuya tare da mata alamun ya yafe mata duniya da ƙiyama,
sai kuma ta juyo da sauri ta kalli Baba Malam murya a harde tace.
"Baba Malam ka yafe min shi yace ya yafe min".
Gyara zama Baba Malam yayi kana yace.
"To in na yafe miki me kuma shirinki na gaba zaki sake, gudawa ne? Ko dai kinyi tuba na gaskiya ne zaki zauna ɗakinki, ko bazaki zauna ba?."
A hankali ta sunkuyar da kanta zazzafan hawaye na zuba murya na rawa tace.
"Har Abadan bazan sake guduba, zan zauna iya raina da mutuwata har sai dai in na mutune zan bar gidanshi babu inda zanje duk rintsi koda ko ba daɗi zan zauna Baba malam zanyi biyayya kwatankwacin wanda Adda Maryam tayi maka, koda daɗi ko ba daɗi zan zauna."
Gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi hatta shi kanshi Baba malam tausayi ta ya rufeshi,
cikin sanyi yace.
"Kin san yayi aure bayan guduwanki?".
Cikin kuka tace.
"Ban saniba saida naje gidanshi naga matar da ɗanshi."
Kai ya jinjina tare da cewa.
"To ki koma gidanki ɗakinki, ban kuma yarje miki fitina da abokiyar zama kina ki zauna lafiya da ita da ƙanneshi da yayunshi, kada inji wani abu tsakanin ki da abokiyar zamanki, kada ki tsokaneta ko kaɗan in kuma itace ta tsokaneta ki mata uzuri ki yafe mata kada kice zaki rama duk abinda tayi miki".
Cikin wani masifeffen kuka tace.
"To Baba Malam in sha Allah zaka sameni mai bin umarni ka".
Kanshi ya gyaɗa cikin tausayinta a ranshi sabida kukanta na ƙunshi da abubuwa da dama, cikin sanyi yace.
"Koda ki tauye haƙƙin mijinki a kanki Zaleeha kada ki haneshi abinda duk Allah ya halattamishi a kanki".
Cikin rawan murya tace.
"To in sha Allah zan zauna dashi sai kuma in shine yace baya sona."
Wani irin tausayinta ne ya rufesu baki ɗaya cikin taushin lafazi Baba Malam yace.
"Tabbas kinci al'barkacin Dirankadi da kuma Saifudddeen, saboda haka kije na yafemiki duniya da ƙiyama, ina roƙon Allah Ubangiji kuma ya shiryeki, Ya sa miki imani azuciyarki ya baki zaman lfy da mijinki da abokiyar zamanki,
haƙiƙa kin ƙuntatawa zuciyata, kin shayar da ahalinki baƙin ciki, Maryam harta koma ga ubangijinta bata taɓa saɓawa maganata ba koda kuwa sau ɗaya ne, na aurar da ita ga zaɓina, kuma ta amince duk da cewa bataso amma tayi Mini biyayya, haka kuma bata taɓa saɓawa mijinta ba, gashi Allah ya ɗauketa adai-dai lokacin da kowa yake da buƙatanta, Ya Allah kajiƙan Maryam kasa al'janna tazamo makoma agareta...".
Kukane ya ƙwacewa Baba Malam ɗin, wanda hakan kuwa yayi matuƙar taɓa zuciyoyinsu, hakanne kuma yasa hawayen dake cikin idanun Saifuddeen samun daman gangarowa, zuwa kan ƙuncinsa, Zaleeha kuwa kuka take sosai kaman ranta zai fita, haka ma Ya Ahmad, wannan karon harta Malam Adam da Dirankadi saida sukayi hawayen, tausayin ahalin.
Ya Ameenu kam, bai iyayin kuka ba, saboda ayanzu kukan zuci yake, wanda yafi na fili ciwo, adai-dai wannan lokacin kuwa shi kaɗai yasan me yakeji. Cikin matsanancin kukan, ta rarrafa inda ta ƙarasa gaban Ya Ahmad wanda ke kuka sosai, tana zuwa ta kifa kanta akan cinyansa, tana kuka sosai har kaman zata shiɗe, hannu Ya Ahmad ɗin yasa ya dafa kanta, lokaci guda kuwa ƙarfin kukansa ya ƙaru, gaba ɗaya falon haka ya ɗauki shiru babu abun dake tashi sai sautin kuka anrasa me rarrashin wani, hatta Malam Adam da Dirankadi gaba ɗaya jikinsu amace yake, gaba ɗaya zuciyoyinsu sunyi rauni.


Da ƙyar Baba Malam ya iya share hawayensa, cikin muryarsa da ta ɗan dashe yace.
"Nayafe miki Allah ya yafe mana baki ɗaya, ki tashi ki koma ɗakin mijinki, Sannan in mijinki ya amince miki duk sanda kuka samu lokaci kuje gidan Maryam ta barmin wasiyar tayi miki ajiya cikin durowar ta ta jikin gado."
Hannu yasa ya share hawayenshi kana yaci gaba da cewa.
"Kuma matuƙar kika sake mugun saɓawa Saifuddeen ba irin wanda dole akwaishi tsakanin ma'aurataba wallahi! bazan taɓa yafe miki ba Zaleeha, kuma daga wannan lokacin kiceri kanki daga mazaunin ƴata!!!."


Jin furucin Baba Malam ɗinne yasanya cikin kuka ta ɗago daga jikin Ya Ahmad, dawowa gaban Baba Malam ɗin tayi tare da durƙusa guiwowinta a ƙasa, kanta ta ɗaura ajikin Baba Malam ɗin tana wani irin kuka me ɗaga hankali, gaɓa ɗaya jikinta rawa yake, ga kuma wani sheshsheƙa da take saki wanda yasa numfashinta keyi kaman zai ɗauke. Cikin kukan da kuma muryarta wanda bata fita sosai tace.
"Nagode Baba Malam! Nagode sosai da ka yafemin, kuma insha Allah zaka sameni me biyayya agareka dashi Hamma Saif..."
Kuka take sosai harda majina, Ahankali Saifuddeen ya haɗe hannuwansa, tare da ɗan lumshe idanunsa, alaman godiya, still kuma hawayene kwance akan fuskarsa. Murmushi Baba Malam yayi tare da sanya hannu ya shafi kan Saifuddeen ɗin, tabbas Saifuddeen mutunne me nagarta, da kuma zuciyar imani, sai yanzu yake ƙara aminta cewa bazai taɓa danasanin bawa Saifuddeen auren ƴarsa ba, haƙiƙa Saifuddeen yacika me kyakkyawar zuciya, tabbas irinsu aduniya basu da yawa. Malam Adam ne ya rarrashi Ya Ahmad wanda yake ta kuka, Dirankadi ne yayiwa Baba Malam ɗin godiya, ganin irin kukan da take, yasa Baba Malam yiwa Saifuddeen alama cewa ya ɗauki Zaleehan suje. Wheelchair ɗinsa ya hau, sannan ya sanya hannu ya ɗago ta, kuka take sosai, haka ya riƙe hannunta suka fice daga cikin falon.
Anan cikin ɗan corridor ɗin ƙofar falon ya tsaya, tare da zaro handkerchief a al'jihunsa idanunsa wanda suka ɗan lumshe ya zuba mata, sannan ya miƙa mata handkerchief ɗin,
Cikin wani irin zazzafan kuka ta faɗa jikinshi tare da kife kanta bisa cinyoyinshi ta saki kuka mai cike da rauni,
wani irin tausayinta yakeji na ratsashi a hankali ya ɗan magoya kana ya kuma miƙa mata handkerchief din hannunta na rawa haka ta amshi handkerchief ɗin, ahankali take goge hawayen fuskarta tana sakin sheshsheƙa.








Littafina na kuɗine in kina buƙata ga no 09097853276


Wannan shafin nakune NAKASA BA KASAWA BACE fans 3&4 inayi muku fatan al'khairi


By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Sbpejny Cikin sheshsheƙan kuka, da kuma muryarta dake dashe tace.
"Ayyah Hamma Saif kayi haƙuri ka kaini na bawa su Mamy dasu Aunty Lubna haƙuri, dan suma fushi sukeyi dani."
Kyawawan idanunsa ya ɗan lumshe, tare da jinjina mata kai, alaman "To."
Hannunta dake cikin nasa ya ɗan murza, sannan suka nufi ɓangaren Mamyn.
Har zuwa yanzu kuwa bata daina sakin sheshsheƙan kuka ba, hasali ma amaimakon kukan nata ya tsaya, ƙaruwa yayi, saboda wani irin yanayi da takejin kanta aciki.
Anan bakin kofar shiga sashin Mamyn ya tsaya, saboda aganinsa bai kamata ya shiga musu kai tsaye ba tare da an masa iso ba.
Ganin ya tsaya ne, yasa ta juyowa ta kalleshi, gani tayi ya zuba mata kyawawan idanunsa, wanda da zaran ta kalli cikinsu, to sai taji wani iri ajikinta.
Ɗan lumshe idanun nasa yayi tare kuma da buɗe su alokaci guda, wani irin abu ne taji yabi jikinta, hakan yasa ta zare hannunta daga cikin nasa.
Ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar falon, ta shiga bakinta ɗauke da sallama, wanda muryarta ko fita da kyau bayayi tsabar kukan da tayi.


Mamy, Aunty Lubna, da kuma Goggo Maryama, da Ziyada, sai kuma su Zainab da Ubaida ne zaune a cikin falon, jin sallaman Zaleehan ne yasa su duka ɗago kai suka kalleta, ahankali take takawa har ta ƙaraso cikin falon, da ɗan sassarfa taje ta faɗa jikin Mamy, tare da sakin sabon kuka me sauti, rungume Zaleehan Mamy tayi, tana mejin matsanancin tausayinta aranta, jin Mamyn ta rungumeta ne, yasa ta ƙara volume ɗin kukan nata, haka falon ya ɗauki shiru ba abun dake tashi cikinsa sai sautin kukan Zaleeha, hakanne yasa hawayen dake cikin idanun Mamy suka samu daman gangarowa.
Cikin sheshsheƙan kukan ta ɗago daga jikin Mamyn, muryarta na rawa tace.
"Mamy dan Allah ki yafemin, kinga Baba Malam ma ya yafemin, kuma yace na koma ɗakin mijina na zauna, fushin Baba Malam ya tsoratani sosai Mamy, wallahi bazan sake gudun ku ba, nasan nayi kuskure me girma dana tafi na barku, bayan kuma aduniya bani da wasu sama daku, dan Allah Mamy kema kiyi haƙuri kinji, Ya Ahmad ɗina ma ya yafemin."
ta ƙare maganar tana me kamo hannun Mamyn ta riƙe.


Murmushi Mamy tayi tare da share hawayenta, tabbas taji daɗin jin cewa Baba Malam ɗin ya yafewa Zaleeha, dan ko itama adole taƙi kula Zaleehan, bawai dan tana fushi da ita ba, duk da ma tasan cewa abun da Zaleehan tayi bai dace ba, amma fushin da aka yi da ita yayi yawa, ba a fushi me tsanani ga ƴa mace irin haka.
Ɗan shafa bayan Zaleehan tayi, cikin kulawa tace.
"Kukan Ya isa haka Zaleeha, tabbas naji daɗi ƙwarai da Baba Malam ya yafe miki, nidama tuncan Zaleeha ba fushi nake dake ba, kuma na yafe miki, sannan dan Allah kada ki sake kamanta irin kuskuren da kikayi abaya kinji, sam guduwa ga ƴa mace ba ɗabi'a bace me kyau, ki zauna agidan aurenki kiyi zama me kyau, kada ki saɓawa mijinki, tasanadiyar hakan da zakiyi saikiga kin samu aljanna da yardan Allah."


Cikin kuka ta jinjina kanta alaman gamsuwa, da kalaman Mamyn, ahankali taɗan janye jikinta tare da tashi ta ƙarasa gaban Goggo Maryama, durƙusawa tayi tare da, ɗaura kanta akan cinyar Goggo Maryama'n, cikin sheshsheƙan kuka tace.
"Dan Allah Goggo Maryama ki yafemin, nasan kema kina fushi dani, dan Allah Kuyi hakuri, yanzu al'barkanku nake nema."
Goggo Maryama kuwa Ɗan share hawayen dake cikin idanunta tayi cikin sanyi tace.
"Babu komai Zaleeha na yafe miki, Allah ya yafe mana baki ɗaya, fatana dai shine ki nutsu kiyi zaman aurenki, insha Allah saikiga Al'barka nata bibiyan rayuwarki."
Kanta ta jinjina, cikin sanyi tace.
"Nagode sosai Goggo ." tashi daga jikin Goggon nata tayi, kai tsaye jikin Aunty Lubna ta faɗa, rungumeta tayi ƙam, tana ɗan sakin sheshsheƙa, itama Aunty Lubna'n hawayene cike a idanunta, saida sukayi kuka sosai kafun, Zaleehan ta sake riƙe Aunty Lubna'n, cikin dashashshiyar muryarta tace.
"Aunty dan Allah ki yafemin, kidaina fushi dani, kinga Ya Ahmad ma ya yafemin."
wani irin tausayin Zaleehan ne ya cika zuciyar Aunty Lubna, cikin kulawa tace.
"Ni dama ban ƙullaceki da komai ba Zaleeha, wallahi na yafe miki har acikin zuciyata."
Ziyada dake zaune agefe ne ta taso tare da ƙarasowa ta rungume Yayarta ta, nan tasaki kukan tausayinsu, juyowa Zaleeha tayi ta rungume Ziyada'n, wanda ayanzu take ganinta kamar Adda Maryam, dan sanyin zuciyar Ziyada dana Adda Maryam ɗin iri ɗaya ne.


Acan ƙofar shigowa falon kuwa Saifuddeen ne zaune ya sunkuyar da kansa ƙasa, Zakariyya wanda shigowansa gidan kenan, hango Hamma Saifuddeen zaune akan wheelchair ɗinsa yasa shi ƙarasowa cikin sauri, fuskarsa ɗauke da ɗan murmushi ya taɓa kafaɗan Saifuddeen ɗin, tare da cewa.
"La Hamma Saifuddeen kaine."
murmushi Saifuddeen yayi tare da miƙawa Zakariyya'n hannu suka gaisa, fuskar Zakariyyan ce taɗan fidda rauni, asanyaye yace.
"Hamma da Adda Zaleeha kuka zo?". ahankali ya jinjina masa kai alaman "Eh" wani irin daɗi Zakariyyan yaji acikin ransa shikenan yasan Baba Malam ya yafewa Zaleeha, cikin zumuɗi ya kama saman wheelchair ɗin Saifuddeen ɗin, tare da cewa.
"Hamma mu shiga ciki to."
Haka suka shigo cikin falon na Mamy, bakin Zakariyya ɗauke da sallama.
Har tsakiyan falon Zakariyya ya ƙaraso da Saifuddeen ɗin, nan cikin body language ɗinsa ya gaishe da Mamy, da kuma Goggo Maryama, fuska asake haka suka amsa masa, gaishe da Aunty Lubna yayi itama ta amsa tanayi masa murmushi, dan Allah ma yasani itakam Saifuddeen ɗin na burgeta, mutum ne shi me mutunci da kamun kai, komai nasa daban, babu ruwansa da cewar shi nakasashshe ne, abunda ta fahimta ma shine shi nakasar tasa ado ta zame masa, dan idan yana kan wheelchair ɗinsa zaka ɗauka cewa wani sarkine mai cikakken iko,,
sosai abun keyi masa kyau.
Zainab da Ubaida ne suka gaidashi, cikin body language ɗinsa ya amsa yana ɗan murmushi, sukam daganinsa mamakine yakusan kashesu, sunsan dai Zaleehan gurgu kuma kurma ta aura, amma ko kusa basusan haɗuwa da kyawunsa har yakai haka ba, dan idan ma ba dan sunsan cewar shi gurgu bane, to zasuce ya hau keken ne kawai dan ƙarawa kwalliyarsa armashi, Ubaida ne ta jinjina kanta, acikin zuciyarta tace.
"Lallai Zaleeha bata da hankali, wace macece zata samu wannan santalelen namijin sannan ta gudu ta barsa? hmmm ai irinsu Saifuddeen koda na kasarsu mata wawansu suke, saboda koba komai akwai kyau da cikar haiba."
Ziyada ne ta taso daga jikin Zaleehan tare da taƙarasowa gabansa, ɗan durƙusawa tayi, cikin sanyinta tace.
"Hamma Saifuddeen ina wuni."
Murmushi yayi wanda yaɗan bayyana fararen haƙwaransa, hannu yasa ya ɗan shafa kanta, cikin kulawa ya jinjina mata kai alaman "Lafiya" Zakariyya kuwa ƙarasawa wajen Zaleeha wanda kanta ke jikin Aunty Lubna tana ta faman sakin sheshsheƙan kuka yayi, cikin sanyi yace.
"Adda Zaleeha." ɗago kanta tayi ta kalleshi, sai kawai ta faɗa cikin jikinsa, tana sakin sabon kuka, shikansa Zakariyyan saida yayi ƙwalla, da ƙyar ya saitata ta iya tsaida kukan nata, hannunta ya kamo sannan ya haɗa dana Saifuddeen cikin kulawa yace.
"Muje na rakaku part ɗin Mama."
Hakan kuwa akayi har part ɗin Maman ya kaisu, anan falo suka iske, Mama, Aunty Ruda, da kuma Aunty Aisha, da Maman Mama da dai sauran ƴan uwanta arnataku,
gaba ɗaya sunyi jigum dasu.
Jin motsin shigowarsu, da kuma ƴar siririyar sallaman Zaleehan ne ya sasu ɗago Idanu suna kallonsu, Zaleeha na tafiya asanyaye, yayinda Zakariyya kuwa ke tura saman keken Saifuddeen ɗin, ahaka suka ƙaraso cikin falon, anan gaban Mama Zaleeha ta durƙushe tare da ɗan ɗaura kanta akan cinyar Maman, haƙiƙa uwa uwace komin munin halinta kuwa tana nan a mazaunin ta na uwa, sannan kuma ba'a taɓa sanjata, idanu Zaleeha ta lumshe, hakanan taji wani sabon kuka nason zuwar mata.
Su Mama kuwa gaba ɗaya tun shigowarsu idanunsu akan Saifuddeen suke, musamman ma Aunty Ruda da Mama dan tunda suke basu taɓa ganinsa ba sai yau ɗin, ganin hakanne yasa Saifuddeen sakin ɗan murmushi tare gaidasu cikin body language ɗinsa da Aunty Ruda'n, da kuma Aunty Aisha, fuska asake kuwa Aunty Aisha ta amsa masa, Aunty Ruda kam idanu ta zuba masa, tana mamakin tsantsar kamala kwarjinin da kyaun sa.
Juyowa yayi ya ɗan kalli Mama, cikin yanayin girmamawa ya gaisheta, idanu taɗan zuba masa, asanyaye da muryarta wanda ta dashe saboda tsabar kukan da tayi na rasuwar Adda Maryam ɗin ta amsa masa, lokaci guda kuma tayi ƙasa da kanta, saboda hakanan taga yayi mata kwarjini, acikin idanunta kunya mai ƙarfi da dana sani suka rufeta, dan kwata-kwata bata ɗauka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login