Showing 228001 words to 231000 words out of 239422 words

Chapter 77 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11840

kusa samun ƙanin Adeel, jiya tunda muka dawo Baby keta amai ashe, cikine ni bamu saniba sai ɗazu ya Adnan ke sanar min."
Cikin tsananin jin daɗi Ishaq yace.
"Alhamdulillah, kai nayi farin ciki, kai mutumina ba sauƙi kai ko yaushe bugu ɗaya kake jefa ƙollo a raga".
Dariyar keta Saifuddeen yayi tare da cewa.
"Sune zalamammu daga na basu sai su ƙarɓa, kuma dama Zaleeha kam addu'ar da nayi tayi kenan, har a kaba na roƙi Allah ya azirtamin samun haihuwa da ita akai-akai kafinma ta ankara, gidana ya zame mata farin cikin duniyar ta, ta haifo min yara dozin-dozin".
Dariya sosai Ishaq yayi kana yace.
"Mugu, to Allah ya sanya al'khairi ya sauƙeta lfy".
Amin Amin yace kana sukayi sallama".
Daga nan ya shiga falon Zaleeha a falon suka haɗu cikin kula ya miƙo mata hannu, kana suka nufi falon Ummi.


Suna shiga, duk suka gaggaisa, hannu Zaleeha tasa ta karɓi Adeel dake hannun Hayatuddeen,
cikin kula sukayi mata sannu da jiki.
Ameena da Rayila ne da suka gama shirya breakfast a dinning table suka iso falon cikin sakin fuska Ameena ta kalli Saifuddeen fuska a sake tace.
"Congrats Abban Adeel, Allah ya sauƙeta lfy".
Amin Amin sukace baki ɗayansu,
Ita kuwa Zaleeha sunkuyar da kanta tayi ƙasa cikin tsananin jin kunya.
Shi kuwa Saifuddeen wani irin fitinenne kallo yakewa Ameena kallo mai cike da mutun taka, ji yake tamkar ya kamota ya ruggumeta, amman ba dama, ita kuwa ganin kallon da yake matane yasa ta meda kanta kan Zaleeha sabida taga Saifuddeen kallon farin cikin tayashi murnar da tayi yake mata ta hango wani baiyanenne farin ciki a fuskarshi cikin kula tace.
"Ammin Adeel ya jikin?".
A hankali tace.
"Na worke fa Ummu Adeel".
Dariya Raliya tayi tare da cewa.
"In kinci abinci ne zamu yarda kin worke".
Da sauri Saifuddeen ya jinjina mata kai alamar da kyau.


Ahmad kuwa dariyar ƙeta yayi tare da cewa.
"Allah ya fito mana da _Sodangi_ mu lfy, dan dai shine ya somu yasa aka gudu aka kuma dawo,
Jingudo haka sunan yake ko macece ko na mijine".
Dariya sukayi dukansu, Ameena kuwa shiru tayi.
Kalmar Jingudo da Ahmad ya kira ta amsa mata tarin tambayoyin dake ranta na cewa ina Zaleeha taje
Dan duk cikekken bafulatani in yaji an kira yaro da Jingudo ko Sodangi to yasan auren dole akawa mace, ta haifeshi a gidan wanda aka aura mata dolen, to shi ake cewa Jingudo."
A ranta ta tuno kalmar Adda Rahma inda take cewa mata.
"Kan Abu ɗaya ya taɓa nuna ƙulafashinsa a duniya a kanta ne kaɗai,
Sai ta kuma nazarci kalmar Ahmad na cewa Allah ya fito mana da Sodanginmu lfy don dai shine ya somu an gujemu an dawo".
Kai ta rausayar jin Ummi na cewa suje suci abinci.
kan dinnin table ɗin suka nufa, tana mai magar zuciya.
"Uhumm Ahmad kenan da kenan ka sani yanzu son Abban Adeel da nake hangowa cikin idonta ya wuce zaton mai zato, Allah sarki wato auren dole akayi mata, da alama kuma guduwa tayi lokacin da Adda Maryam ta rasune ta dawo ikon Allah to meyasa Zaleeha zataƙi Abba Adeel duk da tarin kyanshi da dukuyarshi basu ruɗeta ba."
Jin Saifuddeen ya murza hannunta alamun taci abinci ne yasa tasa hannu ta fara ci.
Zaleeha kuwa sanadin alluran da akayi mata to ta samu taci abinci sosai,
shiyasa duk jiri da murɗa da duhun suka tafi sai ɗan kasalar da ba'a rasaba.




Ranar dai Saifuddeen wuni yayi yana jinya,
shida kanshi kuwa ya kira Ya Ameenu da ya Ahmad ya sanar musu batun cikin Zaleeha,
sosai Ya Ahmad yai tawa Zaleeha wasa wai ashe yanzu kam girma yazo zata bar guje-guje.




A can gidan ya Ameenu kuwa suna gama yin mgnar ya kalli Ziyada dake zaune gefenshi hannunta ya rike a hankali yace.
"Kinji Adda Zaleehan takima bata da lfy, tanata aman laulayi ciki gashi kema har yanzu tafiyarki bata gama gyaruwa ba,
kiyi haƙuri sai kin ƙara samun sauƙi sai in kaiki ku wuni kinjiko Mar'tus saliha na tuba".
Kai ta jinjina cikin sanyinta irin na adda Maryam tace.
"To Ya Ameenu".
Jawota yayi ya ruggumeta domin biyeyyarta sak Maryam yake gani sam basu da gardama.


Bayan sati ɗaya lokacin cikin Zaleeha ya cika watanni uku cib-cib kuma Alhamdulillah ba laulayi sosai yanzu sai yawan cin abinci.
Da dare Ameena ce ke zaune gefen Saifuddeen wanda yake waya da Dr Acash prasat,
nan yake gaya mishi. "Lokacin dawowarka fa ya kusa".
Kanshi ya gyaɗa dan video call sukeyi cikin nitsuwa yace.
"Eh inata shirin zuwa ai".
Da sauri Dr Acash prasat yace.
"No karka taho India, ƙarshen watan nan zamuyi taron ƙarawa juna sani na duniya baki ɗaya, zamuyi taron ne kuma a Istanbul na kasar Turkey.
So kayi ƙoƙari mu haɗu a can, zan haɗaka da wani babban Dr da zai dubaka wanda duk ya fimu sanin matakan warakar ciwon insha Allah zaka samu dace".
Cikin gamsuwa da wani sahirtaccen jin daɗi Saifuddeen yace.
"To ba matsala".
Daga nan suka katsa wayar,
cikin kula Ameena tace.
"Kai ƙasa mai daɗi kena Instabul weather su akwai masifar daɗi."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Sanyi su ne keda yawa, tsarin ƙasar is Gud, a dai irinmu masu larurar spinal cord injury jikinmu irin garin yakeso".
miƙewa tayi tare da cewa.
"Eh sosai ma kuwa".
A hankali yace.
"Ina zakije kuma kika tashi."
Hannu tasa ta tallaɓe ƙirjinta tare da cewa.
"Zan ɗauko Adeel ne naji mamanshi nata tsastsafo alamun ya tashi a bacci kenan".
Dariya yayi tare da cewa.
"Tsakanin uwa da ɗanta sai Allah".
Murmushi tayi kana ta fita.
Shi kuwa text message ya turawa Zaleeha.
"Salam, Baby maman baby kinyi bacci ne?".
da sauri ta maida mishi amsa.
"A a banyi ba, ina cin abin daɗin ne Ummi na ta dafa min."
murmushi yayi tare da rubuta mata.
"Abin daɗin kam ai yana wurina".
Murmushi tayi.
da sauri ta duba sakon daya kuma tura mata.
"Kinada E Passport ne"?".
a hankali ta rubuta mishi "Eh to gsky nawa ya daɗe bazaiyi aikiba yanzu".
"To ki shirya gobe da safe zamuje imagireshon Office, aiyi miki E Passport ɗin".
ido ta lumshe cikin tsananin farin ciki dan dai tasan ƙasar za'a bari da ita kenan tunda taji ana neman E Passport a zahiri kuma sai cewa tayi to.


Washe gari kuwa da safe sukaje akayi mata E Passport ɗin ta,
daga nan airport suka wuce,
ya fara nema musu damar barin ƙasar,
sai azahar suka dawo gida.




Alhamdulillah yanzu tana cin abinci ba laulayi, kamar yadda Ameena ta raini cikinta a sauƙaƙe,
to haka itama ko dan jinin mutun ɗaya ke gudana a jikinsu.


Rashida da Ishaq kuwa sunata dandatsa Amarci baba kama hannun yaro.


Yanzu cikin Zaleeha ya shiga wata huɗu, kuma ya ɗan fara baiyana duk da ƙugunta da mazaunanta ne suka fi buɗuwa sukayi tib-tib gwanin sha'awa sai ƙirjinta da yayi tamtsan-tamtsan


Yau tunda safe Ziyada keta shirin zuwa gidan Adda Zaleehanta,
sai dai Ya Ameenu ya mata tsiya yana ganinta shirya ta shirya Ayman murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
"Ayman zo in ai keka wurin baba maigadi, kace ya tsinko maka nunnen maggoro ka kawo min".
Da sauri yaro yace.
"To Daddy innce adda ni ko a bani mai yawa dana Aunty Ziyada ko?".
Kai ya gyaɗa mishi tare da cewa,
"Eh maza yi sauri ɗan al'barka".
Ai kuwa a guje ya fita,
yana ganin fitan yaron ya jawo hannunta sukayi cikin ɗaki a hankali ya rufe ƙofar da sauri tace.
"Ya Ameenu ka rufe ƙofar kuma?".
Kanshi ya gyaɗa mata tare da cewa.
"Kizo mu ɗanyi wata mgna kafin ya dawo, nasan zasu dade a cikin labbun kafin su samu nunnenen mangoro".
Ba musu ta bishi suka hau gadon cikin raɗa yace.
"Kullum in Maryam zataje anguwa, in tayi kolliyar sai mun ɓata kolliyar forkon muyi wonka tare kafin tayi na biyu".
Cikin sanyi ta tace.
"To in da zaka kaini?".
Zip ɗin rigarta ya fara zugewa tare da cewa.
"In kin min duk abinda nayi mikiba".
Da haka ya shagalar da ita ya biya musu buƙatarsu sannan, suka sake wonka suka sake sabon shiri sannan ya kaita gidan Zaleeha,
yana sauƙeta ya juya ya fita


Ita kuwa a hankali ta nufi sashin Ummi tana tafe cikin nitsuwa.
A hankali ta murɗa ƙofar falon tare da yin sallama.
Da sauri Raliya tace.
"A a Ziyada maraba da zuwa."
Zaleeha dake kitchin ne ta fito da sauri jin an kira sunan ƴar uwarta.
Da sauri ta nufesu tare da cewa.
"Oyoyo my Ayman miss you so much".
ɗagoshi tayi tsam ta riƙeshi.
Kana ta kalli Ziyada dake ɗan murmushi cikin jin daɗi tace.
"Allah sarki Ziyada sai yau kika tunani?".
Murmushi Ziyada tayi kana ta juyo ta kalli Ummi da yanzu ta fito ɗakinta cikin kula tace.
"A a lale marhabin Ziyada sannu da zuwa".
A hankali tace.
"Yauwa Ummi sannu, ina kwana?".
"Lafiya lau ya mai gidanki?".
Ummi ta faɗi cikin kulawa ita kuwa Ziyada a sanyaye tace.
"Alhamdulillah Ummi yace in gaidaki ma, yace ince miki sai yazo ɗaukarmu zai shigo ku gaisa, yanzu yana sauri ne".
Cikin kula Ummi tace.
"Ayyah to mgd sosai".
Raliya ce ta kalli Ziyada tare da cewa.
"Ina kwana ya gida?".
Fuska a sake tace.
"Lfy lau Alhamdulillah, ya ayyuka?".
Alhamdulillah tace.
cikin girmamawa Ziyada ta kalli Zaleeha dake ta shafa kan Ayman tuni ida nunta sun cicciko da hawaye,
kanta ta kawar dan ganin hawayen Zaleeha zaisa nata hawayen fitowa a hankali tace.
"Inna kwana Adda Zaleeha".
Murya a sanyaya Zaleeha ta kalleta tare da cewa.
"Lfy Ziyada ya gida, ina ya Ameenu?".
"Alhamdulillah gida lfy Ya Ameenu yana lfy yace in gaidaki".
Shiru suka ɗanyi ganin haka ne Zaleeha ta miƙe tare da cewa.
"Taho mu isa".
To Ziyada tace kana tabi bayanta,
har sunje bakin ƙofane Zaleeha ta ɗan juyo ta kalli Raliya tace.
"Yauwa Goggo Raliya na gama aikin gaba ɗaya sauran kwashe abincin ne ki ɗan ƙarisa mana".
To Raliya tace kana ta nufi kitchin ɗin.


Su kuwa Zaleeha na gaba riƙe da hannun Ayman, Ziyada kuma na biye da ita a baya,
Har cikin bedroom ta wuce dasu
Bisa tsakiyar gadonta suka zauna,
cikin sauri Ziyada ta kwanta tare da cewa.
"Wash Allah na, Adda Zaleeha nayi kewarku, kuma babu wanda yake leƙeni sai Baba Malam nane kawai duk ran jumma'a zaije mu gaisa".
Murmushi Zaleeha tayi Cikin son ƴar uwantata tace.
"Ke kinma ji daɗinki ke yar gatar Baba Malam ce, tunda har zuwa yake har gidanki, ni da yazo nanma bai iso yaga ɗakina ba".
Murmushi jin daɗi Ziyada tayi tare da cewa.
"A a wlh Adda Zaleeha ba batun ƴar gata, ai ranan da yaje nace mishi yazo wurin kine? Sai yace min a a ,
Ya za'ayi yazo gidanki, ga surkanki ga ƙannen mijinki ga abokiyar zamanki,
sai yace min ranan dai da yayi kewa ki kuma yaji baki da lfy, yasa Hamma Saif ya kai mishi ke ya ganki".
Dariya sosai Zaleeha tayi cikin jin daɗi tace.
"Oho dama shine yasa Hamma Saif yace muje gida aifa nayi mmki ban tambaye shi zuwa ba kawai yace muje gida, Allah sarki Baba Malam, Allah ya bar mana shi".
Amin Amin Ziyada tace cikin jin daɗi.
Nanfa sukayi ta hirar yaushe gamo hirar ƴan uwa sun sa Ayman a tsakiyarsu sunata shafa kanshi,
sai kiran sallan azahar da akayine suka tashi sukayi salla.
Daga nan kuma suka fito falo,
Abincin da Raliya ta kawo musune suka zauna sunaci suna hira.
Cikin hirar ne Zaleeha ta ɗan ƙoƙƙofi Raliya dan ta fahimci irin zaman da sukeyi da Ya Ameenu cikin kula tace.
"Uhum ni kam Ziyada, a ɗakin Adda Maryam kike ko?".
Cikin sanyi tace.
"Eh ana baba Malam yace in zauna".
Kansu suka ɗan sunkuyar dukansu hawaye na son zubo musu sai kuma suka shanye,
cikin sanyin murya Zaleeha tace.
"To Ya Ameenu kuma ina yake".
Ɗan jim Ziyada tayi kana a hankali tace.
"A ɗakinsa yake mana".
Kai ta gyaɗa kana tace.
"Kece kike kwana da Ayman ko?".
Da sauri tace.
"Eh".spoon ɗin hannunta ta ajiye tare da cewa.
"To shi ya Ameenu ne yake zuwa ɗakinki ko kece kike zuwa ɗauki shi?".
Cikin rauni da nitsuwarta da ƴarda da kusancin ƴar uwarta tace.
"Uhum last 2 week ya fara shiga ɗakina,
Adda Zaleeha nasha wuya ranan nai kuka har na kusan mutuwa, na tuno Adda Maryam in ba mutuwaba ya za'ayi in auri mijinta har mu haɗa makonci, ya Ameenu yana ban tausayi komai zai sai yace min haka sukeyi da Adda Maryam".
Cikin sauri suka share hawaye su a tare jin motsin shigowar Saifuddeen,
ido ya zubawa Zaleeha tare da jujjuya mata kai in boddy language yace.
"Kuka kuma, ba Addu'a zakuyi mataba, ke babba ke ya kamata ki rarrasheta taji sanyi sannan ki tasata gaba kina kuka".
Da sauri tace.
"Na bari".
Ita kuwa Ziyada cikin sanyin rai da murya tace.
"Hamma Saifuddeen ina wuni".
Lfy lau ya gida, ya amsa in boddy language.
A hankali ta kuma cewa.
"Ya Adda Zaleeha da jiki?".
Da sauƙi ya kuma amsa mata da yaren kurame.
sannan yayi musu nasihar kada su sake kuka daga nan ya wuce side ɗin shi.


Su kuwa nan sukayi ta hira har la'asar kafin suka tashi sukayi salla,
daga nan sukaje cikin gida,
Suka shiga kitchin su biyu,
koda Raliya tazo zatayi aikin Ziyada tace.
"Ke kam zauna ki huta muyi ta hira, yau na karɓa miki".
Cikin dariya Raliya tace.
"Ai nima yanzu na ban kwana nake musu dan, mun kusa ƙaura".
Da sauri Zaleeha tace.
"Wai yanzu fisabilillahi Ya Ahmad da gske yake nufin zaku ƙara?".
Dariya Raliya tayi kana tace.
"Sosai ma kuwa, kinga har yafa nema min gurbin karatu a G.S U yace muna ƙaura zan fara karatu, wai tunda Allah bai bamu haihuwa inyi karatu har sai inda nace na tsaya in kuma yi aiki."
Haka nan sai Zaleeha taji tausayin Raliya sabida tasan suna son haihuwa ita da Ahmad Allah bai basu, cikin sanyi tace.
"Ɗanki yana kan hanya in sha Allah, nakine ni na baki tun yanzu nasan kuma Hamma Saif bazai hanaku ba".
Cikin wani irin jin daɗi Raliya ta ruggumeta tare da cewa.
"Aunty Zaleeha ko baki baniba kin gaya min mgna mai daɗi ngd ngd matuƙa Allah ya sauƙeki lfy".
Murmushi Zaleeha tayi kana a hankali tace.
"Amin, karki damu kema zaki haifa, kuma zan baki wannan tunda mu ga Adeel".
Dariya sukayi dukansu ita kuwa Ziyada sai murmushi yakeyi tana kallon ɗan tudun cikin yayar tata.




A haka suka gama abincin dare.
Suka shirya komai a dinning table,
Zaleeha ta ɗauki food flask data sa nasu suka sallami Ummi sukayi side ɗin ta,
Raliya kuwa ta haura sama ɗakinta.


Suna gab mashagar side'nsu suka haɗu da Hamma Saif yana fito da alamun al'wala yayi cikin kula ya jawo hannun Ayman dake hannun Zaleeha ya mishi alamun yaje yayi al'wala yazo su tafi masallaci.
Ganin kamar Ayman bai gane bane yasa Zaleeha ce mishi.
"Ayman kaje can pom-pom kayi al'wala kazo kuje masallaci.
ai kuwa da gudu yaje yayi al'wala kana ya kama hannunshi suka tafi masallacin.


Su kuwa suka shiga sukayi salla kana suka ɗanyi hira kafin isha'ayi tayi sukayi salla kafin suka zauna cin abinci sunaci suna hira.


Saifuddeen kuwa da Ahmad da Hayatuddeen da Ayman kai tsaye falon Ummi suka shiga nan suka samu Ameena ma ta dawo,
nan sukaci abinci,
kana suka dawo cikin falo suna hira suna nan a zaune,
Ya Ameenu ya shaidawa Saifuddeen ya iso,
Ahmad ne yaje ya mishi jagora,
ya shigo suka gaisa da Ummi kana ya fita tare da Saifuddeen da Ayman.
cikin kula Saifuddeen yace.
"To Ya Ameenu har yanzu fushin akeyi da mune baza'a shiga ba?".
Murmushi mai kama da Dariya yayi kana a hankali yace.
"No ba fushi bane saurine".
Kai ya gyaɗa kana yace to bari inje in kirawo ta,
dariya ya ɗanyi kana yace.
"Nama kirata a waya".
Dai-dai lokacin kuma suka iso wurin, a hankali Zaleeha tace.
"Ya Ameenu ina wuni?".
Cikin ɗan sakin fuska yace.
"Lfy, ya jiki?".
"Alhamdulillah jiki da sauƙi".
Ta bashi amsa.
har sun shiga mota sai kuma Ziyada tace.
"Ab ya Ameenu nayi mantuwa tsaya".
Cikin kulawa yace.
"To na tsaya Saleeha".
fita tayi cikin sanyi tace.
"Adda Zaleeha ya Ameenu yace in gaya miki, kije ki ɗauki saƙon da Adda Maryam ta bar wasiyar ta bar miki, to tunda nazo na manta sai yanzu na tuna".
Cikin sauri tace.
"To Ziyada in sha Allah zanje".
sai ta kuma kalli Hamma Saif a hankali tace.
"Hamma Saif zaka kaini ko?".
Kai ya gyaɗa mata alamar eh.
Ganin haka Ziyada ta shiga mota suka tafi, su kuma suka koma cikin gida.




Bayan kwana biyar da zuwan Ziyada,
Zaleeha ta tambayi Saifuddeen batun zuwa gidan Adda Maryam ɗauko saƙon da ta bar mata,
sai yace ta bari ranar yanada hidima duk randa yake free zai kaita.


A ranar ne kuma komai na shirin tafiyarsu Istanbul ya kammala, saura kwana uku zasu tafi,
ita harma ta mance da batun E Passport da akayi mata.


Da safe bayan duk sun gama cin abincin,
kasancewar ranar Ameena zata karɓi girkin, kuma su da safe, zaka amshi miji ba sai yamma ko dare ba so daga anyi breakfast mai karɓan girki ita ke dashi, shiyasa yanzu girkin Ameena ce,
sai ya nufi side ɗin ta, a falon tama ya konta bisa 3 str Yana danne-danne a system ɗin shi.


Ita kuwa Zaleeha falonshi ta leƙa ganin baya nanne ta dawo falonta ta tura mishi text.
"Salam Hamma Saif ka fitane?".
Yana ganin saƙon yace mata.
"A a. Ina nan kina buƙatan wani abune?".


"To ina kake nazo falonka baka ciki, na leƙa bedroom ma baka ciki".


"Ina falon Ummu Adeel, kizo".


Jin haka yasa ta miƙe ta ƙofar falonshi tabi,
gefenshi ta zauna,
tana zama yasa hannunshi kan cinyarta a hankali ya cusa hannun cikin rigarta ɗan tudun cikinta ya fara shafawa a hankali hankali.
cikin sanyi tace.
"Hamma Saif dama batun zuwa gidan Ya Ameenu ne nace bari in tuna maka tunda yau weekend ne baka da fita, ko zaka kaini."
Kai ya ɗan rausayar kana ya rubuta mata.
"Sai gobe, zamuje, gidan Baba malam yayi mana addu'an ALLAH ya raya inƙanta mana babynmu ya kuma fito mana dashi lfy daga nan sai muje gidan Ya Ameenu ɗin".
Cikin jin daɗi tace.
"To Allah ya kaimu".
Daga nan ta miƙe ta fita.




Washe gari, bayan anyi sallan la'asar, wanda ya kama kuma gobene zasu tafi Istanbul,
kusan a tare suka shiga falon Ummi cikin shiga ta,
al'farma sunyi kyau dasu,
bayan sun sallami Umminshi ne,
suka fita suka tafi.
Kai tsaye, makey suka nufa.
Suna shiga taga ya fara tsintan abubuwan da kamar su turamen zannuwa Getzner turaruka,
sabulai da dai sauransu,
saida suka gama kuma ta sashin suka shiga sashin kayayyakin taɓa ka lashe.
Sai kuma taga yana shiga layin kayayyakin sanyi masu ɗan karen kyau riguna masu kyau na sanyi irin na mutanen ƙasashen da ake musu ruwan dusar ƙanƙara.
saida ya zaɓi masu kyau kusan kala biyar biyar na maza dana mata.
Daga nan sukaje wurin biya aka ya biya,
aka zuba kayan a ledodi uku.
Atampopi da yadin mazan da turaruka a leda ɗaya.
Kayan kwalamace kuma leda ɗaya kana sai kayan sanyin suma a lede ɗaya,
Yana gaba tana binshi a baya, sunzo dab ƙofar fita, tayi maza tayi baya ido ta zubawa matar da tani a gefenta,
Tabbas bazata mance matarnan ba cikin nitsuwa tace.
"Sanunki".
Da sauri matar ta juyo tare da cewa.
"Yauwa sannu".
Saifuddeen kuwa a bakin baranɗar ya tsaya daya juyo yaga tana ciki bata fitoba kuma da alama mgna takeyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login