Showing 183001 words to 186000 words out of 239422 words

Chapter 62 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11902

gane zahirin zance yafi gane yaren faɗa, cikin haɗe fuska tace.
"Koma ka zauna, Hayatuddeen, wato abun da kake aikatawa kenan ko?, kai atunaninka cewa idanunmu ba akan ka su ba ne, hmmm najima ina zarginka da aikata rashin gaskiya da kuma abun da bai dace ba Hayatuddeen, musamman ma ga yanda bakaso ko wayarka aɗauka, wato shine wannan rayuwar daka zaɓawa kanka Hayatuddeen kana ganin me kyauce? ko irin tarbiyan dana baka kenan?."
Hawayene suka cika idanunsa, sosai jikinsa yayi sanyi, ahankali yaɗan shiga girgiza mata kai alaman "A'a." cikin muryan kuka yace.
"Dan Allah kiyi haƙuri Ummi, wallahi bazan sake ba, kuma hakan ba halina bane, bansan me ya ruɗeni ba Ummi, bansan meyasa nake aikata haka ba, bayan kuma nasan da cewa babu kyau, nasan nabiyewa sharrin zuciya da kuma na aboki, amma bazan ƙara ba, wallahi dama Khamis ne ya koya min, kuma nayi miki rantsuwa Ummi, Wallahi ko hannun mace ban taɓa riƙewa ba, tsoro nakeji Ummi, idan keda Hamma kukayi fushi dani, wallahi rayuwata watsewa zatayi, bazan iya jure fushinku ba Ummi, dan Allah kuyi haƙuri."
Fashewa yayi da wani irin kuka, mai ɗauke da zallan nadama haɗi da danasani.
Kai kawai Ummi ta girgiza cikin sanyi tace. "Bansan yaushe kazama haka ba Hayatuddeen, a iya sanina dakai babu ruwanka da duk irin waƴannan abubuwan na banza, saboda ban koyar daku hakan ba, nasan giyar samartaka ne ke ɗibanka daga kai har Khamis ɗin, kunajin cewa kuma kun tasa, kun fara zama samari, shiyasa kuke ƙoƙarin gurɓata rayuwarku amaimakon gyarata, bahaka na tarbiyantar dakai ba, wannan ɗabi'ar kuma ba irin ta cikin gidan nan bane, na lura kuma barinka da waya da mukayi ne, duk ya jawo hakan insha Allah kuma, daga yau kadaina riƙe babbar waya har abadan kenan, domin da mummunar rawa gwamma ƙin tashi." kuka ya sake fashewa dashi, har acikin ransa yayi danasani da kuma nadama.
Ganin yanda yake kuka sosai ne, yasa Ummi kwantar da murya, cikin nutsuwa ta shigayi masa nasiha mai ratsa jiki, tana gamawa kuwa Ahmad da Saifuddeen harma da Raleeya suka ɗaura nasu, sosai jikinsa yayi, sanyi haka ya dinga sakin sheshsheƙan kuka, tare dayi musu rantsuwa kan cewar bazai sake ba. Nan dai sukayi masa faɗa sosai. Ummi ne ta fara tashi ta wuce ɗakinta, saboda akwai abun da zatayi aciki, Saifuddeen ne nabiyun tashi, saida safe yayiwa su Ahmad sannan ya fice daga cikin falon.
Hayatuddeen kuwa cikin falon ya koma, ya zauna tare da kunna tv, tashar MBC Action ya kamo, inda ya samu suna haska film ɗin MULAN, sanin cewa yaga tallen film ɗin a net, ya sashi maida hankalinsa ga tv'n yana kallo duk hankalinshi na kan tv.
Ganin haka ne yasa Ahmad sanya hannu ya jawo Raleeya jikinsa, ɗan shagwaɓe masa tayi, akasalance tace.
"Nifa Allah ko Habibi jikina ciwo yake." Murmushi yayi, tare da sanya hannu ya shafi kyakkyawar fuskarta, harshensa yasanya inda yaɗan lashi lips ɗinta, cikin mayen sonta yace. "Muje maza namiki maganin gajiya my kyakkyawar matata." Yana gama faɗan haka, ya ɗagata sama, ƙoƙarin zillewa take amma yaƙi bata daman hakan, haka suka haura sama, yana ɗauke da ita kaman ƴar ƙaramar baby. Hayatuddeen kuwa baisan ma me sukeyi ba, dan gaba ɗaya hankalinsa naga tv. Acan part ɗin Zaleeha kuwa fitowarta daga wanka kenan, towel ta sanya inda taɗan goge ruwan dake jikinta, wani fitinannen body lotion mai ƙamshin gaske ta shafa ajikinta, tare da bin kowani lungu da saƙo na jikinta da daddaɗan turare.
Wata irin fitinanniyar sleep gown ta sanya ajikinta, wanda gaba ɗayanta net ne, sannan an ƙawata gabanta da wasu igiyoyi, sosai rigar tayi mata kyau, yayinda kuma ta bayyana komai na jikinta, gaba ɗaya shape ɗin jikinta a bayyane yake, kasancewar rigar nada breast cup hakan yasa, bata sa brezia ba, wanda hakan yasa shatin pink nipples ɗinta suka bayyana acikin rigar. Wani perfumed ta fesa lungu da saƙo na jikinta tare da yin parking dogon gashinta, atsakiyan kanta.
Tayi kyau sosai,
A hankali ts hayewa saman gado, tare da jawo laptop ɗinta, wayarta ta shiga ɗan duddubawa, tunowa cewar ta manta shi a falon Ummi yasa taɗan dafe goshinta tare da cewa.
"Mitsee wlh na gaji". tsai kuma ta tashi tare da zaro wani ƙaton hijab daga cikin drawer'nta, sanya hijab ɗin tayi, tare da zura wani bedroom slipper aƙafanta, har zata fita kuma sai idanunta suka sauƙa akan sweet ɗin da ta ciro acikin firij wanda har sun zama dutsen ƙanƙara, guda uku ta ɗauka sweet ɗin masu ƙamshin strowberry, ɗaya ta ɓarewa ta jefa a bakinta, kana ta riƙe biyu a hannunta tanajin sanyi su na ratsata, niyarta inma ta shanye ɗayan kafin ta dawo ga biyu a hannu, handle din ƙofar ta murɗa sannan ta fice daga cikin ɗakin, kaitsaye sashin Ummi ta nufa.


Da sallama abakinta ta shiga falon, Hayatuddeen dake zaune ne ya amsa mata, ƙarasowa cikin falon tayi, tare da dubansa cikin kulawa tace.
"Auta har yanzu bakayi bacci ba."
Kansa ya jinjina mata, tare da cewa.
"Wani latest film nake kallo Adda Zaleeha, yayi kyau sosai."
Murmushi tayi, tare da ƙarasawa kan kujeran da ta zauna ɗazu, tana ɗage pillown dake jikin kujeran kuwa, taga wayarta, ɗaukan wayar tayi, dai-dai lokacin Ummi ta fito daga cikin ɗaki. Ganin Zaleeha yasa tace. "Ikon Allah Zaleeha dama baki shiga bane." Ɗan murmushi tayi tare da cewa.
"A'a Ummi na shiga, harma na kwantama saina tuna nabar wayata shine na dawo na ɗauka." Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Ai kuwa naji daɗin dawowanki, dama yanzu Hamman ku ya turo min text wai Hayatuddeen ya kai masa coffee, tunda gaki ai shikenan, shiga kitchine ki haɗa masa saiki kai masa ko." Kanta taɗan sunkuyar cikin yanayi na ɗan jin kunya tace.
"To Ummi." kitchine ta wuce, inda Ummi kuma ta zauna anan falon. haɗaɗɗen coffee ta haɗa masa, wanda lokaci ɗaya ya cika falon da ƙamshi, fitowa tayi daga kitchine ɗin, hannunta ɗauke da ɗan tray wanda samansa ke ɗauke da ɗan ƙaramin flask da kuma cup, saida safe tayiwa su Ummin, sannan ta fice daga cikin ɗakin. Koda ta doshi sashin nasa, hakanan taji ƙirjinta na bugawa, wani irin fargaba ta samu kanta aciki, ɗan dakewa tayi tare da murɗa handle ɗin kofar falon nasa ta shiga.
Komai dake cikin falon nead, babu abun dake tashi sai ƙamshi, da kuma wani irin fitinannen sanyin ac mai ratsa sassan jiki da zuciya, ɗan Adam lumshe idanunta tayi, ahankali take ƙarewa falon nasa kallo, komai na cikinsa me kyau da burgewa ne, musamman royal chairs din da suka matuƙar burgeta, ɗan waige-waige ta somayi, ganin baya cikin falon yasa taɗan turo ƙaramin bakinta gaba, ashagwaɓe tace.
"To kuma ina yake?." ƙoƙarin aje tray ɗin dake hannunta tayi, wani tunani dayazo ranta ne, yasa ta juya tare da nufar ƙofar bedroom ɗinsa, sanin cewar idan ta ajiye masa coffee ɗin afalo, balallaine ya gani ba, maybe kuma yasake ƙiran Ummi yace akawo masa coffee, bata so kuma Ummi tayi zaton bata kai mishiba ne. ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga, bakinta ɗauke da sallama, daddaɗan ƙamshin airfreshener ne ya daki hancinta da wani shegen sanyin ac daya ninka na falo, cikin ranta tace.
"Na shiga uku wannan sanyin baya damunshi ne, haba shiyasa ko matarsa mutun ya shiga sai kaji sanyi har cikin ƴaƴan hanjinka, Allah sarki Sule shi kam har ya saba,
da makaken gadonsa ta fara arba, ɗan zaro idanunta waje tayi, abayyane tace.
"Wow, wannan wani irin gado ne?".
Tsayawa tayi tana me ƙarewa ɗakin nasa kallo, cikin ranta tace.
"Chab aljannar duniya kenan mutun komanshi kamar na ɗawisu".
ɗan takowa tayi a hankali ta ƙaraso jikin gadon nasa, ahankali tasanya hannu taɗan shafa saman gadon, wanda design ɗinsa yayi matuƙar kyau.
Sam ta shagala cewar coffee ta kawo masa, hasali ma kuma rashin ganinsa aɗakin baida meta ba sai dai tanajin sanyi sweet ɗinta dake cikin tafin hannunta.


Ahankali ya buɗe ƙofar toilet ɗin yafito, sanye yake da white bathrobe, yayinda gaba ɗaya jikinsa ke ɗauke da danshin ruwa, da dukkan alama wanka yayi, ɗan tsayawa yayi, yana kallon ta fuskarsa cike da mamakin ganinta acikin ɗakinsa a ransa yace.
"Uhum yarinya kin kawo kanki".
Ita kuwa Zaleeha jin kaman motsin mutum abayanta, yasa tayi saurin juyowa, idanunsu ne suka sarƙe acikin na juna, da sauri taɗan ja da baya, tare da turo bakinta gaba, idanunsa ya ƙura mata, tare dayi mata alama kan in boddy language cewa.
"Wayace kishigo min ɗakinna?."
sake turo baki gaba tayi, ashagwaɓe tace.
"To ni ba Ummi bace, tace na kawo maka coffee."
tsumammun idanunsa yaɗan lumshe, tare da sakin wani irin killer smile, ahankali yaɗan soma turo kekensa zuwa gareta, ganin haka yasa da sauri ta ajiye tray ɗin, tare da juyawa ta nufi hanyar barin ɗaƙin, cikin azama ya rigata ƙarasawa bakin ƙofar ɗakin ganin guduwa takeda niyar yi, hannu ta ɗaura akan handle din ƙofar, dai-dai lokacin shikuwa ya sanya hannunsa ya kare ƙofar, ta yanda bazata iya buɗewa ba.
Idanu taɗan zaro waje cikin mamaki tace.
"To miye haka, nidai ka matsamin nafita, ai dama coffee akace na kawo maka, to kuma baga can coffee ɗin na ajiye maka ba."
tafaɗi maganar tana kakkarya ƴan yatsun hannunta tare da sunkuyar da kanta. Rikitattun idanunsa ya watsa mata, wanda har saida taji, tsikar jikinta sun mimmiƙe.
Ɗan rolling idanunsa yayi, tare dayi mata alaman cewa.
"Ai tunda kika shigo ba zaki fita ba."
Idanunta ta zaro, tare da ɗan murguɗa masa ƙaramin bakinta, asakalce tace.
"Dan Allah nidai kabarni na fita kaji."
ɗan karyar da wuyansa yayi, tare da girgiza mata kai, alaman yaƙi ɗin.
Hannunsa yasa inda ya murzawa ƙofar key, tare da zare key ɗin yasa a aljihunsa, ganin haka yasa ta kwaɓe fuska, take idanunta sukayi rau-rau dasu.
Ɗan janye jikinsa baya yayi, tare da ƙarasawa gaban dressing mirror ɗinsa, cikin nutsuwa ya ɗauko body lotion ɗinsa yana shafawa. Idanu ta zuba masa, sai faman tattaune lips dinta take, zuciyarta kuwa duka yake da ƙarfi, ganin cewa yama manta da ita, hidimansa kawai yakeyi, yasa ta ƙaraso har gabansa, ahankali ta shiga ɗan bubbuga ƙafanta, asakalce tace. "Dan Allah ni dai kabuɗemin ƙofa na fita, bacci nakeji."
Ɗago idanunsa yayi ya kalleta, tare dayi mata nuni da gadonsa alaman ga gado nan ta kwanta. Fari tayi da idanunta, tare da cewa.
"Nidai bazan kwanta akan wannan gadon ba, ai nima ina da nawa, nidai ka buɗemin naje na kwanta a ɗakina."
Murmushin gefen baki yayi, tare da mata alamar.
"Ai ni ba'a shiga ɗakina, a fita ba'a kwanaba, haka kuma ɗakina yanada dokoki".
Cikin sanyin murya tace.
"Ni dai ɗakina zan koma in kwana".
A ranshi yace.
"Eye yanzu dai kin yarda nan gidanki ne wato harda wani a ɗakinki zaki kwana, to saura in tabbatar miki ni mijinki ne kuma nan ɗakin mijinkine.
Ba tare daya kulataba, ya ƙarasa gaban drawer ɗinsa, wani 3quater mai taushi ya ciro, ganin yana shirin zare bathrobe ɗin jikinsa agabanta ne, yasa tayi saurin kawar da kanta gefe tare da rumtse idanunta. Shikuwa babu wani ɗar ya cire bathrobe ɗin, tare da zura tattausan wondon ɗin ajikinsa. Body spray ɗinsa ya fesa, sannan ya ƙara gudun AC'n ɗakin,
Wayarshi dake kan mirror ya ɗauka, juyowa yayi ya kalleta, da sauri ta janye idonta dan ganin yadda ya haɗe mata fuska, rubutu yayi a wayarshi kana ya miƙa mata, ba musu ta karɓa ta fara karanta abinda ya rubuta mata.
"Ki shiga bathroom kije kiyi al'wala kizo, dan ni ba'a kwana ɗakina saida al'wala".
Miƙa mishi wayar tayi cikin sanyi tace.
"Inada al'wala, sweet kawai nasha".
alama ya mata taje ta kurkure bakinta to.
tura baki tayi da niyar zatayi mgna sai kuma tayi shiru ganin ya ɗaga mata hannun kana ya mata nuni da hanyar bathroom ɗin nashi.
Sumai-sumai ta wuce jiki a mace,
koda ta shiga tsayuwa tayi tana kallon tsari da zubin bayan gidan nashi, cikin sanyi tace.
"Son kai komai nashi yafi namu kyau".
Ta ƙarishe mgnar tare da kurkure bakinta kana ta juya ta fito.
Ido ta ɗan zuba mishi ganinshi sanye da wani farin jallabiya kana yana bisa sallaya ga kuma wani sallayan a gefenshi,
kai ta jujjuya ganin yana nuna mata kan sallayan,
cikin mmki tace.
"Ai ni nayi sallan isha'a na tun ɗazu kuma nayi shafa'i da wittirinama".
Fuska ya tsuke babu alamar wasa ya miƙa mata wayarshi daya rubuta mata.
"Na sani ai, ko ce miki akayi ni ɗin banyi sallan isha'a ɗin bane? Kizo Nafila zamuyi, in roƙa miki Allah ya shiryeki ya rabaki da guje-guje nan da kokenki na tsoro dan karki sake guduwa da kuka".
Wani irin bugawa taji ƙirjinta yayi dan ta fara tsinkewa da manufarsa, cikin sanyi da ɗan tsoro tace.
"Ɗan guntun rigar bacci a jikina fa".
Kai ya gyaɗa mata tare da mata alamun ai hijabin jikinta ƙatone mai kauri kuma gashi har ƙasa".
Babu damar wani musu dole ta matso gefenshi a hankali ta ajiye sweet ɗinta gefen kulan dake kan bedside sannan ta dai-dai-ta tsayuwar ta kan sallayar,
shi ya limanceta sukayi nafila raka'a biyu.
Koda suka idar juyowa yayi ya fuskanceta hannunshi ya ɗaura bisa kanta ya kama goshinta cikin ransa yayi addu'o'in kana, ya saketa,
haka nan taji jikinta yana rawa kar-kar, shiyasa tana jin ya saketa ta yunƙura zata miƙe,
da sauri ya kamo hannunta ya maida ita ta zauna gab dashi,
cikin yin rau-rau da ido tace.
"bacci nakeji".
Bai kulata ba, sai hannunshi yasa ya sauƙo da wannan kular, da Adda Rahma ta sa mishi gasasshiyar zabuwar nan, ya ajiye kulan a gabanta, sannan ya buɗe ɗan madaidaicin firijin dake gefenshi, goran madarar nan ya fitar ya ajiye gabanta,
Zuwa yanzu lamarinshi ya fara sata shakku,
wani irin ƙamshine taji ya ziyarci ƙofofin hancinta sanda ya buɗe kular, a fakaice ta kalli dangwaleliyar zabuwar da tasha gashin tukunya mai ɗan karen kyan gani da daɗin ɗanɗano, to Zaleeha dai dama uwar kwalamace, bata san cewa kazar ci inciki bane, kazar bashi kanaci kaima ɗin za'a tsotseka,
tura mata kular yayi gabanta tare da mata alaman taci.
Kai ta ɗan jujjuya duk da yawunta da taji ya tsinke, cikin rauni tace.
"Na ƙoshi".
Kici-kici yayi da fuska cikin bada umarni ya mata alamu.
"Maza taci, shi ba'a kwana ɗakinshi da yunwa".
Sosai yayi mata kwarjini, kana ta kuma tuno al'khairin da taiwa Baba Malam na cewa zatabi umarninsh,a hankali tasa hannu ta ɗan yagi kaɗan daga jikin ƙunɗun zabuwar dai-dai irin farin tsokar nan tibis taji tsokar sai nason mai da takeyi,
ido ya zuba mata ganin bata kai hannunta bakinta ba,
hannunshin yasa ya kamo natan ya ɗagashi ya kai matashi kan bakinta,
kana ya mata alamu da idonshi cewa ta buɗe bakinta,
Rau-rau tayi da idonta kana a hankali ta buɗe bakinta tasa tsokar namar,
wani irin tsinkewa yawunta yayi sabida yadda ɗanɗanon naman zabuwar ya ratsa mata jijiyoyin bakinta, a hankali ta fara sarrafa naman,
shi kuwa Hamma Saif sake kamo hannunta yayi ya maidashi cikin kularar, kana ta kuma yago gutsuren naman, still ya kuma kai mata hannun bakinta,
haka yai ta mata saida ta cinye rabin tsokar ƙungun, kana ya barta sabida taƙi sake yarda ta buɗe bakinta tunda tace mishi ta ƙoshi.
Rufe kular yayi kana ya tureshi gefe,
goran madarar ya buɗe wacce tayi sanyi kalau, rabinshi yasha, sannan ya kai mata bakin goran bakinta,
tana buƙatan abu mai ruwa-ruwa tunda taci maiƙo shiyasa ba musu ta buɗe baki ta.
Tasha mai ɗan yawa dan taji garɗin madarar da zuma sai ya tuna mata zamanta a numan.
janye kanta tayi tare da yin gyatsa cikin sanyi tace.
"Na ƙoshi, zanyi bacci".
Rolling idonshi yayi tare da nuna mata hanyan bayan gida alamun taje ta wonke hannunta, dan shi bai taɓaba ko loma ɗaya.
A hankali ta miƙe ta nufi bayan gidan da wonko hannun nata.


Shi kuwa Hamma Saif ninke sallayoyin yayi ya ajiyesu wurin zamansu, kana ya ɓare sweet ɗin nan mai ɗan karen ƙamshi ya afashi a bakinshi, kana yaje gaban mirror ya kuma fesa turare sannan ya nufo jikin gadonshi da yafi kamanni da gadajen sarauta ko kuma na indiyawa dai-dai lokacin kuma ta fito daga bayan gidan.


Ƙarasawa kan gadon yayi, ya kwanta kana ahankali ya lumshe idanunsa.
Ganin haka yasa ta tako a hankali ta iso gefenshi baki ta tura tare da cewa.
"Ni dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login