Showing 135001 words to 138000 words out of 239422 words

Chapter 46 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11906

Ahmad, sai ya zaro masa wata maganar kuma.
Ɗan jingina bayansa yayi da jikin wheelchair'n ɗinsa, tare da ɗan juyowa ya kalli gadon nasa,
cute smile yayi, cikin zuciyarsa yace. "Wannan gadon ayanzu bashi da amfani agareni, saboda Ameena taci amarcinta akai son ranta, yanzu kuma lokacin Zaleeha yayi, saboda haka dole nakawo sabin furnitures kodan saboda Zaleeha, dan kamar yanda take sabuwa, haka ma dole gadona yakasance sabo bazan haɗa mata komi sauran ta'annabina ba."
wani murmushi ya sake yi, wanda shi kaɗai yasan ma'anarsa da kuma abunda yake nufi. Ahankali ya tura wheelchair ɗinsa ya fice daga cikin ɗakin, kaitsaye part ɗin Ummi ya wuce.
A falo ya sameta zaune ita da Raleeya, ƙarasowa cikin falon yayi, ganin haka yasa Raleeya tashi taje ta kawo masa kunun aya me sanyi, wanda ɗazu Zaleeha ta haɗa. Babu musu ya amsa kuwa yasha, tun aɗanɗanon farko yasan cewa ba Raleeya bace tayi, haka yaji kunun yayi masa daɗi, har baisan sanda yasha fiye da rabin ƙofin ba.
Ɗan ɗagowa yayi ya dubi Ummi, cikin body language ɗinsa yake faɗa mata cewar, zai sanja bedroom furnitures ɗinsa.
Da mamaki Ummi tace. "Zaka sanja kayan ɗaki kuma Saifuddeen, me ya samu waƴan can ɗin, da kake ƙoƙarin sanjasu ka kawo wasu?". Murmushi ya ɗanyi cikin body language ɗinsa yace.
"Ummi basuyi komai ba, kawai dai naga furnitures ɗin Goggo Dada duk sun tsufa ne, shiyasa nakeso idan aka kawomin sabi sai akai mata waƴancan ɗin." Murmushi Ummi tayi tare da jinjina kai, cikin kulawa da jin daɗi tace.
"Masha Allah, to Allah ya ƙara arziki, ai kuwa kam gaskiya Goggo Dada taci sabin furnitures, gaskiya ka kyauta."
da "Ameen" ya amsa, sannan ya ce da ita
"Zai dan fita wajen aiki." "Adawo lafiya." Ummi da Raleeya sukayi masa, sannan ya juya yafita daga falon, bayan ya shanye gaba ɗaya kunun ayan da Raleeya ta zubo masa cikin kofi.

Cikin ikon Allah da yamma kuwa sai gashi ankawo furnitures ɗin, wanda kyawunsu ya zarta gaba ɗaya kayan ƴan gidan, wasu irin haɗɗaɗɗun white furnitures ne masu kyau da tsadar gaske, saboda tsabar haɗuwansu haka akayi design ɗinsu kaman na sarauta. Ma'aikatan companyn da kansu suka shirya masa kayan bayan suncire tsofin furnitures ɗin.
Gadon da aka sanya masa, irin gadon nan ne da ake ƙira aljannar duniya.
Makeken gadone me ɗauke da tambarin MEGO luxury furnitures, wanda aka ƙawata kwalliyan jikinsa, da white and golden colour, yayinda samansa kuwa aka ɗanyi masa wani abu kaman rumfa, wanda yasha decoration mai masifar kyau, shikansa gadon kaɗai abun kallone, domin ya isa tafiya da hankalin mutum, gefe dashi kuwa, wasu haɗaɗɗun bedside ne wanda samansu ke ɗauke da mirror gold, sunyi kyau har sun gaji, idan aka matsa daga gefen dama kuwa, wani irin haɗaɗɗen drawer ne mai girma da tsari, kusan duka murafensa mirrors ne amma me zubin gold, ga kuma design na royal da akayi ajikinsa, yayi masifar kyau da burgewa.
Daga gefen hagu kuwa, wani dan ƙareren dressing mirror ne wanda shima aka tsara masa zane me kyau na royal, wanda suke shige da zubin gold, daga gefen mirrorn kuwa wani ɗan ƙaramin drawer ne, irin wanda ake aje takardu ciki, asaman sa anyi masa wani design na gold me masifar kyau da burgewa, har wani ɗan flower green aka sanya aciki. Sosai kayan furnitures ɗin sukayi kyau, sun kuma dace da ɗakin nasa ƙwarai, Ummi ita kanta da ta shigo ta matuƙar yabawa da kayan, gashi sun zauna aɗakin sunyi ɗas, saikace fadar shugaban ƙasa, saidai kuma kallo ɗaya zakaiwa kayan kasan sunja million's of Naira, dan kayane masu kyaun gaskene. Haka dai aka kwashi furnitures ɗin daya cire din, aka wuce dashi Dukku gidan Goggo Dada.

Koda ya dawo daga wajen aikin nasa kuwa sashin Ummi ya wuce. Anan ne Ummi take sake tambayar sa kan cewa. "Har yanzu baiga key ɗin ɗakin Zaleehan ba?" wani irin murmushi yayi tare da jinjina mata kai alaman.
"Eh." Idanu Ummi ta zuba masa, aɓoye itama tasaki murmushi, cikin ranta tace.
"Hmm dama ni ai najima da sanin cewa akwai abun da kake ƙoƙarin shiryawa, ajuri zuwa rafi dai wata rana dai tulu saiya fashe." Hira suka ɗan taɓa kaɗan a falon Ummi kafun daga bisani ya tashi ya tafi ɓangarensa, shikansa ya yaba sosai da kyawun furnitures ɗin daya saya ɗin, wanka yayi sannan ya nufi ɗakin Ameena, dan yasa aransa cewar bazai sake barinta taje ɗakinsa ba, shi zaike binta ɗalibta , har sai randa ya amshe budurcin Zaleeha bisa gadon kenan, saboda kwata kwata shi bai sayi wannan gadon saboda ita ba ya sayane dan cin amarci in ya amshe m'budurcin in yaso suci gaba da zuwa turakanshi.
Ameena kuwa koda ta gansa aɗakinta tayi mamaki ƙwarai, amma sanin cewa bayason yawan tambaye tambaye yasa taja bakinta tayi gum, sai hakan ma ya zame mata kamar abun farinciki, dan yaune rana ta farko daya biyota ɗakinta shiyasa hakan yayi masifar mata daɗi.

Washe gari.
kamar yanda ta faɗa jiya, yau awajen Zaleeha tabar Adeel, bayan ta aje madara da duk kuma wani abun daya kamata da za'a bashi.
Sosai Zaleeha taji daɗin barin Adeel ɗin awajenta, haka ta saɓasa akafaɗanta tanayi masa wasa, cikin ikon Allah kuwa ko kuka baiyi ba. Da rana ne kuwa Hayatuddeen yaje ya kwaso su Zakariyya, Isma'il, Imran, Sulaiman, Zaleeha taji daɗin zuwansu ƙwarai, nan falon Ummi suka baje, haka suka kafe kai da fata wai dole ita zata shiga kitchine tayi musu ferfesu, acewarsu wajenta suka zo ba wajen Ummi ko Adda Raleeya ba, haka dole ta sauƙe Adeel ta shiga kitchine ɗin, cikin ƴan mintuna ƙalilan kuwa ta dafa musu indomie, da kuma ferfesun naman kaji, nan tsakiyan falon suka zauna su kaci, gaba ɗaya surutunsu ya cika gidan, haka sukayi wa Ummi kaca-kaca da falo. Sunjima sosai agidan dan sai wajen bayan sallan la'asar kafun suka tafi.

Ameena kuwa yau ƙarfe 5 ta dawo, koda ta dawo kuwa bata karɓi Adeel ba, yana nan awajen Zaleeha, saima da akayi sallan magriba ne ta karɓeshi ta bashi nono.


*Bayan Kwana ɗaya*


Sannu ahankali haka rayuwa ta cigaba da tafiya, inda acikin kwanaki biyun nan kullum sai Ameena tabarwa Zaleeha Adeel, awajenta yake wuni harta dawo daga wajen aiki. Hakanne yasanya shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakanin Adeel ɗin da kuma Zaleeha tana jin yaron har cikin ranta.

Saifuddeen ne zaune kan wheelchair ɗinsa, wayarsa ya jawo sannan ya turawa Raleeya, text akan taƙira Hayatuddeen suzo tare yana son ganinsu, kasancewar yau Hayatuddeen ɗin baida lecture'n safe shiyasa baije school ba.
Suna shigowa cikin part ɗin nasa ya miƙowa Hayatuddeen key tare da cewa.
"Karɓi key ɗin part ɗin Zaleeha ne."
cikin yanayin zumuɗi Hayatuddeen yace. "Nakai mata." Hararansa Saifuddeen ɗin yayi, cikin body language ɗinsa yace. "To sarkin azarɓaɓi bahaka nakeson cewa ba."
Ɗan zumɓura baki Hayatuddeen ɗin yayi, cikin shagwaɓa yace.
"To me za ayi dashi."
Duban Raleeya Saifuddeen ɗin yayi, cikin body language ɗinsa yayi mata alaman cewa.
"Su shiga ɓangaren Zaleehan, suɗanyi share share."
Murmushi Raleeyan tayi, har acikin ranta taji daɗi, saboda hakan alama ne dake nuna cewa Zaleehan ta kusa dawowa ɓangarenta, jan hannun Hayatuddeen tayi suka wuce sashin Zaleehan, shikuwa Saifuddeen laptop ɗinsa ya ɗauka ya cigaba da aikinsa.
Raleeya da Hayatuddeen kuwa suna shiga sashin Zaleehan, suka soma ƴan share share da goge goge, kafun awa biyu tuni sun tsab tace ko ina sun gyara komai, haka falon yadawo sabo fil sai sheƙi yake, inda suka fesa turaren air feshener,
suna tsaka da aikin ne Ahmad ya ƙira Raleeya dan tun ɗazu ya dawo baiganta ba, ya kuma sauƙo har ƙasa bai ganta ba.
Nan take sanar masa cewa tana ɓangaren Zaleeha Hamma Saifuddeen yaɗan sasu suyi mata share-share da gyare-gyare.
Ƙwafa Ahmad yayi tare da cewa.
"Lalle ma Saifuddeen so yake ya maidamin da mata baiwa ko? yarasa wazai sa yayiwa Zaleehan share-share sai ke, zanyi maganinsa ne badai yayi mata biyu ba yaseen zamu ƙaura." Dariya Raleeya tayi sannan ta kashe wayan, nan dai suka kammala komai suka fice daga sashin.


Washe gari ne Goggo Dada taturowa Saifuddeen saƙon godiya, da kuma fatan al'khairi kala-kala, dan sosai taji daɗin kyautar nasa.
Nan yake ce mata. "Bakomai, Goggo Dada ai kema uwace agareni kuma uba".
ananne ma yake ce mata.
"Lafiya ko batazo tayi ta'aziyyan rasuwar Adda Maryam ba".
cewa tayi.
"Itama tana tason zuwa to amma Allah ne baiyi ba."
take kuwa yace washe gari zai turo sule driver ya ɗaukota, haka dai tayi ta masa godiya, daga nan sukayi sallama . Murmushi yayi bayan ya aje wayar, cikin zuciyarsa yace.
"Awannan karon Goggo Dada dake zanyi amfani wajen dawo da Zaleeha ɗakinta, tun alokacin da Ummi ta bini akan na bada key ɗin ɗakinta ban nemeshiba, yanzu kuwa dana ga key ɗin bani da wani ƙarfin guiwan da zan iya tunkaran Ummi nace mata ga key ɗin ɗakin Zaleeha, amma yanzu tunda dai zakizo nasan lokacin dawowan Zaleeha ɗakinta yayi, zanyi komai asauƙaƙe tayanda Ummi bazata zargeni ba."
Haka dai yayita saƙawa da kuncewa, sosai ƙudurinsa ke ƙara ƙarfafa acikin zuciyarsa.
Kaman yanda ya faɗa kuwa washe gari yasa Sule driver yaje har Dukku ya ɗauko Goggo Dada'n, Raleeya ne ta rakata gidan su Zaleehan tayi musu ta'azziyya, daga nan kuma suka dawo gida.


Yauma kamar kullum Zaleehan ne tayi musu girkin abincin dare, kusan atare sukaci abincin, koda suka kammala cin abincin, nan cikin falon ta koma ta zauna akan sofa tare da tanƙwashe ƙafafunta, sama sama take ɗan kallon tv, ahaka taɗan jingina kanta da jikin kujeran falon, bacci takeji sosai, saidai sanin cewa Goggo Dada na cikin ɗakin nata yasa bata shiga ta kwanta ba, saboda kallon suruka takewa Goggo Dada'n.


Ɗan sake jingina bayanta da jikin kujeran falon tayi, tare da lumshe idanunta, ta kuma sake riƙe Adeel dake jikinta ƙam, bacci takeji tare da gajiya, amma sam tanajin bazata iya shiga ɗakin nata ba, saboda Goggo Dada dake ciki, kunyanta takeji, musamman ma da takeson kafun ta kwanta tayi wanka. Hayatuddeen ne ya lura da yanda Zaleehan keta lumshe idanunta, alaman bacci.
Hannu yasa ya ɗan taɓa kafanta cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha bacci kikeji, kije ki kwanta mana."
ɗan buɗe idanunta tayi, tare da sakin sassanyar murmushi. Raleeya dake jinsu ne taɗan ɗago kai, tare da duban Hayatuddeen ɗin tace.
"Ai tun ɗazu Goggo Dada na ɗakin." Ɗan marairaice fuska Hayatuddeen yayi yace. "To Adda Zaleeha ki tashi ki hau saman kujera mana."
Ummi da fitowarta daga ɗaki kenan, duk taji abun da suka faɗa, duban Raleeya tayi, cikin kulawa tace.
"Raleeya tashi kije kicewa Goggo Dada ta dawo nan ɗakina mu zauna tare, duk ai zai ishe mu, abu ba yaro ba ba komai ba." "To" Raleeya tafaɗa tana me miƙewa tsaye. Saifuddeen da tun shigowar Ummin yake kallon yanayin yanda bakinta ke motsi, hakan yasa shi danna madannanin wheelchair ɗinsa ya nufi hanyar fita daga falon, dama tuntuni wannan damar yake jira shiyasa koda suka kammala dinner bai tafi ba.
Kai tsaye ɓangarensa ya nufa, yana shiga kuwa ya zaro wayarsa, text ya turawa Hayatuddeen akan cewar "Yazo yana son ganinsa." Hayatuddeen na zaune yaga saƙon Hamman nasa, tsam ya miƙe ya fice daga cikin falon, kai tsaye sashin Hamman nasa ya nufa.
Anan falo ya iske Saifuddeen ɗin, yana shan Maltina, ƙarasowa cikin falon yayi tare da cewa.
"Hamma gani." Kai ya jinjina tare da sanya hannunsa acikin al'jihun rigarsa ya zaro key, miƙawa Hayatuddeen key ɗin yayi, nan cikin body language ɗinsa yace. "Ka kaiwa Zaleeha, ta dawo ɗakinta tabarwa Goggo Dada wannan ɗakin."
Yanayin yanda yayi maganan yana wani basarwa, shine abun daya sanya Hayatuddeen yaji wani irin dariya ta kamasa, amma sai ya share, da murna ya karɓi key ɗin, tare da cewa.
"To zan kai mata." juyarda akalan kekensa yayi ya nufi bedroom, Hayatuddeen kuwa binsa yayi da kallo yana murmushi, yana ganin ya shige ɗakin, yayi ɗan tsalle tare da cewa. "Yess yanzu itama Adda Zaleeha zata koma ɗakinta."
juyawa yayi cikin sauri ya fita daga falon. Anan falon Ummi kuwa har yanzu suna nan a zazzaune, gefe kuwa ga Ameena da zuciyarta keta raya mata abubuwa iri iri.
Da murna Hayatuddeen ya shigo cikin falon, yana ɗan rawa, harda su shaku shaku, baki Ummi dasu Raleeya suka buɗe suna kallonsa, da mamaki Ummi tace.
"Kai Hayatuddeen lafiyanka kuwa?." Murmushi mai ɗauke da dariya yayi, tare da miƙowa Raleeya hannu, cikin jin daɗi yace.
"Adda Raleeya maza maza taso muyi rakiya ."
Hannunsa ya miƙa ya karɓi Adeel dake kan cinyar Zaleehan, ɗaga Adeel ɗin yayi sama tare da cewa.
"Adeel kaima kayi murna yau Amminka ta zama zata bar mana side ɗin Umminmu ta koma can ɗakinta."
Ya faɗi maganar yana me cilla Adeel ɗin sama. Jin abunda Hayatuddeen ɗin ke faɗa yasa Ummi sakin murmushi tare dayin ƙwafa, dama ai ita ta jima dagane shirin Saifuddeen ɗin, kuma zatayi maganinsa ne. Ameena kuwa kalaman Hayatuddeen ɗinne suka zuciyarta tsananta bugawa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login