Showing 141001 words to 144000 words out of 239422 words
Chapter 48 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
kishinta, ya kasa ɓuya akan fuskarta.
Ganin irin kallon da takeyi masa ne, ya sashi ƙura mata ido cike da ɗan mamaki, dan zallan ɓacin rai da kuma kishi yake gani acikin ƙwayan idanunta.
Ahankali yaɗan turo wheelchair ɗinsa kusa da ita, tare da ɗan kai hannunsa zai taɓa ta, afusace ta ɗaga masa hannu, cikin wutar kishin dake cinta tace.
"Da Allah Karka taɓa ni banaso, kaje kawai, ka koma can inda ka fito, kaje can ka taɓa ta, tunda dama haka kakeso kuma ka zaɓa."
taƙare maganar tana ne sake ƙara sautin kukanta, wanda yake ɗauke da tsananin takaici da kuma azababben kishi. Shiru yayi cike da mamaki ya zuba mata kyawawan idanunsa, sosai yake nazartar ta, wuta-wuta haka yake ganin kishi acikin ƙwayan idanunta, ɓoyayyan ajiyar zuciya ya sauƙe, batare da tunanin komai ba, ya sake ɗan tura wheelchair ɗinta ya nufo gareta, asonsa shine ya ɗan kwantar mata da hankali sannan ya kuma rarrasheta.
Ganin haka yasa cikin matsanancin kishi tace. "Nace maka kada ka taɓani,sannan kuma kada ka matso kusa dani, kafita min aɗakina kawai, dama yarona ne ka kawomin saboda haka, kafitamin daga ɗaki, kaje can inda idan ka shiga kake jimawa, ka koma ka cigaba da jimawan ka!" Tafaɗi haka cikin kishin da ya rufe mata ido, har acikin ranta ƙuna takeji, kishin Saifuddeen din da kuma haushin Zaleeha da takeji suna neman tarwatsa mata zuciya ta mancema yau ranar Zaleeha ne sai takeji kamar girkinta ya kaimata abin kuwa baya rasa nasaba ne da saba ita kaɗai gareshi duk da tasan yanada wata matar amman yanzu sai takega kamar ita yayiwa kishiya.
Ganin yanda gaba ɗaya idanunta suka rufe yasa shi girgiza kansa, tabbas yasan ayanzu idanunta sun rufe, bazata taɓa fahimtar komai ba, juyawa yayi cikin nutsuwa ya fice daga cikin ɗakin, ko waiwayenta baisake yi ba.
Ganin ya fitane yasa ta fashewa da sabon kuka, tare da faɗawa saman gadon, hakanan takejin kaman tayi ta kurma ihu ko zataji sauƙin abun dake zuciyarta, ya zatayi da kishin Saifuddeen dake damunta? ina zata kai baƙincikin abun da takeji, akullum akuma koda yaushe, akullum zata ga Zaleeha saita ji duk ta raina kanta.
Saifuddeen kuwa kaitsaye ɗakinsa ya wuce.
Yana shiga ɗaga kai yayi ya kalli agogo, ganin ƙarfe 12:10 am na dare ne, ya sashi ɗan zaro idanunsa, dan ya shiga ɗakin Zaleehan ne tun 11, amma sai 12 yake fitowa kwata kwata baisan ya ɗauki lokaci acikin ɗakin har haka ba. Ahankali ya ƙarasa tare da rage hasken wutan ɗakin, kan haɗaɗɗen makeken gadonsa ya kwanta, kana ya jawo blanket ya rufa ajikinsa, wata irin sassanyar ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da ɗan lumshe idanunsa, sosai yake mamakin mood ɗin da yaga Ameena aciki, sam bai taɓa ɗaukan cewa zafin kishinta har yakai haka ba, har yanzu yana mamaki, dan kwata kwata baiga dalilin da zaisa ta ɗau zafin kishi ta sanya aranta ba, aganinsa bai kamata ma tayi kishi da Zaleeha ba, dan idan da zata lura, Zaleehan ba wani damuwa tayi dashi ba, ko bayan haka ma bata nuna kishi akansa, amma ya lura gaba ɗaya tunda Zaleeha ta dawo gidan Ameena ta tashi hankalinta, Allah ma ya san zuciyarsa, shi adalci kawai yake son ya kamanta atsakaninsu bashi da niyar tauye haƙƙin kowa a cikinsu, domin ko wacce da matsayin ta a ranshi da zuciyarshi da rayuwarshi. Ɗan sake lumshe idanunsa yayi ahankali moment ɗinsu da Zaleehan ya dawo masa, lokaci guda yaji wani irin kasala ya saukar masa, take yaji tsikar jikinsa na zubawa, ga kuma wani irin fitinannen feeling dake neman hautsuna mai tunani, tunowa da taushin breast ɗinta dayaji a tafin hannunsa shi yasa yaji gaba ɗaya jijiyoyin jikinsa na miƙewa, harshensa yasa ya ɗan lashi kyawawan laɓɓansa, acikin ransa yace.
"Uhumm komai nata me kyau ne, yanayinta, fushinta, kukanta, tsoronta, dama duk wani yanayin da take ciki kyau yake mata."
tunowa da irin yanda take ta ƙif ƙifta idanu, yasa shi sakin wani killer smile, cikin zuciyarsa yace.
"baki kam akwaishi cakwai-cakwai amma sai shegen tsoro, kamar farar ƙura."
sake gyara kwanciyarsa yayi, tare da kai hannu ya ɗan dafe saman mararsa, da kuma manhood ɗinsa dake ta faman harbawa, tunanin Zaleeha kaɗai ya birkita masa lissafi, gefe guda kuwa ga kyawawan saman breast ɗinta, dake ta faman yi masa gizo acikin idanunsa, wanda yasa yaji yayi weak.
Ɓangaren Zaleeha kuwa Saifuddeen ɗin na fita, ta sake hayewa can saman gado ta takure, tare da matse jikinta waje ɗaya, sosai wani irin tsoro ya shigeta, musamman ma akan abunda yayi mata yanzun, tuna abunne yasa taji gaba ɗaya tsikar jikinta na tashi, tana jin wani iri ajikinta, blanket ta ja ta rufe jikinta, tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, cikin sakalci haɗi da zallan shagwaɓa, kaman yana gabanta tace. "Allah saiya sakamin, wai har zai gyaramin wuyan rigana, saikace shiya sakamin rigar ko ance masa ni ƴarin yace da sai an gyara min rigata". Tafaɗi maganar tana me sake naɗewa acikin bargon nata, zuciyarta cike take da fargaban kada ya kuma dawowa, gashi bata da key ɗin ɗakin balle ta rufe, ahaka dai atakure bacci me nauyi ya ɗauketa. Ɓangaren Ameena kuwa kuka tayi sosai, duk kuwa yanda taso bacci ya ɗauketa abun yaci tura, dan zuciyarta tafasa take, baƙin ciki da kishi sun hanata sakat, ga kuma wani sabon ƙuncin rai da tasamu kanta aciki, musamman ma da ta tuna da irin jimawar da Saifuddeen ɗin yayi anan ɗakin Zaleehan, tasan cewa yana ɗakin Zaleehan ne, saboda taƙira Hayatuddeen ne kan cewar ya kawo mata Adeel, sai yake shaida mata cewa Adeel ɗin na wajen Zaleeha, kuma Saifuddeen ya tafi zai ɗaukoshi, wannan abun shiya sanya taji ta tsani komai, take wani irin zargi ya ɗarsu acikin ranta, zuciyarta ce keta raya mata abubuwa, musamman akan jimawan da Saifuddeen ɗin yayi aɗakin Zaleeha, gashi wani ƙarin haushin, shine kwaso ƙamshin jikin Zaleehan da yayi ya kawo mata ɗakinta. Haka ta dinga juyi tana ta sambatun baƙin ciki da kishi duk akan Zaleeha, da ga ƙarshe ma ganin bacci bazai ɗauketa ba, saboda fitinannen kishin dake damunta yasa ta tashi ta zauna, sake saka sabon kuka tayi, saikace kamun aljanu can kuma ta miƙe taje tayi al'wala tazo taita nafilfili tana addu'o'in Allah ya sassauta mata zafin kishinta kuma Alhamdulillah ta ɗanji sanyi.
Washegari.
Ƙiran sallan asuban farko ne ya sauƙa acikin kunnuwanta, azabure ta ɗan farka, tana me kakkame jikinta, dan dama baccin nata atsorace tayi shi, ahankali ta zuro da kyawawan ƙafafunta ƙasa, bayan tayi addu'an tashi daga bacci, kaitsaye toilet ta wuce, ruwan zafi ta haɗa tayi wanka, tare da ɗauro alwala, koda ta fito wani jan jallabiya mai kyau na mata ta sanya ajikinta, sosai tigan tayi mata kyau dan tana ɗaya daga cikin na aurenta, kasancewar rigar ƙiran tukish ne yasa aka ƙawata jikinta da wani irin haɗaɗɗen ado, harma da hula akayi mata, duk da cewar rigar bata bayyana shape ɗin jikinta ba, amma ta yi mata kyau sosai, hijab ta sanya sannan ta tada sallah, saida tayi raka'atanul fajir, sannan tayi sallan asuban, koda ta idar Azkar tayi sannan taɗan taɓa karatun Alƙur'ani.
Tana kai karshe kuwa miƙewa tayi, wani ɗan ƙaramin vail ta yane kanta dashi, sannan ta fesa turarenta me dadin ƙamshi, wayarta ta ɗauka, sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin, cikin nutsuwa ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fice. Kanta tsaye sashin Ummi ta nufa, bakowa afalon, hakan yasa ta nufi ɗakin Ummi kaitsaye, tana knocking kuwa aka bata izinin shigowa, murɗa handle ɗin ƙofar tayi ta shiga, anan kan sallaya ta samu Ummi najan carbi, durƙusawa tayi ta gaisheta cikin girmamawa, fuska asake Ummi ta amsa, mata. Bata wani jima aɗakin Ummin ba, ta miƙe tsaye, kaitsaye ɗakin Goggo Dada ta shiga, nan ta iske goggo dadan itama najan carbi, cikin girmamawa ta gaishe da goggo dada'n, haka goggo Dada ta amsa mata cikin kulawa da sakin fuska.
Koda ta fito daga ɗakin goggo dadan, anan falo suka haɗu da Raleeya, bayan sun gaisane, suka nufi kitchine saboda ɗaura breakfast, Raleeya ne me fere dankali, ita kuwa Zaleeha ferfesu take haɗawa, sai kuma sandwich, aikin suke cikin nutsuwa suna ɗan taɓa hiransu. Koda Ummi ta fito falo, ganinsu a kitchine suna aiki,yasa tayi murmushi, nan kan kujera ta zauna, tare da maida hankalinta ga TV inda take kallon Sunnah tv. Saifuddeen kuwa tunda ya tashi da asuba ya wuce masallaci bai dawo ba sai yanzu, tafe suke Hayatuddeen na riƙe masa saman kekensa, sai zuba yake yana basa labarai kala-kala, ahaka suka ƙaraso falon Ummin.
Ummi naganinsu haka ta saki murmushi, har acikin ranta tana godewa Allah daya haɗa mata kan ƴaƴanta, kana yasanya musu soyayyar juna azuƙatansu, wannan haɗin kan nasu shine matakin nasaran rayuwarta.
Ƙarasowa gabanta Saifuddeen yayi, cikin body language ɗinsa ya gaisheta, amsa masa tayi tana murmushi. Hayatuddeen ne yazo ya zauna akusa da ita, cikin kulawa ya kamo hannunta yace.
"Ummi kinsan me?" dubansa Ummi tayi da kyau, dan duk atunaninta serious magana ce, cikin nutsuwa tace.
"A'a saika faɗa." pink ɗin laɓɓansa wanda suke shige dana Hammansa ya lashe, tare da cewa.
"Wallahi Ummi ƙamshin girki nakeji tun fa kam mushigo cikin falon nan, tun da ga gate, to ni narasa a ina ƙamshin yake fitowa."
ya kare maganar yana ɗan kallon ƙofar kitchine. Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Ehem aikin kenan, to su Raliya ne suke dafa break fast."
Murmushi yayi tare da suɗe bakinsa, dan dama yunwa yakeji.
Dai-dai lokacin kuwa Zaleeha ta fito daga kitchine din hannunta ɗauke da food flask, lumshe kyawawan idanunsa da suka sauƙa akanta yayi, sosai tayi masa kyau cikin jan rigar saikace wata sarauniya, Raleeya ne ta fito da sauran kayan abincin da suka girka, nan suka shiga jerawa akan dinning table. Ameena ce ta shigo cikin falon, Adeel rungume akan kafaɗanta. Sanye take da uniform ɗinta na aiki tayi kyau sosai cikin shigar nasu.
Ƙarasowa cikin falon tayi, tare da durƙusawa ta gaida Ummi.
Cikin kulawa Ummi ta amsa, tare da tsare Ameenan da ido, cikin kulawa hankalinta a tashe, tace. "Subahanallahi Ameena me ya samu idanunki haka naga sunyi ja?". Ɗan sadda kai ƙasa Ameenan tayi, murya aɗan sanyaye tace. "Babu komai Ummi, kawai dai mura ne keta damuna jiya kusan kwana nayi banyi bacci ba, saboda tari da atishawa."
Kai Ummi ta girgiza cikin tausayawa haɗi da kulawa tace.
"Allah sarki, sannu kinsha magani kuwa?" Kaita jinjina alaman "Eh" Hayatuddeen ne yace. "Ayya Aunty Ameena sannu ko."
Ɗan murmushi tayi masa tare da jinjina kanta, Saifuddeen kuwa idanu ya zuba mata, yana me mamakin ƙaryar da ta zabga, yanayin yanda yaga fuskarta yasa shi gane cewa kwana tayi batayi bacci ba, shikam yarasa irin kishin Ameena, dan kishine da takeyinsa babu wani dalili. Zaleeha dake tsaye nan kan dinning area, jin cewar Ameenan bata da lafiya ne yasata ɗan ɗago kanta, cikin sakin fuska tace.
"Ummu'n Adeel barka da safiya, ya jikin?" Jin muryan Zaleehan yasa ta ɗago dakai ta kalli inda taji muryar Zaleehan na fitowa, wani irin bugawa kirjinta yayi, take taji wani irin masifaffen kishi ya sake rufeta, musamman ma ganin yanda Zaleehan tayi kyau cikin doguwar rigan jikinta, haushi da takaicin Zaleehan ne suka turnuƙe mata zuciya, gudun kada su Ummi su zargi wani abu, yasa ta ɗan danne zuciyarta, murmushin yaƙe, wanda yafi kuka ciwo ta saki, can ƙasan maƙoshi tace.
"Yauwa barka, jiki Alhmdlh."
Kai Zaleeha ta jinjina cikin sanyin da ta dawo ɗabi'arta tace.
"Masha Allah, Allah Yaƙara sauƙi."
Kasa amsa mata tayi, dan kuwa wani abune yazo yayi mata tsaye acikin rai, jin muryar Zaleehan acikin kunnuwanta yasa taji kaman ta kurma ihu, ƙasa-ƙasa ta watsawa Zaleehan harara, cikin zuciyarta tace.
"Shegen iyayi, koma menene ai duk sanadinki nasamu kaina ahaka, wallahi da ace ina da yanda zanyi Saifuddeen ya daina ganinki acikin gidan nan da nayi, lokacin da bakyanan ai hankali akwance yake, yanzu kuma da dawowarki da shegen farar fuska kaman mayya duk kin wargaza min nitsuwa ta."
Ta ƙare maganar tana me sakarwa Zaleehan harara ƙasa-ƙasa, Zaleehan, ko zataji sanyi aranta.
Ummi kuwa ganin su Zaleehan sun gama shirya break fast ɗinne yasa tace.
"Dukansu su tashi suje suci abinci." Anan kan dinning suka zauna, yauma kamar kullum Zaleeha ne tayi seving ɗinsu, inda take komai nata acikin nutsuwa. Saifuddeen kuwa gaba ɗaya yau yakasa ɗauke idanunsa akan matan nasa Zaleeha'n, tayi matuƙar kyau, ga fresh skin ɗinta dake ta shinning,
Ameena kuwa tausayinta yakeji da yanada hali da ya yaye mata wannan kishin ta huta, ahankali yake tauna abincin bakinsa, yana wani irin lumshe ido, sosai yakejin daɗin abincin Zaleeha'n, dan zai iya cewa agidan bayan Umminsa babu wanda yakai Zaleeha iya girki duk da yasan Ameena ma ba tayar bayaba bace. Ameena kuwa gaba ɗaya ko daɗin abincin ma bataji abakinta, cuccusawa kawai take, komai bayayi mata daɗi, saboda zafin kishin da ta sawa kanta, ɗan ɗagowa tayi ta kalli gefen Saifuddeen, dan tun da suka zauna bata ɗago kai ta kalleshi ba, kasancewar har yanzu fushi take dashi. Ganin yanda yake sakin murmushi da kuma yanda ya ke kallon Zaleeha wanda take tauna abincin bakinta cikin nutsuwa, yasa taji gaba ɗaya ranta ya ɓaci, wani irin maƙaƙi ne ya zo maƙoshinta, hakan yasa batasan lokacin da ta ƙware ba, take kuwa tasoma tari, kumburarrun idanunta suka kaɗa sukayi ja.
Hankalin Ummi a tashe tace. "Subahanallahi Ameena tarin ne?".
Kai ta jinjina alaman "Eh." tana me riƙe ƙirjinta dake mata zafi. Saifuddeen kuwa hannunsa yasa yana ɗan bubbuga bayanta cikin kulawa.
Zaleeha da Raleeya kuwa atare suka haɗa baki wajen cewa. "Sannu."
kasa amsa musu tayi saboda matsanancin kishi da kuma ɓacin ran dake cinta, Hayatuddeen cikin kulawa yace.
"Ayya Aunty Ameena sannu, kisha ruwa kinji." Yafaɗi maganar yana me miƙo mata goran ruwan faro me sanyi. Babu musu ta amsa tasha, saida tasha sosai kafun take kifa kanta ajikin dinning ɗin tana meda numfashi. Ahankali Saifuddeen ya aje spoon ɗin dake hannunsa, tare da ɗanjan kujeransa baya, ƙoƙarin barin dinning area ɗin yake, Ummi tace.
"Inakuma zaka ana tsaka dacin abinci?" Ɗan shagwaɓe fuska yayi, tare da sanya hannu ya shafi lafaffen cikinsa alaman