Showing 30001 words to 33000 words out of 239422 words
Chapter 11 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
yanayi na tsokana Raihana ta dubeta, tare da cewa.
"Kikulamin da Hammana da kyau da kyau, dan ko ƙuda bama son ya taɓa manashi."
Dariya sukayi gaba ɗayansu,
itakuwa Zaleeha ɗan guntun murmushi tayi, yayinda taji wani malolon abu ya tokare maƙoshinta, cikin zuciyarta tace.
"Lallai kuwa zai mutu, indai nice zan kula dashi!.
Yo ni me haɗina dashi kunamai ma su sauƙa ajikinsa mana ba ƙuda ba ni me yadameni."
Motar su Raihana baigama fita daga gidan ba saiga Dr.Adnan nan shima yazo ɗaukar matarsa, nanfa suka gaisa, inda Zaleeha tagaishesa cikin mutuntawa, Farouq da Adam kuwa sai tsalle suke dan sunga babansu, duk girmansu baigani ba haka yasasu ajikinsa, babu yanda basuyi ba akan cewa Daddy yazo su tafi ba amma yaƙi, waishi ala dole yasamu sabuwar Aunty yace shi Dukkunma bazai komaba, kusan saida yabawa kowa dariya haka suka tafi anata raha.
Daddy kuwa da ƙyar suka iyayi masa wayo yabi iyayen nasa da karatunshi, Ahmad ne yazo da motarsa wanda dama shine zai mayar dasu Goggo Dada gida, lokaci ɗaya fa gaba ɗaya jama'an baƙin biki suka watse gida yayi shiru.
Ummi Raliya da kuma Zaleehan kawai aka bari, dama Saifuddeen yana part ɗin Ummi, kasancewar shi baifito rakiyan ba, shikuwa Hayatudden sarkin bacci, yanacan tun dawowansa daga sallan asuba daya koma bacci shine haryanzun baitashi ba.
Direct Zaleeha part ɗinta ta koma, inda su Ummi da Raliya suka koma wajen Saifuddeen.
Tana shiga cikin ɗakin nata ta cire hijabin dake jikinta, kan gado ta faɗa tare da ɗan lumshe idanunta, sosai takejin wani sabon bacci naƙoƙarin ɗaukarta.
Can ɓangaren Ummi kuwa, Saifuddeen naganin dawowansu, ya sakawa Ummin nasa shagwaɓa, sanin halinsa na sakalci kaman wani ƙaramin yaro yasanya Ummi da kanta tashiga kitchine inda ta haɗa masa coffee, sosai yaji daɗin haɗin coffee ɗin da Ummin tayi masa, ɗaukan mug ɗin yayi tare da bar musu falon, kai tsaye yanufi sashinsu.
Saifuddeen nafita, Ummi tayi murmushi cikin jin daɗi tace.
"Allah kenan maiyin yadda yaso a lokacin da yaso, kafun auren nan kowa yasan cewa yarinyar nan bason auren nan take ba, amma yanzu cikin ƙuduran Allah gashi suna zaune lafiya, kinga ta saki ranta."
Murmushin gefen baki Raliya tayi tare daɗan muskutowa, cikin jimamin abun dake damun zuciyarta tun daren jiya tace.
"Hmmmm hakane kam Ummi, amma nikuwa jiya naga abun daya ɗauremin kai ya bani mmki, dan nima da fari da naga ta saki ranta naji daɗi."
Dubanta Ummi tayi tare da cewa.
"Mene kuma yafaru?."
Gyara zama Raliya tayi tare da cewa.
"Ummi kinsan kuwa cewa jiya awaje cikin garden ta kwana? wallahi Ummi abun yabani mamaki sosai, inata tunanin dalilin da zaisa ta kwana cikin garden, idan har zatana gudunsa haka, meyasa ta amince da aurensa?."
Cikin matsananci mamakin jin maganan da Raliyan ta faɗa Ummi ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya, jiki amace tace.
"Raliya kin tabbatar da abun da kike faɗa kuwa?."
Kai Raliya tajinjina tare da cewa.
"Wallahi Ummi da idanuna naganta jiya a garden ta kwana, kuma koda natashi sallan asuba dana leƙa naganta, alokacin tana ƙoƙarin barin wajen, kuma tabbas nasan babu makawa itace dan Abban Farida ma ya ganta dayazo tafiya masallaci."
Ɗan jim Ummi tayi tare dajinjina kanta, take taji zuciyarta tayi mata wani irin ba daɗi, hankali ya tashi fargaba ya cika mata zuciya wato har ƙiyayyar ta kai haka, jiki a mace tace.
"To Allah dai ya kyauta."
Amin Amin Raliya ta amsa jiki a mace.
Haka dai zaman yaci gaba da gudana har tsawon kwanaki, Kullum in gari ya waye Zaleeha na idar da salla zataje ta gaida Ummi a mutunce, lokuta da dam takan samu Saifuddeen a wurin Ummi, amman tsakaninta dashi sai harara da murguɗa baki,
tana son kowa na gidan yayinda suma duk suke matuƙar sonta musamman Raliya da takanje har ɗakin Zaleeha su ɗanyi hira,
dan itacema ta tayata shirya tarin akwatunan kayan aurenta da kimtsa mata duk abinda zata buƙata a durowa, sauran akwatunan suka kaisu ɗaya ɗakin,
Hayatuddeen kuwa dama akwai sabo a tsakaninta haushinta da yaji kan cewa da tayi bata son Hammanshi yanzu babushi tunda yanaga har ta yarda da auren ta zauna lafiya dashi.
tana matuƙar girmama Ummi wanda hakan yasama mata soyayya a idanunsu,
tana mutunta Ahmad a cewanta mai sunan yayanta ne dan Yaya ma take kiranshi tun tana gaidashi yana amsawa a yatsine har dai ya fara ɗan sasaautawa.
Har yau kuma a woje take kwana cikin gardin,
wannan abun shine yasa Ahmad yake matuƙar jin baƙin cikinta,
shi kuwa Saifuddeen da fari baisan bata kwana a ɗakintaba dan baya shiga kuma da safe yana ganinta a wurin Umminshi,
To tun shekaran jiya daya dare ya ankara da bata ɗakin, ya dudduba ko ina na cikin part ɗin nata babu ita ba dalilinta, falonshi ya koma wayarshi ya ɗauka tare da yin mgnar zuciya,
"To ina take zuwa ta kwana yau kwana biyu kenan bata kwana a nan."
Kanshi ya ɗan jingina da jikin kujerarsa tare daci gaba da mgnar zuci.
"To waya sanima ko ta daɗe da barin kwana a nan."
sai kuma yayi ajiyan zuciya tare da cewa.
"ko dai part ɗin Ummi take kwana? kai Anya kuwa Ummi zata barta ta kwana a side ɗinta,
to ko dai part ɗin Raliya take kwana."
Text ya rubutawa Ahmad,
"Kayi bacci ne?."
Ahmad da ke zaune a falo shida Raliyya suna mgnar Zaleeha dan hango wucewarta da sukayi,
murya a sanyaye Raliya tace.
"To wai ko dai Hamma Saifuddeen bai san bata kwana a ɗakinba?."
Ajiyan zuciya Ahmad ya sauƙe tare da cewa,
"Ina zaton bai saniba, kinfa san shi da miskilanci, in kuwa yasan bata kwana a cikin to yasan inda take kwanan shiyasa bai kulataba ai jiki magayi."
da sauri ya ɗago wayarshi ganin saƙon Saifuddeen ne ya sashi cewa.
"To ina ga dai bai san bata kwana cikiba sai yanzu dan ga text ɗinshi wai nayi bacci ne."
ido Raliya ta zuba fuskar wayarshi tana ganin amsar da yake rubuta mishi.
"A a banyi bacci ba, lfy dai ko?."
jim kaɗan sai ga wani saƙon.
"To lafiya dai zance,amman Zaleeha na wurinku ne?."
murmushi Ahmad yayi tare da cewa Raliya,
"Hmmm zanyi mgnin yarinyar nan."
sai kuma ya rubuta mishi amsa.
"A a Zaleeha kuwa, bata nan."
a take sai ga wani saƙon.
"Kasa Raliya ta dudduba nan wurinku, taje Side ɗin Ummi ma ta duba ko tana can."
yana gama karan tawa yace.
"Lafiya dai kam ko?."
tsaki Saifuddeen ya ɗan ja kana ya rubuta mishi,
"Nima ban saniba lafiya ko ba lfy ba, ina dai zargin yarinyar bata kwana a gidan nan, dan tun shekaran jiya na lura babu motsinta, sannan yanzu na dudduba ko ina bata ciki side ɗin."
cikin nuna fargaba Ahmad yace.
"Innalillahi, to ina take zuwa ta kwana, gani nan fitowa."
sai ya kuma miƙe ya kalli Raliya tare da cewa,
"Maza kije side ɗin Ummi ki gaya mata, ana neman Zaleeha ki kuma ce karta nuna tasan inda take kwana zanyi mgninta."
to tace tare da juyawa ta nufi side ɗin Ummi,
kana shi kuma Ahmad ya nufi ƙofar falon Zaleehan nan yayi kicibis da Saifuddeen daya fito,
"To wai ina ta shigane, mufa mun dudduba wurinmu babu ita."
kai ya jujjuya mishi alamun shimafa ya dudduba wurinsu babu ita.
dai-dai lokacin kuma Ummi da Raliya suka iso, nan fa suka haɗu suka nuna basu san inda takeba.
ita kuwa Zaleeha tun fitowan su Ahmad ta buɗe ido,
jin ita ake nema yasa ta zame a hankali ta konta a ƙasan kujerar fulawi ke zagaye da ita.
Ahmad kuwa yana hangota hakan ya sashi cewa.
"Hmmmm zaki gane kurenki."
wayarshi ya zaro lallatsata yayi ya nemo number Ya Aminu,
ya kirashi kana ya kara wayar a kunnenshi.
Can cikin bacci Ya Ameenu yaji wayarshi nata suwa,
a hankali ya ɗan zare Maryam daga jikinshi,
hannu yasa ya ɗauki wayar time ya duba ƙarfe ɗaya na dare.
"Ahmad kuma a daren nan lfy kuwa?."
sosai yaji fargaba ,kar dai Zaleeha nacan na tarfa musu rashin ɗa'a, jiki na rawa ya amsa kiran cikin sauri yace.
"Salamu alaikum ,Ahmad lfy kuwa?."
cikin nuna tashin hankali yace.
"Ya Ameenu Zaleeha ce bamu ganiba mun nemata ko ina a gidan babu ita ba dalilinta,
kuma Saifuddeen yace tun shekaran jiya bata kwana a side ɗinsu,
to sai yayi tunanin wai ko side ɗinmu take shigowa ta ɓuya ko na Ummi,
to shine yanzu ya sanarmana zatonsho tana wurinmu,mun duba kab gidan bata, nan shine nace bari in kiraka ko ta dawo gidane?."
cikin kaɗuwa Ya Ameenu ya miƙe tare da cewa.
"Zaleehan to ina take zuwa?."
a taƙaice Ahmad yace.
"To ko tana gida ne?." rai a ɓace Ameenu yace.
"Kai anya kuwa sam bata gida, to ina take zuwa ta kwana, yi haƙuri bari in kira Baba malam."
to Ahmad yace kana ya katse kiran sannan ya gaya.musu yadda sukayi da Yayanta Ameenu,
kana yace su shiga ciki kafin Ameenun ya kirashi.
Shi kuwa Ya Ameenu wani irin tashin hankali ne da ɓacin raine mai tsanani ya rufeshi to ina Zaleeha take zuwa ta kwana ina take tafiya ta bar ɗakin mijinta me haka yake nufi?
kiran Baba Malam yayi bawan Allah yana zaune bisa sallaya yana karatun qur'an kiran Ameenu ya shigo wayarshi,
har wayar ta katse bai ɗaukaba duk da yaga Aminune so yake yaje ƙarshen surar Arrahaman da yake karantawa,
yayinda wani fargaba ya rufeshi lfy kuwa kira da tsakiyar daren nan.
Yana zuwa ƙarshen surar kira na uku na shiga wayar, da hamzari ya amsa kiran,
"Barka da dare Baba Malam kayi haƙuri na tada kai daga bacci."
Ameenu ya faɗa a ladabce,
murya a ɗan harɗe Baba Malam yace.
"Ameenu lfy kuwa meke faruwa?."
cikin sanyi Ya Ameenu yayi mishi bayanin da Ahmaɗ yayi mishi, ya ƙara da cewa.
"Ko dai ta taho gida ne?."
lumshe ido Baba Malam yayi yana jin wani irin suya da zuciyarshi keyi me Zaleeha ke nufi zubda mishi mutunci da kima a idanun mutane ko?
a hankali ya cewa Ameenu.
"Ameenu bana zaton tana cikin gidana ,bazata zo nanba, amman dai bari in bincika."
to Aminun yace kana y katse kiran.
shi kuwa Baba Malam fitowa yayi da kanshi yayi tabin luggu da saƙo na gidan ya duba ko ina kab babu ita, koda ya titse Mama da tambayar ina Zaleeha ke zuwa ta kwana,
rantse-rantse tayi ta mishi akan ita bata san ina Zaleeha ke zuwa ta kwanaba.
a daren Ameenu ya kira goggonsu Maryama da duk inda suke zaton zataje ko ina sai ace musu bata zoba.
Wannan abu yayi matuƙar tada hankalin Baba Malam ya Ameenu kuwa ji yake in yaga Zaleeha zai kusan karta,
dole ya kira Ahmad yace,
wlh bata wurinsu amman tunda da safe tana dawowa zai zo ya sameta, har ɗakinta.
Da wannan kowa ya koma ɗakinshi, Ahmad kuwa ranshi ƙal yasan Zaleeha zata gane kurenta.
Washe gari kamar yadda ta saba, suna tafiya masallaci ta koma ɗakinta wonka tayi da ruwan ɗumi wai ko tsamin cizon sauro da jikinta keyi zai ragu, wanka da al'wala tayi,
kana ta fito tazo tayi salla koda ta idar azkar tayi sanan ta miƙe ta kimtsa jikinta cikin wata doguwar rigar mai ɗan karen.kyau wanda duk na kayan aurene, da mayafinshi ta yane kanta ,kana ta nufi sashin Ummi.
a falo ta samesu, dukansu, cikin nitsuwa ta isa gaban Ummi dake mata murmushi tare da cewa.
"Gari ya waye ko ɗiyata?."
murmushi tayi tare da rusunawa gaban Ummi cikin ladabi da sanyin lafazi tace.
"Ummi Ina kwana?."
cikin kula Ummi tace.
"Lafiya lau ya baƙunta?."
kai a sunkuye tace,
"Alhamdulillahi."
"Masha Allah." cewar Ummi kenan
Hayatuddeen ne ya gaidata ta amsa fuska a sake, kana ta kalli,
Ahmad dake zaune kusa da Saifuddeen bisa alamu lissafi sukeyi,
cikin sanyin sauti tace.
"Yaya ina kwana?."
a taƙaice yace.
"Lafiya lau." daga nan kuma sai ta miƙe tare da cewa Ummi .
"Raliya na kitchen ko?."
cikin jin daɗi Ummi tace.
"A a tana sashinta yau wai kanta ke ciwo."
a hankali tace,
"Ayyah ban saniba Allah ya bata lfy."
Amin Amin Ummi tace,
Kana sai ta ɗan rusuno tare da cewa,
"To Ummi bari in shiga kitchen, me zan haɗa mana breakfast?."
sosai Ummi take jin daɗin yadda take sakewa da Raliya su shiga kitchen tare, gashi yanzu har tana shiga ita ɗaya ma tayi musu girki.
cikin kula Ummi tace.
"Bari inzo mushiga tare to."
da sauri tace .
"A a Ummi ki bari zan iya ki huta."
sai kuma ta kalli Hayatuddeen daketa murmushi tace,
"Zo muje kitchen ka tayani hira."
da sauri ya miƙe yabi bayanta, yana cewa.
"Yauwa muje ki min dege-dege."
da ido Ummi ta bisu har suka shiga kitchen ɗin.
koda suka ƙarasa cikin kitchine ɗin, hayewa kan wata kujera Hayatuddeen yayi ya zauna, wayarsa ya fiddo daga aljihunsa tare da soma latsawa, ita kuwa Zaleeha, direct wajen fridge ta nufa, buɗe cikin firjin dake shaƙe da kayayyakin abinci tayi, nan ta zaɓo manya manyan kaji guda biyu, sake wankesu tayi sannan ta ɗaura akan wuta tare dasa kayayyakin ƙamshi dana danɗano.
nan ta ɗibo irish patatoe tasoma ƙoƙarin ferewa, Hayatuddeen ne ya taso tare da soma taya ta, haka suka cigaba da firan, yana ta zuba mata surutu, mayafin dake jikinta ta ajiye, tare da soma yin aikinta cikin nutsuwa, yayinda Hayatuddeen gaba ɗaya ya sakota gaba da surutunsa, cikin abun da bai wuce awa ɗaya da rabi ba, ta kammala haɗa barbecued chicken da kuma patotoe balls, sai kuma bread Pizza, wanda gaba ɗaya ƙamshinsa ya cika kitchine ɗin, Hayatuddeen dake zaune agefe sai haɗiye miyau yake, dan har ya tsara irin cin da zaiyiwa bread pizza ɗin, da ƙamshinsa ya cika masa hanci, spearmint tea ta haɗa, sannan ta juyesa acikin flask, nan ta kimtsa gaba ɗaya kayan akan wani babban tray, duban Hayatuddeen tayi tare dayi masa alama akan yazo ya tayata ɗauka, aikuwa shi ya kwashe komai inda ya jere musu break fast ɗin akan dinning table, ita kuwa Zaleeha har yanzu tana kitchine, fruit salad ta haɗa, inda ta zubashi cikin wani babban glass bowl, tunanin haɗa chocolate fudge cake ne yazo mata, nan ta duba taga akwai komai na buƙata, kanta ta jinjina, sannan tashiga ƙoƙarin haɗawa, cikin mintuna ƙalilan kuwa ta kammala, ita kanta saida tayaba da ƙamshin chocolate fudge cake ɗin, Hayatuddeen dake falo kuwa koda ƙamshin yaje masa, saida yakasa haƙuri ya biyota zuwa kitchine ɗin, ganin, fudge cake ɗin yasan yashi cewa.
"Wow fantastic, Aunty Zalee dama wai kin iga girki har haka ne?, na ɗauka a faɗa da masifa chart da zuwa wurin aiki kawai kika iya."
Hannu tasa takai masa bugu, da sauri ya kauce yanayi mata dariya, hararan wasa ta watsa mai, tare da cewa. "Kaɗauka yanda kuke sakarkaru kaida Zakariyya haka kowa ma yake ne baku da aikin sai yawo a gari dama tsokana da ci."
Taƙare maganar tana me miƙo masa, wani haɗaɗɗen tray wanda ciki tashirya chocolate fudge cake ɗin, amsa yayi yana wani malau malau da baki, tare da cewa.
"Hmmm ai yanzune ma zakuga tashen jami'a zakusha mmki bari dai in gama sabawa da jami'ar kin san banfi sati ɗaya da fara zuwa ba."
Dariya ta ɗanyi tare da cewa.
"Yo ai da an ganka ansan kanka na fizga da igiyar iskar sabin shiga jami'a ka dai yi a hankali yaro dan ita jami'a gidan ban kashine."
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
"Gobe zan kawo miki sabon abo kina Khamis ku gaisa. kiga irin salon takun mu, yaseen ki kuma cewa mijinki ya saya min mota.
Dan ni ba yaro bane da za'a rinƙa kaini ana ɗaukoni kamar wani ɗan primary ko kayan wonki da za'a rinƙa kaini ana ɗaukoni".
Ya ƙarishe mgnar yana wuce zuwa dinning, food flask ɗin dake gefenta wanda ciki ta shiryawa Raliya abinci ta ɗauka.
Koda ta fito falo, nan ta iske Ummi, da kuma Saifuddeen, da Ahmad, Hayatuddeen kuwa tuni ya baje kan dinning, inda ya turo baki gaba, wai don saboda yace suzo suci, sunce yajira Zaleehan tagama sai suci tare, sam shi gaba ɗaya yaƙosa yaji yana tauna abincin, musamman ma da ƙamshin abincin ya cika masa hanci.
Zaleeha na fitowa daga kitchine ɗin ta dubi Hayatuddeen, fuskarta ɗauke da murmushi tace.
"Autan Ummi sarkin ci!."
Baki Hayatuddeen yaƙara turowa gaba, ashagwaɓe yace.
"Eh naji, amma please kice musu suzo muci, I swear am feeling hungry fa!."
yafaɗi maganar yana me shafa cikinsa, wanda hadda ganin abincin ma yaƙara masa jin yunwa.
Murmushin daya bayyana zallan cute face ɗinta tayi, tare da girgiza kanta.
Ummi ne tayi murmushi tare da duban Zaleehan, cikin so da ƙaunar yarinyar tace.
"Sannu da aiki, Allah yasaka miki da al'khairi, ya kuma baki ƴaƴa masu al'barka, wanda zasuyi miki fiye da haka."
Saɗa kai kasa Zaleeha tayi tare da ɗan sakin guntun murmushi a kunyace murya a sanyayaye tace,
"Amin Ummi."
Saifuddeen kuwa a fakaice ya ƙura mata idanu, yana kallon duk wani motsinta sosai yake mamakinta, har yau har yanzu ya rasa ita wace irin mutum ce mai fuska biyu da jujjuyawa tamkar hawainiya, ji yanda take ta murmushi tare da sakewa dasu, tanayin komai kamar wata wanda keson zama dasu da gaske.
Shi mamakinta ma yake, tawani irin sakewa sai kace ba itace, su keta gantalin nema ba jiya.
Kawar da kansa yayi daga kallonta, tare da maida hankalinsa, ga laptop ɗinsa,
wanda a zahiri laptop yake kallo a baɗiri kuwa fuskata yake kallo ta cikin madubin system ɗin,
rumtse ida nunshi yayi a hankali tare da sauƙe nannauyan ajiyan zuciya,
"To ina take zuwa ta kwana dasu waye take kwana, me take aikatawa a inda take kwanan?."
haka yaji waɗannan tambayoyin sun cika mishi zuciyarshi dake cike da azabebben kishi, gaba ɗaya ya rasa wani irin kishi Allah ya ɗora mishi a kanta ji yake tamkar zai faɗi ya mutu dan baƙin ciki.
Ahmad kuwa dubanta yayi tare da sakin murmushi, cikin ransa yayi ƙwafa, ahankali yace.
"Zaki sanine yarinya."
Duban Ummi Zaleeha tayi tare da ɗan rusunawa, cikin nutsuwa tace.
"Ummi bari na kaiwa Raliya abincinta, tunda batajin daɗi nasan ba lallaine tasamu fitowa ba."
Sosai Ummi taji daɗin kulawan da Zaleehan ta nuna ga Raliya'n, amma sai tace.
"A'a Zaleeha da kanki, bazaki bari Hayatuddeen yakai mata ba."
Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Bakomai Ummi, kinga Hayatudeen ɗin yace bazai iya komaiba sai yaci abinci,inaga bazai iya matsawa akan dinning ɗinnan batare daya lodawa cikinsa abinci ba, kin sanshi acicine kazar birni!."
Zaleehan tafaɗa tana kallon Hayatuddeen, ba iya Ummi ba harta Ahmad saida yaɗanyi murmushi sabida sunan data kira Hayatuddeen Acici kazar birni, Ummi ce tace, idan takaiwa Raliyan abincin ta dawo suci abincin, nan tace zasuci da Raliyan acan.
Koda ta ƙarasa ɓangaren Raliyan, akwance ta isketa, nan ta shiga ɗan kimtsa