Showing 54001 words to 57000 words out of 239422 words
Chapter 19 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
idanunsa, kansa ne ke sarawa, cikin body language ɗinsa, yace.
"Bawai zaɓinki bane banaso Ummi, ni auren ne banaso, ki dubeni ki gani fa, tayaya zan iya rayuwa da mata biyu, ko kun manta abun da Dr. ya faɗa ne, ina ɗauke da nakasa banjin cewa, zan iya bawa mata biyu kulawan daya dace dasu ba."
Dariya Ummi tasanya, tare da dubansa, saida tayi dariya sosai sannan taɗan soma tsagaitawa, shikuwa Saifuddeen kafeta yayi da idanunsa, tare da sanya mata fuskan tausayi.
Ɗan tsagaitawa da dariyan Ummi tayi tare da cewa.
"Ikon Allah, Yau kuma Saifuddeen kaida kanka kake ƙiran kanka da Nakasashshe? duk saboda ance ka ƙara aure shine har ka aminta cewar kai nakasashshe ne, har kuma ma kake ƙiran kanka da hakan, tsawon lokaci ban taɓa ji kaƙira kanka da wannan sunan ba, amma yau sai gashi da bakinka ka faɗa, ka kuma nanata. hmmm lallai ma kuwa to wallahi in sha Allah auren nan babu fashi, sai anyi shi, na kuma gama yi maka zaɓi, umarni ne idan kuma kace a'a, shikenan saika ƙira surukin naka wanda ya yanke hukuncin, kace masa kai bazaka bi umarninsa ba."
Idanunsa ya lumshe, jin zuciyarsa yake tayi masa nauyi, a kasalance, cikin yanayi marar daɗi yace da Ummi, ta sanar dashi, "Wacece zaɓin nata?."
Nan Ummi tace.
"Idan yana buƙatar sani, zai iya zuwa ya tambayi Adda Rahama, zata sanar dashi koma wacece."
Jin haka yajuya yafita jiki a mace, yana mai saƙawa ransa to wacece ina take ina suka samota da zasu liƙa mishi ita, tuno babu in da zai samu amsoshin duk waɗanan-nan tambayoyin sai wurin Adda Rahma.
Ae kuwa kaman jira yake cikin sauri ya juya ya fice daga cikin ɗakin.
Kai tsaye ɓangarensa ya nufa, inda ya kimtsa kansa, koda ya fito text message ya turawa Ahmad kan cewar yana son ganinsa.
Kasancewar Ahmad ɗin na cikin gida, hakan yasa mintuna kaɗan sai gashi ya fito.
Cikin body language Saifuddeen ɗin yace da Ahmad.
"Ya kaishi gidan Adda Rahama."
Sanin kwanan zancen yasa babu musu, Ahmad ya ɗauko musu mota, nan suka shiga, inda ya jasu zuwa gidan Adda Rahaman bayan sun biya jonapwd sun ɗauƙi ishaq wanda a zaton Saifuddeen ishaq zaibi bayanshi.
Koda Adda Rahama ta gansu batayi mamaki ba, don tun kafun zuwansu Ummi ta ƙirata ta yi mata bayanin komai.
Tray ɗin drinks masu sanyi ta dire agabansu, Ahmad ne ya ɗauki kwalin exotic ya miƙawa ishaq kana shima ya ɗauka inda yasoma kwankwaɗa, don shi fes yakejin ransa bashi da wata damuwa.
Hakama ishaq da shi yafi kowa jin haushin Zaleeha, kuma Babanshi ya mishi bayanin son ƙarawa Saifuddeen aure da Baban Zaleeya ya shiryawa.
Saifuddeen kuwa fuska ya marairaice, duban Adda Rahama yayi, tare da ɗaukan wayansa, cikin message ɗin Ummi ya shiga, nan ya nuna mata fuskar wayar, tare da yi mata alaman tambaya, kan cewa.
"Wacece? Ina take?".
Murmushi Adda Rahama tayi masa tare da cewa.
"Miye abun tada hankalinka haka ne Saifuddeen? da ka nutsu ma don amaryar taka ba ɓoyayya bace awajenka kasanta."
Cikin son ƙarin bayani ya zubawa Adda Rahama'n fararen idanunsa.
Duban tsab Adda Rahama tayi masa, kana cikin nutsuwa tace.
"Nasan kasan Ameena ae, wannan nurse ɗin da ta baka kulawa, lokacin da kake jinya a Abuja, kafun ku wuce India, to ita ce dai Ummi ta zaɓa maka, nima kuma nayi na'am don yarinyar akwai hankali, Masha Allah.
Ka tuna har gida tazo itada Mamanta suka dubaka da jiki."
Idanunsa ya zazzaro waje tare da jujjuya kai da ƙarfi sosai yashiga mamaki, lokaci ɗaya yaji kaman an watsa masa ruwan zafi, amamakance ya ɗan ƙanƙance idanunsa, cikin yanayin maganarsa wanda ya saba, wato body language yace.
"Allah ya sauwaƙe ni dai na auri wannan Ameenan, mezanyi da ita bazawara ce fa!."
Cikin tsananin mamaki Adda Rahama ta dubeshi, kallonsa tayi da kyau tare da faɗin.
"Kai Saifuddeen banda sharri bazawara kuma? wa ya faɗa maka cewar bazawara ce?".
Murmushin gefen baki yayi, tare da jijjiga kansa, in a body language ɗinsa yace.
"Impossible!, nine zan auri bazawara? chab hmmm Allah ma ya sauwaƙe, sam banason sauran wani wlh Allah ya kiyasheni suɗe ƙashin da wani ya rigani tsotsa."
Baki Adda Rahama ta buɗe fuska cike da tarin mamaki sauƙe a jiyan zuciya tayi tare da cewa.
"Wai nikam wayace dakai itaɗin bazawara ce?."
A shagwaɓe ya rubutawa Addan nasa.
"Ae basai an faɗa min ba, duk ckekken Namiji in dai ya nitsu idan mace bazawara ce zai gane ta ido, kuma nayi imani cewa Ameena bazawara ce, saboda haka ni dai bana sonta wlh bazan iyaba, ba kuma zan aure ta ba."
Ahmad da Ishaq kam dariya sukeyi sosai fahimtar abinda yake faɗin.
Baki Adda Rahama ta taɓe, inda ta gyara zamanta, dubansa tayi da kyau,ido cikin ido tace.
"Naji koma dai bazawara ce, ita Ummi ta zaɓa maka a matsayin mata, sannan da kake ta maganar cewa, ita bazawara ce, kai ɗin dakake magana saurayi ne kai? inace kaima bazawarinne tunda dai kayi aure."
Bakinsa ya turo gaba, a shagwaɓe ya narke fuska, cikin body language yace.
"Wallahi ni banason Ameena, yarinyar da idanunta abuɗe suke, ta fa riga da tasan Namiji, sannan kuma har yanzu ni matashin saurayi ne, tayaya ma zan yarda na auri Ameena."
Duban Adda Rahaman yayi tare da kamo hannunta, cikin yanayin daya saba musu alaman magana yace.
"Kin sanni tun ina ƙaramin yarona ma ko ta yaya bana amfani da tsohon abu, hatta kaya idan ya kasance gwanjo ne bana sawa, sannan idan yakasance wani ya taɓa amfani da abu, bana kuma amfani da abun, a iyaka tsawon rayuwata nafison komai sabo, koda wajen zama ne nafison sabo, banason wanda wani ya taɓa amfani dashi, harta mota ko wayar hannu, ban taɓa sayan second ba, komai na nafison yakasance sabo, ko lokacin da nake makaranta, ko yaushe ni nake zuwa first a acikin aji, bana taɓa yarda nazo second akomai na, to me yasa yanzu zan yarda na auri mace second hand? sauran wani, wanda wani ya cakalkala ya bari, ragowar wani fa Adda tunda nake gidannane kawai nataɓa sayan abu second hand kuma kin san shima saida na sabunta mana shi, bazan iya auren sauran waniba kinfa san inada kishi."
Kansa ya girgiza tare da cije laɓɓansa.
Baki buɗe Adda Rahama ke kallonsa, sosai take mamakin ƙarfin hali irin na Saifuddeen ɗin.
Shikuwa Ahmad da shaq dake gefe sai ƙyalƙyala dariya suke tayi, don sosai show ɗin na Saifuddeen keyi musu daɗi.
Ajiyar zuciya Adda Rahama ta sauƙe tare da cewa.
"Koma menene dai Ummi ta gama magana, kuma ta yanke hukunci, wanda mu dukan mu mun gamsu, ta kuma ce zata sanar wa Bappa Ali, don asamu ayi bikin cikin gajeren lokaci, kaman yanda Baba Malam ya buƙata, kai da za'ayi maka auren gata ma, miye na damun kanka, sadaki, kayan aure, komai da komai, duk fa Baban Zaleeha yace ya ɗauke ma, wannan kaɗai bai isa saka farinciki ba, auren huce haushi fa zaiyi maka."
Jan kujeransa baya yayi, inda ya kwaɓe fuska, nan ya dubi Ahmad yace dashi.
"Su tafi." kana ya ja hannun ishaq
Shidai Ahmad dariya kawai yake, har hakan yaso ƙular da Saifuddeen.
Haka dai suka dawo gida, bayan sun sauƙe ishaq ko amota Saifuddeen fuskar nan tasa aɗaure take tamau.
Suna isowa gida, kai tsaye part ɗin Ummi ya sake komawa.
Ganinsa yasa Ummi kafesa da ido, cikin sanya fuskar tausayi, yayiwa Ummi alaman cewa.
"Shi bayason Ameena, saboda bazawara ce, sannan kuma shi tsoronta ma ya keji, gata da kallon tsiya, sai kace mayya, gaba ɗaya idanunta abuɗe suke."
Dubansa Ummi tayi, tare dayin dariyar zuci batayi mamakin jin cewa Ameenan bazawara bace, saboda kafun isowarsu Adda Rahama ta kirata tasanar mata.
gyara tsayuwa tayi tare da cewa.
"Allah mai iko, yau kuma Saifuddeen kai ne me tsoron mace? uhmm saboda bakason auren ta shiyasa kake tsoronta ko?"
Sake shagwaɓe fuska yayi, duk yanda yaso Ummi ta fahimce sa, ƙiyawa tayi, daga ƙarshe ma juyawa tayi ta koma cikin ɗaki.
Ganin haka yasashi komawa part ɗinsa, ransa duk ba daɗi, wani haushin Ameenan nema duk ya cika masa zuciya, wannan rana haka dai yayi bacci zuciyarsa duk ba dadi.
Washegari.
Yana gamayin break fast ya shirya kansa, inda ya ɗauki Sule driver suka nufi gidan su Ishaq, don tun adaren jiya ya tsara cewa zai je yasamu Dirankaɗi da maganar, wato Baban Ishaq kenan."
Koda yaje Ishaq ne yayi masa jagora zuwa falon mahaifin nasa, bayan sun gaisane Saifuddeen yayi masa bayanin duk wani abun daya kawosa, ta hanyar yi masa rubutu a laptop ɗinsa.
Koda Dirankaɗi ya karanta murmushi yayi tare da duban Saifuddeen ɗin.
Cikin son basa ƙarfin guiwa yace.
"Tayaya kake tunanin cewa, bazaka iya auran mata biyu ba? Kai jarumi ne Saifuddeen, saboda haka kada kasa wani damuwa aranka zaka iya."
Nan fa Saifuddeen ya tubure masa kan cewar lallai shi bazai iya ba, ganin haka yasa Dirankaɗi ɗaukar wayarsa, inda ya ƙira Bappa Ali, shi kuma Ishaq dariyan Saifuddeen ɗin kawai yake.
Gaba ɗaya abun da Saifuddeen ɗin ya faɗa, shi Dirankaɗi ya maidawa Bappa Ali, nan Bappa Ali yace da Dirankaɗi, ya faɗawa Saifuddeen ɗin, aure babu fashi, tunda Baba Malam da kansa ya yanke hukunci.
Koda Dirankaɗi ya faɗawa Saifuddeen ɗin, take yace.
"To Baba nifa banida kuɗin auren ma in da ba sadakanta iyayenta zasuyi ba".
Nan Dirankaɗi da Ishaq suka saka dariya, dubansa Dirankaɗi yayi tare da cewa.
"Ae dama ba kaine zaka sayi komai na auren ba, auren gata za'ayi maka ae."
Haka duk yanda Saifuddeen yaso ya kaucewa auren, Dirankaɗi da Bappa Ali sunƙi basa dama, dama shi Baba Malam baisan wainar da ake toyawa ba.
Dole haka Saifuddeen ya dawo gida, zuciyarsa cike da tunani kala-kala.
Haka akayi ta kai ruwa rana da Saifuddeen inda yaketa cemusu wai aifa Dr yace bazai iya zama da mata biyuba, Ya Adnan kuma yace a a ba wani Dr daya faɗi hakan.
Ɓangaren Baba Malam kuwa, tuni ya turawa Yaya Ahmad kuɗi, kan cewar ya bawa Aunty Lubna ta shiga cikin shoprite na Abuja, tayi musu sayayyan kayan lefe, wanda za'aiwa Saifuddeen sabon aure dashi.
Yaya Ahmad ne yace da Baba Malam ya amshi kuɗinsa, shi zai haɗa lefen da kansa, nan Baba Malam yace "a'a so yake komai na auren yayi da guminsa, da kuma haƙƙinsa, don ya ƙudurta aransa cewa, auren huce haushi da kuma gata zai yiwa Saifuddeen ɗin."
Can ɓangaren Zaleeha kuwa, rayuwarta mai sauƙi take gudanarwa acan garin na Numan, zuwa yanzu bata da wani abinci sai kayan fruits, dangin su apples da kuma ayaba, goiba dabina sai su water meloon, acikin ƴan kwanki kaɗan ɗin, tuni abubuwa da yawa sun sau ya mata, zuwa yanzu abu biyu ne ke damunta, wato tana jin can ƙasan zuciyarta bata son gudowan da tayi tana kewan kowa hatta su Ummi tana kewansu, ji take kamar ta koma amman da zaran ta tuna ta koma ɗin sai taji kanta yana juyawa sai taji ta gigice lokaci ɗaya taji kamar an ɗaure mata zuciyarta.
Sai kuma nata soyayyar mutumin da har yanzu takasa sake sanyashi acikin idanunta, sosai soyayyarsa ke ƙara ninkuwa acikin zuciyarta, dashi take kwana kana dashi kuma take tashi, yayi mata tsaye acikin rai.
Yanzu ma zaune take akan katifarta, laptop ɗinta ne agabanta, inda ta saka earpiece akunnenta, wani series film take kallo acikin laptop ɗin nata, don tahakane take samun rage kewa, wayarta dake gefe ne ta soma ƙara alamar shigowar ƙira, sunan Balkeesu ne ke yawo akan screen ɗin wayar, saida ta kusa katsewa ta ɗauka tare da kara wayar akan kunnenta.
Daga can ɓangaren Balkeesu tace.
"Mutanen ƙauye."
Baki Zaleeha ta taɓe tare da faɗin.
"Ya akayi ne."
Balkeesu kuwa dariyar dake cinta arai ta danne tare da faɗin.
"Lafiya lau, ya kike kwana biyu ina ƙiran number ki baya tafiya."
Ajiyar zuciya Zaleeha ta sauƙe, cikin halin rashin kulawa tace.
"Maybe matsalan network ne."
Dariya Balkeesu tayi inda cikin zuciyarta tace.
"Ko kuma matsalan wuta ba." Afili kuwa cewa tayi.
"Dama Rabeel ne yace nayi miki magana, yana ta ƙiran wayarki amma bakya ɗauka, sannan yayi miki text duk babu reply, meyasa bazaki ɗauki wayarsa ba, ko kin manta cewar abokin aikin ki ne?."
Baki Zaleeha ta taɓe tare da cewa.
"Tayaya kike tunanin zan ɗaga ƙiransa, halan ya manta cewar ina da aure ne? igiyoyin auren wani ne fa akaina, to me yasa zan ɓata lokacina nakuma ɗaukarwa kaina zunubi wajen magan, da Rabeel wanda kuma bai zama lalle dole sai munyi magana ba."
Hararan wayar Balkeesu tayi, kamar Zaleehan na ganinta, taɓe baki tayi tare da faɗin.
"Uhummm su aure manya, dama naƙira ne kawai don naji ykk, da kuma dalilin ƙin ɗaga wayar Rabeel da kikayi."
Ɗan jim Zaleeha tayi tare da cewa.
"Bani da wani dalili naƙin ɗaga wayarsa sai na darajar auren dake kaina, kuma ma koda zai ƙira sau 100 bazan ɗaga wayarsa ba, saboda ina da aure, kuma shi ba muharrami na bane babu yadda za'ayi nayi magana dashi ina matar aure."
"Okay." Balkeesu ta faɗa ataƙaice tare da kashe ƙiran,
ita so take taga rayuwar Zaleeha tazama lalatacciya ta yadda zata samu damar maye gurbinta a ma'aikarsu da kuma gidan Saifuddeen, amman ta kaicinta ɗaya Zaleeha nada riƙo da mutuncinta na ɗiyamace musulma tana kare budurcinta da lallaɓashi tamkar ranta ga ibada.
Ita kuwa Zaleeha aje wayar tayi tare da maida hankalinta akan laptop ɗinta.
Itan kuwa Balkeesu tana kashe wayan, ta saki dariyan mugunta, inda a fili tace.
"Ko ahaka aka tsaya awasan nasamu kaɗan daga cikin abun danakeso tunda ko yanzu shirinki na mushaƙata ya dawo hannuna."
Can ɓangaren su Baba Malam kuwa, gaba ɗaya sun fita daga sha'anin Zaleeha, ko zancenta ma Baba Malam baiso ayi masa.
Maryam kuwa sosai take cikin damuwa, domin kullum da tunanin ƴan uwa da kuma mahaifiyarta take wuni, ganin yanda ta damu sosai ne, yasa Ya Ameenu ɗaukan ta ya kaita wajen Baba Malam, nan Baba Malam yayi mata kalamai irin na mahaifa masu kwantar da zuciya, tare da sa mata al'barka, hakan kuwa yasa zuciyarta ta saki, kaɗan daga cikin damuwarta ya kau.
Rayuwar Mama a Ɓilliri kuwa abun yazo mata cikin wani irin yanayi, komai ba yayi mata daɗi, zaman takura kawai takeyi agarin nasu, yayinda Zahira kuwa kullum bata da wani aiki, sai ƙworafi da mita, kan cewar ita lallai saida Maman ta maida ita gida, ita kuwa Mama har yanzu gani take kamar Baba Malam ɗin zai sauƙo yace su dawo gidan, don tasawa kanta aƙidar cewa bazata taɓa ƙiransa ta basa haƙuri ba, har sai shida kansa ya gaji yace su dawo.
To gatanan dai rayuwar batayi mata daɗi, abinci ma bata samun wanda takeso, gaba ɗaya komai yayi mata duhu, badon komai ba kuwa saidan tana rayuwa acikin mutanen da gabansu da kuma bayansu duk duhu ne, basa ɗauke da haske ko kaɗan, zaman Ɓillirin sam baya yi mata daɗi Babanta kuwa duk da kafurine yaga rashin kyauta warta, shiyasa ya tsananta mata yace gata ga ƙauyen ta zauna kuma damuna na dawowa noma zatayi, Zahiri kuwa ji take kamar a rami take gida ba wuta bare fanka ko AC ba Radio bare tv babu firij bare kayan more rayuwa babu gado bare lafiyayyan katifa babu ƙamshin komai sai warin burkutu, rayuwa dai ta masu tsamari gashi ita Zahira an katse mata karatu ta. Ruda kuwa Addan Mama daɗi hakan taji dan ko yanzu ta samu sun zama dai-dai da ƙanwar tata, itama ta wahalan dai.
Bayan Kwana Uku, da turawa Ya Ahmad kuɗin lefe, Baba Malam da kansa ya kimtsa, inda ya tsara tafiyarsu Abuja, shi da Dirankaɗi, da kuma Bappa Ali, yayinda za suje nemawa Saifuddeen auren Ameena, Alhaji Naseer Maichanji shine mariƙi ga Ameena, wanda yake ɗan kasuwa ne sosai, hakan yasa mafi yawancin mutane sun sanshi, koda zasuyi tafiyar tasu ta yanzun da expriance ɗinsu zasu tafi, kasancewar Dirankaɗi yasan Alhaji Naseer wanda a binciken da Dr Adnan yayi akan Amina a wurin Dr Aliyu ne sukaji komai na Amina.
ananne Dirankadi ya gane ɗiyar tsohon abokin kasuwancishi shiɗin, har ma number'n wayarsa yana dashi, domin sun sha haɗa busineess dashi Alhaji Naseer ɗin tun shekarun baya.
To kuma bisa jagorancin Dirankadin zasuyi tafiyar da tuni sun sanarwa Alhaji Nasir Daddy kenan zuwan nasu.
Ɓangaren Saifuddeen kuwa shi har yanzu ganin abun yake, kamar almara, musamman idan ya tuna da cewar.
"Ameena ɗin bazawara ce." Sai yaji sam shi bazai iya mu'amala da ita ba.
Ƙarfe 10 na safiya dai-dai jirgin da zai ɗaga zuwa Abuja, ya kwashi su Baba Malam da Bappa Ali. Inda suka tafi da niyar cewa bazasu dawo nan Gombe ba sai an tsaida lokaci da kuma ranan aure, don suna sa ran cewa.
"Insha Allah Alhaji Naseer ɗin bazai hanasu ɗiyarsa ba."
Sun isa garin Abuja lafiya, inda Ya Ahmad da kansa yaje ɗauko su a airport, nan fa dukansu suka shiga motar, kaitsaye unguwar Asokoro suka nufa, wanda anan gidan su Ameena yake.
Yayinda duk abinda akeyi Amina bata da labari.
Maigadi ne ya wangale musu gate ɗin gidan, nan cikin parking space ɗin gidan Ya Ahmad yayi parking, dai-dai lokacin wani ɗan Dattijon mutumi me cike da kamala, wanda yasha adonsa cikin manyan kaya, yafito daga cikin wata ƙofa, ganinsu da yayi yasa ya nufosu cikin sauri, fuskarsa ɗauke da fara'a ya miƙa musu hannu, nan suka shiga gaisawa cikin mutunta juna, kai tsaye yayi musu jagora zuwa ɓangarensa, wani babban falo ne mai kyau, inda anan yake tarban baƙinsa masu mahimmanci.
Zama sukayi, tare da sake sabon gaisuwa.
Duban Dirankaɗi Alhaji Naseer yayi tare da cewa.
"Alhaji Ma'aruf ashe rai kan ga rai?."
Murmushin manya Dirankaɗi yayi tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa Alhaji Naseer, gashi bayan lokaci mai tsawo da muka ɗauka gashi kuma mun sake haɗuwa."
Shima Alhaji Naseer ɗin murmishi yayi tare da cewa.
"Allah Mai iko, gashi kuwa harda Malam Bashir Sulaiman Dukku kuka zo, a gaskiya yau gidana yana ɗauke da manya manyan baƙi, masha Allah sannunku da zuwa."
ya ƙarishe maganar yana miƙawa Baffa Ali hannu
Dai dai lokacin masu aiki suka shigo, nan suka cika musu gaba da kayan ciye ciye harma da dangin su snacks.
Drinks ɗin kaɗai suka ɗan taɓa, nan Baba Malam da kansa ya gyara zama, duban Alhaji Naseer yayi tare da cewa.
"Nasan zakayi mamakin ganinmu, to amma ance wanda yake da buƙata shi yake zuwa, ko ba haka ba?."
Nan dukansu suka jinjina kai, inda Alhaji Naseer yace.
"Ƙwarai haka ne."
Ajiyar zuciya Baba