Showing 66001 words to 69000 words out of 239422 words

Chapter 23 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11863

buɗewa, taɗan tura kanta kaɗan, hangosa tayi zaune akan wheellchair ya bawa ƙofar baya.
Hakanne yasa sauƙe akiyan zuciya kana ta ƙarasa shigowa cikin ɗakin.
Ƙarasowa tayi kusan shi, hakanne ya sashi ɗan waigawa, nan fa ya sauƙe idanunsa akanta, dama kuwa tun kan taƙaraso sa hancinsa ya jiye masa baƙon ƙamshi, hakan yasa ya gane cewa, anshigo ɗakin nasa ne.
Haɗuwar idanunsu waje ɗaya yasa tayi ƙasa da kanta.
Ajiye tray tayi bisa stoll ɗin dake gabanshi.
Cikin nutsuwa ta ɗan sunkuyo a hankali ta fara haɗa masa coffee ɗin.
Shi kuwa Saifuddeen hannunta ya tsurawa ido zuciyarsa na raya masa abubuwa da yawa, wani irin abu yakeji, wanda shi kansa baisan dame zai ƙirasa ba, kishi ne koko haushi yakasa tantancewa.
Musamman ma da yake tuna cewa, kafun shiɗin ta taɓa haɗawa wani abu da hannunta, sannan kuma kafun shiɗin wani ya taɓa mallakarta a matsayin mata duk abinda zatayi mishi ta taɓa yiwa wani ƙaton, Allah ya sani shi dai yanada zafin kishi, shiyasa har kishi yake taya Zaleeha na aure mata shi da Amina tayi.
Ɗan taɓe lips ɗinsa yayi kana ya ɗan kawar da kansa gefe.


Anutse ta ɗago kofin tea ɗin, ɗan rusunawa tayi tare da miƙa masa.
Hannunsa yasa ya amsa.
Ɗan dubansa tayi tare da yin ƙasa da kai cikin sanyin murya tace.
"Bayan wannan akwai wani abun da kake buƙata ne?." ta ƙare mgnar da mishi misali da hannu.
Kansa ya girgiza mata alaman, "A'a"
Dubansa tayi inda asanyaye tace dashi.
"Saida safe."
Still kansa ya jinjina mata.
Haka ta juya ta fice daga cikin ɗakin.


Ɗakinta ta koma ta kwanta cike da matsanancin begensa, kullum ta ganshi sai taji ƙarin sonsa da kishinsa acikin ranta.


Shikuwa baiwani sha coffee ɗin sosai ba, yana kammalawa kuwa ya kwanta.


Yau kwana uku kenan da zuwan Ameena cikin gidan amma kuma, ko ka ɗan bata wani samun sakin fuska daga garesa, hasalima sosai zaman kaɗaici ke damunta, donma wani lokaci Hayatuddeen na ƙoƙarin ɗebe mata kewa, daga ɓangaren Ummi dasu Raliya kuwa, suna nuna mata ƙauna dai-dai gwargwado.


Yau kuwa gidan nasu ya karɓi baƙoncin Adda Rahama, wacce tazo duba Ummi da zazzaɓin mura ke damunta jin labarin zuwan Adda Rahma a bakin Raliya ne yasa Ameenan tatafi takanas har zuwa part ɗin Ummi inda suka ɗan taɓa hira da Adda Rahaman.


Ameenan na fita dan ta koma ɓangarensu ne Adda Rahama ta gyara zama tare da fuskantan Ummi cikin kulawa tace.
"Nikuwa Ummi anya Saifuddeen yana kulawa da yarinyar nan?,
ki duba fa shigowarsa ɗazun yasame mu dukan mu, amma ko kallonta baiyi ba anya zaman nasu da daɗi."
Ɗan jim Ummi tayi tare da cewa.
"Nima ina tunanin haka, domin kuwa kullum idan tazo gaisheni ta iskesa, anan part ɗin nawa take gaishesa, hakan kuwa kinga alama ne dake nuna cewa ba'a ɗaki ɗaya ma suke kwana ba."
Gyara zama Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Ae kuwa bai isa ba, hakanan bazai kunyata mu idon mutane ba, wanda yake haukan so da ƙulafashinta ɗin ba ita ke gudunshi ba, yasamu wacce zata zauna dashi kuma shi sai yafara gudunta.
Ina a nan Zaleehan ke kwanan garden duk dan kada ta haɗa makwanci dashi, hmm bari zanyi maganinsa ne ɗan nema."
Nan ta zaro wayarta, inda ta tura Saifuddeen ɗin text, kan cewar tana son ganinsa afalon Ummi, sannan kuma ya taho mata da key ɗin part ɗin Zaleeha.


Ganin saƙonta yasa Saifuddeen ya shiga mamaki me zatayi da key ɗin side'n Zaleeha, haka dai ya ɗauko key ɗin ya nufo ɓangaren na Ummi.
Yana zuwa kuwa Adda Rahama ta amshi key ɗin, dubansa tayi tare da cewa.
"Daga yau zan kulle part ɗin Zaleeha tunda dai bata nan, sannan kuma zan tafi da key ɗin na ajiye, daga yau kuma idan zaka shiga side ɗinka, sai ka nabi ta ɓangaren Ameena tunda duk nan ma hanya ne."
Idanunsa yaɗan zaro waje, cikin yanayin mamaki, tabbas abun nasu yanason shallakewa tunaninsa.
Fuska ya ɓata cikin body language yace.
"Haba Adda Rahama, wai me yasa kukemin haka ne, hanya ma sai an zaɓamin wanda zanbi, kamar wani ƙaramin yaro."
Hararansa Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa dole in zaɓa maka inda zakabi."
Ummi dai ido ta zuba musu.
Ita kuwa Adda Rahama
miƙewa tayi ta fice daga cikin falon, ta nufi part ɗin Saifuddeen da matan nashi.


Shikuwa Saifuddeen duban Ummi yayi tare da marairaice fuska, kau da kai Ummi tayi, don sam bazata ɗauki excuse ɗinsa ba.
Ganin haka ya gane abin nasu haɗin bakine, a ranshi yace.
"Sai ta cinye muku ni ai kun huta."


Adda Rahama kuwa jawo ƙofar part ɗin Zaleeha tayi ta kullesa.
Nan ta wuce ɓangaren Ameena.
Afalo ta sameta, tayi jigum ganin Adda Rahaman yasa Ameena sakin murmushi tare da cewa.
"Sannu da zuwa.
ɗanmurmushi tayi cikin sakin fuska ta zauna kusa da Aminan,
A hankali tace.
"Ke kaɗai ne ma?."
Da sauri ta gyaɗa mata kai tare da cewa.
"Eh ni kadai gidan shiru."
Ɗan gyara zama tayi kana tace.
"Gsky kam gashi kin saba zuwa aikin nan kuma shiru,
Amman dama Ya Adnan yace in sanar miki shida da Dr Aliyu sun sa an miki transfer zuwa nan F,M,C Gombe, in kin gama hutun bikin dai zakici gaba da zuwa aikinki a nan."
Cikin tsananin jin daɗi tace.
"Kai naji daɗi ngd matuƙa Allah ya saka da al'khairi."
Amin Amin Adda Rahma tace kana ta fuskanceta da kyau
cikin kulawa ta ƙira sunanta.
"Ameena." jin yadda ta kiratanne yasa ta
ɗago kai a hankali ta dube ta.
Gyara zama Adda Rahama tayi tare da sanya hannu ta dafa kafaɗan Ameenan.
Cikin kulawa tace.
"Ban san irin zaman da kukeyi da ɗan uwana ba kuma basai namiki dogon tambaya ko bindiddiba, ko ko nace ki faɗamin sirrinku ba."
Shiru ta ɗanyi ta zubawa Amina ido,
Ita kuwa Amina shiru tayi a ranta kuwa cewa take ina na ganshi mutumin da guduna yakeyi.
Ganin tayi shirunne yasa Adda Rahma taci gaba da cewa.
"Amma tabbas nasan dacewa, har zuwa yau babu wani abu da ya shiga tsakaninki da Saifuddeen, kiyi haƙuri wani zubin hakanan yake, bai fiye son shiga rayuwar kowa ba, bai shiga harkan mutun kai tsaye, kuma baida saurin sabo,
amma kuma kema ya zama dole kitashi tsaye, ke dai ba ƙaramar yarinya bace Ameena, saboda haka ke zaki zage ki jawosa jikin ki, kada kuma kijira cewa sai yazo, ko ko sai ya miki magana kafun ki amsa masa, a'a koda bai gayyaceki ba kije garesa, sabida ke halaliyanshi ne.
Haka yake duk yadda yake son abu baya nuna kulafashinsa, tunda yake a tsawon rayuwarsa kan abu ɗaya, abu ɗaya tai ya taɓa nuna mana kulafashinsa a kanta.
Tun yana yaro koda wani abin cine duk yadda yake son abin in dai ba an bashi bane bazai taɓa roƙaba ko ya nuna yana so.
Dan haka na roƙeki da Allah kada ki bari kinesanta kanki dashi idan dare yayi, kinsan hanyar da zaki bi wajen jawo hankalinsa, saboda haka wuƙa da nama duka suna hannunki, mu dai kwanciyar hankalinsa da farin cikinsa shine namu, kada ki bari kuna raba makwanci na roƙeki da Allah."
Ta ƙarishe maganar tana mai haɗe hannayenta wuri ɗaya alamun roƙo da neman al'farma.
Kai Ameena ta jinjina cike da gamsuwa sabida itama tana fatan samun kusanci dashi, nan tayiwa Adda Rahaman godiya, sannan suka ɗan taɓa hira, daga haka Adda Rahama ta tafi.
Haka dai Ameena ta wuni yau ɗin cike da son dare yayi.


Ƙarfe 9 na dare dai-dai ta gama kimtsa kanta, cikin nutsuwa ta nufi ɓangaren nasa.


Zaune yake akan wheelchair ɗinsa, dagashi sai wani 3 guater jeans da kuma wata fara ƙal ɗin singlet.
Yau ɗin agajiye yakejin kansa hakan yasa shi yunƙurin kwanciya da wuri.
Turo ƙofar ɗakin tayi wanda kuma dama idanunsa na kan ƙofan.
Ganinsa yasanya taji zuciyarta na bugawa da sauri, sannan kwarjinin sa ya cika mata ido, haka dai ta ƙaraso cikin ɗakin, ƙarasowa gabansa tayi inda ta tsaya gefenshi kaɗan.


Dubanta yayi cikin yanayin mamaki, don dai baice yana da buƙatar wani abu ba bare yayi zaton wani abun ta kawo masa.
Hannu ya ɗaga mata alaman "Lafiya dai."


Ɗan shagwaɓe fuska tayi tare da yin ƙasa da murya, a shagwaɓe tace.
"Ni dai tsoro nakeji, dana kwanta sai naga kaman abun tsoro zai zo ya kamani."


Idanunsa ya ƙura mata, cike da tsananin mamakin maganar nata, mintuna 3 ya ɗauka yana kallonta, kafun ya sauƙe ajiyar zuciya a ranshi yace anzo wurin tazo zata cinyeni ai na sani wannan harijar ƴarinyar bazata barni in samu salamaba.
cikin body language ɗinsa yace.
"To yanzu da kikazo nan, nine zan kare miki tsoron ko kuma me?."


Gane abun da yake nufi yasa tasake saka muryar shagwaɓa.
Dubansa tayi tare da cewa.
"Nidai gaskiya anan zan kwana, dan tsoron ɗakin can nakeyi."
Duk mgnar da zatayi mishi takan haɗa da misalta mishi da yarensu na kurame, dan har yau bata san yana iya fahimtar mgnar mutunba.
Shikam dama ya jima da harbo jirginta, ace duk tsawon kwanaki ukun da tayi bata taɓa jin tsoro ba, sai yau, hmmm.
Taɓe laɓɓansa yayi tare da nuna mata kan gadon, alaman gata ga gadon ae saita kwanta.
Wani irin sanyi taji acikin ranta, saboda ko ba komai zata kwana tana jin sassanyan ƙamshinsa kuma bai koreta kamar yadda ta zataba ko ya nuna mata kyara.


Shi kuwa Saifuddeen sauƙa yayi daga kan wheellchair din inda ya hau kan gadon, abaki bakin gadon ya kwanta, tare da jan bargo yaɗan rufa rabin jikinsa, hannunsa yakai inda ya kashe hasken wutan dake ɗakin, bedsite lamp ya kunna.
Ta daɗe a tsaye jin shiru ya kuma kashe wutan ɗakin ne yasa Ameena ƙarasowa ta hau gadon, can bayansa ta kwanta, inda ta aje kanta bisa lallausan pillown dake ta fitar da ƙamshi.
Lumshe idanunta tayi sakamakon jin yanda ta nutse cikin lallausan katifan, ga kuma wani fitinannen ƙamshi da sanyi me dadi da wani irin azabebben sanyin ɗakin.
Ƙura masa ido tayi tana mejin matsanancin shauƙi na fusgarta, ji take kaman tayi hugging ɗinsa, amma kwarjini da nauyi bazai iya barinta ba.
Shikuwa Saifuddeen baya ya bata, tare da lumshe idanunsa, bacci yakeji sosai, hakan yasa batare da yayi tunanin komai ba bacci ya ɗaukesa.


Ameena kam tajima batayi bacci ba, saboda tuni ta faɗa wata duniyar ta daban, sosai ta shiga tunani.
Sai wajen 10 na dare kafun bacci ya ɗauketa.


Washegari kuwa koda ta tashi bata iskesa cikin ɗakin ba, toilet ɗinsa ta shiga tayi al'wala, sannan tayi sallah, tana idarwa ta kimtsa masa ɗakin, sannan ta je ta gaishe da Ummi, kamar kullum ita da Raliya suka haɗa kayan break, sannan ta koma sashinta.
Wunin yau ɗin kusan kab ɗinsa da Hayatuddeen suka ƙaresa, kasancewar yau ɗin ba school, sosai kuwa ya ɗebe mata kewa. A nanne ta gane ashe Saifuddeen na iya gane mgnar da mutun keyi muddun yana gani motsin bakin mutun, jin wannan abu yasa wata iriyar kuya ta rufeta,kenan duk abubuwan data faɗa mishi a asibitinsu yana jinta, wannan shine shuka a idon makorwa.


Taso ta ƙoƙƙefe Hayatuddeen taji labarin Zaleeha amman sai ta gane cewa Haytuddeen ɗin wayone dashi kamar dila, wato duk surutunshi yasan abinda yakeyi,
sam yama ƙi bata fuskar suyi mgnar,
Dan da tace mishi.
"Ni kam ina uwar gidan take ne?."
Sai ce mata yayi.
"Nine mijinku?." yayi mata halin ɗan Nigeria amsa tambaya da tambaya, haka yasa tayi murmushi tare da cewa
"A a."
daga nan sai ya meda hankalinshi kan wayarshi.
Ita kuwa a ranta take cewa.
"Kaji yaro da iya zaro zance, ashe haka yakeda wayo kamar dila,
wato in ina son ji in tamɓayi mijinmu kenan."
Uhm ta nisa tare da maida hankalinta kan tv.


Yau ma dai da misalin ƙarfe 9 dai-dai, ta kuma kaiwa ɗakinsa ziyara, shidai baice da ita komai ba.
Hasalima yauɗin tarigasa bacci, don shi ya jima yana amfani da laptop inda yake aikinsa na sirri, ya daɗe yana aikin kafun ya kwanta nan baki bakin gadon.


Yau dai kusan kwana uku kenan da Ameena ke kwana a ɓangaren nasa, sai-dai kuma har kawo yau banda gaisuwa babu wani abun dake haɗasu, haka ma duk da cewa agado ɗaya suke kwana, amma ko ƴar yatsarta bai taɓa taɓawa ba, haka itama...


Kwanci tashi yau dai kwanan Ameena 13 agidan, sosai kuwa tashaƙu dasu Raliya, sannan idan suka haɗu a falon Ummi, sosai suke shan hira da Ahmad, Ishaq da Salisu kuwa suna yiwa ango tsiyar wai ya samu mace kusa dashi yayi bulum buƙui ya dena leƙa kasuwa ko kaɗan. ɓangaren Saifuddeen kuwa har yanzu ba wani sabo atsakaninsu, idan tashiga ɗakinsa kuwa iya kanta bacci, da gari ya waye kuwa tatashi ta fita....


Yau tun da safe taketa kiran Dr Batulu da suke cewa Mommy ta kirata a kalla sau uku dan tana buƙatar ƙarin bayanin yadda masu irin larurar Saifuddeen ke iya mu'amala da mace.
Amman sai ta kasa yiwa Dr batulu tambayar a ƙarshe dai text ta rubuta mata tambayarta,
aiko tana ganin tambayar Amina ta kirata da kanta ta bata duk wani ƙarin bayani.


Fitowarta daga wanka kenan, body lotion ta shafa ajikinta, tare da ɗan murzawa fuskarta powder, wata nighty gown me fitar da shape ɗin jiki ta sanya, babu laifi kuma dama tana da sura me ɗan kyau, nan rigar ta lafe ajikinta, inda tayi mata kyau, ɗan madaidaicin gashinta ta ɗaure sannan tayiwa jikinta wankan turare.
Koda ta kalli kanta amadubi tasan cewar tayi kyau.
Cikin nutsuwa tafice daga ɓangarenta batare da ta sanya mayafi ko wani abu ta rufe jikinta ba, yau dai kam ta ƙudurta aranta cewa, zata bawa kanta nutsuwa daga garesa koda ƴar kaɗance.
Ahankali ta tura ƙofar ɗakin nasa ta shiga.
Yana zaune a tsakiyar gado yasa system ɗinshi a gaba wayarsa na riƙe ahannunsa yana dannawa.
Jin ƙamshinta ya cika masa hanci ya sashi ɗago da kansa, inda ya sauƙe idanunsa akanta.
Dai-dai lokacin ta maida ƙofar ɗakin ta rufe.
Ƙura mata idanu yayi yana me bin ko ina na jikinta da kallo, sosai shape ɗinta ya bayyana har takai ga yana iya hango komai na ƙirjinta.
Cikin salon jan hankali tashiga takowa zuwa garesa, inda ta kafesa da idanunta wanda suke cike da mayen soyayyarsa, shiɗin ma yau dai kasa ɗauke idanunsa daga gareta yayi.
Ahaka taci gaba da ta kowa zuwa garesa, tana isowa kusa dashi ta lumshe idanunta tare da haurawa kan gadon, kanshi ya ɗan kauda ya maida ida nunshi kan wayarshi,
shiru yayi ya bar daddanna wayar tashi jin ta matso kusa dashi gab da gab,
juyowa yayi ya ɗan kalleta kwaɓe fuska tayi tare da cewa.
"Zan kwanta bacci nakeji."
Da idonshi ya nuna mata wurin kwanciya,
Madadin ta kwanta inda ya nuna matan sai kawai tasa hannu ta ture system ɗin na shi,
da sauri ya sunkuyo dan tare system ɗin daga faɗawa ƙasa, sunkuyowan da yayine ya bawa jikinsu daman haɗewa,
fuska ya haɗe tare da yi mata kallon zaki min ta'adi.
A hankali tace.
"Sorry."
Daga nan ta koma ta kwanta,
shi kuwa ya ɗan jima a zaune yana chat da Ishaq, in da yake ce mishi yanzu dai saura shida Mudassir suyi aure, tunda shi dai sun nace sun liƙa mishi mata.
Jin hakane ishaq yace.
ina amaryar.
ɗan juyowa yayi ya kalleta, da sauri ya kauda kanshi ganin har yanzu batayi bacciba kuma shi ta zubawa ido.
Taɓe fuska yayi tare da rubutawa ishaq.
"Gata nan a gefena ta zuba min ido kamar mayya ina ga dai yau kam cinyeni zatayi."
Ishaq na karanta saƙonshi ya turo mishi amsa.
"In ta cinyeka ma ai halal ɗinta taci,
Pleess Saifuddeen mu bar wasa, kayi ƙoƙarin yiwa yariyar nan adalci."
Da sauri ya maidawa ishaq amsa cewa.
"To naji me nayi mata na rashin adalci, me ta nema ta rasa ban zagetaba ban doketaba,
Da tace ɗakina take son kwana ma ban hanataba, kuma gadona na bata ba'a ƙasa nace ta kwanta.
Me ya rage zan mata?."
Da sauri ishaq yace.
"Haƙƙin aurenta mana wanda yake kanka, waji bine bayan ciyarwa da shayarwa ka biya mata buƙayar ta na ƴa mace ka kawar mata da buƙatan Namiji."
Uhum Saifuddeen yace lokacin daya karanta batun ishaq cikin sanyi yace.
"To ai batace tana soba. Ni kuma banji inada buƙata ba, amman in tace tana so ai gani gata ba sai tayiba tunda ai tasan komai, kuma a ɓurme take tunda ta taɓa aure wani gardin ya taɓa ɓurmata, ni ba rami kawai aka kawo min ba."
Sosai ishaq yayi dariyar daga bisani yace,
"Tana mace ya za'ayi tace tana so."
Cikin ƙosawa da zancen yace.
"Uhum baka santa bane wannan da idanu a tsakar ka, ai fyaɗe ma zata min. Kuma na gaji sai da safe."
Yana faɗin haka ya rufe data sannan ya ajiyo woyar da laptop ɗin bisa bed side kana a hankali ya kwanta tare da yin miƙa, a hankali yake sauƙe nufamshi dan ya daɗe a zaune gugunshi ya gaji.


Shiru sukayi baki ɗayansu a tunaninshi Amina tayi bacci.


Ita kuwa idonta biyu, jin motsin ya kwanta ne yasa, ta ɗan buɗe idonta a hankali ta mirgono ta matso kusa dashi.
ƙara matsoshi tayi cikin tsananin ƙaunarsa ta manna ƙirjinta da bayanshi,
yana jin hakan a jikinshi yace.
"Uhummm ta nan kikafi ƙarfi."
A zahiri kuwa juyowa yayi da niyar yaga fuskarta sai kuma yayi lub bisa gadon jin ta ruggumeshi da kyau, wani irin yam tsikar jikinshi ta bada,
ita kuwa Amina kanta ta ɗan nago ta kalli fuskarsa cikin sanyi ta mirgino jikinta kanshi gaba ɗaya tayi mishi rumfa,
hannunta tasa tana shafar sajenshi,
har zuwa haɓarshi a hankali ta lumshe ida nunta kana ta manna bakinta kan nashi,
da ƙarfi ya sauƙi numfashi lokacin da yaji ta lome tattausan lips ɗinshi tanayi musu wani irin zazzafan tsotso wanda yasan hucewa takeyi a kansu.
Shiru yayi mata kamar baisan me takeyi ba ya dai bata jikinshi tayi yadda takeso dan bashi da hurim hanata,
ita kuwa lallatseshi tayi son ranta sannan ta sahirta mishi ta koma ta konta, tana sauƙe numfashi.
shi kuwa gaba ɗaya yama rasa meke gudana a jiki da zuciyarshi.
A haka duk sukayi bacci.


Washe gari da safe, koda suka haɗu a falon Ummi ƙin yarda yayi su haɗa ido ya lura so take ta titse mishi idanu.
Ganin ta dameshi da kallone ya sallamesu ya fita.


Kasan cewar yau jumma'a kai tsaye shirin zuwa masallaci yayi.
Wata ɗanyar shadda mai kalan sararin samaniya ya sanya, sosai shaddan tayi masifar yi mishi kyau, hulan zanna bukar ya kafa akansa, inda ya ɗaura tsadadden agogon apple watch a hannunsa, yayi kyau ƙwarai, sai tashin ƙamshi yake, ƙwarai Saifuddeen ya iya tsantsara gaye sosai.
Direct wajen Ishaq ya nufa.
Daga wajen ishaq ɗin kuwa gidan Baba malam suka wuce,
dan kai mishi gaisuwar jumma'a kamar yadda suka saba.
Nan suka samu Ya Aminu da Ya Habu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login