Showing 27001 words to 30000 words out of 239422 words

Chapter 10 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11908

fararen cinyoyinta ne suka cika masa idanu, ahankali yasauƙe idanunsa akan shape ɗin bayanta, inda kyawawan hips ɗinta suka bayyana sosai, still idanunsa ne suka sauƙa akan dogon gashinta dake baje bisa bayanta.
Idanunsa ya lumshe tare da shaƙan daddaɗan ƙamshinta dake shawagi acikin falon, sake buɗe idanunsa yayi inda ya ƙurawa shape ɗin bayanta ido, take yaji gaba ɗaya tsikar jikinsa sun mimmiƙe, lokaci guda wani irin fitinanniyar sha'awa ya taso masa.
Take yaji wani abu na harbawa acikin jikinsa.
Zaleeha kuwa ɗan gajiya da tsayuwan tayi hakan yasa ta juyo dan dawowa cikin falon, kanta aƙasa dan kwata-kwata bata tsammaci ganin wani awannan lokacin ba.
Kusan numfashin Saifuddeen ne yaso ƙwacewa alokacin da idanunsa sukayi masa tozali da cikakkun breast ɗinta, wanda suka bayyana kansu ta cikin rigar hartakai ga ana iya ganin kusan rabinsu ta saman rigar, uwa uba ga shatin nipples ɗinta daya bayyana raɗau tacikin lafaffiyar rigar dake jikinta.
Wani irin yaarr yaaarr haka yaji ajikinsa, take wani abu ya mamaye gaba ɗaya ilahirin jikinsa, batare daya saniba wani irin numfashi ya ƙwace masa.
Jin fusgar numfashin mutum yasa Zaleeha ɗago kanta atsorace, ƙara tasake, sakamakon ganinsa da tayi, tare da saurin ja da baya, sam bata tsammaci ganinsa awannan lokacin ba.
Da sauri ta sanya hannu ta dafe ƙirjita, cikin tsoro haɗi da bugun zuciyarta daya tsananta bugawa, ajiyar zuciya take sauƙewa, sosai ganinsa ya tsoratata,
shikuwa Saifuddeen tsuke fuska yayi tare da kafeta da mayan idanunsa, wanda lokaci guda suka sanja launi, inda suka tashi daga fafare zuwa wasu kalan na daban.
a fakaice yake kallon ƙirjinta, wanda yake ɗagowa ahankali- hankali yasa, tabbas tsoratan da tayine yasa hakan, laɓɓansa ya cija tare da yamutsa fuska kana ya sanya hannu ya ɗan shafa kekyawan sajenshi da ya kwanta lib-lib,
cikin wani irin yanayi yasake kallonta, saidai wannan karon bai yarda yasauƙe idanunsa akan beautiful breast ɗinta dasuke mugun rikirkitashi ba, musamman ma shatin nipples ɗinta, wanda idan ya kalla sai jijiyar jikinsa ta harba.
Shiyasa ya kauda kanshi dan bafa yason raini, kada tayi zaton sha'awarta ke rinjayarsa kada kuma ta ɗaukeshi mayen mace.


Ɗan janye hannunta daga kanta tayi tare da dubansa, lokaci guda ta haɗe fuska tare da sanya hannu ta kama waist ɗinta.
Cikin faɗa da tsiwa wanda dama tuntuni suke kwance aƙasan zuciyarta ga kuma tsoro baki ta murguɗa mishi tare da cewa.
"Ae bai kamata bama nayi mamakin ganinka at this time ba, because aljani koda yaushe yana nan kuma zaije ko ina kuma zaiyi abinda yake so!."
Hararansa tayi tare daɗan juya idanunta cikin halin ko inkula tace.
"Meye kake wani kallona? idan ma kai mayene wallahi saidai kaci kanka domin nidai nafi ƙarfinka, kurwata kurrrr ni wallahi ka dena tsareni da waɗannan mayatattun ida nun naka."
Taƙare maganar tana jujjuya masa idanu, haɗi da kama ƙugunta, sam tagama mantawa da shigar dake jikinta kwata kwata.
Shikuwa Saifuddeen murmushin ƙasan zuciya yayi kana ya lumshe idanunsa tare da buɗewa yakuma watsa mata su, da sauri ta ɗauke idanunta daga kallonsa tare dajin wata irin faɗuwar gaba ya rusketa kwarjininshi da haibarsa suka mamaye fuskarsa a take taji shakkarshi da shayinshi.
Lokaci guda taji wani irin abu yana bi ta cikin jikinta har zuwa cikin zuciyarta dake harbawa da sauri-sauri.
Ahankali ya danna madannin kekensa inda yasoma nufowa gareta, ganin haka yasa tasoma ja da baya baya, still shikuma baidaina biyota ba, babu abun dayaso gusar da tunaninta kamar yanda ƙwayan idanunsa suka sanja launi daga farare zuwa ja, sannan gaba ɗaya sun rikiɗe sun canja launi zuwa yanayin bacci.


Saura baifi taku uku tsakaninsu ba, ta juya inda ta buɗe ƙofar ɗakinta ta faɗa ciki da gudu, tana shiga da sauri ta murzawa ƙofar ɗakin key.
Ganin alaman saka key aƙofar yasanyashi lumshe idanunsa tare yin murmushin mugunta da sanya hannunsa ya dafe goshinsa, ahankali yajuya yanufi ɓangarensa, idanunsa tuni sun rufe wani irin masifaffen sha'awa ne ke taso masa irin wanda bai taɓa ji ba kuwa. A ranshi yake cewa.
"Farar kura ba ga tsoro ga son bada tsoro, wai ita in an barta ni zata razana, fitinanniya mai bakin tsiwa, yarinya zanyi mgninki bakin zai mace."
Adaddafe yasamu yahau kan gadonsa, lumshe idanunsa yayi tare dayin kwanciyar rubda ciki, sosai yakejin wani matsanancin feeling, yayinda dazaran ya kulle idanunsa, hoton haɗaɗɗen surar ƙirjinta dana bayanta keyi masa gizo, tabbas shikam ya yaba da kyawu haɗi da cikar surar Zaleeha, ƙam haka ya ruggume pillow, sosai yakejin matsananfin feelings ɗinta, tunowa da yanda ya tsotsi laɓɓanta jiya, shiya sanya ya ƙara rikicewa, sosai yake sonjin ɗuminta acikin jikinsa, saidai kuma bashi da wani zaɓi wanda ya wuce haƙuri, dan shi tunani ma yake duk randa ya kusan ceta yaga ta kanshi dan yaga alamun tara mishi jama'a zatayi.


Ɓangaren Zaleeha kuwa tana murzawa ƙofar key, da gudu ta haura kan gado tare da shigewa cikin blanket, ƙam haka ta kulle idanunta gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi, sai alokacinne ma tatuna da irin shigar dake jikinta, take wani irin abu ya tokare maƙoshinta, tashi zaune tayi tare da duban kanta, ganin rabin ƙirjinta awaje, yasa ta cije baki, cikin takaici haɗi da kishin kanta tace.
"Sam baicancanci yaga surata ba, wayyo ni maiyasama nafita ne?."
Tsuka tayi tare da komawa ta kwanta, baccin tsorone ya ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba.


Shikuwa Saifuddeen saida yasha artabu da jikinshi da zuciyarshi sosai kafun ya iya maida bacci.


Washe gari.
Kamar yanda takeyi tun da tazo gidan haka yauma tayi, tana gama idar da sallah tatafi ɓangaren Ummi inda tagaisheta.
Yau ɗinma Ummi cikin so da ƙauna ta amsa mata gaisuwarta,
a falo ta haɗu da Saifudddeen da Hayatuddeen bisa dukkan alamu daga masallaci suke,
cikin sakin fuska Hayatuddeen yace,
"Barka da safiya Aunty Zaleeha."
ɗan tsayawa tayi fuska a sake tace.
"Barka dai autan Ummi."
murmushi yayi tare da cewa.
"Ya amarci da gajiyan biki."
hararansho taƴi cikin sanyi ta ratsa gefen Hamma Saifuddeen ɗin harara ta cillamishi, sai kuma tayi wuf ta wuceshi kamar dai tsoro take kar ya cabketa
abinma dariya ya basu kana suka bita da ido.
daga ɓangaren na Ummi kaitsaye part dinsu ta dawo, komawa tayi tanaɗe akan gado inda tacigaba da baccinta.


Acan gidan su Zaleeha kuwa sai jiya Mama tadawo daga tafiyanta da tayi, Baba Malam dai ko sannu baice da ita ba, koda ya lura cewa Zaheera bata gidan, tana can gidan Zaleeha, sosai ransa ya ɓaci, nanfa yasa Ya Ameenu Habu akan su kwashi kayayyakinta na aure da motocinta su kai maita kana su ɗauko Zahira sannan su ƙara yiwa Zaleehan nasiha inda yaje.
Hakan kuwa akayi, tuni Ya Ameenu da Habu sukatafi dan ɗauko Zaheeran bayan duk sun lodo kayan aurenta a motocintan.
Koda sukaje gidan nasu Saifuddeen sai Ya Aminun ya bawa Habu kuɗi yacewa Habu ya hau keke napep ya koma ya ɗauko motarshi su samu wacce zasu koma da ita tunda duk motoci biyun da suka zo dasu na Zaleehan ne ɗaya na cikin kayan aurenta ɗaya kuma wacce Ya Ahmad ɗinta ya saya mata,
Ya Aminu na fitowa cikin motar ya nufi wurin maigaɗinsu akan yaje ya mishi sallama da masu gidan a nan suka haɗu da Ahmad, inda suka gaisa cikin girmamawa da mutum ta juna, Ahmad ne yayi masa jagora har cikin gidan, saida Ya Ameena yafara zuwa ɓangaren Ummi tukunna, cikin mutum tawa ya gaida ta, sannan yayi mata bayanin cewa yazo ɗaukar Zaheera ne, sosai Ummi taji daɗin karramata da yayi, nan tasake aminta da tarbiyan gidan Baba Malam ɗin, Ahmad ne yayiwa Ya Ameenu jagora zuwa ɓangaren Zaleehan, don kuwa Saifuddeen bayanan, sun tafi meeting ɗin ƙungiyarsu na Jonapwd shida Ishaq.
Sosai Zaleeha taji daɗin ganin yayan nata, saidai kuma jin cewa Zaheera yazo ɗauka, yasanya taɗan ɓata fuska, saidai kuma bata isa cewa komai ba, sanin cewa Ya Ameenun nada zafi sosai, babu ruwansa yanzu saiya solleta soso da sabulu.
Haka Zaheera ma ranta baiso ba, don dai kawai Ya Ameenun ne yazo da kansa, amma da wanine bazata bisa ba, don ita ke gadin Zaleeha a cewarsu a yadda suka tsara kenan wai ai duk nacinsa bazai zo inda takeba in Zahira nan kuma da ita aketa plant ɗin yadda Zaleeha zata gudu,


Haka dole ta haɗo kayanta, Gyara zama ya Ameenu yayi, cikin kulawa haɗi da kwantar da murya, yashigayiwa Zaleehan nasiha, dayi mata nuni akan tabi mijinta, idan ya umarceta da yinnabu matuƙar bai saɓawa shariya ba yace tayi to koda bataso tayi, domin hakan shine dai-dai domin al'jannarta na ƙarƙashin diga-diginsa .
Itadai Zaleeha jinsa kawai take, amma bata ɗauƙa, koda yazo tafiya har compound ɗin gidan ta rakosu,
nan kuma yasa Hayatuddeen da Imran dasu Zakariyya kwashe kayayyakinta kab suka shigar mata,
sannan ya bata car keys ɗinta duka biyu a hannunta, godiya tayi tare da cewa ya gaishe mata da Ƴar uwarta Maryam.
Haka Ya Ameenu yatasa Zaheera suka bar cikin gidan, shikansa ya yaba da tsarin gidan, musamman ma part ɗin Zaleeha wanda yayi matuƙar kyau, shida kansa ya ƙyasa, ya kuma yabawa Saifuddeen sosai, don bakowani namiji bane zai iya ɓarnatar da dukiyarsa wajen ƙawata gida mai kyau kamar haka ba.


Tafiyan Zaheera yasa Zaleeha duk taji gidan bayayi mata daɗi, hakanan taji komai ya tsaya mata, batasan dacewa motsin Zaheeran na ɗebe mata kewa ba, sai ayanzu da Zaheeran tatafi, haka ta koma ɗaki ta kwanta, zuciyarta cike da saƙe-saƙe kala-kala.
Tananan ƙule aɗaki har akayi sallan isha,
Nanfa wani irin tsoro yashiga diro mata, take fargaba ta cika zuciyarta, sam batajin zata iya kwana itakaɗai aɗakin batare da wani nata ba, sosai tsoron sa yashiga zuciyarta, tabbas ayanda taga cikin idanunsa jiya to idan tayi wasa komai zai iya aikata mata, abanza saiya rabata da virginty ɗinta, shikenan kuma daganan yagama cutanta, dan tasa aranta cewa bamakawa daga ranan daya yayi disvirgin ɗinta tofa shikenan itakam ta sallama rai da rayuwa, don baƙinciki ne zaiyi ajalinta tabbas.
Tashi tayi daga kan sallayan tare da kai dubanta jikin ƙofar ɗakin, ganin babu key ajikin ƙofar yasa gaba ɗaya hankalinta ya ƙara tashi, atsorace tashiga neman key ɗin amma bata gani ba.
Ƙirjintane yatsananta bugu alokacin da taji motsin mutum a falonta.


Shikuwa Saifuddeen lokacin dawowansa kenan daga masallaci, kaitsaye ɗakinsa ya wuce, dan yanaso yaɗan watsa ruwa, kafun ya ya ɗa ci abinci.
Jin motsin buɗe kofar falonsa, dakuma rufewa yasanya taɗanji zuciyarta tayi sanyi, cikin hanzari ta ɗauki blanket da pillow, saikuma phone ɗinta, saɗab-saɗab tafito daga cikin ɗakin, ahanzarce tayi hanyar fita daga cikin falon, tana samun kanta aɗan compound ɗin shashin nata kuwa ta saki ajiyar zuciya, kaitsaye garden ɗin dake cikin part ɗin nata ta nufa wanda yake cike da sanyi da sauraye, kan wata kujera dake ɗan cikin garden din ta kwanta, tare da jawo blanket ta rufa jikinta, ɗaura kanta tayi akan pillow tare da sauƙe ajiyar zuciya, ta dai gwammace kwana awajen da dai ta tsaya aciki ya illata mata rayuwa, zata jure komai amma bazata iya jure abinda zai iya mata ba, hakanan bata tsaya wani mugu yayi disvirgin ɗinta ba tunda ta duba ɗaya ɗakinma babu key sai tayi zaton shine ya zaresu dan karta rufe ƙofa ya samu damar shigowa ya mata fyaɗe injita da faɗi.


Raliya kuwa wacce tazo rufe window'n ɗakinta dake abu ɗe ne taga kaman wulgawan mutum ya shiga cikin garden, kanta tasake zurowa ta cikin window'n, nan idanunta suka gane mata Zaleeha dake ƙoƙarin kwanciya akan wata kujeran ƙarfe.
Mamakine yakusan kasheta awajen, sosai abun ya ɗaure mata kai, komawa cikin ɗakin nata tayi ta zauna tare dayin jigum, me hakan yake nufi kenan? tsanar da Zaleeha tayiwa ɗan uwanta har yakai wanda zataƙi haɗa shumfuɗa dashi? har ta gwammaci kwana acikin sauro da ciyawi da sanyi a kan kujerar ƙarfe akan ta kwana dashi.
Kanta ta jinjina tare da rumtse idanunta wanda suka ciko da ƙwalla, sam bahaka ta ke wa ɗan uwannata fata ba, babban burinta shine yasamu ingantaccen kulawa daga wajen matar tasa amma meyasa Zaleeha ke gudunsa?
kwaffa tayi tare da cewa.
"Ko ya zakiyi wlh in sha Allah sai dai ya raɓi jikinki in Allah ya yarda duk iskancinki kin shiga hannu kenan mutu ka raba, ato sai yaci sadakinshi."
Tana faɗin haka sai kuma ta miƙe da sauri ta nufi.....!










Littafina na kune in kin ganshi a wojema na satane, turo ɗari 300 ta wannan no 09097853276 ko ka/kiyi min transfer'n 300 ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.








Wanda ya karanta na sata Yaseeeen doguwa.

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Cikin bedroom ɗin ta da nufin zataje ta sanarwa Ahmad,
ko meye ta tuna kuma, oho sai ta koma ta zauna tana nazari.
Sosai abun yayiwa Raliya ciwo, koda Ahmad ya fito ganin meya tsareta, kamar zata faɗa masa saikuma tayi shiru, shi kuwa da bai san meke faruwaba sai janta yayi suka koma bedroom ɗinta dan yana tare da begenta.


Ɓangaren Saifuddeen kuwa kwata-kwata ma bai nemi Zaleehan ba, yana fitowa daga wanka kwanciya kawai yayi, sam bayaso yaje gareta, harma yaga abun da zai rabasa da nutsuwarsa, dan shikaɗai yasan irin azaban dayasha jiya, saboda haka baya sake fatan shan wani azaban kalan wannan, kasancewar agajiye yake hakan yasa yana kwanciya bacci ya ɗaukesa.
Zaleeha kuwa gaba ɗaya tatakura akan kujeran da take kwance, sam kujeran bata da daɗin kwanciya bare daɗin bacci, cikin mintuna ƙalilan har jikinta yasomayi mata ciwo, gawani irin masifaffen sanyi dake busawa acikin garden ɗin, mutsutstsuka jikinta kawai takeyi, sosai takejin wuyanta ya ƙage amma kuma bata da wani zaɓi, wanda ya wuce yin haƙurin kwana awajen.
Atakure haka bacci ɓarawo yasamu nasarar ɗaukarta.


Ƙiran sallan asuban fari da akeyine ya ratsa jikinshi ya bashi lokacin salla yayi, ahankali ya buɗe idanunsa, ɗan miƙa yayi tare da haɗawa da salati a zuciyarsa, nan yatashi zaune, kekensa ya jawo tare da hawa kanta, cikin nutsuwa da ɗan sauran kasalan bacci yakai kansa banɗaki, wanka yayi tare da ɗauro alwala, kaitsaye yafice daga ɓangaren nasa.
Har yaƙarasa jikin ƙofar na Zaleehan saikuma wani tunani yazo masa, take yafasa shiga tada'ita da yayi niyya, sai ya ƙonƙasa mata ƙofar, kana ya juya ya tafi,
kai tsaye yawuce masallaci.


Zaleeha kuwa dama gaba ɗaya batayi wani ishashshen bacci ba, dan sanyine awajen sosai, jin motsi alaman cewa yatafi masallaci yasata tashi zaune, cikin sauri ta ɗau bargon haɗi da pillow'n ta, ahanzarce tanufi ƙofar falon nata, dai-dai lokacin Ahmad yafito daga ɓangarensu dan zuwa masallaci, idanunsa ne suka gane masa Zaleeha, fuskarsa ɗauke da ɗan mamaki yabita da kallo, ganin fitowarta daga cikin garden gashi hannunta riƙe da bargo da kuma pillow alamun nan ta kwana kenan yasanyashi girgiza kansa, cikin ransa yace.
"Allah Ya shirya ki, ae dama mai hali baya taɓa fasa halinsa, saidai in ba'a zauna ba kuma dai duk tsaurin wayon amarya to wlh sai ansha manta anci sadaki an suɗe ki dai gama ɓoye-ɓoyenki."
Nan yawuce masallaci.
Itakuwa Zaleeha sam-sam ma bataga Ahmad ɗin ba, kaitsaye ɗakinta ta wuce, cikin hanzari tasoma rage kayan jikinta, ruwan ɗumi ta haɗa inda tayi wanka, tana fitowa daga wankan ta zura wata farar jallabiya mai kyau, hijab tasanya tare da ta da sallah, koda ta idar da sallan bata tashi akan sallayan ba saida tayi azkar, nan ta ɗauko ɗan ƙaramin Qur'aninta tasoma karatu, ba'ita ta rufe Qur'anin ba saida taga gari yaɗan somayin haske,
wasu bedroom slippers masu kyau ta zura aƙafafunta, inda tasake feshe jikinta da turare me daɗin ƙamshi.
Koda tafito daga ɓangaren nasu kai tsaye part ɗin Ummi ta nufa, bakinta ɗauke da sallama haka ta kutsa cikin falon, wanda ke cike da jama'a, Raihana ne da Saminu waƴanda zasu koma Kaduna asafiyar ta yau, saikuma Goggo Dada da Aunty Meena wanda zasu koma Dukku, Aunty Rahama ma yau zata koma, don tunjiya Dr.Adnan keyi mata waya, kan cewar yayi kewarta gashi weekend yana gida shiyasa yace zaizo da safen ya ɗauketa.
Cikin yin ƙasa da kai haɗi da nuna tsantsar ladabi taƙaraso cikin falon, har ƙasa ta durƙusa inda ta gaishe da Ummi, cikin fara'a haɗi da sakin fuska Ummi ta amsa mata gaisuwan nata, tare da miƙo mata hannu ta kamo nata, cikin kulawa Ummi tace.
"Taso kizonan kusa da Umminki yarinyar kirki, kema ai ɗiyatace, tunda kika shigo cikin mu kuwa kinzama jininmu."
Tasowa tayi daga inda take tare da ƙarasowa kusa da Ummi,
Ummi ne tajawota inda ta zaunar da ita agefenta, sadda kai ƙasa Zaleeha tayi tana murmushi, hakanan itakam Allah ya samata son matan aranta, sosai take ganin ƙima da kuma darajan Ummi'n, su Raihana ne suka gaishe da Zaleehan, amatsayinsu na ƙannen Saifuddeen, haka ta amsa musu fuska asake, ɗan zamowa ƙasa tayi inda tagaishe da Goggo Dada dakuma Aunty Meena, sai kuma babbar yaya wato Adda Rahama, da kuma Saminu wanda ke zaune gefen Saifuddeen, da fara'a akan fuskarsu duka suka amsa gaisuwar nata, komawa gefen Ummi tayi ta zauna a ƙasan carpet dan tana matuƙar ji da ganin darajar Ummi, shiru tayi yayinda ko kallon inda Saifuddeen yake batayi ba, shikuwa har acikin ransa mamakin irin tsantsar ladabinta ga ƴan uwansa yake, tanason kowa acikin ahalinsa tana mutuntasu da girmamasu, amma wato shine marainin wayonta sam bata ganinsa da gashin ido, murmushi yayi wanda shi kaɗaine yasan ma'anonin murmushin ransa yace.
tabbas kuwa zanyi maganinta ne, very soon zankashe bakin tsiwan, badai ni ta raina ba?."
hmmm yasha alwashin duk randa ya kamata kuwa zataji ajikinta.


Saminu ne yace da Raihana su hanzarta sutafi, bayason tafiyar da bata safiya ba, saboda alokacinne yakejin karsashi ajikinsa, nan kowa yatashi don yi musu rakiya zuwa compound ɗin gidan, ciki kuwa harda Zaleeha wanda ta kamo hannun Daddy yaron Bappa Ali wato Junior mai sunan Abbandu Saifuddeen kenan, kasancewar yaron kyakkyawane yasanya sosai yashiga ranta, gashi nan da wayonsa irin yaran nanne masu shiga zuciya, haka suka fito compound ɗin gidan inda yaketa zuba mata surutu, itakuwa murmushi kawai take tayi masa, har bakin mota suka rako su Raihanan, nan sukayi sallama da juna, cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login