Showing 192001 words to 195000 words out of 239422 words

Chapter 65 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11895

saida yayi kuka sosai, sannan ya ɗago daga sujjadar, adaddafe ya shiga toilet ya ɗauro alwala yana fito ya zura jallabiya bisa gajeren wondon da ya saka,
sallah raka'a biyu yayi, ko acikin sallan saida yayi kuka sosai, haka da zazzaƙar muryarsa ya dinga yiwa Allah kirari da sunayensa tsarkaka, yana idar da sallan, yaɗan janyo jikinsa ya jingina da bango, hannunsa yakai yaɗan taɓa Zaleeha, gani yayi komai nata asake yake gashi kuma bata numfashi, hawayen tsananin tausayinta da kuma ƙarin ƙaunarta ne suka kwaranyo daga cikin idanunsa, hannunta ya kama ya riƙe gam, haka yakeji kaman ya maida ita cikin jikinsa. Tabbas Zaleeha rayuwarsa ce, itace silan komai na nakasarsa, itace gaba ɗaya duniyarsa kuma yanzuma gashi itace silar warakanshi. Samunta HASKE ne acikin rayuwarsa. Jin ana ƙoƙarin shiga sallan asuba, yasa adaddafe yayi sallan dan bayajin zai iya zuwa masallaci, saboda ko zama me kyau baya iyawa, koda yazo yin sallan ma saida yaɗan jingina, saboda yanda jiri da kuma zazzaɓi me zafi da suka rufeshi ga ƙugunshi da yakeji kamar ya ida gwamɓalewa, idan yayi sujjada kuwa da ƙyar yake iya ɗagowa, saboda yanda bayansa ke riƙewa.
Yana idar da sallan, adaddafe yajawo kekensa ya hau, ko iya jingina bayansa da kyau bayayi, saboda yanda yakeji, haka ya nufi sashin Ummi, yana ganin dishi-dishi a idanunsa. Da ƙyar ma ya iya bude ƙofar falon yashiga, babu kowa afalon, kaitsaye ɗakin Umminsa ya nufa, jikinsa gaba ɗaya ba ƙarfi, hakan yasa ahankali ya ɗan murɗa handle ɗin ƙofar, jin ƙofar arufe gam yasashi, juyawa, ya nufi ɗakin Hayatuddeen yana zuwa kuwa, ya samu ƙofar abuɗe, koda ya shiga ɗakin bai taradda Hayatuddeen ba, da alama baidawo a masallaci ba. Ƙarasawa cikin ɗakin yayi, inda yaɗan zamo daga kan kekensa, akan lallausan gadon Hayatuddeen ɗin ya kwanta, tare da jawo blanket ya rufa ajikinsa, har yanzu jikinsa rawan sanyi yake, saboda tsabar karkarwan da jikinsa keyi kuwa, hatta gadon ma saida ya ɗauka.
Hayatuddeen kuwa tare da Ahmad suka dawo daga masallaci, sai faman zuba hamma yake dan bacci bai ishesa ba.


Kai tsaye ɗakin Ummi suka nufa, Hayatuddeen ne yayi knocking, Ummi wanda idar da sallanta kenan tasowa tayi ta buɗe ƙofan dan tasan bazai wuce suɗin ba, cikin girmamawa Ahmad ya durƙusa ya gaisheta, fuska asake ta amsa masa, Hayatuddeen kuwa cikin gigin bacci ya gaisheta, amsa masa tayi tare daɗan ranƙwashin kansa, murmushi sukayi su duka, sannan Ahmad ya juya ya haura sama, shi kuwa Hayatuddeen juyawa yayi ya nufi ɗakinsa.

Yana shiga kuwa ya ja kofar ya rufe, juyowan da zaiyi ne idanunsa suka sauƙa akan wheelchair ɗin Saifuddeen, da kuma shi kansa Saifuddeen ɗin dake kwance yana ta masassara, har kana iya jiyo hucin numfashinsa daga bakin ƙofar ɗakin. Idanu Hayatuddeen ya zazzaro, atsorace ya ɗan dafe ƙirjinsa, cikin sauri ya juya ya fice daga ɗakin har yanacin tuntuɓe.
"Ummi! Ummi!! Ummmee"
Haka yake ƙiran sunan Ummi da ƙarfi.
Ummi dake zaune aɗaki jin yanda Hayatuddeen ke ƙiranta, yasa taji gabanta ya faɗi haka yasa jiki na rawa ta miƙe ta buɗe ƙofar ɗakin jin yadda Hayatuddeen ke danna mata kira babu ƙaƙƙawautawa, tana saƙo kanta woje shi kuma yana sako kansa ciki haka yasa sukayi kiciɓis a bakin ƙofar.
A birkice Hayatuddeen ya kamo hannunta cikin firgita yace.
"Ummi Hamma Saifuddeen! zo muje kiga Hamma a ɗakina baida lfy sai rawan sanyi yakeyi".
A take Ummi taji wani zufa ta karyo mata haka nan taji jikinta na rawa, dan kuwa mafarkin da tayi daren jiya ne ya faɗo mata wai ƙugun Saifuddeen ɗinta ya ida gwambulewa.
Cikin sauri tabi bayan Hayatuddeen.
Ahmad kuwa har ya haura sama jin yadda Hayatuddeen ke ƙiran Ummi a gigicene ya sashi juyowa zai sauko dan hakanan yaji a jikinsa cewa ba lafiya ba.


Cikin sauri Ummi ta shiga ɗakin Hayatuddeen ɗin, hankalinta a tashe isa zuwa jikin gadon Hayatuddeen ɗin wanda Saifuddeen ke kwance, akai yanata faman masassara, cikin sauri Ummi tasa hannunta ta ɗan yaye blanket ɗin daya ya rufe jikinsa dashi, ganin yadda gaba ɗaya jikinshi karkarwa ne yasa tace.
"Subahanallahi Saifuddeen meya sameka? dama baka da lafiya ne?."
Tayi maganar tana ɗan jijjigashi sanin da tayi cewa idan bata taɓashi ba bazai gane tazo ɗinba, saboda ya bawa ƙofar shigowan ɗakin baya.
Shi kuwa Saifuddeen Jin muryar Umminshi ne cikin kunnuwanshi wanda rabon da yajita tsawon shekaru 20 kenan.
A hankali ya ɗago kansa wanda yake jinsa kamar zai rabe biyu,
wasu irin zafafan hawaye ne suke zubo mishi daga ida nunshi.
Ganin haka Ummi tayi masifar gigicewa cikin tashin hankali da kiɗima tace.
"Innalillahi wa innalillahi rajiun, Saifuddeen meya sameka?, ina Zaleeha meya meya sameka?"
a hankali ya lumshe Idanunshi tare da motsa lips ɗinkin cikin wata iriyar murya mai ɗauke da rauni da baiyanar da azabar da yakeji yace.
*"Ummy"* cikin wani irin fitinenne ruɗani fargaba da kuma kaɗuwa Ummi taja da baya, lokacin ɗaya taji wani irin shock ya shiga jikinta gaba ɗaya wanda hakan yasa jikinta karkarwa idanunta suka firgita woje jin sauƙar muryar da bazata manceba tsawon shekaru 20 kenan da ta daina jin amo da kuma sauti wannan muryar, tun tanasa rai da jinta har ta cire,
mafarki takeyi ne ko kuwa da gaske ne?so take ta tantance hakan yasa ta dafe kanta dake juyawa da kuma ƙirjinta dake barazanan fitowa waje, hannu tasa ta soma mutsstsuke idanunta.
Ahmad ne wanda shigowarsa cikin ɗakin kenan yajie sautin muryar Saifuddeen ɗin ya daki dodon kunnenshi muryar da bazai taɓa mancewa da itaba komin yawan shekarun da aka kwashe bai jitaba kuwa.
Ji yayi gaba ɗaya jikinsa ya soma rawa tsikar jikinsa na mimmiƙewa idanunsa ne suka ciko da wani irin ƙwalla.
Saifuddeen kuwa ganin irin kallon da Ummi keyi mashine mai ɗauke da tantama yasashi miƙo hannunshi jiki na rawa ya kamo hannunta, cikin tsananin rawan jiki da kaɗuwa Ummi tace.
"Saifuddeen!!!". Ido ya rumtse da ɗan ƙarfi yace.
"Na'am Ummi!". wani irin tsuma da karkarwa jikinsu keyi gaba ɗayansu,
Hayatuddeen kuwa samun kansa yayi cikin wani irin masifeffen tashin hankali da kuma firgici abune da wanda shi dai zaice bai taɓa zaton ko tsammanin ba asalima kuma shi zai iya cewa bai san kalan muryar Hammanshin ba tunda yana ɗan ƙarami Hamman nashi ya kuramce, bai taɓa jin yayi maganaba sai yau,
cikin wani irin razana ya fasa wani ihu na tsananin kaɗuwa da farin ciki take kuma ya tafi luuu ya faɗi a sume,
da sauri Ahmad ya tareshi ya kontar dashi bisa carpet, dan sam hankali Ummi baya kanshi, shi kuwa Saifuddeen zafin ciwo yasa bai kula da suman da Hayatuddeen yayiba shima kanshi Ahmad hankalinshi na kan Saifuddeen shiyasa kawai sai ya kontar da Autan Ummi kamar maiyin bacci.
A kiɗine Ummi ta matsoshi tare da cewa.
"Babana kana jina kana mgna, Ya Allah na in mafarki nakeyi ma ka tabbatar min dashi".
Cikin dauriyar ciwon da yake ji ɗin yace.
"Ummy a zahiri ne, ba mafarki kikeyi ba, ƙudurar ubangiji ce, dare ɗaya ya ɗauke jina da mgnata, kana bayan tsawon shekaru ashirin ya dawo min jina da mgnata a dare ɗaya".
Cikin wani irin kaɗuwa Ummi tace.
"Yaushe ka fara magana yaushe ka fara jin mgna? Saifuddeen".
Wani irin rumtse idonshi yayi dan jin kanshi kamar zai rabe gida biyar ga wani irin sarawa da ƙugunshi keyi a fizge yace.
"Ummi daren jiya na fara jin Zaleeha tana kiran sunana, tana ihu, Ummi sunana da kuka da ihun Zaleeha na fara ji tamkar zai fasa min dodon kunne Ummy kuka Zaleeha tai tamin".
Sai ya kuma saki hannun Ummi ya riƙe kanshi da hannu biyu da ƙarfi ya matse kan nashi murya na rawa yace.
"Wayyo! Allah na wayyo bayana Ummy bayana zai ɓalle inaji kamar ana haɗa jijiyoyin ana ɗinkewa Ummy bayana, kaina, wuyana, ƙuguna, cinyana, ƙafata,
Cikin tsananin kiɗima Ahmad ya matso
Saifuddeen ɗin tare da kiranshi.
"Saifuddeen!." Ɗago idanunsa da suka kaɗa sukai jajazir yayi, murya na rawa yace "Na'am Ahmad." Idanu Ahmd ya zazzaro cike da shock, sai kawai ya fashe da wani irin kuka, tare da jawo Saifuddeen ɗin jikinsa ya rungumesa sosai. Dai-dai lokacin kuwa Raleeya ta shigo cikin ɗakin aguje, ganinsu ahaka yasa ta yi turus tana me ƙare musu kallo. Ganin yanda Ummi da Ahmad ke kuka yasa taji gaba ɗaya ƙafafunta sun fara rawa, ƙoƙarin buɗe baki take dan tayi magana, ta hango Hayatuddeen a yashe aƙasa baya motsi, kansa tayi agigice ta durƙusa tana jijjigasa, hankalinta amatuƙar tashe tace. "Hayatuddeen ka tashi dan Allah, me yake faruwa, Yaya Ahmad me kukayi masa? meyasa baya motsi? wayyo dan Allah Ummi kizo kiga Hayatuddeen baya motsi.."
tafaɗi maganan tana me jijjiga Hayatuddeen ɗin dan gaba ɗaya ta ruɗe. Saifuddeen ne ya ɗan janye jikinsa daga na Ahmad ɗin dan ji yake kamar gatari ake kima mishi a bayanshi komawa yayi ya konta tare da rumtse idanunsa, dan ciwo yakeji sosai acikin jikinsa.
Ummi ne ta tashi daga durƙuson da take inda ta ƙarasa kan Hayatuddeen zuwa lokacin kuwa tuni Raleeya ta ɗauko goran ruwa ta yayyafa masa, wata iriyar ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauƙe.
Ganin haka yasa Raleeya itama sakin ajiyar zuciya. Ummi kuwa akan gadon ta zauna, har yanzu hawayene ke tsiyaya daga cikin idanunta, Hannun Saifuddeen ta kamo, cikin muryarta dake rawa tace. "Saifuddeen Babana hankali ya tashi gani nake kamar mafarki nakeyi, meya sameku ina Zaleeha."
tafaɗi maganan tana me ɗan shafa gefen fuskarsa.
Idanunsa da suke lumshe ya buɗe tare da zubawa Ummin nasa su, sake riƙe hannunsa dake cikin nata yayi, laɓɓansa yaɗan motsa ahankali yace.
"Ummi baya na zai golɓole. Allah ya bani lafiya ayanzu na zama akaman kowani meji da faɗa amman kuma baya zai tsinke."
sabon kukane da fargaba ya sake ƙwacewa Ummi, cikin zuciyarta take ambaton sunan Allah tare da neman agajin Allah. Raleeya kuwa haka ta zama kaman gunkin da aka sassaƙa, ganin abun take kaman awata duniya ta daban, jikinta ne ya ɗauki ɓari, saboda yanda taga Hamman nata na magana, abune wanda bazatace ga lokacin da ta taɓa gani yayi ba, ko adacan baya lokacin daya kurumce bata da wani isashshen wayo.
Hannu tasa ta dafa kanta dake bugawa, muryarta na rawa tace. "Hamma Saifuddeen." Jin muryan Raleeya acikin kunnensa yasashi daurewa ya kalleta, tare da sakar mata murmushi, cikin muryarsa me fidda azabar da yakeji yace. "Na'am Raleeya."
Wani irin kukane yazo mata, take ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa, lokaci guda kuwa ta saki kuka me sauti, tare da ƙanƙamesa, cikin kukan tace.
"Alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimussalihat, Alhamdulillah Ya Allah, Hamma Saifuddeen kaine, kake magana, Alhamdulillah Allah." Sai kawai ta sake sakin sabon kuka.
Shi kuwa Saifuddeen ji yayi kamar anja bayanshi da ƙarfi hakanne ya sashi zubda wasu hawayen azaba.
Hayatuddeen wanda farfaɗowansa kenan, janyo jikinsa yayi, inda ya raɓa jikin Hamman nasa, ya saki wani irin kuka me taɓa zuciya, wace irin ranace yau tazo me cike da al'khairi agaresu?. Saida sukayi kuka sosai kafun suka ɗan janye jikinsu daga nashi, dan jin yanda jikin nasa ya ɗauki zafi zau kaman wuta, gashi sai rawan sanyi yake, haka Raleeya ta fita daga ɗakin da gudu kaman wanda aka tsikara.
Ummi ne ta matso kusa dashi, tare da kamo hannunsa ta zuba masa ido, tanajin wani irin farinciki da fargaba na neman fasa mata zuciya. Shikuwa zuwa lokacin shikaɗai yasan me yake ji ajikinsa, ciwo sosai yakeji.
Hannun Ummin ya kuma damƙewa, cikin muryarsa dake fitar da rauninsa yace.
"Ummi ciwo nakeji acikin jikina, bayana inajinsa kaman zai ɓalle, kaina ciwo yake Ummi, zazzaɓi nakeji, ko zama bazan iyaba Ummi bayana zai ɓalle." Hawayen da suka cika idanunta ne suka samu daman gangarowa, hankalinta amatuƙar tashe tace.
"Saifuddeen me yasamu bayan naka? ,mekakeji ajikin ka? kafaɗamun ko wani irin ciwo kakeji sai na ƙira Dr Adnan yazo ya dubaka."
Duka Ummi tayi masa tambayar tana me shafa gashin kansa. Awahalce yaja numfashi, murya asanyaye yace.
"Ummy bayana." Hannu Ummi tasa ta rufe fuskarta tana sakin sheshsheƙan kuka, tare da ambaton Allah acikin ranta, tanayi masa godiya tare da rokowa ɗanta lfyar bayanshi da yaketa ce mata zai tsinke, lallai Allah ma buwayi ne gagara misali, meyin yadda yaso alokacin dayaso, ya bada alokacin da yaso, ya kuma hana alokacin da yaso, yakanyin duk yanda yaso, babu wani meyi masa shamaki, shine sarkin kowa da komai.
Ahmad ne ya kamo hannun Saifuddeen ɗin ya riƙe, jin haka yasa Saifuddeen ɗin, awahalce yace.
"Ahmad Bayana, inajin zogi da zafi sosai." Hawaye Ahmad ya share tare da cewa.
"Sannu kaji Saifuddeen, zaka daina jin hakan insha Allah, ko wani abu ya samu bayanne?." Kai ya gyaɗa alaman "Eh." dan zuwa yanzu maganan ma daƙyar yake saboda yanda yakeji. Ummi ne cikin matsanancin tausayawa. tace.
"Saifuddeen ina Zaleeha?." Dogon numfashi yaja asanyaye yace. "Zaleeha bata da lapiya Ummi, tun jiya da daddare ta suma, dan Allah Ummi kije ki taimaka mata, kada wani abu ya same ta." Idanu Ummi ta ɗan zaro cikin tashin hankali tace. "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un, ta suma kuma?."
Kansa kawai ya iya jinjina mata alaman "Eh." cikin sauri Ummi tatashi daniyar zuwa ɗakin Zaleehan.
Hannun Ummin ya kamo hakan yasa ta juyo tare da zuba masa ido. Kansa yaɗan girgiza akasalance yace.
"Dan Allah Ummi karku faɗawa Zaleeha cewar nafara magana, banaso tasan cewar kunnuwana sun dawo, dan Allah kumin al'kawarin cewar bazaku faɗa mata ba." Ɗan jim Ummi tayi, wani tunani dayazo ranta ne yasa ta jinjina kai, tare da cewa.
"Insha Allah bazamu faɗa ba harsai ka nemi hakan."
Sakinta yayi, ta fice daga cikin ɗakin da sauri, Hayatuddeen ne ya matso kusa dashi,Yanzu Hammansa najin duk wani motsi, kuma yana faɗin duk abun dake rai da zuciyarsa, me yafi hakan daɗi da farinciki awajensu? farinciki, lafiya, da kuma jin daɗin Saifuddeen shine nasu baki ɗaya.
Raleeya kuwa tana fita daga ɗakin, da gudu ta haura sama, wayarta ta ɗauka hannunta har rawa yake wajen dannawa numbern Adda Rahama ƙira. Bugu biyu kuwa Adda Rahama ta ɗauka, kuka me haɗe da Dariya Raleeyan tasa, jin haka yasa Adda Rahama dake zaune miƙewa tsaye, hankalinta ne yasoma tashi jin kukan Raleeya'n, cikin ɗan tashin hankali tace. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, lafiya kuwa Raleeya, meyake faruwa?."
Ɗan tsaida kukan Raleeya tayi, murya na rawa tace.
"Adda Rahama, ranan yau takasance mana rana mafi al'barka agaremu wanda bazamu taɓa mantawa da ita ba, Adda Rahama kunnuwan Hamma Saifuddeen sun buɗu, yanzu yanajin duk abun da mutum zai faɗa, haka kuma idan kaƙira sunansa zai amsa, Adda Rahama Hamma Saifuddeen ya warke daga cutan kurumta, yanzu yazama mutum me lafiya ji da magana." Wani irin shock Adda Rahama taji ajikinta, sosai maganan ya daki zuciyarta, saboda abune wanda bata taɓa zato ko tsammani ba, tasan tabbas Raleeya bazata taɓa yi mata wasa ƙo ƙarya akan irin wannan babban al'amarin ba. Samun kanta tayi itama da fashewa da kuka, kasa cewa komai tayi, haka tayi wurgi da wayan nata, da gudu ta nufi falo inda Dr Adnan ke zaune. Tana isa falon kuwa ta faɗa jikinsa, tare da sakin wani sabon kuka. Hankalin Dr.Adnan ne ya tashi, ɗagota yayi cikin kulawa yace. "Subahanallahi lafiya kuwa me ya faru?"











By

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login