Showing 180001 words to 183000 words out of 239422 words
Chapter 61 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
musulmai irinsu masu tasowa suna ganiba, wanda ya zama dole atsaya akansu gudun lalacewar tarbiyarsu da rayuwarsu."
Cike da tashin hankalin fahimtar abunda Saifuddeen din ya faɗa yasa.
Baban khamis zare hular dake kansa, ya somayi wa fuskarsa fifita, fuskarsa ɗauke da tsananin kaɗuwa da damuwa haɗi da tashin hankali ya dubi Khamis, wanda tuni jikinsa ya fara jiƙewa da gumi, sosai tsoro da rashin gaskiya suka bayyana ƙarara akan fuskarsa,
cikin tashin hankali Baban nasa yace. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, ya Allah ka dubemu da idon rahama lallai nasan tabbas kowa da irin jarabawarsa arayuwa, ya Allah kada ka jarabcemu da lalacewar tarbiyar ahlinmu ta hanyar aikata al'fasha ko wanne irine, tunda nake ban taɓa aikata zina ko fasikanci ba, haka ma kuma sam koda ina ƙiruciyata bana kula mata, har izuwa yanzu kuwa na tsare mutumcin kaina,
Khamis kai ɗayane ɗana dana haifa aduniya, hakanne yasa na baka kulawa da duk wani gata, saboda rayuwarka tayi kyau ta inƙamta, yanda kowa zai amfana dakai gaba bawai inai maka gata dan lalata rayuwarkaba, ashe abun da kuke aikatawa kenan, ashe neman mata kakeyi Khamis da ƙananun shekarunka, so kake ka tozartani ko, ban taɓa tunanin haka daga gareka ba Khamis, ashe nuna maka gata, zai iya zama silan lalacewar rayuwarka."
Hawaye ne suka cika idanun Baban Ƙhamis ɗin, wanda hakan yasa gaba ɗaya jikin Khamis yayi sanyi, take shima hawaye suka cika idanunsa, kansa ya ɗan soma jujjuyawa cikin muryarsa da tayi sanyi yace.
"Dan Allah Baba kayi haƙuri, wallahi ni sau ɗaya ne ma na taɓa yin lalata da yarinya ɗayace , kuma ma daganan ban ƙara ba, kuma nan ma yarinyarce take ta bina, bani kuma na nemeta ba, dan Allah Baba kayi haƙuri, Allah bazan sake ba."
Hayatuddeen kuwa can gefe ya koma tuni zufa ya keto masa, narai narai yayi da idanunsa, cikin tsoro yace. "Nikam ma wallahi ban taɓa aikata zina ba, na rantse da allah da Manzonsa ko hannun mace wallahi ban taɓa riƙewa ba, Khamis shima shaidane ban taɓa riƙe hannun wata mace ba wallahi."
tuni hawaye sun cika idanunsa, wani irin tsoro da fargaba haɗi da matsanancin takaicin kansa da kuma nadama ne ya cika zuciyarsa. Kai Baban Khamis ɗin ya jinjina, cike da alhini da kuma tsoron abun da ɗan nasa ke aikatawa, tabbas yasha mamaki ƙwarai, dan ko kaɗan bai taɓa kawo aransa cewa Khamis ɗin na bin mata ba, kuma wai harma zina ya taɓayi, jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, haƙiƙa Saifuddeen ya taimakesa, da bai ɓoye masa abun da yaran ke aikatawa ba, duk da cewa kuwa harda ƙaninsa aciki, yayi mamakin halin ɗan nasa ƙwarai, saidai kuma amma yasan cewa babu irin jarrabawan da Allah baya bawa bawansa, wasu tasu jarrabawan akaran kansu ne, wasu kuwa akan ƴaƴansu aka jarrabesu, kowa dai da irin nasa, tabbas basai ka kasance fasiƙi ko mazinaci Allah zai jarrabi ƴaƴanka ba, ita jarabawa da ƙaddara Allah kan ɗaurawa duk wanda yaso. Hawayen da suka cika idanunsa yaɗan share, cikin sanyi ya dubi Khamis da Hayatuddeen tare dayi musu alaman su ƙaraso gabansa yanason ganinsu, jiki asanyaye kuwa suka rarrafo kusa dashi, Khamis kam dan tsoro haka yakejin kaman ƙirjinsa zai fito waje. Cikin kulawa haɗi da sanyin jiki yace.
"Da forko dai Khamis nida kaina zan kaika ayimaka Hukuncin Allah kaida yariyar ayi muku bulalin haddi, kana tayi istibira'i, kuma in aura maka ita in ta kasance mai yin tuba na gskya."
Shiru ya ɗanyi ganin yadda Khamis keta gyaɗa mishi kai alamar to ya yarda, jiki a mace yaci gaba da cewa.
"Ku yarane wanda asannu watarana zaku zama iyaye, shin alokacin da kuka kai munzalin zama iyaye, idan kuka kama ƴaƴanku suna aikata irin abun da kuke aikatawa ayanzu ya zakuji acikin ranku? shin kuna ma da tunanin cewa ayanzune ya kamata ku inganta rayuwarku?
Nasha mamaki ƙwarai Khamis, ace kana matsayin ɗana kake aikata zina, har kana faɗi da bakinka cewa wai sau ɗaya kataɓa yi? kasan girman zina kuwa Khamis? kasan girman laifin zina kuwa? Kasan hukuncin zina kuwa? to wallahi kasani mazinata ko alahira wutarsu daban ne, ko kuma saboda kana ganin kai kaɗaine baka da ƴa baka da ƙanwa, kai kuma Hayatuddeen kana ganin cewa baka da ƙanwa, shiyasa kuke aikata abun da kukeso ko, haƙiƙa idan mu bama ganinku Allah na ganinku, kuma kome kuka aikata na zunubi sai an rubuta muku shi acikin littafinku, sai kuma Allah ya tambayeku akan hakan, kusani jin tsoron Allah shine gaba akan komai, yau idan akace baku da wani ginshiƙi me tsaya muku arayuwa, zakusha wahala, domin wannan halin naku da kuka ɗauko, bazai taɓa bari kucimma nasara arayuwarku ba, musamman ma kai Khamis, wanda wuyanka yayi kauri, har kayi riƙan da zaka iya aikata zina, wallahi wallahi rayuwar mazinaci ko mazinaciya baya al'barka, sannan komai nasu bashi da al'barka, kama daga kan dukiya da duk wani abun da suka mallaka, yanzu Khamis da wani ido kakeso na kalli mahaifiyarka nace mata ɗanta wanda har kusan rasa ranta tayi, wajen ƙoƙarin haihuwarsa mazinaci ne, kanaga akwai wani farinciki ko soyayyarka da zaiyi saura azuciyarta? Sabida gudun lalacewar tarbiyar ka yasa mukaƙi barinka ka tafi karatu ƙasashen turawa, ashe bamu saniba tana ƙasa tana dabo wai sai wanda yaje yayi karatu a ƙasashen woje ke lalacewa ba." Kuka Khamis ya fashe dashi me tsuma zuciya, wanda hakanne yasa Hayatudeen ma fashewa da kuka.
Kai Saifuddeen ya girgiza, cikin takaicin rayuwar da ƙannen nasa suka jefa kansu aciki, ƙazamar rayuwa marar ɓullewa.
Saida sukayi kuka sosai, kafun Baban Khamis ɗin yayi musu faɗa sosai, tare dayi musu nasiha mai ratsa jiki, wanda yasa atake sukaji duk sun tsani wayoyinsu ma, balle kuma akai ga kallace kallacen batsa da sukeyi.
Sosai kuwa Baban Khamis yayiwa Saifuddeen godiya, dan yaji daɗin zuwan Saifuddeen ɗin, saboda yayi imani badon shi ba, da Khamis ɗinsa zai jima yana aikata aikin ashsha, wanda bazai tashi ganewa ba, sai lokaci ya ƙure masa.
Haka dai suka ɗan taɓa hira da Baban Khamis ɗin, bayan sun sake yiwa yaran faɗa sosai, Khamis kam yasha kuka, musamman ma da Hamma Saifuddeen ɗin ya ƙara tunatar dashi, girman laifin Zina, da irin hukuncin da za'aiwa wanda ya aikata ta, yayi kuka sosai kuma yayi nadama ƙwarai, gaba ɗaya haka yaji ya tsani abokansa wanda su suka fara ɗorasa ahanyar, har shime yake ƙoƙarin ɗora Hayatuddeen, duk dama shi shaida ne kan cewa Hayatuddeen bai taɓayin zina ba, hasalima baya taɓa shiga sabgan ƴan mata, baya kula wata mace ko ɗaya.
Haka dai sai kusan sallan jumma'a, kafun su Hamma sukayi yunƙurin barin gidan.
Nan Baban Khamis ke ƙara yiwa Saifuddeen ɗin godiya, tare da cewa. "Ya bashi amanan Khamis ya kula masa dashi."
kasancewar Khamis ɗin bashi da ɗan uwa ko ƴar uwa, shi kaɗai ne awajen su, saboda haka bayansu babu wani mesanya idan akanshi, wanda babansa kuma ɗan kasuwa ne, da kuma siyasa, hakan yasa baya yawan zama agida, mamansa kuwa babbar ma'aikaciyar banki ne, itama bawai ta cika zama agida bane. Saifuddeen yaji daɗin hakan kuma ya amshi, amanar da Baban Khamis ɗin ya basa, hakanne ma yasa koda suka tashi tafiya.
Khamis ɗin yace zai bisu, suje masallaci, dan dama daga nan gidan su Khamis ɗin masallacin jumma'a zasu wuce. Direct kuwa daga gidan su Khamis ɗin, Buba Yero Central Mosque suka nufa, wato masallacin sarki kenan. Koda aka idar da sallan jumma'an, ba gida suka nufa ba, can ƙungiyar su Saifuddeen na Jonapwd suka nufa, anan cikin mota Saifuddeen ya barsu, shikuwa ya shige wajen amininsa Ishaq, sosai suka sha hira, anan ma sukayi sallan La'asar, daga nan ne suka biya suka sauƙe Khamis agida, su kuma suka wuce gidan Adda Rahma hira sosai sukayi ta ƴan uwan juna, Dr Adnan da Saifuddeen suna falo sunata hira, nan Ya Adnan yake tuntuɓarsa batun komawarsa India, dariya ya ɗanyi tare da mishi alamun, shifa ya worke.
Adda Rahma kuwa da Hayatuddeen kitchin suke, gaba ɗaya gidan ya cika da ƙamshin zazzafan gashin kaji da Adda Rahma keyiwa Umminta duk bayan wani lokaci.
Koda ta gama a kula ta juyesu da zafinsu sunata turiri, kana ta sawa auta kura a filet, ya fita falo yanaci yana sjishita.
Ita kuwa Adda Rahma sanin Saifuddeen baya cin kazane, yasa ta zaro dangwaleliyar zabuwa a firijin, wonke zabuwar tayi a gudarta ba tare da ta yayyanka kataba ta sata cikin tukunya, wadataccen al'basa ta yanka ta zuba a kai kana ta watsa tafarnuwa akai, maggi da time da corry ta yaryaɗa, kana ta ɗebi dakekken citta da kanamfari ta yayyarfa dai-dai misali, sannan ta rufe ta ɗaura a huta, attaruhu da al'basa da tafarnuwa ta jajjaga mai rai da lafiya, wani irin fitinenne ƙamshi ya cika side ɗin nata gaba ɗaya, har zata ɗaura wata tukunyar jin kiran da Ya Adnan ɗinta ke mata yasa ta fito da sauri,
Ganin Hayatuddeen a tsayene yasata cewa.
"Ina zuwa?".
Saifuddeen ne ya mata alamar.
"Zamu tafi gida lokacin salla ya ƙara to".
Kai ta juya tare da nunawa Hayatuddeen kujera kana tace.
"Koma ka zauna bari in gasa mishi zabuwa nasan baya cin kaza".
Zama yayi tare da cewa.
"To amman dai hardani a zabuwar ma ko?".
Ya Adnan ne yayi dariya tare da cewa.
"Kai Auta wai kai baka gajiya da namane".
Da sauri ya gyaɗa kansa alamar eh,
Saifuddeen kuwa, hannun Adda Rahma ya kama tare da mata alamun ta bari karta damu ta sani shi ba wani damuwa da nama yakeba".
Kai ta juya tare da cewa.
"Bana son gardama Saifuddeen ku jira yanzu zan gama".
Baya iya mata musu shiyasa yace to.
Cikin awa ɗaya da ƴan mintuna tayiwa zabuwar nan wani irin fitinenne gashin tukunya mai ɗan karen daɗi da azabar ƙamshi,
a wata kekyawar kula ta saka mishi ita da zafinta sai tururi takeyi,
ta fitowa ta miƙawa Hayatuddeen tace.
"Gashi wannan kuna komawa ka kai mishi ɗakinshi, ga madarar shanun shima ka kai mishi, bance da kaiba a zubuwar da madarar uban ciye-ciye".
Tura baki yayi tare da cewa.
"To ni dai gsky ki bani mgnar rabona in ba haka sai nasha nashin."
Dr Adnan ne yayi dariya kana yace.
"Ɗauko mishi gora ɗaya".
Jin haka yasa ta ɗauko mishi ai da murnarshi ya amsa ya fita kana suka bishi a baya suna dariyar sangarcin autan Ummi saida Saifuddeen ya shiga gidan Baba Bello ya gaidashi kafin suka shiga mota suka wuce gida.
Acan gida kuwa, gaba ɗayansu zaune suke afalon Ummi, Zaleeha wanda gama girkinsu yasa taje tayi wanka, wani sabuwar shiga ta sanja, inda tasha kyau cikin wata tighty gown sky blue me kyau, sosai tayi, kyau yayinda ta tubke gashinta ta bar jelanshi sake , hakan yasa ta zama kamar wata ba india.
Zaune take agefen Raleeya yayinda taɗan jingina kanta da kafaɗan Raleeyan daketa kitse mata jelan gashin yana kuma koncewa sabida santsinshi kuma ba iya kitson tayiba,
sai kuma Adeel dake gefenta yana ta wasan sa,
shigowarsu cikin falonne yasa taɗan yunƙura tare da matse jikinta waje ɗaya, kasancewar babu mayafi akusa da ita, sam kuma batayi tunanin dawowarsa yanzu ba. Ƙarasowa cikin falon yayi,
Ameena dake zaune ne ta sakar masa murmushi, shima murmushin yayi mata tare da lumshe mata ido, cikin nutsuwa ta miƙe ta ƙarasa gaban fridge inda ta ɗauko masa lemo maisanyi, karɓa yayi yaɗan sha, sannan ya juya ya ya karɓi kulan zabuwarshi da madararshi dake hannun Hayatuddeen kana ya juya ya koma part ɗinsa, dan yanaso yaɗan watsa ruwa.
Raleeya kuwa kitchine ta shiga, inda ta haɗo musu fruit salad wanda ta cika madara acikinsa, Kaɗan Ameena tasha dan ita haka take kayan fruits basu wani dame ta ba kayan zaƙima duka bai dameta ba.
Zaleeha kam dama abincinta ne, saboda haka sosai tasha, ɗago idanu tayi ta kalli Hayatuddeen wanda gaba ɗaya yazama wani silently dashi, da duk kan alama akwai abun dake damunshi, hakanan taji duk ba daɗi, saboda tasa aranta damuwar Hayatuddeen damuwarta ne, tashi tayi daga zaunen da take, tare da ƙarasawa kan kujeran da yake zaune, zama tayi gefenshi, cikin kulawa tace.
"Sweet bro me yake damunka? ko baka da lafiga ne autanmu?." Ɗan ɗagowa yayi ya kalleta, asanyaye ya jingina kansa da da jikin kujera.
Yana jin yadda ƙirjinsa ke bugawa, wani irin tsoro yakeji, yasan idan Hamma ya faɗawa Ummi halin da yake ciki, zatayi fushi dashi sosai, shi kuma tsoron hakan yakeji, gashi kuma yaga Hamman nasa ma, bawai ya sake dashi bane, ganin yanda ya marairaice fuska yasa Zaleehan ɗan gyara zama ta fuskanceshi da kyau, ahankali ta miƙa masa cup ɗin fruit salad din dake hannunta, babu musu kuwa ya amsa ya sha, cokali huɗu kawai, ta ɗan hararesa tare da cewa.
"To ya isheka haka malam, dan naga alaman idan na biyeka zaka shanyemin."
Dariya sukayi gaba ɗayansu, miƙewa tayi, tare da ɗaukan Adeel, ɗayan hannunta kuwa bowl ɗin fruit salad ɗinta ne, wanda bata gama shanyewa ba, zata je ta sanya acikin fridge. Kaitsaye part ɗinta ta nufa, nan cikin firdge ta sanya bowl ɗin fruit ɗin, sannan ta ajiye Adeel akan gado, jin anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba ne, yasa taje ta ɗauro al'wala, koda ta fito daga toilet ɗin sallaya ta shumfuɗa tare da tada sallah.
Tana idarwa kuwa taji anayi mata knocking ƙofa, tana buɗewa kuwa ta ga Ameena ce tsaye cikin shirinta na zuwa wajen aiki.
Ɗan faɗaɗa murmushin kan fuskarta tayi tare da cewa. "Ummu Adeel har kin shirya."
Murmushi itama Ameenan tayi tare da cewa.
"Eh wallahi, kinsan idan na tsaya saina makara, ni kuma banason makara wallahi sam, ina Adeel ɗin yake sarkin son jiki, yazo na goyashi".
Murmushi Zaleeha tayi, tare da komawa cikin ɗakin ta ɗauko Adeel ɗin, miƙawa Ameenan shi tayi, tare da cewa "Gashinan ai sai wasan sa yake tayi abinsa."
Karɓansa Ameenan tayi tare da goyasa, sai wutsil-wutsil yake wai shi adole wajen Amminsa zai zauna, har bakin ƙofa Zaleehan ta rako Ameena, tare dayi mata adawo lafiya, da "Ameen." ta amsa, sannan ta juya ta koma ciki.
Zama tayi akan sallayan tana ɗan addu'o'i, tana nan azaune kuwa har aka ƙira sallan isha.
Tana idar da sallan kuwa ta wuce sashin Ummi, nan kan dining ta taradda Saifuddeen, da kuma Hayatuddeen ɗin azaune, sai kuma Ahmad, shigowarta yayi dai-dai da fitowar Ummi daga ɗaki, ƙarasowa tayi cikin girmamawa tayiwa Ummin
"Barka da dare." fuska asake Ummi ta amsa mata, sannan suka zauna akan dinning table ɗin.
Raleeya ne tayi seving ɗinsu, nan suka fara cin abincin cikin nutsuwa. Bata wani ci abincin mai yawa ba, dan ta ƙosa da irin kallon da Saifuddeen ɗin keyi mata, gaba ɗaya jinta take wani iri, kuma dama bawai yunwa takeji ba, dan tasha fruit salad, kuma shi kaɗai ma ya ƙosar da ita, miƙewa tsaye tayi tana goge bakinta, dubanta Ummi tayi tare da cewa. "Zaleeha ya kika tashi, badai kin ƙoshi ba." Kanta ta jinjina tare da cewa.
"Eh Ummi naƙoshi sosai, kinsan ɗazu munsha fruit salad, kuma ma inaso ne naɗanyi aiki a system ɗina."
Kai Ummi ta jinjina cike da gamsuwa tace.
"To masha Allah, ayi aiki lafiya, Allah ya tashemu lafiya."
da "Ameen" ta amsa, , cikin kulawa tace.
"My Autan Ummi good night da safe zamuyi magana kaji."
Kansa ya jinjina mata yana murmushi, duban Raleeya da Ahmad tayi, tare dayi musu saida safe, fuska asake duka suka amsa mata, sannan ta fice daga cikin falon, kaitsaye ɗakinta ta wuce.
Su kuwa cikin nutsuwa suka kammala cin abincinsu, Hayatuddeen ne ya soma ƙoƙarin tashi tsaye, hannunsa Ummi ta kamo tare da zaunar dashi, ɗago idanunsa da sukayi rau-rau dasu yayi ya kalli Ummi'n, wanda tun ɗazu kunyan kallonta yake, idanu Ummi ta zuba masa, tare da ɗan watsa masa harara, cikin bayyanar masa da ɓacin ranta dan shi baida nitsuwar Saifuddeen shiyasa bata mishi irin Hukuncin da takewa Saifuddeen wanda shi da idoma yakan ɗimauce in tana hukuntashi da kallon tuhuma, to shi autanta yafi