Showing 48001 words to 51000 words out of 239422 words

Chapter 17 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11859

isowa cikin garin Numan, kai tsaye bakin kogi ya nufa, wato gidan Yayan Maman nasu, cikin sa'a, kuwa yana kaiwa kusa dagidan, yayi kiciɓus da Unlce ɗin nasu, fuska ɗauke da mamaki solomon ya tarbi Habu, gaisawa sukayi inda Ya habu yayi masa bayanin abun daya kawosa, sosai Solomon yasha mamakin yanda akayi suka san da cewa, Zaleehan na wajensa, don kuwa Mama tafaɗa masa cewa babu wanda yasan Zaleehan na wajensa, domin cewa dashi tayi ya ɓoye mata Zaleeha'n, ganin cewa sun gano cewar tana wajensa ne yasanya sa jin cewa bashida zaɓi, wanda ya wuce barin Habun ya gana da ita.
Shine agaba yayinda habu ke binsa abaya, haka suka shiga cikin gidan.
Zaleeha dake zaune atsakar gidan, jin motsin shigowar mutum cikin gidanne, yasa Zaleeha ɗago kanta, wani irin faɗuwar gaba ne da matsanaicin tsoroya ne risketa, azabure ta miƙe daga zaunen da take, tare da sanya hannu ta dafe ƙirjinta, hakan yafarune sakamakon ganin Ya Habu da tayi.
Wani irin mugun harara mai cike da tsana Ya Habu ya watsa mata, tare da ɗaure fuskarsa ta mau.
Ganin haka yasa ta sadda kanta ƙasa, sosai ƙirjinta ke bugawa, wani irin masifaffen tsoro haɗi da fargaba ne, suka cika zuciyarta, sosai tacika da mamakin ganin Ya Habun, don sam bata taɓa zaton cewa zasu san inda take ba, kujera Ya Habu yaja ya zauna, sake haɗe fuska yayi, tare da watsa mata harara, murya adake yace.
"Ba zama nazo yi ba, maza kishiga ciki, duk wani abu da kikasan mallakin Saifuddeen ne, ki fitomin dashi, idan ba haka ba kuma na tattakaki awajen nan!."
Saida cikinta ya bada wani sautin ƙuuu, domin kuwa tsawan da ya daka mata bana wasa bane.
Da sauri ta juya inda tashiga cikin ɗakin, jikinta na rawa da tsuma, zamewa tayi ta zauna daɓas aƙasa, sam takasa koda kyakkyawan motsine, tsoro takeji sosai, hakanan zuciyarta ya shiga, bugun no stop, hannu tasa ta dafe dai-dai saitin ƙirjinta, dake bugawa sabida a fili ta hango tsanarta a idanun ɗan uwan nata.


Shiru-shiru Ya Habu dake jiranta, yaga har yanzun bata fito ba, hakanne yasa shi fusata nan ya kutsa kansa cikin ɗakin, ganinta azaune ya sashi buga tsaki, nan ya shiga wargaza gaba ɗaya kayanta,
iya abunda ya sani wanda akayi mata na gidane kawai ya barmata gaba ɗaya akwatunan da tazo dasu ya buɗe, wanda ke cike da sabin kaya, nan yaja akwatunan ya rufe,
duk wani abu dayasan sabo ne wanda yake da kuɗin Saifuddeen aka saya saida ya tattare ya fiddasu tsakar gida, dubanta yayi cikin tsawa yace.
"Bani makullin motar Saifuddeen wanda kika taho dashi, banza marar kunya, wanda batasan darajar kanta dana iyayen ta ba hegiya mai fuskar yahudu da nasara bakya son mutun amman kina son kayanshi."
Kanta ta sadda ƙasa, lokaci ɗaya taji hawaye sun cika idanunta, tsawa ya sake buga mata tare da cewa.
"Zaki bani ne ko kuma saina rabaki gida biyu!!!."
Azabure tatashi inda ta ƙarasa wajen da ta aje makullin motar, da sauri ya sunkuyo ganin harda ATM ɗinta a wurin gaba ɗaya ya kwashe komai haka ya dinga jidon kayan yana sawa a motar, saida ya rabata da fiye da rabin kayan da tazo dashi gaba ɗaya, akwai sabuwar laptop ɗinta ƙiran companyn apple daya gani awajenta, shima saida ya ƙwace.
Saida ya gama kwashe komai sannan ya dubeta, cikin takaicinta yace.
"Kinzaɓi barin ƴan uwa da mahaifanki, akan wani banzan dalili naki wanda bashi da ƙarfi ko, good kamar yanda kika gudu da ƙafafunki, kika kuma tozarta Baba Malam, bazamu taɓa buƙatarki ba, duniya ce ae kuma gaki acikinta, saboda haka kisha zamanki ki huta cikin arnatakun, babu wani wanda zai sake nemanki, haka babu wani wanda zaizo gareki da sunan maidaki gida, in kin ga dama ki riƙe Allah da addininki in kuma kinga dama ki koma zuwa coci da cin aladu da karnuku tunda baki godewa Allah da ni'imar da ya mikiba!."
Yana gama faɗan haka, ya juya yafice daga cikin gidan, motar ya shiga inda yayiwa Uncle ɗin nasu bankwana, ko mintuna 4 bai ƙaraba yayiwa motar key tare da barin ƙofar gidan.
Kaitsaye ya ɗauki hanyar komawa cikin garin Gombe.


Zaleeha kuwa ɗaki ta koma, inda ta faɗa kan gado, cusa kanta acikin pillow tayi tare da sakin kuka, wanda ita kanta batasan kukan na miye bane, hakanan takejin wani ƙunci acikin ranta, tabbas tanajin cewa tsanar Saifuddeen bazai taɓa gushewa acikin ranta ba, saboda duk asanadinsa tabar ƴan uwanta yayunta ƙannenta da mahaifanta, danginta aikinta har yanzu kuma tana kan bakanta na cewa bazata taɓa zama dashi ba.
Kuka sosai tayi, sabida ya Habufa ya kwashe mata rabin jin daɗinta,
tunowa da kuɗin data haɗa ta irga jiya da dareta ajiyesu ƙasan pillow'nta ne yasa tayi sauri tashi ta ɗaga pillow ganin suna nanne yasata jin sanyi a ranta, a fili tace.
"Alhamdulilla Ya Habu mugu harda ɗaukanmin ATM to zanyi mgninka ai bari in samu caji zan yakeshe kuɗin kab in maidasu asusun Mama ko na Bilkeesu."
abinda Zaleeha bata saniba tuni Habu yaje cikin numan ya yashe mata account.
Dan ba wani abundan bai saniba na sirrin ƙannen nashi.


Sai dare Ya Habu ya samu isowa garin na Gombe, nan ya damƙawa Baba Malam ɗan makullin motar, sannan ya nuna masa duk wani abu daya ɗauƙo, sosai Baba Malam yaji daɗin hakan, nan ya sallami Habu inda yace gobe da safe zai je har gidan su Saifuddeen ɗin.


Washe gari kuwa da misalin ƙarge goma Baba Malam ya shirya tsab don zuwa gidan su Saifuddeen, bayan yasa Ya Habu yayi gaba da motar da suka amso awajen Zaleeha'n, Shida Ya Ameenu suka fita inda Ya Ameenun ne keyi musu driving, kai tsaye gidan Dirankaɗi suka nufa, wato gidansu Ishaq, kasancewar tun jiya Baba Malam ya ƙirasa sukai magana, akan hukuncin da ya yanke, koda yaje ɗaukan Dirankaɗi'n sukayi, nan suka nufo cikin federal low cost, wato unguwar su Saifuddeen, koda suka ƙaraso Ahmad ne yayi musu jagora har zuwa babban falon Ummi. Inda
Ummi da Saifuddeen ke zaune.


Cikin girmamawa haɗi da mutunta juna suka gaisa. gayara zama Baba Malam yayi inda yasake basu haƙuri akan abun daya faru, sosai ya basu haƙuri, hakanne yasa har Ummi saida taji kunyar haƙurin dayake ta basun.
tace mishi ba komai komai ya faru yine na Allah.
haka dai ya koma gida jiki a mace.


Yau kusan sati uku kenan da guduwan Zaleeha,
tunda aka gane inda take hankalin kowa ya konta.
Amman banda Baba Malam yawanci yakan zauna yana nazarin me zaiyiwa Saifuddeen ya huce mishi baƙin cikin da ƴarsa ta cusa mishi,
a cikin hakanne ya nazarto wani matakin da zai ɗauka.


Saifuddeen kuwa gaba ɗaya hankalinshi na kan shige da ficen Dalla ne,
dan yadda zai samu kamashi cikin laifi dumu-dumu,
yayinda shima Dalla ya fahimci akwai mai bibiyarsa da bin diddiginshi,
shiyasa ya sauya salo da tsarin fajircinshi dan ya sake barin gombe ma sabida ya gane ana gab da kamashi kuma binshi akeyi dan a samu kwakkwaran hujjar kamashi.


Ummi kuwa tana yawan tuna Zaleeha dan ita kam har ga Allah tana son ƴarinyar, sabida ita dai bazata ce ga wani mugun abu ko raini data daɓa yi mataba cikin kwanakin da suka zauna tarenba,
asalima ta fahimci yarince mai biyayya da tarbiya da iya zama da mutane.


Hayatuddeen kuwa yaci gaba da zuwa makarantarshi sabonshi da Khamis yanata ƙaruwa.


Amina kuwa da Asma'u har gobe suna dakon soyayyar Saifuddeen a ransu,


A hankali ya gama kimtsa kanshi cikin wani tattausan yadi mai azabar kyau da taushi yadin farine ƙal-ƙal sai ɗigo-ɗigon bulu mai haske,
an mishi ɗinkin mai kyau dai-dai da jikinsa an ɗan tattarfa surfanin bulu a aikin rigar,
hular kanshi fara mai ratsin bulu,
kana sai takalmansa sau ciki mai kalar bulu sai igiyansu daya kasance farare.
Manyan idanunshi ya buɗe tare da kallon fuskarsa a madubin jikin durowar tashi,
a hankali ya fidda sassanyan numfashi tare dasa tattausan tafin hannunshi ya shafa sajenshi da ya kwanta lib yayiwa fuskarsa ƙawanya,
lips ɗinsa ya ɗan tsotsa tare da turosu gaba,
wayarshi ya ɗauka ya da niyar zurata a aljihun gaban rigarshin sai yaga shigowar saƙo,
Ganin Bappa Aline ya sashi buɗe saƙon.
"Sallamu alaikum, Saifuddeen ka cewa Umminku yau ina kan hanya nida Malam Ashiru, dan surkinka yace yana buƙatarmu, to yanzuma muna tahowa,
yace kuma zaizo har gidan ya samemu,
to nayi ta kiran wayan Unminka bata shiga."
Idanunshi ya ɗan lumshe tare da buɗesu a ranshi yace.
"To wai meyasa Baba malam ya kasa kontar da hankalinshi ne a kan batun wannan fitinanniyar yariyar tasa,
infa har yazo yau to zuwansa na uku kenan yana bamu haƙuri."
Kai ya ɗan jujjuya kana ya rubutawa Bappa Ali amsa ya tura mishi.


Daga nan ya zura wayar a al'jihunshi kana ya fice ya nufi side ɗin Ummi.


Shiru falon ba kowa dan haka kai tsaye ya wuce bedroom ɗinta,
kan sallaya ya sameta bisa dukkan alamu tayi walahane,
shiru yayi yana kallon yadda ta ɗaga hannayenta sama tana kwaranyo musu addu'o'i shida ƙannenshi, wanda mafi yawan addu'ar a kanshi ne a hankali take cewa.
"Ya Allah ga bawanka Saifuddeen cikin matsalolin rayuwar daka jarabceshi, ya Allah ina mai roƙa masa sassauci da salama da sauƙi a rayuwarshi ta duniya da lahira.
Ya Allah ka yaye mishi duk wani cuta dake jikinshi ka bashi lfy ka ƙaddara mishi sake miƙewa saye da sawunshi da sake mgna da ji,
Ya ubangijin talikai ka yassare masa ƙofofin samunshi gabas da yamma kudu da arewa, ya Allah ka al'barkaci kasuwancinsa ka tsare minshi daga sharrin mahassada damasharranta tsakanin mutun da al'jan, ya Allah ka tsare min imaninshi ka bashi ikon cinye jaraboɓunshi."
Sai ta kuma ƙara ɗaga hannu cikin kushu'i da ƙanƙan da kai take cewa.
"Ya Allah kayi mishi zaɓi mafi al'khairi tsakaninshi da matarsa Zaleeha in ita al'khairinsace Allah ka bashi haƙuri da juriyar duk wani abinda zai faru daga gareta, in kuma ita ba al'khairinshi bace, ya Allah ka musanya musu da abinda yake al'khairi a garesu baki ɗaya. Ya Allah ka karemin surkata a duk inda take."
sosai Saifuddeen yake wani irin lallausan murmushi yayinda shima ya ɗaga hannayenshi sama yana mai amsa cikin ransa da .
"Amin Amin. Ameen ya rabbil izzati ya Ummi."
sosai ya tsura mata ido likacin da take cewa.
"Ya Allahna ga ɗana Hayatuddeen cikin ganiyar ƙuriciya da tashen balaga ya Allah ka shirya minshi ka tsare minshi, da tarbiyarsa ka kare min imaninshi ka sa mishi nitsuwa da kamala kwatan-kwacin na ɗan uwanshi, ya Allah ka yaye mishi wannan rawan kan da gigin ƙuruciya".
Sosai yake Murmushi Allah sarki Ummi wato rawan kan Hayatuddeen na tsoritata.
numfashi ya sauƙe a hankali ganin tana cewa.
"Ya Allah ka al'barkaci ahlina ka shirya minsu dama dukkan al'ummar musulmai ka azurta ɗiyata Raliya da samun haihu da ƴaƴa na gari ka basu zaman lfy da mazajensu."
Haka dai tayi ta musu addu'a yana mai amsawa da amin.
A tare suka shafa addu'an,
kana ta juyo ta fuskanceshi da kyau cikin sakin fuska tace.
"Dama kana gidane!."
Kai ya jinjina mata tare da mata bayanin zuwan bappa Ali da Baba Malam,
ya ƙara da cewa Bappa Ali yace sun tasoma dan haka zai jirasu kawai.
kai ta gyaɗa tare da miƙewa ta cire hijabin jikinta tana mai ninkewa take cewa.
"Eh lallai Faroq ya ɗauki wayar yana game to inaga ya gama da cajinta ne ,
dan naga yazo ya sata a cajin.
jin haka ya ɗan juyo ya jawo wayar dake haɗe a caji nan kuwa ya samu a kashen take.
juyawa yayi ya fito falon Ummi na biye dashi a baya tana gyara mayafin jikinta.




Suna zama ba jimawa kuwa su Bappa Ali suka iso.
suna cikin gaggaisawa ne Baba Malam da Malam Adam da Dirankadi suka iso bisa jagorancin Ahmad wanda yanzu ya dawo gida dan kiran bappa Ali daya samu.




Falon shiru bayan duk sun gama gaggaisawa,
A hankali Ummi ta miƙe da niyar basu wuri a matsayinsu na maza kuma manya su tattauna komai tsakaninsu,
sai kuma ta koma ta zauna jin Baba Malam yana cewa.
"Uhummm Ummin Saifuddeen zauna, akwai mgna mai mahimmancin da nake son muyi ne."
shiru tayi cikin jin tausayin mutumin wato wannan shine ɗan kuka mai jawa uwarsa jifa."
Duk shiru sukayi suna sauraranshi.
Shi kuwa gyara zama yayi cikin nitsuwa da cikar kima yayi gyaran murya tare da cewa.
"Da forko dai zan fara da baku haƙuri akan rashin ɗa'a da Zaleeha tayi mana baki ɗayanmu,
wanda nake zargin kaina da cewa duk nine sila, tunda ku dai kun so'a janye batun auren tun kafin ayi auren, ni na kafe nace ayi sabida zatona itama irin Maryam ce in anyi auren zatayi biyayya ta zauna ɗakinta, amman sai gashi ta samu asarar lokaci da dukiya da mutuncina ta gudu ta watsar da auren."
shiru yayi sabida yadda Bappa Ali ya fuskanceshi tare da cewa.
"Dan Allah na roƙeka Malam Bashiru ka daina bamu haƙuri da ɗaurawa kanka wannan laifin,
Wannan aurefa nufine na Allah, Allah ne ya ɗaura aurennan kafin mu muka ɗaurashi, kuma har gobe muna kyautata zaton zata dawo ɗakinta ta zauna."
Malam Ashiru ne ya amshi zancen da cewa.
"To mun isa muja da ikon Allah ne, babu laifin kowa a cikinmu, da Allah malam Bashiru ka daina tada hankalinka kam zancen yarannan."
ita dai Ummi shiru kawai tayi,
Saifuddeen da Ahmad shirun sukayi.
Sai kuma Dirankadi da Malam Adam ne suka ƙara kwantarwa Baba Malam hankali kan dan Allah kada ya sake zuwa da batun badu haƙuri.
Cikin jin sanyi a ranshi ya kallesu baki ɗaya kana ya fuskanci Saifuddeen da kyau cikin sanyi yace.
"Dan Allah Saifuddeen ina neman wata al'farma a wurinka."
da sauri Saifuddeen ya nuna kanshi da ƴar yatsarshi alamun.
"Ni kuma al'farma kuma?."
Kanshi gyaɗa mishi alamun eh kai ɗin dai.
sai ya kuma gyara murya da zama kana ya kalli Ummi, Bappa Ali da kuma Malam Ashiru yace.
"Ina neman al'farma a wurin ɗanku ɗalibani kuma surkina a wani sashin kuma ɗana.
Dan Allah Saifuddeen kayi haƙuri akan duk wani abun da Zaleeha tayi maka daka riƙe igiyar aurenka da ita naroƙi al'farma a wurinka da iyayenka duk rintsi kada ka saki Zaleeha, lallai kam nasan saki halalne duk da ubagiji baya son shi, ina roƙonka da Allah da manzonsa kada kayiwa Zaleeha abinda take buru da son kayi mata ka riƙe igiyar aurenku duk rintsi, domin inada yaƙinnin wata rana zata dawo gareka."
ya ƙarishe mgnar cikin rauni da alamun neman al'farma.
Su kuwa gaba ɗaya idanu suka zubawa Saifuddeen daya fara musu bayani da yarensu na kurame wanda gaba ɗayansu suna gane hakan,
A hankali ya matso gaban Baba Malam cikin tanƙwashe ƙafafu yace.
"Baba Malam umarni zaka bani ba neman al'farma ba, in sha Allah bazan saki Zaleeha ba,
ka daina tada hankalinka."
shafa kanshi Baba Malam yayi tare da cewa.
"Ngd ngd Saifuddeen Allah yayi maka al'barka ya azirtaka da yara masu biyayya."
Amin Amin suka amsa baki ɗayansu,
Ummi kuwa sosai taji daɗin addu'arshi ga Saifuddeen ɗinta,
Shi kuwa Baba Malam kallonsu yayi baki ɗaya kana ya fuskanci Saifuddeen da kyau cikin muryar bada umarni yace.
"Maganata ta gaba ba al'farma nake nema a gareka Saifuddeen umarnune nake baka a matsayina na Malaminka kuma surkinga, ina mai baka umarni da fito da wata matar auren zan aura maka ita ko ƴar wayece ni ne nan zan auro maka ita, Saifuddeen aure za ƙarayi, a cikin watannan!."
Wani irin zabura da zare ido Saifuddeen yayi cikin tsananin mmki da kaɗuwa ya fara nuna kanshi da alamun tambaya.
"Aure kuma? Ni kuma inyi wani auren kuma, to ita Zaleehanfa, in mata kishiya."
Dirankadine yayi murmushi tare da dafa kafaɗun Saifuddeen ɗin.
Jin an dafashi ne ya sashi juyowa ya kalli wanda ya dafashin kai ya runƙa jujjuyawa jin Dirankadi na cewa.
"Haba Saifuddeen aurefa akace kayi ba yaƙiba, me na wannan firgitan da ɗimaucewa,
to kai a zatonka barinka zamuyi ka zauna ba matane?."
Kainshi ya jujjuya tare da zaro wayarshi ya fara rubutu dan yanaga kamar dai basa fahimtarsa ne.
"Baba aure kuma, ko wata ɗaya banyi da yin aureba, yaza'ayi kuma inyi wani auren,
ina da mata ai zata dawo, dan Allah baba ka bawa Baba Malam haƙuri, bazan fa iya zama da mata biyu ba."
Murmushi Dirankadi yayi tare da cewa.
"Me zai hana Saifuddeen tsab zaka iya zama da mata biyu."
Wayyo Ahmad kam ji yake tamkar ya tashi ya rinƙa taka rawa dan daɗin wannan umarni na Dottijon arziƙi Baba Malam, a ranshi yake cewa.
"Hegiya ifiritiya kin jazawa kanki kishiya,
Aure nai dai in sha Allah za'ayishi."
Ummi kam ita kanta taji daɗin wannan abu,
Yes tunda ɗanta nada lfy har yanada muradin aure ainyi kuma ta gudu asheko dole a nemo mishi wata matar.
Murmushi tayi lokacin da Saifuddeen ya juyo yake mata mgna da yarensa.
"Wai Ummi kema naga murmushi kikeyi, nifa mijin mace ɗaya ne, ta yaya zan ƙara wani auren?."
Cikin dariya tace.
"A a to ni kuma ina ruwana, ka dai ji umarni ne yace ya baka ba neman al'farmaba."
Tirƙashi wannan shine ana wata sai ga wata,
kawai shi kam Saifuddeen ido ya zuba musu ganin da gaskefa sukeyi kuma Bappa Alima yayi na'am da hakan har cewa yake.
"Ahmad kuyi ƙoƙari ku fito da matar aure dan cika umarnin surkinku, kunji dai yace nanda mako biyu yakeso ayi auren,."
Wani mugun harara Saifuddeen ya dannawa Ahmad ganin yadda yaketa dariyar jin daɗi harda cewa.
"In sha Allah kuwa, Kawu Ali zumu fito da matar, ayi komai kamar yadda malam yake so."
Shi kuwa Baba Malam cikin son kontarda hankalin Saifuddeen yace.
"Ka nemo matar da take sonka,
Ni zanyi maka komai na auren ko sisinka bana buƙata."
Shifa yanzu ganinsu yake kamar al'mara,
su kuwa nan suka gama tattauna komai.


Ganin azahar tayine yasa suka yi addu'a suka tashi a taron kana suka sallami Ummi suka fita baki ɗayansu su.
Anan matsallacin jikin gidan nasu sukayi salla kana su Baba Malam da Dirankadi da Malam Adam suka tafi.


Su bappa Ali kuwa suka dawo cikin gida sukaci abinci sannan suka ƙara jaddawa Saifuddeen batun auren sannan suka tafi.


Su Babba Ali na fita Ahmad ya kwashe da dariya harda dukan cinya cikin jin daɗi ya kalli Saifuddeen daya haɗe fuska girarshi ɗaya ya ɗaga mishi tare da cewa.
"Ya akayi ne angon mata biyu a wata ɗaya, kai Alhamdulillah lallai wannan dattijon ya cika adali mutun, kaga nanda mako biyu kana tare da sabuwar amaryarka dal a leda."
Wani irin bugu ya ya kaiwa Ahmad,
da sauri ya kauce tare da cewa.
"Sai fa an maka auren na."
Dariya Ummi tayi ganin yadda Saifuddeen ɗin ya haɗe fuska cikin dariyar tace.
"To wai duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login