Showing 57001 words to 60000 words out of 239422 words
Chapter 20 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
Malam ya sauƙe tare da cewa.
"To kamar dai yanda ka ganmu dukan mu nan al'khairi ne ya kawo mu, dan kuwa munzo newa ɗan mu auren ɗiyar ka Ameena, muna fatan Allah yasa ba ai mata miji ba."
Ajiyar zuciya Alhaji Naseer ya sauƙe, tare da ɗan numfasawa, cikin murna haɗi da farin cikin ganin manyan malamai sunzo neman haɗa zuriya dashi a hankali yace.
"Masha Allah, Haƙiƙa naji daɗin wannan zancen naku ƙwarai, sannan kuma ba aiwa Ameena miji ba, saidai kuma bazan ɓoye muku ba, magana ta gaskiya banine mahaifin Ameena ba, nine dai mariƙinta, dani da mahaifinta kuwa uwa ɗaya uba ɗaya muke, sannan kuma magana ta biyu dai ita ce, Ameena ba budurwa bace, bazawara ce, don kuwa ta taɓa aure, ta auri ɗan wajena Amir, sai-dai kuma da yake Allah bai tsara zamansu tare ba, sati ɗaya kacal auren yayi Allah ya kawo ƙarshensa, sannan ahalin yanzu dai babu wani wanda ta tsayar mazaunin wanda zata aura."
Ajiyar zuciya suka sauƙe su dukansu, cikin gamsuwa Baba Malam ya gyara zama, inda ya fuskanci Alhaji Naseer, cikin yanayin dattako yace.
"Alhamdulillah, duk da kafun muzo bamusan da wannan magana ba, koda muka jita yanzu kuwa bazaisa mu fasa niya da kuma ƙudurin dake ranmu ba, saidai kuma muma zamu faɗa muku cewar ɗan mu na ɗauke da laluri, wanda idan akayi dubida ƙaddara ce wanda zata iya hawa kan kowa, sannan kuma duk cikinmun nan babu wanda baisan cewa, Lafiya da rashinta duk na Allah bane, sannan shike sawa bawa cuta, kuma shike yaye masa, sannan lalurar da ɗan mu kedashi, bai tauyesa daga zama cikakken ɗa namiji ba, domin yana da lafiyar da zai iya kusantar mace, sannan yana da wadatar da zai iya zama da mace, saboda haka muna fatan hakan bazaisa ku hanamu ƴarku ba, saboda shi aure nufi ne na Allah, matar mutum kuma ance kabarinsa."
Bappa Ali ne ya gyara zama tare da soma yiwa Alhaji Naseer ƙarin bayani, dan gane da larurar Saifuddeen ɗin, bai ɓoye masa komai ba, ya fayyace masa komai yanda zai fahimta.
Jinjina kai Alhaji Naseer yayi tare da cewa.
"Nafahimce ku, ƙwarai kuma ai nakasa ba kasawa bace, kana nakasashshe zai iyayin abun da wani mai lafiyan ma bai iyawa, tabbas kuma idan na fahimta kune iyayen Saifuddeen ko?."
Cikin Mamaki suka kalli juna, Dirankaɗi ne yace.
"Ƙwarai kuwa, amma dama kasan Saifuddeen ɗinne?"
Murmushi Alhaji Naseer yayi inda yace.
"Ƙwarai kuwa, ai sanadiyar ita Ameenan nasanshi, don ita ta kula dashi lokacin da yayi jinya anan, sannan kuma koda suka koma india, danaje wani business ɗina naje har New Delhi na dubasa, gaskiya ni kaina na yarda da ƙwazon sa, don dagani matashi ne mai tsayayyar zuciya, tabbas wannan nakasa tasa bazata sa mu hanaku auren Ameena ba, sai-dai kuma kunsan cewa itaɗin bazawara ce, ba budurwa bace daza'ayi mata dole, saboda haka idan kunbani dama zan shiga ciki don na tambayo ra'ayi da kuma zaɓinta, sannan zan ƙira ɗan uwana awaya zan sanar dashi nasan bazaiƙi amincewa ba."
Nan su Baba Malam sukaji daɗin hakan sosai, har saida murnarsu takasa ɓoyuwa, Nan dai Alhaji Naseer ya miƙe ya wuce cikin gida, inda yace su bashi mintina kaɗan.
Acan cikin gida kuwa, koda yasamu Momma da maganar sosai tashiga mamaki, sai-dai kuma wani tunani daya faɗo ranta, hakan yasata sakin murmushi tare da cewa.
"Masha Allah, ae kuwa nasan Ameena ba zata ƙi ba, bana ƙirawo maka ita yanzun nan saikaji ta bakinta."
Nan Momma tawuce ɗakin Ameena, koda Momma ta shaidawa Ameena ƙiran da Daddyn nasu keyi mata, hakan taji gabanta yaɗan faɗi, hijab ta zura ajikinta sannan ta nufi falon.
Durƙusawa tayi agaban Daddy'n nasu, cikin rusunawa tace.
"Daddy gani."
Dubanta Alhaji Naseer yayi cikin kulawa, yayi mata bayanin komai.
Mamaki, haɗi da zallan farin ciki ne suka cika zuciyar Ameena, wannan shi ake ƙira da ƙarfin ikon Allah, haɗi da kuma falalar addu'a, tabbas ko kaɗan bata taɓa kawowa aranta cewa zata samu Saifuddeen anan kusa ba, tabbas takai kukanta wajen ubangiji gashi kuma ya amsa addu'arta, inda ya share hawayenta, alokacin da bata zata ba.
"Ameena kinyi shiru."
Maganan Daddyn ya katseta.
Murmushi tayi, cikin sassanyar murya tace.
"Idan dai har ka aminta da auren Daddy nima na amince, bani da wani zaɓi sai naka."
Farin ciki da jin daɗi ne suka lulluɓe zuciyar Daddy, nan yashiga sanya mata al'barka, inda yace tatashi taje.
Wayarsa ya zaro, inda ya ƙira Alhaji Sadam, wato Baban Ameena, koda Baban Ameenan ya ɗauka, nan Alhaji Naseer ya labarta masa komai, hakanan Alhaji Sadam yaji zuciyarsa ta aminta da batun, nan take yace ya amince, inda yace da ƙanin nasa yayi komai, ai Ameena ƴarsa ce.
Nan fa Alhaji Naseer ya koma falon tarban baƙinsa, nan yasanar dasu Baba Malam Amincewar Ameena, da kuma mahaifinta, take suka cika da tsananin farinciki, sosai sukaji daɗi, ƙwarai kuma sun yaba da karamcin mutanen.
Nan take suka tsaida magana, inda anan wurin a take Baba Malam yabada sadaki Naira dubu Hamsin, sannan ya kuma ce nan da kwana uku za a kawo kayan lefe, ananne Alhaji Naseer ya yanke musu lokacin biki, wato nan da sati biyu masu zuwa, domin kuwa dukansu ajiƙe suke da naira saboda haka babu wani amfanin jan bikin yayi nesa.
Haka suka rabu cikin mutunta juna, kowa zuciyarsa fes.
Ɓangaren Ameena kuwa tana shiga ɗaki, tsalle ta buga cikin matsanancin mamaki tace.
"Ya Allah idan mafarki nake ka tasheni na farka ka kuma tabbatarmin dashi a zahiri. Wayyo Allah na wai dagaske Saifuddeen zai aureni? zan zama mata agaresa, wayyo Allah na!! Alhamdulillah."
Sulalewa ƙasa tayi inda tayi sujjadan godiya ga Allah, cikin matsanancin jin daɗi tace.
"Tabbas Allah Shi kaɗaine bashida wani abokin tarayya, sannan shike isar mana da komai namu."
faɗawa kan gado tayi cikin matsanancin murma tayi hugging pillow.
Nan fa tashiga birgima akan gado tana dariya, mai ɗauke da tsananin farinciki.
Littafina na kuɗine ga mai buƙata ya min mgna ta wannan no ɗin 09097853276.
*By*
*GARKUWAN FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Sbp egwl
Ɓangaren su Baba Malam kuwa, kai tsaye gidan Ya Ahmad suka koma, inda anan suka ɗan huce gajiyansu, zama sukayi suna maida batun karamci da kuma halin dattako irin na iyayen Ameena'n, tabbas sun shaida cewa suna da mutumci, kana kowani mutum zai so haɗa zuri'a dasu.
Da misalin ƙarfe 6 na yammaci jirgin da zai maidasu Gombe zai tashi, hakan yasa 5::40 pm ababban filin airport na Nnamdi Azikwe International Airport Abuja.
Ƙarfe shida dai-dai kuwa jirginsu ya tashi, bayan Baba Malam ya ƙara jaddadawa Ya Ahmad, maganan haɗo lefe da wuri, nan Ya Ahmad yace.
"Insha Allah zaisa Aunty Lubna ta haɗo lefen, nan bada jimawa ba." Bakwai dai-dai jirgin da ya ɗaukosu daga Abuja zuwa Gombe, ya sauƙa acikin Gombe International Airport. Ya Ameenu da kuma Ahmad ne sukazo ɗaukarsu anan airport ɗin. Motar Ya Ameenu Baba Malam ya shiga, inda Bappa Ali da Dirankadi kuwa suka shiga motar Ahmad, don sune zasu je suiwa Ummi bayanin duk abun da ya wakana. Haka suka rabu da juna cikin aminci da salama.
Tun daga yanayin yanda Ahmad yaga fuskokinsu ɗauke da annuri, hakan yasa shi fahimtar cewa lallai anyi nasara tafiya tayi kyau, sosai kuwa yaji sanyi azuciyarsa.
Koda suka ƙarasa gidan, a falon na Ummi suka zauna, cikin nutsuwa kuwa Bappa Ali da Dirankadi sukaiwa Ummi bayanin komai, sosai Ummi ta cika da farin ciki haɗi da jin daɗi, haka kuma lokacin da aka sanya auren yayi mata daɗi sosai, dama ba ta son aja lokacin, nan dai tasa aka kawowa su Bappa Alin kayan ciye ciye, nan suka ɗan taɓa, daga haka Dirankadi ya ƙirayi driver'nsa, nan ya zo ya maidasa gida, shikuwa Bappa Ali anan zai kwana, kasancewar qdare yayi, idan yaso gobe da safe, Ahmad ko sule driver ɗaya daga cikinsu zai maidashi.
Can ɓangaren Saifuddeen kuwa, ganin sun dage da gaske suke maganar auren yasa, wunin yau duk bai fito waje ba, anan ɓangarensa ya zauna, yayinda ya maida hankalinsa kan Laptop ɗinsa yana aiwatar da sabon aikin da shugaban DSS suka bashi.
Koda ya dawo sallan Isha, kai tsaye part ɗinsa ya koma, kasancewar yau din ana yanayin sanyi hakan yasa shi kwanciya da wuri, luf yayi acikin lallausan bargonsa, inda ya ɓoye kansa acikin bargon, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da lumshe idanunsa, tunaninta ne kwance acikin zuciyarsa, sau da yawa idan ya tuna da ƙiriniya da kuma rashin ji irinta na yarintarta dama yanzun da takega ta girma, yakan samu kansa da sakin murmushi. Da haka bacci ya ɗaukesa.
Washegari.
Tun da ya dawo daga sallan asuba ya koma bacci, bashine kuwa ya farka ba sai wajen ƙarfe 10:30 am. Ahankali yazuro da ƙafafunsa ƙasa, tare da jawo wheellchair ɗinsa, wanda akullum take kusa dashi, sam baya bari tayi masa nisa, hawa samanta yayi, kai tsaye ya nufi toilet, koda ya shiga ruwan wanka mai ɗam ɗumi ya haɗawa kansa, cikin haɗaɗɗen jakuzzie, nan ya zuba turaren wanka mai daɗin ƙamshi acikin ruwan, Luf ya kwanta acikin jakuzzien tare da ɗan lumshe idanunsa. Sama da mintuna 10 ya ɗauka ahaka, yayinda yakejin daɗin ruwan, kasancewar ruwan nada ɗan ɗumi, shiyasa yakejin daɗi yanayin, domin kuwa yanzu ana weather ne na sanyi hunturu.
Wanka yayi kana ya ya rufe jikinsa da wani fari ƙal ɗin towel, haka ya nufi ƙofar fita daga cikin toilet ɗin, jikinsa ɗauke da danshin ruwa, yayinda kwantaccen sajen dake kan fuskarsa ya ƙara lafewa, saman kumatunsa.
Kaitsaye gaban drawer ɗinsa ya nufa, inda ya zaro kayan da zaisa, wani ƙaramin towel ya ɗauka sannan ya shiga goge ruwan dake jikinsa, yana kammalawa, ya ɗauki handryer wanda dashi yayi amfani wajen busar da tarin sumar dake kansa, cumb yasa inda yaƙara gyara lallausan sajensa, yayi kyau matuƙa, wani body lotion mai sauƙin ƙamshi ya shafa ajikinsa, dogon wandon pencil jeans ya sanya, kana ya zura wata haɗaɗɗiyar riga, wanda take kaman na sanyi domin harda hulanta, kasancewar rigar nada kalan grey hakan yasa sosai tayi masa kyau, yayinda agaban rigar aka rubuta NIKE da manyan baƙaƙe, wasu combat shoe wanda suma na company'n NIKE ɗin ne ya sanya aƙafafunsa, sosai shigar tayi masa kyau, saiya fito kaman irin shahararren jarumin ƙwallon ƙafa, wani simple watch ya ɗaura akan tsintsiyar hannunsa, kana ya feshe gaba ɗaya jikinsa da turare, take ɗakin ya gauraya da daddaɗan ƙamshin turarensa. Wayoyinsa ƙiran iPhone da kuma Samsung ya ɗauka, kana ya zura su cikin ajihun dake jikin haɗaɗɗiyar rigar tasa.
Daga part ɗinnasa kai tsaye barayin Ummi ya nufa.
Tun kafun isowarsa falon nata, ƙamshin turarensa ya rigayesa isowa.
Cikin nutsuwa ya ƙarasa shigowa cikin falon, Hayatuddeen ne zaune akan dinning area, yayinda ya saka pepper meat soup agaba sai sha yake. Ƙarasowa dinning area ɗin yayi, dubansa Hayatuddeen yayi cikin kulawa yace.
"Barka da fitowa Hammana."
Kai ya jinjinawa Hayatuddeen din bayan yasaki taƙaitaccen murmushi, dai-dai lokacin Ummi tafito daga ɗakinta, ganin Saifuddeen ɗin yasa ta sakin murmushi cikin kulawa tace.
"Masha Allah ka fito kenan, yanzu fa nake cewa Hayatuddeen ya gama ya ƙiraka, kazo kayi break fast."
Ummi taƙare maganar tana mejan kujera wanda take facing na Saifuddeen ta zauna, duk dama shi always akan wheellchair ɗinsa yake zama.
Raliya ce tafito daga cikin kitchine, hannunta ɗauke da plate. Ganin Hamman nata yasata sakin murmushi, cikin nutsuwa tace.
"G/N Hamma."
Kansa ya jinjina mata alaman ya amsa, zagayowa ɓangaren da yake tayi, nan ta aje masa plate ɗin da ta fito dashi daga kitchine ɗin, wanda saman sa ke ɗauke da roasted fish, wanda yaji kayan haɗi, hadda lemon tsami. murmushi Saifuddeen yayi tare da dubanta, hannu ya jinjina mata alaman "Thanks." Itama murmushin tayi, don dama tayi hakanne don ta faranta masa, kasancewar tasan yanason roasted fish.
Nan ta zauna, inda suka shiga cin breakfast ɗin cikin nutsuwa, Ya lura dukaninsu suna cikin farinciki, musamman ma Umminsa, wanda duk bayan ƴan mintuna kaɗan take sakin murmushi, haka dai suka kammala break ɗin nasu, nan ya dawo cikin falon Ummin ya kwanta, Hayatuddeen kuwa ɗaki ya koma, inda shima yayi shiga shigen irin ta hamman nasa, nan yafito riƙe da jakarsa ta makaranta, duban Ummi dake zaune afalon yayi, cikin sangarta haɗi da zallan shagwaɓa yace.
"Ummi zan tafi school, 11:30 muke da lecture."
Batare da Ummi ta ɗago kanta ba tace.
"To Autana adawo lafiya."
Jin haka yasashi ɓata fuska ashagwaɓe
yace.
"Ummi kuɗin hannuna fa ya ƙare."
Murmushi Ummi tayi, don dama tasan kwanan zancen.
Dubansa tayi tare da cewa.
"Kullum sai an baka kuɗi Hayatuddeen sai kace ƙaramin yaro."
Cikin tura baki yace.
"Ni ban san ammafin buɗe min ac da Hamma Saifuddeen yayiba, ya tarkata komai ya riƙe ko Atm ɗin ban taɓa riƙewa koda na wuni ɗayaba, sai dai inyi ta ganin Arlet yanata shiga ba sauƙi, ina ganin miliyoyi amman bani da damar taɓasu."
Dariya Ummi tayi hakama Saifuddeen, dan zancen autan nasu ya nuna burinshi na a bashi kuɗi ya fara lalata.
Shi kuwa auta sake shagwaɓe mata yayi, wai adole sai ta bashi kuɗi, saikace ƙaramin yaro, nan Ahmad yashigo ya iske suna maganan, Ahmad ne ya ciro 5k daga cikin aljihunsa, inda ya bawa Hayatuddeen ɗin, nan Hayatuddeen yasaki murmushi sannan yasakai yafice daga cikin falon.
Nan Ahmad ya zauna acikin falon suka shiga ɗan taɓa hira da Ummi, Saifuddeen kuwa, luf yayi tare da lumshe idanunsa, kamar wanda ke bacci.
Abuja Nigeria.
Kwana biyu kenan da zuwan su Baba Malam Abujan, yayinda yau
Tsab Aunty Lubna da kuma wata ƙawarta, mai suna Samira suka shiga cikin shoprite, don haɗo kayan auren, ba laifi kaya masu kyau da kuma tsada suka sayo, duk da cewa ran Aunty Lubna baiso ƙara auren na Saifuddeen ba tanajin taya Zaleeha kishi, tana kuma tausayawa Zaleeha a gaba, to amma tasan cewa koma menene hakan shine dai-dai, don itama guduwan da Zaleehan tayi ya sosa mata zuciya.
Akwatuna goma sha biyu suka saya, kana kuma suka cikasu da kaya, sannan kuma suka saya wasu uku daban wanda ciki aka sanya kayan uwa da na uba.
Haka dai suka dawo gida bayan motarsu cike da kaya.
Aranan kuwa Ya Ahmad ya ƙira Baba Malam, inda yasanar dashi cewa, anagama haɗa kayan auren.
Kasancewar da dare ne Ya Ahmad da Baba Malam ɗin sukai waya, hakan yasa washe gari da safe, Baba Malam yaƙirayi Bappa Ali ya sanar masa, nan Bappa Ali yace.
"Zai sanar da Ummin, sai susa ranan da za'a kai kayan."
Hakan kuwa akayi don bayan sallan Azahar Ummi na zaune akan sallaya, sallame sallan ta kenan, wayarta tasoma ruri, ɗaga ƙiran tayi, bayan sun gaisa da Bappa Ali'n ne kuma, yake shaida mata cewar.
"An kammala haɗa kayan auren, yanzun ita zata sanya ranan da za akai kayan."
Cikin jindaɗi da gamsuwa Ummi tace.
"Masha Allah, amma ni sai nake ga kamar ku ya kamata kutsai da ranan kai lefen, tunda dai auren bawani lokaci mai tsawo aka ɗauka masa ba, yanzu gashi kamar wasa har anci kwana uku acikin ranakun."
Cike da gamsuwa Bappa Ali yace.
"Tunda yau takasance asabar ne, to ranan litinin da safe, sai waƴanda zasu kai lefen su shirya."
Nan Ummi take sanar dashi cewa.
"Goggo dada, Adda Rahama, da kuma Ahmad, sai kuma Hayatuddeen, sune wanda zasuje, amma bawai kai tsaye abujan zasu nufa ba, a Kaduna gidan Raihana zasu sauƙa tukun."
Nan dai tace ya kawo shawaransa. Cikin gamsuwa Bappa Ali yace mata.
"Hakan ma yayi."
Nan akayanke cewa, ranan litinin zasu kai lefen.
Ummi na gama waya da Bappa Ali'n, numbern Adda Rahama ta ƙira, nan take shaida mata duk yanda sukayi da Bappan nasu, sosai itama Adda Rahama tayi na'am da hakan. Nan dai sukayi sallama.
Numan.
Zaman Zaleeha a numan ya miƙa sosai, duk da cewa bawai tanajin daɗin rayuwa acikin ƙauyen bane, amma babu laifi tana ɗan samun abun da take ɗan so, tunda da kuɗi a hannunta, rayuwa take cike da kaɗaici, saidai wani lokaci wayarta da kuma tsohuwar laptop ɗinta suke ɗebe mata kewa.
Sai kuma wata sabuwar ƙawa wacce take ƴar fulani da tayi, inda sun haɗu ne, abakin kogi, don wani lokaci Zaleeha kan zuwa bakin kogin ta zauna, itakuwa sabuwar ƙawar Zaleehan mai suna Aisha, anan cikin wani ɗan ƙaramin rugar fulani dake kusa da Numan ɗin take, wanda yake rugace na zallan fulani sannan kuma dukansu musulmai ne, babu christan ko ɗaya acikinsu, tun Zaleeha bata sake