Showing 231001 words to 234000 words out of 239422 words

Chapter 78 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

06 Dec 2024

11876

da mata police ɗin dake bakin mashigar wurin wacce ita ke kula da shige da ficen matan dake shiga Makey ɗin, baya jiyo muryarsu sabida hada-hadar mutane, Zaleeha kuma baya ta bashi bare ya karanci motsin bakinta.
Ita kuwa Zaleeha cikin nazari tace.
"Sunana Zaleeha Bashir Sulaiman Dukku".
Ido matar ta zuba mata cikin son tuno fuskar a hankali tace.
"Kamar dai na sanki".
Da sauri Zaleeha tace.
"Shekara biyu da ƴan watanni na taɓa kai riport a police station ɗinku na Gombe division, wata rana bayan sallan mangariba, na kai muku riport cewa ƴan kalaren sun tare wani mutun a cikin sitadiyom, suna dukanshi, kin tunani kecema, kika matsa aje a duba".
Cikin sauri Matar tace.
"Yes! Na tunaki ai kuma dan na tuna yadda kikazo a gigice mugun DPO mara mutunci yai ta zaginki".
Da sauri Zaleeha tace.
"Ayyah, wanda yayi tamin masifa ya gargaɗeni cewa kar in yarda in kai ƙarar wani Police station ɗin".
Da sauri matar tace.
"Eh shi dai".
Cikin kaɗuwa Zaleeha tace.
"Dan Allah kunje kun taimaki mutumin da aka daka ɗin ne? Dan washe garin ranar nazo station ɗinku sai na samu duk bakwa wurin sai wasu sabbin fuskoki na samu, da namusu mgnar kuma sai sukace babu wannan mgnar a wurinsu.
Bayan nan nafi wata biyu kullum sai nazo station ɗinkin amman bana samun kowa".
A hankali matar tace.
"Ayyah ai mutumin munje an taimakeshi an kaishi asibiti, to DPO ne ya caccanza mana wurin aiki tun a ranar sabida, da tun lokacin da kikayi bayani ya gane Yaran Dalla ne sukayi dukan, shi kuwa karen Dalla ne,
shiyasa ya koreki ya miki barazana, da ranki da ran mara lfyar dan dama jami'an tsoro na neman Dalla kuma in aka kama Dalla yasan shima bazai tsiraba,
ni kaina daga baya na koma can dan in duba takardar rahotonki ko zan sameta a maida case ɗin hannun DGP gaba to sai na samu babu,
Yanzu haka shi DPO an koreshi a aiki kwana kin baya da aka kama Dalla dan ya tona musu asiri, Ni kuma yanzu a ƙarƙashin DGP nake aiki yanzuma tare muke dashi shiyasa nake bada kariya wa ƙofar shiga dan uban gidana yana ciki".
Sai kuma ta ɗan kalli Zaleeha dake ta nanata sunan Dalla a bakinta, ya abubuwan suke son haɗe mata a kaine suna dagula mata lissafi.
matarce ta kalleta tare da cewa.
"Ɗan uwanki ne suka sassare?".
Da sauri tace a a.
Kana tace.
"Allah sarki, to Allah ya saka mishi kenan? Bani number ki zamuyi mgna daga baya, yanzu sauri nake".
Murmushi matar tayi kana ta bata number tata.
Daga nan bi bayan Hamma Saif ɗin tayi.
Suna shiga mota Sule yaja suka tafi.
Daga nan kai tsaye New G.R.A suka nufa shiru tayi tana ta son tuno wasu abubuwan sam ta kasa samo bakin zaren tunanin nata har suka isa.
Suna zuwa gidan su Zaleeha da farin ciki suka shiga,
kai tsaye falon Baba Malam sukaje bayan sun gaisa ne,
Yayiwa sule text akan ya shigo da ledan atampopin ya kawo,
koda ya kawosu sosai Baba Malam yayi godiya bayan yayi mishi faɗan ya daina musu hidima,
cikin nitsuwa yayiwa Baba Malam bayani, cewa gobe zasu tafi yayi musu addu'a.
Fuska a sake dottijon ya gyara zama tare da cewa.
"To Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy, Allah ya bada sa'an aikin da duk za'ayi maka".
Amin Amin Mama da Mamy da ya Habu da ita Zaleeha suka amsa a zahiri.
shi kuwa Saifuddeen murmushi jin daɗi yayi tare da amsawa a zuciyarshi, shiko Baba Malam cikin nitsuwa yace.
"Zaleeha ki kula dashi da dukkan motsinshi a tafiyar nan da za'ayi kinga zakuje inda bashi da kowa baki da kowa, dukkan taimako da tallafawa a wurinki zai samesu, bana son gardama, na haneki dayi mishi musu".
Cikin sanyi tace.
"In sha Allah Baba malam zan kula".
Cikin jin daɗi yace.
"Allah ya miki al'barka ya kaiku lfy".
Amin Amin sukace duka.
Mama kuwa da Mamy sai kallon ɗan cikin Zaleeha sukeyi wanda yanzu ya cika wata huɗu cib ya kuma fara baiyana kanshi,
duk da ƙaton hijabin da ta zumbula wai duk dan ta ɓoye cikin dan kunya.
Hira suka ɗanyi
kana, suka sallamesu suka nufi gidan Adda Maryam.


Kasan cewar Ya Ameenu na gida shiyasa da kanshi ya musu jagora har falon Ziyada,
bayan sun gaggaisa ne,
jin ana kiran sallan magriba Ya Ameenu da Hamma Saif suka fita a harabar gidan sukayi al'wala, suma su Zaleeha al'wala sukayi kana sukayi sallan basu tashi a kan abin sallan ba ba sukaci gaba da hira,
har saida aka kira isha sukayi salla kana suka fito falon,
nan suka ci abinci,
hira suka ɗan fara, ganin dare ya ɗan fara nisane Hamma Saif yayi mata alamun to su tafi dare nayi".
Gane abinda yake nufine yasa ta miƙe tare da kamo hannun Ziyada cikin sanyi tace.
"Ziyada muje ciki".
Sai ta kuma kalli Ya Ameenu cikin sanyi tace.
"Ya Ameenu a ina soƙon da Adda Maryam ɗin ta ajiye min yake?".
Ido ya lumshe a hankali yace.
"Tace ki duba a bedside drower'nta na gefen gado ta jikin window".
Kai ta gyaɗa kana suka juya suka nufi cikin ɗakin.


Shi kuwa Ya Ameenu da Hamma Saif miƙewa sukayi suka nufi woje, tunda yanzu zata fito su tafi.




Su kuwa suna shiga, Ziyada ta zauna a bakin gado,
ita kuwa Zaleeha gaban durowar ta zauna ɗabas,
a hankali ta buɗe durowar,
wasu robobi ta gani a jere a ciki,
sai kuma wata farar takarda a ninke a akan robar da tafi girman,
da sauri tasa hannu ta ɗago takarda,
da taga anyi rubutu da manyan baƙin.
"Zaleeha, ki buɗe takardar ki karan tata a cikin ɗakina, kisa a ranki kamar da bakina nake gaya miki ina gabanki kina gabana".
Da sauri tasa hannu ta sharce hawayen da tuni suke kwaranya, buɗe takardar tayi jiki na rawa ido ta ware sosai dan ganin rubutun da kyau.
"......!








Littafinan na kuɗine biya ɗarinki uku kacal ki laranta bada haƙin kowaba, turo katin mtn ta number nan 09097853276 sai in saki a group ki karanta salim alim


By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: "Inaji a jikina Zaleeha bazaki dawo ki sameni a rayeba, shiyasa na rubuta miki abinda na fahimta dan in ankarar da ke.
Ina fatan ko kin dawo bayan raina zaki saurari abun da zan faɗa miki, da kunnen basira, kuma inaso kiyiwa kalamaina kyakkyawar fahimta, ki zauna kiyi nazari akan abun da yake faruwa. *Dan inaga kina tare da wanda kike ta wahalan nema kina tare dashi shi kike nema kuma shi kika gujewa* ina kyautata zaton cewa Saifuddeen shine mutumin daya taimaka miki! saboda bayan kin gudu naje gidan Ummin Saifuddeen, naje munyi magana da'ita, ta bani wani labarin daya bani mamaki, wanda kuma labarin irin makamancin labarin da kika bani ne, time ɗin da kika faɗamin haɗuwarku da Dalla, har wani mutumi ya taimakeki, lokacin din da kika faɗamin, lokacin ɗin Ummi ta faɗamin, tace dukan Saifuddeen akayi da magriba, kuma wasu ƴan kalarene suka dakesa da time da date duk iri ɗayane.
suma kawai zuwa kawai police ya sanar musu aka ce musu yana medical centre bashi da lafiya kuma ƴan kalare ne suka dashi, to su a lokacin ta ranshi lfyarsa sukeyi basubi ta kan waɗanda sukayi dukanba, daga wannan rashin lafiyanne kuma ya rasa ƙafafunsa, saboda abayansa suka dakesa, wannan shiya jawo masa matsalan rashin tafiya, saboda haka ne nakeji ajikina Saifuddeen shine wanda ya taimakeki, dan tace bada gurguntakan aka haifesa ba, kwata kwata faruwar abun shekara ɗaya ne da ya wuce, kuma da aka kaisa medical centre, Abuja suka tura su, daga Abuja kuwa aka wuce dashi India, sai bayan shekara ɗaya ya dawo, hakanne yasa nake kyautata zaton Saifuddeen shine wanda ya taimakamiki, amma kiyi bincike akan hakan, wata ƙila hakan ya zama gaskiya, amma ina roƙonki koda bai kasance shiɗin bane, kizama maiyi masa biyyaya, Zaleeha ki zauna agidan aurenki da zuciya ɗaya, darajar ƴa mace shine ɗakin mijinta, dan Allah Zaleeha kizama me biyayya ga mijinki da kuma Baba Malam, ki nutsu kicire tunanin wani acikin ranki, ki rungumi mijinki hannu bibbiyu, insha Allah Zaki ga riban hakan naso in sanar miki a waya to in na kiraki bata shiga." Cikin wani irin yanayi Zaleeha tayi wani zazzafan numfashi tare da sauƙe ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya, da kuma sauƙan wasu irin razanennun hawaye, take taji kanta na jujjuyawa, wasu abubuwane suka shiga dawowa cikin ƙwaƙwalwanta, sai yanzu tunaninta ke ƙoƙarin daidaita, cikin yanayin mamaki da ruɗu da gigicewar tunani tace. "Ziyada Hamma SAIF shine wanda ya taimakeni, tayaya hakan zai kasance?."
Cikin mamaki Ziyada tace.
"Haba dai Adda Zaleeha?".
Kai ta shiga ɗan girgizawa, domin kuwa tashin farko taji zuciyarta na neman gamsuwa da zancen, amma kuma abun tambayar shine wazai tabbatar mata da hakan? idan kuma dagaske shiɗin ne me yasa ya ɓoye mata kansa? Turo ƙofar ɗakin akayi, hakan yasa ta ɗago kanta da sauri, Ya Ameenu ne, cikin kulawa yace.
"Inkin gama kiyi sauri, dan yana jiranki awaje." Kanta ta jinjina, shi kuma ya juya ya fice daga cikin ɗakin Ziyada na biye dashi dan yafitota da yayi alamun tazo, ko minti 2 basuyi da fita ba, cikin sauri ta juya ta fita daga ɗakin, abakin shigowa cikin ɗakin sukayi karo da Ziyada, hannun Ziyadan ta kamo, cikin wani irin yanayin da ta kejin kanta aciki tace.
"Shine Ziyada, inaga da gaske Hamma Saif ne, shine wanda ya taimaka min."
Cikin yanayin mamaki Ziyada tace.
"Shi kuma?." Kai ta jinjina alaman "Eh." dan gaba ɗaya tashiga mamaki da ruɗu. Sakin Ziyadan tayi, cikin sauri ta nufi waje. Dai-dai lokacin kuwa Saifuddeen sun gama magana da Ya Ameenu, harma ya shiga cikin mota, Sule driver ne ya buɗe mata murfin motar ta shiga, bayan tayiwa Ya Ameenu sallama.


Tana shiga kuwa Sule driver yaja motar suka tafi, da sauri ta juyo da fuskarta garesa , akiɗime takai hannunta ta tallafo haɓarsa, juyo da fuskarsa yayi ya zamana suna fuskantar juna, wani irin abune taji yana shiga zuciyarta, cikin muryarta da tayi sanyi, take kuma fidda yanayin da take ciki, tace.
"Hamma Saif wai kaine? kaine wanda ka taɓa taimakona? ka tuna fuskata Hamma Saif, please kafaɗamin, kaine wanda ka taimakeni lokacin da yaran Dalla suka so cutar dani?, kafaɗamin Hamma Saif dan Allah ka tabbatar min da hasashena ka tuna a bakin A.A ALIYU." Idanu ya zuba mata naɗan wasu daƙiƙu, lokaci ɗaya ya saki wani irin murmushi me tsayawa azuciya, bayajin zai iya amsa mata wannan tambayan ayanzu, ba kuma bazai faɗa mata bane, kawai dai yafi so ne ya koyar da ita zazzafan soyayyarsa, amatsayinsa na kurma kuma gurgu, duk dama dai ayanzu yasan ta zurma cikin kogin sonsa.


Ganin ya kawar da kansa gefe, yasa ta kamo hannayensa, tare da zubawa gefen fuskarsa ido, wani irin sabon yanayi takeji na ratsa zuciyarta, ahankali ta matsa jikinsa, kan kafaɗarsa ta ɗaura kanta tare da lumshe idanunta, har yanzu jin abun take wani iri, sai-dai murmushin da taga ya mata, ya matuƙar sata a ruɗani.
Ahaka har suka isa baice da ita komai ba, Sule driver na gama parking ɗin motar, ya fito, ware wheelchair din saifuddeen ɗin yayi, cikin nutsuwa ya buɗe murfin motar ya fito, anutse ya hau kekensa ya wuce cikin gidan, da sauri Zaleeha ta rufa masa baya, cikin sassanyar muryarta take ƙiran sunansa, sam bai tsaya ba balle har tayi tunanin zai juyo ya kalleta, sun kawo dai-dai bedroom ɗinsa ne cikin sauri ya shige tare da jawo ƙofar ya rufe, hakanne yasa bata samu daman shiga ba, fuska ta kwaɓe tare da ɗan karyar da wuyanta gefe, a bayyane tace.
"Me yasa bazaka amsa min tambayoyina ba Hamma Saif why?." asanyaye ta juya ta fice daga cikin falon. Shikuwa yana shiga cikin ɗakin nasa ya saki wani irin murmushi, dariya ya ɗanyi me sauti, cikin tsantsar nishaɗin daya samu kansa yace. "Kina yarinya ƙarama amma bakya iya gane mutane to in kin tsufa kuma wato wata ranama cewa zakiyi ni ba mijinki bane ki sani uku".
daga haka kayan jikinsa ya ɗan rage sannan ya wuce toilet.


Zaleeha kuwa daga sashin nasa part din Ummi ta wuce, rashin ganin kowa acikin falon yasa taɗan ɗaga murya, tana ƙiran sunan Ummi'n, jin shiru babu amsa ne yasa ta nufi ɗakin Hayatuddeen kasancewar ta jiyo muryar Hayatuddeen ɗin yana ce mata.
"Ummi ta shiga wonka".
kana taga ƙofar ɗakin nasa abuɗe, ahankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama.


Shi kuwa Hayatuddeen zaune yake akan sofa, yayinda ya baje hotunan Abbansu da Ya Nuruddee da Saifuddeen tun kafin ya samu matsalar tsayuwa, kasan cewar in Ummi taga hotunan tana kukane yasa suka ɓoyesu, yanzuma begen ganin mahaifinsu da babban yayansune yasa ya fito dasu.
Hotunan Saifuddeen ne agabansa yana kallo, wanda kuma yayi hotunan ne tunkafun yasamu nakashewar ƙafafunsa, hankalinsa ya ɗanyi nisa shiyasa baiji sallaman nata ba, Ahankali ta ƙaraso cikin ɗakin, tare da baza idanunta akan hotunan dake gaban Hayatuddeen ɗin, wani irin bugawa taji zuciyarta tayi, alokacin da ta sauƙe idanunta kan wani hoton Saifuddeen wanda yake tsaye akan ƙafafunsa shidasu Ahmad dasu Salisu Ishaq yana murmushi, ga fuskarnan tasa fayau ta bayyana, babu wani cikar ƙasumba asamanta, saɓanin yanzu da saje yayi mata ƙawanya, hannunta dake rawa tasa ta ɗauko hoton, gaba ɗaya jikinta ɓari yake, bakinta na rawa tace. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, Hayatuddeen waye wannan?."
jin muryanta yasashi ɗago kai, murmushi yayi yana ɗan kaɗa kai yace.
"Kaman yaya waye wannan kina nufin baki ganeshi bane?." Cikin ruɗani tace. "Please Hayatuddeen kafaɗamin waye shi, karkacemin shine Hamma Saif kuma na kasa gane shine dan zan jawa kaina Allah ya isa, ka cemin wanine daban ba Hamma ba."
Cikin yanayin mamaki yaɗan shafi sumar kansa, shaye da mamaki yace.
"Ikon Allah yau kuma Hamma Saif ɗinne baki gane ba, to ki wanke idanunki wannan ba kowa bane face Hamma Saif, nasan kinyi mamakine saboda kin ganshi tsaye kan ƙafafunsa, lokacin bai samu matsalan spinal cord injury bane shiyasa." Durƙushewa tayi akan ƙafafunta, murya na rawa tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, wallahi shine, shine mutumin daya taimakeni Hayatuddeen Hamma Saif ne, shi ya ceceni daga hannun ƴan iskan da suka so tarwatsamin rayuwata, shine wanda ya zamemin Garkuwa alokacin da babu me iya taimakona, shi ne wanda ya zama makari kuma madubin dubawata, da ace alokacin babu shi, da yanzu rayuwata wani babin take fuskanta ba wannan ba, Wallahi Hamma Saif ne Hayatuddeen, shi nake ta nema tsawon shekaru Wlh Hamma Saif ne!!!." Ta ƙarishe mgnar da ƙarfi Baki Hayatuddeen ya buɗe yana kallonta, shikam cike yake da mamakin Zaleehan, dan kalamanta sun ɗaure masa kai.
Dai-dai lokacin Ummi ta shigo cikin ɗakin da sauri, kasancewar fitowarta falo kenan, taji tashin maganganun Zaleeha'n, Zaleeha kuwa ganin Ummi yasa ta ƙarasa gabanta cikin sauri, tuni hawaye sun kwaranyo daga cikin idanunta, hannuwan Ummin ta kamo tana jijjiga kai tace.
"Shi ne Ummi Hamma Saifuddeen ne, wallahi da gaske shi ne! Gskyan ADDA MARYAM tayi gsky."
Da mamaki Ummi ke kallonta, cikin rashin gane inda maganganun Zaleehan suka dosa tace.
"Bangane me kike faɗa ba Zaleeha, shi ne wa?". Ganin Ummin kaman bazata fahimceta ba, yasa cikin sauri ta nufi hanyar fita daga ɗakin, baki buɗe Ummi ta bita da kallon mamaki.


Hayatuddeen kuwa zuwa yanzu ya fahimci abun da Zaleehan ke nufi, dan baya taɓa mantawa sun taɓa taɗin da Zakariyya, wani irin dariya yayi, tare da shafa sumar kanshi, cikin matsanancin farinciki yace.
"Yess dama ashe akan mune aketa wannan badaƙalar, wannan shine rashin sani yafi dare duhu, mu ake so kuma mu ake gudu, batare da ansani ba."
Dariya yayi sosai, hakanne yasa Ummi da Raleeya wanda ta shigo yanzu, suka zuba masa ido, cikin ƙufula Ummi tace.
"Wai kam lafiyanka, kaketa dariya?." gyara zamansa yayi, cikin zumuɗi ya labartawa su Ummi duk abun daya sani.
Ai kam su Ummi sosai suka shiga mamaki, sun kuma yi farinciki sosai, tabbas sun yarda cewa Allah Babu yanda baya abunsa.
Raleeya kuwa cewa tayi. "Lallaima Aunty Zaleeha ashe dama duk wannan guje gujen naki, akan Hamma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login