Showing 195001 words to 198000 words out of 239422 words
Chapter 66 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Kanta ta shiga jinjina masa, cikin kuka me ɗauke da murmushi tace.
"Ya Adnan Kunnuwan Saifuddeen sun buɗe, Saifuddeen ya fara jin magana da yin magana." Idanu Ɗr Adnan ya ɗan zaro cikin yanayin mamaki haɗi da kaɗuwa yace.
"Kinsan me kike faɗi kuwa Rahama, Saifuddeen ya fara jin magana fa kikace?". Kanta ta jinjina masa, tare da ɗan sharce hawayen farin cikin dake kan fuskarta, cikin farinciki tace.
"Eh Ya Adnan wallahi dagaske yanzu Raleeya ta ƙirani tana kuka take faɗamin".
wani irin matsanancin farinciki ne ya lulluɓe zuciyar Dr Adan jawo Adda Rahma'n jikinsa yayi tare da rungumeta ƙam, take suka shiga yiwa Allah godiya.
miƙe Ya Adnan ɗin yayi tare da mikar da ita cikin tsantsar jin daɗi yace. "Maza tashi muje gidan Ummi'n, tashi da sauri mu tafi".
cikin farinciki kuwa ta miƙe ɗaki tashiga ta ɗauko mayafinta,
Shi kuwa Ya Adnan miƙewa yayi, zuciyarsa cike da farinciki, ya nufi ɗakinsu Faruq yana shiga ya kamo hannun Farouq da kuma Adam tare da cewa.
"Yaran kirki kuzo mu tafi gidan Ummi".
Cikin Mamaki Faruq ya kalleshi tare da cewa.
"Daddy da sassafen nan".
Kai ya gyaɗa mishi tare da cewa.
"Uncle Saifuddeen ne ya worke shi zamuje mu dubi".
Wani irin zabura sukayi a tare tare da cewa.
"Dady ya worke? yana yanaji? kuma yana magana? da tafiya?".
Cikin sauri Ya Adnan yace.
"Ku dai kuzo muje".
aifa tuni sunyi gaba, Adda Rahma kuwa tana fitowa suka ɗunguma zuwa mota.
Raleeya kuwa tana jin Adda Rahama ta katse wayan, numbern Raihana ta nema, wayar bata wani jima tana ringing ba, Raihanan ta ɗauka, kaman yanda Raleeya ta sanarwa Adda Rahma muryarta na rawa, haka ma ta sanarwa da Raihana, kusan sumewa Raihana tayi saboda tsananin mamaki da kuma shiga shock, sosai taji abun wani iri acikin kunnuwanta, saboda abune da bazasu taɓa zato ba, duba da irin yanda aka kwashe tsawon shekaru baya ji ba kuma ya magana, kuka ta fashe dashi, dan takasa jurewa bare ita dama saurin kukane da ita,
ji take kaman tayi tsuntsuwa ta ganta acikin garin Gombe, Sameenu dake zaune agefenta, wanda shima yaji komai ne ya jawota ya rungumeta ƙam acikin jikinsa, shi kansa saida idanunsa suka kawo ƙwalla, sosai shima yaji hankalinsa ya taho Gombe, take ya miƙe cikin kula ya janyeta daga jikinshi cikin tsananin farin ciki yace.
"Zauna Ummu Affan, bari yanzu inje airport inda in bincika man in akwai jirgin da zai tafi Gombe, yau ko gobe zamu taho Gombe'n.
Cikin tsananin jin dadi tace to.
Kana ta kuma jawo wayar ta kira Raliya kan zata ce mata ta haɗata da Hammansun taji muryanshi to kuma wayar Raliya sai tana sa mata line busy dole ta haƙura.
Raleeya kuwa suna gama waya da Raihana, numbern Bappa Ali ta dannawa ƙira, yana ɗagawa taji wani sabon kuka yazo mata, saboda jin Bappa Alin suke kaman Babansu mahaifi, hankalin Bappa Ali ne ya tashi sosai, jin yanda muryan Raleeyan ke rawa, cikin nuna damuwarsa yace. "Raleeya lafiyanki kuwa, me yake faruwa? Meya samu gidan?."
Ɗan jan sheshsheƙa tayi murmushi ne kuma yazo mata, cikin zumuɗi tace.
"Bappa Ali kunnuwan Hamma Saifuddeen sun buɗu, yanzu Hamma yanajin magana kuma yana iya mayarwa." amatuƙar ba zata Bappa Ali yaji sauƙar maganan Raleeyan acikin kunnensa, wani irin farinciki ne yaji ya lulluɓe zuciyarsa, irin wanda bai taɓa jiba a rayuwarsaba ko randa aka haifa mishi Dady baiji wannan farin cikinba, Idanunsa ne suka ciko da ƙwalla, jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi, sanyi, cikin ƙarfin guiwan da ya samu kansa aciki, yace. "Alhamdulillah,
Allah abun godiya. Tabbas dama idan da rai to tabbas da rabo, sannan ba acire rai da ni'ima haɗi da kyautar Allah, ni dama tun can bancire rai da cewar Saifuddeen bazai sake ji ko magana ba, tunda dama ciwo ne daya sameshi a sama, bawai da shi aka haifesa ba.
Alhamdulillah Raliya mun godewa Allah mai rayawa mai kashewa mai badawa mai hanawa mai cuta da waraka".
Sosai ya nuna farincikin sa akan hakan, har ma yace gashinan zuwa Gombe'n, dan idan ba zuwa Gombe'n yayi ba, kwata-kwata bazaiji zuciyarsa ta gamsu ba.
Suna gama waya da Raleeyan ya shige cikin gida dan ya faɗawa Aunty Meena, fuskarsa cike take da fari'a, kallo ɗaya zaka masa ka fahimci cewa yana cikin matsanancin farinciki.
Kai tsaye makullin matarshi ya ɗauka wacce Baga daɗe da saya mishi ita kuma hannunshi bai gama faɗawa a tuƙin sosaiba. Kai tsaye unguwar Sirankiyo ya nufa gidan ƙanwarsa Goggo Dada mahaifiyar Ahmad,
koda taji wannan dadɗan labarin da sanyin safiya cewa tayi ƙafarshi ƙafarta da ita zaije.
Acan ɗakin Hayatuddeen kuwa, Ahmad ne ya ƙira Ishaq ya faɗa masa buɗuwan kunnen Saifuddeen ɗin, sosai Ishaq ya shiga shock dajin haka'n, lokaci ɗaya kuwa ya zube akan guiwowinsa inda yayi sujjada, tare da yiwa Allah godiya, sannan ya fashe da kukan farinciki, wanda shi dama yanaji ajikinsa cewa, watarana Allah zai dubi Saifuddeen ya yaye masa koda ɗaya daga cikin larurorinsa, kukan farinciki yayi sosai cikin gida ya shiga ya sanarwa Ummanshi da Babansu sosai sukayi farin cikin wannan labarin inda shima sukayi mishi addu'ar Allah ya yaye mishi tasa larurar shima ɗin.
, take kuma ya miƙe tsaye, waje ya nufa, dan so yake yaji muryan abokin nasa acikin kunnuwansa.
Shi kuwa Saifuddeen har yanzu akwance yake, sai nannauyan nishi yake saki akai akai, dan har zuwa yanzu bayan nasa bai sake ba.
Ummi na fitowa daga sashin nata, sukayi karo da su Adda Rahama, wanda zuwansu kenan. Cikin sauri Adda Rahama ta faɗa jikin Ummi tare da sakin kuka mai ɗauke da dariya.
Saboda farinciki Ummi ma rungume Adda Rahaman tayi, cikin matsanancin farinciki Adda Rahama'n tace. "Ummi ina Saifuddeen, inason naji muryarsa, ina kuma so yaji magana ta, wanda tsawon shekara 20 kenan da ya daina jinta".
Hawaye ne suka silalo daga cikin idanun Ummi, hannun Adda Rahman ta kama.
cikin sanyin murya tace. "Zakiga Saifuddeen Rahama, amma yanzu mutafi zuwa ɓangaren Zaleeha, saboda Saifuddeen yace min tariga da ta suma, muje tana buƙatar taimakon mu".
Idanu Adda Rahama taɗan zaro atsorace, bakinta na rawa tace. "Subahanalli Ummi me yake faruwa ne?".
ɗai-dai lokacin Dr Adnan ne ya ƙaraso inda suke tsayen, cikin girmamawa ya durƙusa har ƙasa inda ya gaishe da Ummi'n, amsa masa tayi tana murmushi, cikin kulawa dan Ya Adnan kamar Nuruddeen take ganinshi cikin jin daɗin zuwansu tace.
"Yauwa Adnan kaje ciki, Saifuddeen yana ta kukan cewa bayansa na riƙewa ka isa ka duba shi yana ɗakin auta".
Cikin sauri Dr.Adnan ɗin yace.
"To." take ya wuce sashin Ummi'n. Ummi kuwa hannun Adda Rahama ta kama suka nufi sashin Saifuddeen, dan dama Saifuddeen din yace mata Zaleehan nacan sashinsa.
Gaba ɗaya hankalin Ummi, da kuma na Adda Rahama atashe yake. tun daga falo suka hango ƙofar bedroom ɗin nasa a buɗe,
cikin sauri Ummi ta ƙarasa Adda Rahma na biye da ita, inda suka kutsa kansu cikin ɗakin, hango Zaleehan da sukayi nannaɗe acikin bargo ne, yasasu ƙarasawa cikin ɗakin da sauri.
Hankalin Adda Rahman a tashe ta ɗan yaye bargon, tare da ɗago hannun Zaleeha'n, luuu haka taji hannun ya sake, idanu taɗan zaro, tare da kai hannunta saitin hancin Zaleeha'n, jin har yanzu bata numfashi yasa hankalinta sake tashi cikin kiɗima ta kalli Ummi data ɗan kauda kanta dan surkunta. Atsorace Adda Rahman tace.
"Ummi Zaleeha fa bata numfashi, meya sameta ne?".
Cikin fargaba Ummi ta janye blanket ɗin da Zaleehan ke lulluɓe dashi dan ganin akwai sutura a jikinta, idanunta ne suka sauƙa akan jinin da ya ɓata farin zanin gadon, wanda har aƙafan Zaleehan, akwai ɗigo ɗigon jini da ya bushe ajikin fatarta.
Wani irin matsanancin tausayin Zaleehan ne ya daki zuciyar Ummi, har saida taji ƙwalla sun cika mata ido.
Adda Rahama ma da idanunta suka sauƙa akan jinin dake jikin zanin gadon, ji tayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, tausayin Zaleehan ne ya kamata, cikin sanyi hawaye na tsastsafo mata cikin ƙwayar idonta ta zauna abakin gadon tare da tallafo kan Zaleehan ta ɗaura akan cinyarta, dan dukkansu sun fahimci me ya faru da Zaleeha'n.
Cikin sauri cikin kiɗima Ummi ta wuce toilet, da kanta ta haɗa wa Zaleehan ruwan wanka me zafi acikin bathtube, wanda tasan idan ta shiga zata ɗanji dama dama, saida ta haɗa komai daya dace, sannan ta fito daga cikin toilet ɗin dan tama mance a samu ta farfaɗo yafi dacewa. Haryanzu kuwa Adda Rahama na riƙe da Zaleehan,
ɗan ƙaramin fridgen dake ɗakin, Ummi ta buɗe, tare da ɗauko goran ruwa, dawowa kan gadon tayi ta zauna, hannu tasa taɗan ɗago kan Zaleeha dake cinyar Adda Rahama, buɗe murfin goran tayi, tare da ɗan tsiyayan ruwan ahannunta, ɗan yayyafa ruwan tayi akan fuskar Zaleeha, waiko zata farfaɗo amma shiru, hakanne yasa zuciyar Adda Rahama soma bugu da sauri sauri, saboda tsoro.
Ummi ma kanta ta tsorata da hakan, sai-dai batayi ƙasa a guiwa ba, saida tayi hakan kusan sau uku, kafun taji Zaleehan ta saki wani irin numfashi, tare da sauƙe nannauyan ajiyar zuciya. Ganin ta farfaɗo yasa su Ummi sauƙe ajiyar zuciya.
Ahankali ta shiga ɗan jujjuya kanta, batare da ta buɗe idanunta wanda sukayi nauyi haɗi da kumburi, cikin muryarta da ta dashe wanda ko fita da kyau batayi, amatuƙar wahalce batare da ta dawo cikin hayyacinta ba tace.
"Dan Allah Hamma Saif kayi haƙuri, zafi nakeji zan mutu, wayyo Allah na Hamma Saif kayi haƙuri dan Allah zafi....".
Wani irin kuka ta fashe dashi me tsuma zuciya, still bata buɗe idanunta ba.
Matsanancin tausayinta ne ya cika zuciyar Ummi, ahankali cikin sassanyar murya tace.
"Zaleeha, buɗe idanunki kinji, ba Hamma Saif ɗinki bane nice Umminkune, buɗe idanunki kinji."
Jin muryan Ummi acikin kunnuwanta, yasa ahankali taɗan soma bude idanunta wanda sukayi dishi-dishi, suka kuma kumbura kaman wanda ta yi sati guda tana kuka.
Ganin Ummi yasa ta faɗa jikinta tare da ƙanƙameta ƙam, sosai ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya dan gani take kamar zai sake zuwa ya danneta. Bayanta Ummi ta soma shafawa, cikin tausayawa tace.
"Ya isa hakanan yi haƙuri ki daina kukan kinji, sannu ko."
Kanta ta shiga girgizawa, dan bazata iya tsaida kukan nata ba, saboda wani irin ciwo da zafi da takeji aƙasanta, ga kuma wani irin zazzafan zazzaɓin da lokaci ɗaya ya sauƙar mata,
Ummi ne ta dubi Adda Rahma, wanda tausayin Zaleehan yasa yanayinta ya sauya, idanunta duk sun kawo ruwa.
Cikin sanyi Ummi tace. "Nahaɗa mata ruwan wanka, kamata kuje toilet, dan Allah Rahma kiyi mata duk wani abun daya dace duk wani abu da kika san zaki iya yiwa Raliya ko Raihana kiyi mata".
Sai ta kuma kalli Zaleeha cikin tausayawa tace.
"Daure Addanku ta taimaka miki,ki ɗauketa kamar Adda Maryam ɗinki kinjiko."
Kai Zaleeha ta gyaɗa cikin sanyi da zubda hawaye tayi ƙasa da kanta dan azabar kunyar Ummi da takeji.
Ita kuwa Ummi murya a tausashe tace.
"Bari naje nasa anemo mata magani, dannaji jikinta da zafi kaman wuta."
Kai Adda Rahama ta jinjina, cikin tausayawa ta jawo Zaleehan, da ƙyar ta iya ɗago ta, saboda yanda ta kasa tsayuwa da ƙafafunta, Cikin lallami Adda Rahama ta jata zuwa cikin toilet ɗin dake cikin ɗakin.
Dr Adnan kuwa koda ya isa ɗakin Hayatuddeen, duƙufa yayi akan Saifuddeen wanda zuwa yanzu bayan nasa ya sake riƙewa sosai. Hankalin Dr Adnan ne ya tashi saboda yanda yaga jikin Saifuddeen ɗin, ya sake ɗaukan zafi. Hayatuddeen kuwa ganin Dr Adnan yazo ya sa ya tashi ya fita daga ɗakin, zuciyarsa cike da murna ya ciro wayarsa daga cikin aljihu, inda ya dannawa numbern Zakariyya ƙira. Wayar bata wani jima tana ringing ba Zakariyya ya ɗauka.
Murmushi Hayatuddeen yayi, cikin jin daɗi yace. "Zakariyya kunnuwan Hammana sun buɗu, Hammana ya warke daga cutar kurumta Zakariyya".
Jin maganan Hayatuddeen ɗin yasa jikin Zakariyya ya ɗauki rawa, samun kansa yayi cikin wani irin farin ciki, dan sosai abun ya taɓa zuciyarsa, cikin matsanancin farinciki yace.
"Masha Allah Alhamdulillah, Hayatuddeen yanzu Hamma Saifuddeen najin magana kenan?" Cikin matsanancin farinciki Hayatuddeen yace.
"Eh Zakariyya, ni narasa inda zansa kaina ma saboda farinciki, yanzu Hammana ya zama kaman kowa, saidai kuma dan Allah kada ka faɗawa kowa hakan, dan Hamma Saifuddeen da kansa yace bayason Adda Zaleeha ta sani, wanda kuma bansan menene dalilinsa nayin hakan ba."
Kai Zakariyya ya jinjina, cikin tsananin jin daɗi yace.
"Insha Allah bazan faɗa mata ba Hayatuddeen, anjima kaɗan nima zanzo, bazan iya jurewa ba Hayatuddeen zanzo naga Hamma na kuma ji muryarsa."
Kai Hayatuddeen ya jinjina, tare da cewa. "Shikenan Zakariyya sai kazo, saidai kuma tun ɗazu Hamma Saifuddeen ke cewa bayansa nayi masa ciwo, amma yanzu Ya Adnan yazo yana dubashi."
Cike da zumuɗi Zakariyya yace. "Ganinan zuwa Hayatuddeen, kuma insha Allah komai zai dai-da-ita."
Acan sashin Saifuddeen kuwa, Ummi naganin shigansu cikin toilet, ta fita daga cikin ɗakin, saboda tanaso taje ta duba Saifuddeen. Adda Rahama kuwa cikin kulawa haɗi da lallami tace da Zaleeha ta cire kayan jikinta, tare da miƙo mata towel tace ta ɗaura kana ta juya mata baya dan kauda idonta kanta, da ƙyar ta iya cire kayan nata, sannan ta ɗaura towel ɗin cikin hikima yadda bata tsaya ba komai a jikinta ba.
Da ƙyar Adda Rahama ta iya zaunar da ita acikin ruwan zafi'n, wani irin narkekken ƙara ta sake, saboda yanda taji ƙasanta na mata zafi da raɗaɗi kaman an watsa mata barkono, kuka ta saka tana ɗan yayyarfa hannunta.
Cike da tausayinta Adda Rahama tace "Sannu ko kiyi haƙuri kinji, idan ruwan ya gama ratsaki, insha Allah zaki ɗanji sauƙi."
Asakalce ta ɗan jinjina kanta, duk da zafin da takeji haka ta ɗan daure ruwan ɗumin ya ratsa cikin jikinta, saida ruwan yaɗan fara salancewa, sannan Adda Rahama ta sake zuba mata wani ruwan me ɗumi, tana sake shiga ruwan kuwa gumi ya fara fesowa daga jikinta, taji zafi sosai saidai bakaman na farko ba. Saida Adda Rahama tasa mata ruwan ɗumi sau uku, sannan ta fita inda tace mata taɗan ƙoƙarta tayi wanka tsarki.
Ummi kuwa daga ɗakin kaitsaye sashinta ta wuce, anan ɗakin Hayatuddeen tasamu Dr Adnan ya saka Saifuddeen ɗin agaba, yana ta faman auna jikinsa.
Cikin kulawa, akuma sanyaye tace.
"Dr Adnan ya jikin nasan dai? Babu wata matsala kam dai ko?".
Ɗan numfasawa Dr Adnan yayi, haɗe da cewa.
"To jikin nasa dai da sauƙi, za 'ace, yanzu so nake naji problem ɗin nasa, dan ina tunanin ma saina ƙira Dr.Aleeyu na faɗa masa ko akwai shawarwarin da zai bamu".
Kai Ummi ta jinjina, tare da sakin wani gauron numfashi, ganin yanda Saifuddeen ɗin keta cije lips ɗinsa ne, yasa ta juyawa ta fice daga cikin ɗakin, kaitsaye kitchine tawuce, dan tanaso taɗan haɗawa Zaleeha tea. Zaleeha kuwa da zazzaɓi yayi mata wani irin mummunan kamu, da ƙyar ta iyayin wankan tsarki da kyar ta ɗaura towel a jikinta kana ta zauna bakin baf ɗin, akasalance da muryarta wanda bata fita ta shiga ƙiran sunan Adda Rahama,
Adda Rahama wanda ta gama kimtsa kan gadon da suka ɓata, jin Zaleehan na ƙiranta ne yasa ta nufi banɗakin, tana shiga Zaleehan ta miƙo mata hannu, cikin sheshsheƙan kuka tace. "Ki riƙeni Adda Rahama jiri nakeji, cikin jikina da ƙafafuna duk ciwo sukemin".
Cikin tausayawa Adda Rahama ta riƙota, haɗe da cewa.
"Sannu kinji kiyi hakuri kinji, Ummi zata kawo miki magani zai daina insha Allah."
ahaka suka fito daga cikin toilet ɗin,