Showing 78001 words to 81000 words out of 239422 words
Chapter 27 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
gidansu Zaleeha zasuje ba ai ita a zatonda ko ɗan wani garding zasu je to koma meye haɗina da gidan".
sosai tsarin gidan ya tabbatar mata da nagarta da darajar masu gidan.
Zakariyya wanda ya fito daga ɓangaren Mamy ne ya hangosu, cikin sauri ya ƙaraso garesu, fuska ɗauke da tsananin farin ciki yace.
"Oyoyo Hamma Saifuddeen, yau kaine agidan namu."
murmushi Saifuddeen yayi tare da miƙawa Zakariyyan hannu, suka yi musabaha, cikin girmamawa Zakariyya ya dubi Ameena, fuska ɗauke da murmushi yace.
"Sannu da zuwa Aunty Ameena."
Murmushi Ameena tayi tare da cewa.
"Yauwa Zakariyya ya makaranta?".
tasan sunan Zakariyyan ne saboda, yawanci tana ganinsa wajen Hayatuddeen.
Zakariyyan ne yayi musu jagora zuwa sashin Baba Malam,
Suna tafene tana mai maganar zuciya.
"Uhum kalli ƙaninta shi da yake na mijima yanada kyau irin kyan da ba'a gajiya da kallon fuskarsa inaga ita mace." sosai taji kishin Zaleeha ya daki ranta tana masifar son Saifuddeen shiyasa kuma take masifar kishinsa, ya zatayi da ranta randa zataga Saifuddeen yashiga ɗaki ɗaya da wata mace sun rufe ƙofa ina zata sa ranta?."
A haka tana zancen zuci suka isa cikin gidan
kasancewar Mamyn ma bata sashinta tana nan wajen Baba Malam ɗin.
Koda suka shiga da matuƙar farin ciki Baba Malam ya tarbesu, cikin girmamawa haɗi da mutuntawa suka gaisa, yaji daɗin ganinsu ƙwarai, nan Mamy ta cika musu gabansu da kayan ciye ciye, itama taji daɗin ganinsu hakanan, saidai kuma ganinsu haka yasa taji sha'awan inama ace da Zaleeha ce, tabbas tasan da zuciyar Baba Malam sai yafi haka sanyi.
Cikin body language Saifuddeen suka sha hira shida Baba Malam, sosai Baba Malam yayi musu nasiha mai shiga jiki, Mamy kuwa kayayyakin humra ta haɗawa Ameenan ta bata, sosai kuwa Ameenta taji daɗi, tabbas taga kirkin mutanen hakan nema yasa ta ɗanji zafin kishinta ya ɗan ragu akan ƴarsu dan ita a zatonta Mamy ce maman Zaleeha.
Nan dai sukayi musu sallama, inda har bakin motarsu Mamy da Baba Malam ɗin suka rakasu. Kaitsaye gida suka dawo, inda Saifuddeen yayi masauƙi a falon Ummi.
Washegari yau ya kamana monday sannan kuma yaune Ameena zata fara zuwa aiki nan Federal Medical Center wato (F.M.C) Dan angama yi mata komai, inda kuwa suka amsheta batare da wani matsala ba, saboda takardunta masu kyaune.
Kamar kullum yau ma saida taje ta gaishe da Ummi, kasancewar babu wadataccen time yasa sama-sama taɗan taya Raliya aiki, dan kuwa ƙarfe 7:30 ne dai-dai lokacin zuwa wajen aikin nata, suna kammalawa ta koma ɗakinta, nan ta kimtsa kanta cikin kayansu na nurse, wato riga da wando farare da kuma ɗan madaidaicin hijab, kayan suna mata kyau ba laifi, sannan kuma basa fidda tsiraicin ta, don basu kama jikinta ba ko kaɗan.
Tana gama kammala shirin nata, taɗauki ƴar handbag ɗinta, kai tsaye ɗakin Saifuddeen ta nufa, nan ta iskesa yana aiki ya saka laptop ɗinsa gaba, zama tayi anan kusa dashi, ɗago kansa yayi ya kalleta, murmushi ta sakarmasa, kana ta miƙe, ƙarasowa gabansa tayi, ɗan ranƙwafowa tayi tare da manna masa kiss akan laɓɓansa, cikin soyayya tace.
"Kakulamin da kanka saina dawo."
tana faɗin haka ta juya tana me ɗaga masa hannu, murmushi yasakar mata tare da ɗaga mata hannu, tana ficewa kuwa ya sauƙe ajiyar zuciya, cikin ransa yace.
"Alhamdulillah, aini naji daɗin fara zuwa aikin naki ma, nasan ko bakomai zakina dawowa agajiye, daganan kuma zan huta da jarabanki, da kuma wannan tsotse tsotsen naki Allah kiyaye hanya hajia rabo tawo."
Murmushi yayi tuno wasu abubuwan da Ameena ke mishi shida kanshi yasan Ameena ta sonshi irin zazzafan so ɗin nan shiyasa yake ƙoƙarin ganin ta samu nitsuwa dashi.
Kansa ya maida ga laptop ɗinsa inda yaci gaba da aikinsa cikin kwanciyar hankali.
Sai dai can cikin ransa yana jin ɓaƙin cikin duk fa abin take mishi ta taɓa yiwa wani ƙaton,
A saman lips ɗinsa yace.
"Waya sanima iya sau dubu nawa ya kusanceta wata ƙil shinema ya maida jarabebbiya yana ɗaya daga abinda yake sashi kasa sakin jiki da ita.
Ameena kuwa Sule driver ne yakaita wajen aikin nasu, cikin ɗaya daga cikin motar Saifuddeen wanda baiwani cika hawanta sosai ba.
*** ***
Alhamduillahi akwana atashi asaran me rai, rayuwa tana ta tafiya kwanaki sun shuɗe i zuwa makonni makkonni su juya i zuwa watanni.
Yau Ameena da Saifuddeen suke cika wata biyu da sati biyu cif-cif da aure, harzuwa yau kuwa Saifuddeen bai taɓa jin son Ameena acikin zuciyarsa ba, sai-dai kuma yana iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin ya sauƙe haƙƙinta dake kansa, sannan kuma yanajin daɗin aikin da yakeyi, ga kasuwancinsa na tafiya. ɓangaren Ameena kuwa sosai rayuwa ta miƙa mata, domin Saifuddeen bai rageta da komaiba duk abinda takeso zai mata in ta buƙaci nitsuwa dashi kuwa yana iya ƙoƙarin shi, kana tana zuwa aikinta cikin kwanciyar hankali, idan ta dawo daga wajen aiki kuwa haka Ummi takesa Hayatuddeen yakawo mata abinci har sashinta, sosai takejin daɗin zama da Ummi da kuma su Raliya, wanda ayanzu takejin cewa sun zame mata ƴan uwa, haka kuma aduk lokacin da take da buƙatar Saifuddeen baya hanata sannan kuma aduk ƙarshen sati yakan tambayanta ko tana da wani buƙata na kuɗi? koda tace batada shi kuwa, yakan bata wasu kuɗi yace ta riƙe watarana ko zatayi amfani dashi.
Sai dai a cikin ƴan kwanakin da suka wuce gaba ɗaya takan kasa ganewa kanta, hakanan take fama da matsanancin ciwon kai, sannan kuma bata wani jin daɗi, sai-dai kuma abun baishiga jikinta ba, dan tanayin komanta batare da gajiyawa ba.
Yaudai tunda ta fito wajen aiki takejin yanayin jiri naɗan ɗibanta, haka dai ta share, har zuwa kusan la'asar, jin abun na tsanantawa ne yasa tayi tunanin cewa kodai yunwa ne takeji, hakan yasa, batare da lokacin tashinsu yayi ba, ta ɗauki excuse, kaitsaye Napep ta tara ta nufo gida.
Koda tashigo cikin gidan ɓangaren Ummi ta nufa, dan har wani ji take cikinta na murɗawa, hakan yasa ta al'laƙanta abun da cewa, yunwa ne kawai keson takurata. Afalo ta iske Ummi da Hayatuddeen wanda dawowansa daga makaranta kenan, jakarta ta ajiye, zama tayi akan sofa tare daɗan ƙaƙalo murmushi, cikin son daurewa yanayin da takejin kanta aciki tace. "Ummi sannu da gida."
Cikin kulawa Ummi tace. "Yauwa Ameena har kuntaso daga wajen aikin?."
Girgiza kai tayi tare da cewa.
"A'a wallahi, kawai dai naɗanji yunwa na damuna ne shine nace bari na gudo gida."
Murmushi Ummi tayi tare da faɗin.
"Ayya sannu to, Raliya na kitchine bara nace ta zubo miki abinci kici ko". Ummi taƙare maganar cikin kulawa.
Akunyace Ameenan ta miƙe tare da cewa.
"Bari naje na zubo da kaina kawai Ummi kada asata wahala."
Nan tamiƙe ta wuce kitchine ɗin.
Ummy kuwa cewa tayi.
"To inaga fa gwara Sule ya rinƙa kai miki abinci bana son wuni da yunwa da kikeyin nan."
Tana ƙoƙarin shiga kitchin ɗinne tace.
"Ba komai fa Ummy in naji yunwa ina sayan abu inci kinga wani Lokacin kuma inama tafiya da abinda zan ci."
Kai kawai Ummy ta jinjina, ita kuwa Ameena.
Raliya ta iske tsaye tana ta ƙoƙarin haɗawa Saifuddeen pepper chicken soup.
Cikin kulawa Ameena tace.
"Sannu agogo sarkin aiki."
Murmushi Raliya tayi tare da faɗin.
"Ke kuma likita bokan turai ba."
Dariya sukayi su dukansu, nan Ameena ta buɗe food flask ɗin da aka zuba haɗaɗɗiyar fried rice aciki, plate ta ɗauka inda ta ɗebi kaɗan, coslow ta zuba asaman shinkafan sannan ta buɗe wata ƴar kula wanda ke ɗauke da liver sauce, kaɗan ta zuba akan abincin, sannan ta sanya spoon tundaga cikin kitchine ɗin tasoma ci. Dubanta Raliya tayi tare da sakin murmushi, har acikin ranta tana ƙaunar Ameenan badan komai ba kuwa saidan ƙaunar Saifuddeen da Ameenan keyi.
Saifuddeen kuwa shigowarsa cikin falon kenan, yana riƙe da kwalin holandia milk inda yake sipping da kaɗan kaɗan.
Dai-dai lokacin Ameena ta fito daga cikin kitchine ɗin, hannunta riƙe da plate ɗin abinci.
Ɗan jim tayi tare da lumshe idanunta, lokaci guda taga wani duhu naneman mamaye ganinta, taku ɗaya zuwa biyu tayi, taji gaba ɗaya jikinta ya saki wani irin jiri mai ƙarfi ya kwasheta, nan tatafi luuuuu tafaɗa kan kujera, take kuwa plate ɗin hannunta ya faɗi, abincin ya tarwatse acikin falon.
Arazane su Ummi da Hayatuddeen sukayo kanta, cikin tsananin damuwa Ummi tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, Ameena! Ameena lafiya kuwa?." aruɗe Ummi tayi maganan tana me jijjiga Ameena'n, Saifuddeen ne ya tuƙa wheelchair ɗinsa inda ya ƙaraso cikin sauri, hannunsa yakai yaɗan taɓa fuskar Ameena'n, tare da ɗan bubbuga kumatunta.
Ahankali taɗan buɗe idanunta wanda sukayi luhu-luhu dasu, dishi-dishi haka take ganinsu.
Hannunta ya kamo ya riƙe acikin nasa, cikin kulawa ya ɗaura hannunsa akan goshinta, jin zafi ajikinta yasa shi ɗago kansa ya kalli Ummi.
Jin jina kai Ummi tayi tare da cewa.
"Hayatuddeen miƙomin wayata naƙira Dr Adnan."
Cikin sauri kuwa Hayaruddeen yamiƙo mata wayan nata.
Dialing numbern Dr Adnan ɗin Ummi tayi, bugu biyu ya ɗauka, nan ta shaida masa abun dake faruwa, cikin sauri kuwa yace.
"To Ummy ganinan zuwa."
Anutse Saifuddeen ya gyarawa Ameenan kwanciyarta akan kujera, inda har yanzu yana riƙe da hannunta acikin nasa. Hakanne yasa Ummi taji wani irin sanyi acikin ranta, saboda dama burinta ne taga Saifuddeen ɗin na kulawa da Ameena.
Cikin mintuna ƙalilan Dr Adnan da ya iso, har zuwa lokacin kuwa Ameena dishi-dishin take gani a idanunta.
Jininta Dr Adnan ya ɗiba, sannan yace zaije yayi checking ɗin jinin nata, yana dawowa, amma kafunnan asama mata wani abu taci.
Ummi da kanta tahaɗawa Ameenan maltina da madara, nan ta ɗan ɗagota cikin kulawa ta bata tasha, tana gama sha kuwa ta koma ta kwanta, gefenta Saifuddeen ya koma, nan dai sukayi jigum suna jiran dawowan Dr Adnan.
Inda duk bayan minti ɗaya sai Ummi tayiwa Ameenan sannu.
Turo ƙofar falon Dr Adnan yayi ya shigo, fuskarsa ƙunshe take da zallan farinciki marar misaltuwa.
Zama yayi akan kujera tare da duban Ummi, murmushi yayi inda ya kuma duban Saifuddeen, cikin farin ciki ya tashi ya rungume Saifuddeen ɗin, abun daya basu mamaki kenan.
Ɗan janye jikinsa yayi tare da kamo hannun Saifuddeen ɗin ya riƙe, cikin yanayin farin ciki yace.
"Congratulation My brother, tabbas ƙarfin ikon Allah ya wuce misali Alhamdulillah yau dai ɗaya daga cikin tabbacin da Dr Acash ya bamu ya tabbata saura na biyu, domin da yardan Allah ka kusa zama Baba, dan kuwa Ameena na ɗauke da ciki har na tsawon wata biyu!!"
Cikin tsananin mamaki Saifuddeen dasu Ummi ke kallon Dr Adnan.
Kai ya gyaɗawa Ummy tare da ce mata,
"Eh Ummy matar Saifuddeen nada shigar ciki har na tsawon wata biyu."
Cikin wani irin matsanancin farin ciki Ummi tace.
"Alhamdulillah Allah abun godiya, Alhamdulillah, tsarki ya tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, tabbas kaine me kowa me komai, me kumayi alokacin da yaso, sannan ya hana alokacin da yaso!".
Tuni har ƙwallan farin ciki sun cika idanun Ummi.
Shikuwa Saifuddeen lumshe idanunsa yayi yana murmushi mai ɗauke da zallan farin ciki.
Hayatuddeen kuwa wani irin tsalle ya buga, tare da faɗawa jikin Raliya cikim matsanancin farin ciki yace.
"Wayyo Allah na daɗi kasheni zanga ɗan Hammana nima."
Raliyanma da matsanancin farin ciki yasa hawaye suka gangaro daga cikin idanunta, ta rungume Hayatuddeen ɗin, duk da cewa ɗazu suka gama faɗa dashi, amma yanzu farin cikin da suke ciki ya goge wannna faɗan.
Ameena kuwa jin abun da Dr Adnan yafaɗa yasa ta ɓoye kanta cikin hijabi, dan wani irin kunyan Ummi ne ya kamata, cikin zuciyarta kuwa wani irin farin ciki ne wanda bata taɓajin irinsa ba ashe zatonta gsky ne cikine da ita.
Tashi Ummi tayi inda tazo ta rungume Ameena'n, cikin matsanancin farin ciki tace.
"Tabbas aurenki da Saifuddeen yazame mana al'khairi agremu Ameena, Allah yayi miki al'barka ya kuma sauƙeki lafiya."
Akunyace Ameena taɗanyi murmushi tare da sadda kanta ƙasa.
Raliya kuwa sakin Hayatuddeen tayi, tare da zagayowa ta rungume Ameena'n, cikin farin ciki tace.
"Allah ya sauƙeki lafiya Auntyna."
Asanyaye Ameena ta rungumeta tare da faɗin "Ameen."
Murmushi Dr Adnan ketayi, yayinda Ummi kuwa bakinta ya kasa rufuwa.
Ashe zataga jinin Saifuddeen ɗinta aduniya? Ta godewa Allah da cewar nakasan sa bata shafi lafiyarsa ba.
Saifuddeen ma murmushi yake ta saki, sosai yaji wani irin farin ciki aransa, ashe shima zai zamanto uba, cikin ransa yake ta yiwa Allah godiya, da wannan kyautar daya basa.
Nan Ahmad ya shigo ya iske labari me matuƙar daɗi, cikin farin ciki kuwa ya rungume Saifuddeen yana me tayasa murna.
Ummi ce tace da Raliya ta taimakawa Ameena'n ta yi wanka sannan ta kwanta ta huta.
Hakan kuwa akayi Raliya ne ta riƙeta suka je har part ɗinsu, sannan ita ta haɗa mata ruwan wanka, tananan har Ameenan ta fito daga wanka, nan ta kimtsa kanta, inda ta haye gado ta kwanta, sai alokacin Ameena tafita don bata waje ta huta.
Can ɓangaren Ummi kuwa Dr Adnan ne ya haɗa kayan aikinsa inda ya musu sallama ya koma office.
Nan Saifuddeen ma ya fice daga falon.
Ummi kuwa waya ta ciro inda ta dannawa numbern Adda Rahama ƙira, koda ta sanar da Adda Rahama maganan cikin Ameena'n, baƙaramin farin ciki tayi ba, har hawaye saida ta zubar.
Nan tace tananan zuwa da yamma.
Ummi na gama waya da Adda Rahama taƙirayi Bappa Ali ta faɗa masa, baƙaramin farin ciki kuwa Bappa Ali yayi ba, sosai yaji daɗin maganan.
Ahankali ya tura ƙofar ɗakinta ya shiga ɗakinda tun da tazo gidan bai taɓa shigaba sai yau kuma yanzu, kwance take akan gado, inda ta lumshe idanunta, dan bacci ne keson ɗaukarta.
Ƙarasowa cikin ɗakin yayi, inda ya nufo inda take.
Jin motsinsa yasa ahankali ta ɗan buɗe idanunta, ganinsa yasa ta sakin murmushi, kusa da ita ya ƙaraso, ahankali yakai hannunta inda ya shafi kanta, cikin kulawa fuska ɗauke da murmushi ya jinjina mata kai tare da buɗe mata hannunshi, alamun tazo yaji ɗumin Baby'nshi murmushi ta kuma sakar masa tare da tashi zaune ta faɗa jikinsa, yau yana cikin farin ciki hakan ne yasa yayi hugging ɗinta, haɗe fuskarsu waje ɗaya tayi nan ta haɗe bakinsu, yau kam biye mata yayi, inda ya soma sucking lips ɗinta tare dasa hannunshi yana ɗan shafa cikinta.
Daga nan kuma ta shiga gwada masa salon romance ɗinta.
Sosai yau ya biye mata, hakanne yasa daɗin da taji yau dabanne, sannan aɓangarensa shima babu laifi.
Da Yamma kuwa saiga Adda Rahama tazo, rungume Saifuddeen ɗin tayi tana mejin matsanamcin farin ciki, haka dai ta zauna har kusan magriba sannan ta-tafi.
Acikin dangi kuwa kowa yaji labarin samun cikin Ameena sai yayi murna sosai ƴan uwa da abokanshi kabsun cika da farin ciki.
Haka dai Ameena keta renon cikin jikinta kulawa take samu sosai da sosai daga wajen gaba ɗaya mutanen gidan, aɓangaren Saifuddeen ma yanzu kulawa na musamman yake bata, duk da cewa bawai yana wani damuwa da ita bane, amma yana kulawa da ita yanda ya kamata, sannan kuma cikin nata ma ba irin me laulayi ɗinnan bane, tana zuwa wajen aikinta, sannan kuma bata yarda ta gaza wa Saifuddeen takowani ɓangare ba, naci da jaraba kuwa sai abunda ya ƙaru, wani lokaci Saifuddeen idan yaga abun nata yayi yawa, guduwa yake sashin Ummi, bazai dawo ba kuwa sai ya tabbatar da cewa tayi bacci in gari ya waye taita fushinta yaita mata dariya yace zata lalata shi daga nan ta huce.
Daga can gidansu Zaleeha kuwa suma murnan samun cikin Adda Maryam wanda yakeda wata ɗaya amman sabida yawan laulayinshi duk dangi sun gane,
inda Ya Ameenu ke cike da farin ciki yana kulada matarsa sanyin idanunshi tamkar ransa .
A hankali rayuwa ke juyawa watanni na tafiya tuni lokaci ya tafi.
Numan.
To zuwa yanzu dai Zaleeha tana jin zazamanta cikin garin Numan ɗin tamkar zama cikin kurku ne, domin hankalinta da nitsuwar kab basa jikinta,
Kullum da begen iyayenta da ƴan uwanta take kwana, musaman Adda Maryam da suna magana da ita.
Tana son komawa cikin ƴan uwanta tayiwa mahaifinta biyayya amman sai taji bazata iyaba.
Sauƙin ta ɗaya tana ɗan samun nitsuwa cikin musulmai ƴan uwanta na rugar fulanin nan,
do kuwa sosai sukayi sabo da Aisha, sannan kuma tana ɗebe mata kewa,
Damuwar da take ciki ya baiyana a jikinta domin ta rame fuskarsa tayi fiyau sai dai daga ɓangaren kyawunta kuwa sai abun da yaci gaba, dan wani irin fresh skin ɗinta yayi, komai nata yayi normal, fatarta takara haske da sheƙi sakamakon kayan fruits da take ci da kuma yanayin ni'imar wurin, ita kanta tanajin sauyi ajikinta sosai ramar da tayi sai yasa hancinta ya ƙara baiyana, daga gefe kuwa kullum Aisha saita kawo mata abinci daga gidansu, Man Liman kuwa sosai yake janta a jiki in tazo ta sameshi a gida har sun ɗan saba.
Yauma tana gidan su Aishan kasan cewar yau jumma'a ne bayan an sauƙo daga sallan jumma'an ne Man Liman ya iske su a tsakar gida ƙarƙashin bishiyar ceɗiya bisa dukkan alamu suma sallan sukayi.
Cikin girmamawa suka haɗa baki wurin ce mishi.
"Baffa sannu da dawowa."
Murmushi yayi tare da miƙa musu ledan cefen da ke hannunshi tare da ce musu.
"Yauwa sannunku tagwayen Baffa, kunyi sallanko?."
Murmushi sukayi tare da gyaɗa mishi kai alamun eh.
Man Liman dattijone me karamcin gaske,
Har ya wuce sai kuma ya juyo ya kalli Zaleeha cikin fullanci yace.
"Zaleehatu taho ki ɗan rubuta min wani abu,