Showing 132001 words to 135000 words out of 239422 words
Chapter 45 - Nakasa Ba Kasawa Bace Part 2 Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt
Ngs Bayan duk sun gama fita daga falon Ummi kaitsaye ɓangarensa ya nufa, ahankali yake tura wheelchair ɗin nasa, wayarsa ƙiran Samsung ya ciro tare da laluɓo number'n Ameena ya tura mata text, ganin saƙon ya tafi ne yasa ya maida wayar cikin al'jihunsa, ahankali ya murda handle ɗin ƙofar ɗakin nasa ya wuce ciki.
Yana shiga kuwa yaɗan rage kayan jikinsa, tare da hayewa saman gadon ya kwanta.
Can ɓangaren Ameena kuwa tana nan zaune taga saƙon text ɗinsa, koda ta karanta ɗan murmushi tayi tare da lumshe idanunta, ita dai dama tun ɗazu da suke cin abincin tagane take takensa, miƙewa tayi tare da ƙarasawa gaban mirror, turare ta ɗan fesa ajikinta, sannan ta fice daga cikin ɗakin, dan dama tun shigowarta ma bata shigo da Adeel ba, yana can wajen Zaleeha.
Ahankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama, duk da tasan cewar bayaji, amma ako yaushe idan zata shigo ɗakin nasa saitayi sallama, kamar yanda addini ya koyar.
Ganinsa kwance akan gado ya sa taɗan saki murmushi, ahankali ta ƙaraso jikin gadon, anan bakin gadon ta zauna. Idanunsa ya zuba mata, ganin haka yasa tace. "Naga message ɗinka, shiyasa nace bari nazo ko kana da buƙatar wani abu ne."
Ɗan lumshe idanunsa yayi, ahankali ya ɗago hannunsa ya nuna ta, alaman cewa.
"Ita yake da buƙata."
Ɗan murmushi tayi, dan har acikin ranta taji daɗin hakan, amma abayyane kuwa gyara zaman ta tayi, tana ɗan murmushi tace.
"Indai nice ae kagama samu, saidai kuma banso shigowa wajenka yau ba, saboda nayi tunanin banice dakai ba yau Zaleeha ce, shiyasa har na kwanta ma ganin message ɗinka ne yasa na fito."
Tafaɗi maganan, tana me zuba masa idanu, dan ƙwarai ta ƙagu tafahimci abun dake wakana atsakaninsa da Zaleeha, wanda yasa bata zuwa ɗakinsa, da kuma zaman da taga tanayi a ɓangaren Ummi.
Take yanayin fuskarsa ya sauya, lokaci guda yaji ransa ya ɓaci, sam baiso jin sunan Zaleehan abakinta ba, dan kwata kwata atsarinsa babu irin wannan rayuwan, da wata daga cikinsu zata kawo zancen abokiyar zamanta agabansa, sam bayaso kwata-kwata, domin yin hakan shikesawa Namiji ya zama kamar munafuki a tsakanin matanshi, shi kuma ko kusa baya fatan haka wa kansa.
Jikin Ameena ne yayi matuƙar sanyi, musamman ma yanda taga ya haɗe gabas da yamma, lokaci ɗaya annurin fuskarsa ta gushe, gaba ɗaya jin zuciyarta tayi babu daɗi dan kwata kwata bataso ɓata masa ba, saidai kuma azuciyarta tana mamakin abun da zaisa ransa ya ɓaci dan kawai ta ambaci sunan Zaleeha, wanda ita kuma tayi hakanne dan ko zataji wani ƙarin bayani daga garesa ta samu ta gwaggwafi sirrin Zaleeha.
Ɗan matsowa kusa dashi tayi tare da kama hannunsa, cikin sanyin murya tace.
"Kayi haƙuri, bansan maganan dana faɗa zai ɓata ranka ba."
Ɗan kawar da kansa gefe yayi, dan yanason nuna mata cewar ko gaba bayason irin hakan. Ganin ya kau da kansa gefe ne, yasa Ameena ta saki ɓoyayyen murmushi, cikin ranta tace.
"To kodai dama bayason zaleeha'n ne? sannan idan da ace ma yana sonta, ai da zaina ƙiranta part ɗinsa, to amma kuma mayataccen kallonta da nake yawan kamasa yanayi mata fa? da kuma zamanta asashin Ummi duk me hakan ke nufi?."
Ɗan jim tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya. " kodai Wataƙila Ummin ne tace ta zauna a part ɗin nasu saboda rashin da akayi mata, dan hakan zai ɗebe mata kewa." Duk acikin ranta take maganan, yarda da abunda zuciyarta ta faɗa mata ne, yasa ta sake kamo hannun Saifuddeen ɗin, tare da tallafo haɓarsa ya zamana suna fuskantar juna,
murmushi ta sakar masa tare da sanya hannu ta kama kunnenta, cikin sanyi tace.
"Kayi haƙuri kaji please." Idanunsa yaɗan lumshe, tare dayi mata alaman cewa.
"Kada ta sake yi masa irin hakan."
cikin ɗanjin daɗi tace. "Insha Allah." rungumesa tayi tare da haɗe bakinsu waje ɗaya. Kasancewar dama tun haɗuwarsa da Zaleehan na ɗazu a cikin mota yakejin kansa amatuƙar buƙace, hakan yasa bai ƙi biye mata ba, haka suka sha romance ɗinsu, bayan komai ya wakana, ya tashi daga kwancen da yake, tare da hawa kan wheelchair ɗinsa, kai tsaye ya wuce banɗaki yayi wanka, yana fitowa itama Ameenan ta shiga, sai sakin ɓoyayyen murmushi take, dan ƙwarai taji daɗin kasancewarsu na yau ɗin.
Koda ta fito ta samu har ya koma ya kwanta, yana ƙoƙarin rufawa jikinsa blanket, kayan baccinta ta sanya sannan itama ta hawo gadon, idanu ya zuba mata, cikin body language ɗinsa yace. "Ina Adeel?"
tana me ƙulle gashinta tace.
"Ai tun ɗazu yana can wajen Amminsa." Ɗan jinjina kansa yayi tare da lumshe idanunsa, dan ya gaji ƙwarai so yake yayi bacci. Ganin baice komai ba yasa ta ce.
"Na karɓoshi ne?" akasalance cikin body language ɗinsa yace. "No idan bazaiyi kuka ba, ki barshi kawai." idanu ta ɗan zaro tare da cewa.
"Chab aikuwa zaiyi kuka kam, halan dai kamanta Adeel ne, abunda kusan kullum da dare sai ya tashi shan nono, ba naje na karɓosa kada ma ya tashi tsakiyar dare ya hanasu bacci."
ta ƙare maganar tana me sauƙowa daga kan gadon, ficewa tayi daga ɗakin, shikuwa blanket yaja ya sake rufe jikinsa, kasancewar har wani sanyi sanyi yakeji saboda gajiya, waist ɗinsa kuwa ciwo yake mai, shikansa yasan me raunine shi awannan ɓigeren, zaiyi ƙoƙarin jurewa, amma fa da za'aran komai ya kammala zaiji gaba ɗaya gaɓɓan jikinsa nayi masa ciwo hakan kuma baya rasa nasaba da larurarsa. Ameena kuwa saida ta fara biyawa ta ɗakinta ta ɗauko hijab kafun ta wucewa sashin Ummi'n, koda taje haka ta samu falon shiru, sai Hayatuddeen kawai dake zaune yana ta faman latsa wayarsa, yayinda ya saƙala earpiece akunnensa, hakanne ma yasa ko shigowan Ameenan bai ji ba, murmushi kawai Ameena tayi, sannan ta wucesa, kai tsaye ɗakin Zaleehan ta nufa, anan bakin ƙofan ta tsaya tare da ɗan ƙwanƙwansawa, jin shiru babu amsa yasa ta ɗan tura ƙofar ɗakin ahankali tasaka kanta ciki. Hango Zaleehan tayi kwance akan gado, yayinda ta ɗaura Adeel asaman cikinta, baccinsu suke cikin kwanciyar hankali, bisa duk kan alama ma Adeel ɗin ya riga Zaleehan bacci, dan yanayin da suke cike ya nuna, kaman cewa Zaleehan na shafa bayansa ne bacci ya ɗauke ta.
Ɗan tsayawa ajikin ƙofar tayi, tana tunanin yanda za'ayi ta tashe su. Ummi wanda fitowrta daga ɗaki kenan ganin Ameena tsaye aƙofar ɗakin Zaleeha yasa ta ƙaraso, cikin kulawa tace.
"Ameena lafiya kuwa, dama bakije kin kwanta bane?".
Ɗan murmushi Ameenan tayi tare da cewa.
"Lafiya ƙalau Ummi, dama Adeel ne nazo ɗauka, gudun kada ya tashi cikin dare yayi ta muku kuka, shine kuma nasamu daga shi har Ammin nasa bacci suke." Murmushi Ummi taɗanyi, ganin yanda Zaleehan ke rungume da Adeel akan cikinta, cikin yanayin ɗan tsokana irin na jika da kaka tace.
"Aikuwa gwara da kikazo dan ban yiyuwa yaro da tsamin murya yazo cikin dare yayita mana kuka, duk ya hanu bacci."
Murmushi Ameena tayi, wanda yayi kama da dariya.
Ƙarasawa Ummi tayi inda ahankali ta ɗan soma janye Adeel ɗin daga jikin Zaleeha, dan bataso ta tashe ta. Zaleeha kuwa dama baccin nata bawai wani nisa yayi ba, cikin bacci taji kaman Adeel din zai faɗi, arazane ta farka tana faɗin.
"Innalillahi Adeel karka faɗi."
Murmushi Ummi tasaki tare da cewa.
"Au dama baccin naki beyi nisa ba kenan, to ba faɗowa zaiyi ba, mamansa ne tazo ɗaukansa, in kuma so kike abarmiki shi ya isheki da kukan dare to." Ɗan mutsutstsuka idanunta tayi, ƙoƙarin tashi daga kan gadon take. Ummi tace.
"Koma ki kwanta, zan miƙa mata shi." Komawa tayi kuwa ta kwanta, ita kuwa Ummi miƙawa Ameenan yaron tayi, tare da sanya hannu ta ragewa Zaleeha hasken wutan ɗakin. Haka suka fito daga cikin ɗakin, Ameena sai murmushi takeyi, tabbas ita kanta ta shida cewar Zaleeha na matuƙar son Adeel, so kuma na tsakani da Allah bawai so na ganin ido ba, kuma har acikin ranta tanajin daɗin hakan, ita dai kishin Saifuddeen ne kawai kesawa taji batason Zaleehan takejin ta tsaneta, amma bacin haka batajin tsanarta acikin ranta. Saida safe tayiwa Ummi kafun ta ficewa daga cikin falon, Ummi kuwa kaɗa kan Hayatuddeen tayi tare da cewa.
Maza yaje ya kwanta, dan tasan halinsa sarai idan ta biyesa sai yakai kusan ƙarfe 1:00 am yana ta faman latsa waya batare da yaje ya kwantaba, sai da asuba kuwa ayita faman tashinsa yaƙi tashi, yana cewa mutane, bacci ne bai ishesa ba, bayan ɓata lokacinsa yake wajen kalle-kalle da kuma rubuce rubucen banza. Falon Ummi ta rufe sannan ta koma ɗaki ta kwanta.
Hayatuddeen kuwa yana shiga ɗakinsa, ya murzawa ƙofar key, nan kan gado ya kwanta, tare dayin playing sabon BF ɗin daya yi downloading.
Ɓangaren Ameena kuwa tana komawa ta samu har Saifuddeen yayi bacci nan ta kwantar da Adeel akan ɗan gadonsa na yara, sannan itama ta haye gado ta kwanta.
Washe gari.
Zaleeha ne zaune nan kan ɗaya daga cikin kujerun falon, kamar kullum sanye take da baƙar doguwar riga, Adeel ne riƙ ahannunta, wanda yasha wanka aka kuma shiryasa tsab cikin wasu haɗaɗɗun riga da wando na yara.
Sosai Zaleeha ke tayiwa Adeel ɗin wasa, shi kuma sai ƙyaƙyata dariya yake.
Raleeya dake zaune agefensu kuwa murmushi kawai take ta yi musu, dan ita kanta tanajin daɗin yanda Zaleehan ke nunawa Adeel ɗin ƙauna.
Ameena ce ta shigo falon cikin ɗan sauri sauri tare da shirinta na zuwa aiki,
Raleeya ne ta dubeta da murmushi akan fuskarta tace.
"Monday tushen aiki ko na sara na tsoranka, kina ta sauri karki makara kenan." Jakan dake hannunta ta rayata tare da cewa.
"Eh wallahi, kinga lokaci nata tafiya, gashi sam banason yin late wallahi." ta ƙare maganar tana me ɗan miƙawa Adeel dake kallonta hannu, Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Ummun Adeel barka da safiya."
Itama Ameenan murmushin tayi tare da cewa.
"Yauwa Auntyn Adeel barka, yi haƙuri na ɗaura miki ɗawainiya, ai danaga idan na tsaya shiryasa zan makara ne, shi yasa naƙira Hayatuddeen nace kawai ya kawosa ashiryamin shi anan ɗin."
Ɗan murmushi Zaleehan tayi tare da cewa.
"Ayya to ki barmin shi yau kam mu wuni mana."
Haɓa Ameenan ta kama tare da cewa.
"Chab aikuwa zaki sha kuka, dan Adeel baya wasa da ci, nan da anjima zakiga ya fara neman nono."
Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Ya gado Bappanshi autan Ummi a cici kazar birni."
dariya sukayi baki ɗaya su,
shi kuwa Hayatuddeen da yanzu yake fitowa tura baki yayi tare da cewa.
"A,a zakarar birni dai." Ummi wanda fitowarta kenan daga ɗaki ta kawar musu rigimar autanta da cewa.
" To ki barshi mana, ba akwai madara da kuma abincin nan na yara basai adama masa yasha ba." Ɗan murmushi Ameenan tayi, tare da cewa.
"Ai idan na fita yau Ummi bazan dawo ba har sai bayan magriba, kuma kinga kafun nan zaita damunku da kuka, saidai gobe ƙarfe 5 zan tashi a aiki, kinga saina bar muku shi goben ko." Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"To Adawo lafiya, dan dama nasan idan kika barsa ni zai dama da wannan rakaɗin muryan nasa."
Dukansu murmushi sukayi sannan Ameena, ta amshi Adeel ɗin ta saɓashi akan kafaɗunta, suka fice daga cikin falon, sai kallon Zaleeha yake, har yanayi kaman zaiyi kuka. Ita kuma Zaleeha hannu ta ɗaga masa tana murmushi.
A can side ɗinsu kuma Saifuddeen ne zaune akan wheelchair ɗinsa, bayan ya gama shirya kansa tsab dan yanaso yaɗan fita.
Har ya juya xai fita daga ɗakin, kuma sai ya ɗan dakata, wayarsa ya ɗauka tare da shiga Whatsapp chat ɗinsa, sunan Ahmad ya nemo dan dama yanaso suyi magana,
cikin sa'a kuwa ya samu Ahmad ɗin online. typing ya shigayi inda yace da Ahmad ɗin. "Aikin kenan always online baka ko gajiya, dama magana nakeso muyi."
Ahmad dake zaune nan kusa da Raleeya ganin saƙon Saifuddeen ɗin ya sashi buɗewa ya karanta, ɗan murmushi yayi tare da cewa "Inajinka wace magana ce?".
ganin saƙon Ahmad ɗin yasa ya ɗan gyara zamansa ataƙaice yace.
"Dama furnitures ɗin bedroom ɗina zan sanja, so na ga wasu a online kuma har na biya kuɗinsu, abun da dai ya rage kawai shine akawomin." Idanu Ahmad yaɗan zaro, cikin mamaki yace. "wani furnitures kuma Saifudeen, meya samu na ɗakin naka, kwata kwata ma yaushe ka saya da har kakeson sanjawa?". Ɗan guntun murmushi Saifuddeen yayi tare da cewa.
"To nidai banason gulma, na faɗa mane dan katsaya min akan kayan saboda suna da tsada sosai, mungama yin magana da masu company'n kuma sunce zasu kawomin har gida, dan na fiso idan aka cire na ɗakina akaiwa Goggo Dada dan naga itama furnitures ɗinta sun tsufa."
Kai Ahmad ya girgiza tare da ɗanyin murmushi yace.
"Agaskiya yaron nan kana wasa da kuɗi da yawa."
Ahmad ya ƙare typing ɗin yana sakin dariya.
Ganin abun da Ahmad ɗin ya rubuta, yasa Saifuddeen ɗin cewa. "Lallaima Ahmad ni kake ƙira da yaro, koda kanmu ɗaya kardai ka manta cewar ƙanwata kake aure, saboda haka yazama dole kaƙirani da sunan Yaya." Dariya sosai Ahmad yayi, sannan yace wa Saifuddeen ɗin, "Bakomai zaiyi duk abun da ya dace, amma ya barshi yanzu lokacin matarsa ce tukun." Murmushi kawai Saifuddeen yayi, tare da aje wayar, dan yasan idan ya biye