Showing 24001 words to 27000 words out of 123822 words

Chapter 9 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3439

dai Hajiya Saratu kira mana ita yarinyar da Sufiyan ya ke kwance a kanta?"
Cikin sanyin jiki jin maganar sauran yaran Momy ta ce "Wannan ita ce Rahmar ai."
Da sauri Aunty ta ce "what, yarinya Waya da suna uku?"
Ku sa da Rahma Aunty ta je, ta ce me ya sa kike sauya suna kuma mene ne sunan ki na gaskiya saboda nasan yarana da kyau ba za su yi man ?arya ba ko sufaWi abun da, ba su da tabbas a kan shi, ki sanar da ni kee wacece?" cikin tsawa Aunty ta yi tambayar.
"Ni Rahma ce sannan wacce suke magana a kanta sam ban san ta ba."
"Ke nan su Hajiya da Alhaji ba su sanki ba bake bace wacce suke nufi ba?"
"Tabbas sai dai mai kama da ni, ko kuma ina yi masu gizo da wacce suke nema."

Cikin Waga murya Dady Nura ya ce "Dan Allah ya'isa haka nan koma mene ne za mu sani nan gaba, karku man ta lokaci kaWan ya rage mana kuzo mu tafi."

A take hankalin su ya koma asibiti kowa da tunanin da ke ma sa yawo cikin ran sa, da haka har suka ?arasa.

Suna zuwa ku sa da Wakin da Sufiyan ya ke Momy ta rike hannun Rahma ta na hawaye ta ce,
"Don Allah ki shiga Wakin nan gurin Sufiyan ki ce da shi kina son sa watakil a dace mu same sa."
Rahma ta yi baya da sauri ta ce, "Momy na ce kuma ina son sa meye haWina da wannan kalmar kuma ma a gurin Yayana?"
"Ke ko kike da haWi da wannan kalmar."
Nan dai Momy ta sanar da ita komai har da dalilin da ya sa, ya ce wasa ya ke mata ba son ta yake da gaske ba.

A take gumi yarin?a zuba a fuskar Rahma tana ja baya tare da girgiza kai ta ce "Momy don Allah ki yi ha?uri amma gaskiya ba zan iya ?ayar so ba."

Salim ya zo ku sa, da ita ya ce "Duk da na san cewa ke ce wacce na ke nema, amma hakan ba zai hana na ro?e alfarmar ki ceci Wan uwanmu ba."

Samir ma abun da ya ce ke nan,
Sannan ya ce,
"Doctor ya ce da wuya ya wuce awa shidda yanzu kuma awa uku ya rage, kuma muma mun duba shi da kanmu duk dai result daya ne."

"Rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah su ke, ba wanda ya san lokacin mutuwar wani sai shi, don haka kuma daina ce man haka, ni ba zan yi ?aryar so ba gaskiya."

Ran Aunty ya gama Saci, ta fizgo Rahma da ?arfi ta wanke ta da mari sai da kowa ya kalle ta cike da mamaki saboda duk sun san sanyin halin ta.
Aunty ta ce "Ke wace irin yarinya ce yaran mu biyu har yanzu ba su ?arasa warwarewa da cutar rashin ki ba, yanzu kuma ga Wayan a kwance muna neman rasa shi duk a kanki, amma kalma Waya ta buwaya fitowa daga bakin ki dan ceton ransa."
"To ki sani idan har wani munan nan abu ya faru da yarona ba zan taSa ya fe maki ba."
Rahama ta ce "Me za ki yi? to ki sani ko da kashe ni, za ki yi ba zan taSa furta kalmar da ban yi niya ba, kun haWu haka kuna son nuna man shi Wan dangi ne, ni kuma marar kowa don haka dole na yi abun da kuke so, to bazai taSa yuyuwa ba."
Dady Munir ya ce "Me ya sa kika mareta don Allah?"
"Kinga ?ata ba wai muna son tursasa ki ba ne, ka wai dai alfarma muke nema agunki, don Allah ko da shiga ne gurin sa ki yi kiga halin da ya ke ciki kin ji ?ata?"

Haka kawai sai taji ya yi mata kwarjini ba za ta iya yi ma sa musu ba, sai kawai ta ce "To bari na je Win."
"Yawwa na gode Allah ya yi maki albarka ?ata."
Da ameen ta amsa, sannan ta nufi hanyar shiga Wakin.

Ta ku sa shiga ke nan Doctor ya fito ya ce "Alhaji sai dai ha?uri amma Allah ya karSi kayan shi, ma'ana Allah ya yi wa Sufiyan rasuwa."

Duk wanda ke gurin sai da ya ji kamar an doka ma shi guduma akai, amma ban da Rahma,
Sai kallon kowa ta ke can ta ce "Wai kukan me kuke yi haka? taya ma za'ace ya mutu?"
Ta kalli Momy ta ce "Na san dole Wanki zai mutu amma kuma ba zan taSa zama sanadi ba in sha Allah."

Barinsu ta yi agurin ta shiga Wakin da sauri ganin yadda ya koma hankalin ta ya ?ara ta shi,
Da sauri ta je gurin sa tari?e hannunsa kawai sai hawaye ya fara zuba a idon ta,
Yaya don Allah ka ta shi karka bari na zama sanadin mutuwar ka, ka ya feman na tuba, ka duba kowa a nan yana bu?atar ka iyayen da ?an uwanka duk suna son ka kaima ka san hakan don Allah ka ta shi."

"Kai fa ka yi man al?awarin za ka rayu da ni za ka zama abokina kuma Yayana me ya sa yanzu za ka karya wannan al?awarin" kuka ta ke sosai kamar ranta zai fita.

Momy ta dafa ta, ta ce "Rahma ki ta shi ka wai lokaci ya ?ure, mun rasa shi" ita ma Momy kukan take sosai.

Sai faman mai maita kalmar INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIM RAJU'UN duk su ke...

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
'
*PAGE* 1?? 8??

Tsaye Rahma ta mi?e ta ce,
"A matsayin ki na mahaifiya kina ji a jikin ki kin rasa Wan ki Momy?"
Shuru Momy ta yi, ta gaza magana sai faman hawaye take.

"To Yayana ba rusarin namiji ba ne, da zai mutu ta wannan hanyar ki yarda da ni don Allah zai ta shi,
Duban kowa ta yi a gurin ta ce "Don Allah ku daina wannan kukan haka nan, ku ta yani yi ma sa magana ko zai ji maganar ku."

Da gudu ta koma gurin Sufiyan ta ce, "Ka ta shi Yaya don Allah."
Shuru ta yi kamar mai tunanin wani abun can kuma ta ce,
"Ba dan kana so na kake a wannan halin ba? to idan ka mutu kabar ni wace riba ka samu a soyayya, ko dai duk ?aryane ba so na kake ba Yaya?"
"Ka sa ni idan har ka mutu ni ma mutuwar zan yi, ba zan rayu da jin cewa ka mutu sanadina ba" amma ko motsi Sufiyan bai yi ba duk wannan surutun na ta.
Ri?e hannunsa Rahma ta yi, ta rintsi idon ta da ?arfi sannan ta ce "Ina sonka ina sonka ina sonka Yayana" cikin Waga murya.

Wani irin numfashi Sufiyan ya ja da ?arfin gaske sannan ta ri ya biyo baya.

Rahma ta ce "Momy na sanar dake bai mutu ba" cikin farin ciki take magana.

Salim da Samir cikin sauri su ka fara duba shi sannan Dady Nura ya kira Doctor.

Doctor na zuwa ya ce,
"Ikon ALLAH lalle soyayyar da yake maki gaskiya ce, wallahi Alhaji na yi matu?ar mamaki, kuma yanzu ya fita cikin ko wane hatsari sai dai ?arfin jiki kawai wanda wannan sai a hankali kuma, amma don Allah kar abari ya sake sanya wata damuwar aransa irin haka."

Dady Ahmad ya ce "Mun gode sosai Doctor."
Can murya a sha?e ba'aji sosai sai wanda yake ku sa da shi Sufiyan ya ce "Rahma da gaske kina so na kuma ba ki taSa nuna man ba?"

Ta rintse ido ta cije baki da?ar ta ce,
"Ina sonka da gaske kuma na gaza sanar da kai ne saboda ina ga kamar muna da banbanci sosai shi ya sa, na ce bari na fara gwadaka tukunna idan na tabbatar son da kake yi man gaskiya ne shi ke nan sai na amince kawai."

"To yanzu kin amince da ni ke nan, kuma kin yarda za ki aure ni?"

Nan ma ta ce,
"A na amince kuma zan aure ka in sha Allah."
Zai sake magana ta yi saurin rufe mai baki ta ce "Kai fa Doctor ne ka san illar yawan magana ga majinyaci, don haka ka yi shuru ka samu sau?i akan lokaci,
in kuma ba haka ba na gaji da jiran ka sai kawai na ce na fasa, ko ba haka ba Momy?" ta yi maganar ta na kallon Momy.
"Wannan gaskiya ne ?ata."

"Ya ce wallahi na yi shuru duk abun da, ba ki so zan daina kuma na ma ji sau?i fa bari ki gani ma" sai kawai ya fara yun?urin ta shi zaune.
Da sauri Rahma ta mai da shi kwance.
"Ta ce me kake yi haka ne? karka sake ta shi kabi a hankali ka ji sau?i sosai."
Rahma ta dubi iyayen nasu ta ce "Ni zan tafi gida na kawo abinci."
Ta na mi?ewa tsaye ya ri?e mata hannu ya ce "Dan Allah kar ki barni kin ji?"

"Ba zan barka ba kawai zan kawo abinci ne kaga dare ya fara ba wanda ya ci ko???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?mai."

"Ki zauna a nan yanzu dare ya yi bai dace ki yi girki ba, ?an uwana za su je, su siyo kar ki damu kin ji."

Rahma ta ce "Wai Yaya baka yarda da ni ba? na ce, na yima al?awarin zan dawo, idan ma sun siyo abincin kowa to naka fa? ka san dole da ban ne saboda baka da lafiya."
"Na yarda da ke ?anwata amma kinga dare ya yi, ki bari kawai ?an uwana su kai ki sai ku dawo tare."

"Shi ke nan kwanta ka huta kafin mu dawo Win."
Ta na faWar hakan ta fita daga Wakin da sauri.
He look at his brothers he said,
Please look after her she can escape even in the night Rahma can run away,
Because am feeling am not still in her heart like 100%
And if she escape you will lose me."

Ya ?arasa maganar da ?yar har hawaye na Wan fita daga idon sa.
Samir said "by the grace of Allah we are going to return with her bro."

Su na fita suka tarar Rahma na ta faman kuka kamar wacce uwarta ta mutu.

Salim ya ce "Mu tafi ko?"
"Samir ya ce "A mu tafi."
Haka Rahma ta bisu har suka isa gida ba mai magana daga cikin su.

Su na isa ta shiga kitchen ta fara haWa abubuwan bu?atar.
Su Salim ne suka shigo kitchen Win su na tambayar ta "Ko kina bu?atar wani taimakon mu?"

Murmushi ta yi sannan ta ce "?a ?an manya ba su iya aikin wahala ba ku bari kawai zanyi da kaina."
"Ki bamu aikin ki gani mana."

"Ba bu?atar hakan gaskiya."
Sai kawai ta mai da hankali kan aikinta cikin ?an?anin lokaci har ta gama,
Abubuwa sosai ta yi, da yake ta nada saurin aiki sam bata da gan da.

Ta na gamawa ta sanar da su suka ri?a ma ta suka shigar mota lokacin 9:pm koma wa asibitin suka yi.
Kowa ya yi mamakin ganin irin abubuwan da suka shigo da su amma banda Momy saboda ta san ?arta, sai kuma Momy Nusaiba da har yanzu bata yarda cewa ba ?arta ba ce.

Haka ta zubawa kowa sannan ta koma gurin Sufiyan ta ce,
"I have come back I did not run away am not scared my brother."

Ka feta ya yi da idanun sa waWan da sunka lumshe sosai saboda jinyar da yake,
"Ya ce dama kina jin turanci ?anwata?"

Ba ta amsa ma sa ba kawai sai ma ?o?arin zuba ma sa abincin da take.
Sai kawai ya yi murmushi shi ma yabar zancen,
Sannan ya ce,
"Na gode ?an uwana dan na san wannan aikin na kune dawo man da ita."

"Au hakama za ka ce? to shi ke nan bari na tafi na ga ni idan za su iya tsayar da ni."
Da sauri ya ce "Ni fa ba dake na keba don Allah abar ma maganar ki yi ha?uri."

Sai da kowa gurin ya yi dariya,sannan ta Wauko nasa abincin da kanta ta rin?a ba shi har ya ishe shi da man can saboda ita kawai yake ci amma baya jin daWin komai.

Yana gamawa ya ce,
"?an uwana ina ro?on Allah daya bayyana maku ?an matan ku kamar yadda ya haWani da wacce zuciya da jikina ke mutuwar so."

Sai kawai ya ga sun yi shuru daga su har iyayen ana ta kallon kallon.
"Kun yi shuru ba wanda ya ce ameen?"
Cikin ya na yi kamar na marar gaskiya su kace,
"Ameen Wan uwa."

Zai yi wata maganar k enan Momy Aisha ta ce "Ya'isa haka nan Wana kwanta ka huta."
"To Momy ya ce.

Yau satin su Waya ke nan kuma cikin ikon Allah Sufiyan ya ji sau?i sosai yana samun kulawa ta ko ina musamman gurin Rahma ta na nuna matu?ar kulawar ta a gurin sa, har mamaki yake su ma mutanen gidan haka amma kuma suna jin daWin hakan sosai.

Sai dai kuma Sangare Waya Salim da Samir na jin ba daWi amma ko wannen su yana ?o?arin Soyewa.

Satin su biyu ke nan da dawowa gida kuma Alhamdulillah jiki yanzu ya yi lafiya sosai,
Bayan sun gama yin breakfast kowa na cikin parlor zaune amma ban da Rahma.

Dady Nura ya ce "Kai Sufiyan je ka yi man kiran Rahma."

Da sauri ya je kiran ta lokacin tana kan keken Winki.
A tare suka shiga parlorn fuskar Sufiyan cike da farin ciki duk'da kwanan nan haka ya ke.
Rahma ta sake gaida su sannan ta zauna ?asa kamar sauran yaran maza.

Dady Nura ya ce "Rahma wannan zaman ku san zan iya cewa naki ne, lokaci ya yi da za mu tafi tun da dai Allah ya nufi yaronmu ya ji sau?i sosai."
"To fa shi ne muka yi shawarar kafin mu tafi ?ara mu tsayar da magana mai ?arfi a tsakanin ku, ma'ana mu sanya ranar auren ku tun da mun fahimci yanzu duk kuna son junan ku, amma kafin nan ya dace mu baki dama da bakinki ki ?ara amsa mana kina son auren ku da Yayan ki Sufiyan."

Da sauri Salim da Samir suka Wago kai suna kallon Dadyn na su amma ba damar magana saboda ba su ga fuskar wasa ba, shi kuma gogan sai ?ara washe baki yake ya nata faman farin ciki...

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' *PAGE* 1?? 9??

Dady ya ce "Kin yi shuru ki yi magana ke muke saurara."
"Ka gafarce ni Dady amma kafin na baka amsa ina son na Wan yi magana da Yaya idan ba damuwa."

Dady Nura ya ce "Ba matsala a nan kike so ku yi maganar ko sai kun fita?"

"A nan ma ya yi Dady" cewar Rahma.

Ta kalli Sufiyan da kyau sannan ta ce "Ka ce kana so na kuma ni ce macce ta farko da ka ji kana so sannan idan karasa ni za ka iya rasa ranka, haka ne?"

"Sufiyan ya ce tabbas haka ne."
Rahma ta ce "To su kuma iyayen da ?an uwanka fa, ka taSa tunanin halin da za su shi ga?"
"Bayan Allah da Manzon sa ba wani wanda zai so ka kamar iyayenka, shin ko da sau Waya ba ka yi tunanin ya dace ka rayu saboda su ba?"

"Ranar da za mu yi ba?i sai da na sanar da kai gab kake da ka yi rashin lafiyar da sai ta Waga hankalin mutane kuma na baka shawarar ka sanar da iyayenka matsalar ka, ka san me ya sa, na faWi hakan?"
"Saboda na san kalma Waya za su faWamaka, sai kuma ka ga cikin ikon Allah ka samu sassauci a cikin zuciyar ka."

"To ka sani farin cikinka ba kai kaWai ke da shi ba har da iyayenka da ?an uwanka,
Ka ji koh Yayana?"
"Na ji kuma na yi maki al?awarin zan gyara in sha Allah."

"Ka yi al?awarin ko da bana cikin rayuwar ka, ba za ka sake saka damuwa a ranka ba har ta so illata ka, za ka rayu saboda masoyan ka na gaskiya iyayenka da ?an uwanka?"

Ya yi shuru ya gaza bada amsa.
"Ina jinka kuma ka yi shuru?"
Da?ar ya iya furta "In sha Allah zan yi ?o?arin hakan."

Ta ce "Maa sha Allah to Dady yanzu zan baka amsar ka,
A gaskiya zancen aurena na amsa ne kawai saboda ina son naga ya dawo hayyacin sa bana son ace ni ce sanadin rayuwarsa saboda na san zan Wauki alhakin mutane da yawa daga ciki har da shi Yayan, amma don Allah ku yi ha?uri, yau ma nake son barin gidan nan watakil idan bana ku sa ya samu natsuwa sosai ya manta da ni."

Sufiyan da sauri ya zo gurin ta ya du?a ya ce "Don Allah ki yi ha?uri ki ceci raina kar ki yi man haka don Allah."

"Amma dai ka san ka yi man al?awari ko? to don haka karka koma baya da zancen ka."
Kuka yake sosai kamar wani ?aramin yaro yama gaza sake magana.

Rahma ta ce "Dady zan iya tafiya shi ke nan koh?"

"Ah Ah ina son ki daure ki sanar da ni laifin da Sufiyan ya yi maki wanda ya sa ba ki son sa?"
"Wallahi bai yi man ko mai ba kawai dai na tsani soyayya ne kuma har da zancen aure."

Aunty ta Waga murya ta ce,
"Wai ke waya Wauke yardar ki haka, da har kike jin ba za ki sake bawa wani yardar ki ba?"

Ita ma cikin Waga murya da hawaye sosai a idon ta,ta ce mutane da yawa sun tafi da yarda ta kuma bana tunanin sake bawa kowa damar shiga rayuwata."

Za ta bar gurin Aunty ta yi saurin ri?o ta.
Rahma ta ce "Ko har da yau ma marin nawa za ki yi kamar wancen ranar? to yau ko mai za ki yi, ba zaisa na sauya zancena ba."

Aunty ta ce "Ba marin ki zan yi ba kuma ba zan tursasa ki ba, amma don Allah ki sanar da mu dalili mai ?arfi wanda zaisa mu yarda da bu?atar ki, na rashin son Wan mu?"

Da sauri Sufiyan ya ce, "Yawwa Aunty haka ne don ALLAH duk'da ba ki son muna yi maki tambaya a kan abun da ya shafi rayuwar ki amma yau ya dace ki sanar damu ko da zan samu sassaci a cikin zuciyata na daina tunanin ko ni ne na yi maki laifi wanda ya sa, ba ki so na."

Rahma ta ce "shi ke nan zan sanar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login