Showing 18001 words to 21000 words out of 123822 words

Chapter 7 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3413

zuwa gurin."
"Momy amma kun san ba ta kaSar komai nawa har yanzu, ta ya kuke tunanin za ta karSi keken?"

Dady ya ce "Amma Wana karka, ba ni kunya mana sai kace ba namiji ba."
"Ba zan ba ku kunya ba in sha ALLAH bari ma, ku ga ni tun yanzu."

Yana faWar hakan ya fita sai Wakin Rahma daidai lokacin ita ma tana ?o?arin fitowa daga Wakin, su ka yi kicibus da juna ya ce.
"?anwata don Allah ki yi ha?uri na san Wazu na Sata maki rai."
"Haba Yaya karka ce haka don Allah ni ce ya, da ce na baka ha?uri dama bari na yi sai zuciyarka ta yi san yi tukunna."
"Ka ga da banje da kai gurin ba, da baka yi faWa da wannan wawan ba."
"Yanzu dai mu bar wannan maganar ta wuce, amma sai dai ina son ki yi man alfarma Waya don Allah."
"Wace alfarma ke nan Yaya?"

A nan ya sanar da ita ?udurinsa na son siyamata keken Winki, da ?yar ya samu ta amince.
A ranar ba'a kwana ba sai da aka kawo keken gidan a matsayin na Rahma.

Tun daga lokacin Rahma ta daina zuwa shagon Winki yanzu ya kai har na Momy ita ce ke yi.

Suna zaune a parlor kamar kullun Momy ta ce
"Ke dai Rahma 'yar baiwa ce, na Wauka ?unshi kawai kika iya da kitso saboda ranar da kika yi wa Zahra ya yi man kyau sosai ashe wai har da Winki ga shi kin iya sosai saboda yanzu idan ba ke kika yi man ba duk sai na ga bai yi man ba."

Sufiyan ya ce "Don Allah ya isa haka nan sai wani koranta ta kike bayan ba ita kaWai ta iyaba ni ma nan da kuke ganina na iya sosai fiye da ita ma."

"To shi ke nan Momy gurin da, ba ?asa nan ake gardamar ko kawa don haka na ba shi yi nin yau gaba Waya ya yi riga kawai."
"Ni ma na baki wannan damar kuma ke za ki fara sannan ba na mata za ki yi ba na maza za ki yi."
"Ni kuma idan har kin yi daidai a warwaron ki zai dawo hannuki, yau sai na ga idan da gaske kina son wannan abun hannun."
Momy ta ce "Amma aika san bana maza take yi ba."
"Na sa ni Momy ai idan na ce, na mata za ayi abu ne mai sau?i a gunta."
"Momy na yarda zanyi, amma kuma bana da kayan maza."

Da sauri Sufiyan ya ce "Ni ina da shi bari na kawo maki."
Cikin ?an?anin lokaci sai ga shi Rahma harta gama.

Kallon Momy ta yi, ta ce "Na gama Momy ki ce, ya ba ni a warwarona."
Wannan a warwaron kwana biyu kenan da Sufiyan ya karSesa daga hannun Rahma tun da ya fahimci ta damu da shi sosai shi ya sa, yake ta yi mata jan rai.

Yanzu ma yana ganin ta gama da gaske ya ce "Wallahi Momy ban yarda ba dama can ta san ta iya ne."

Momy ta ce "Amma wannan baya cikin sharaWinku dan haka kabata kayan ta, shin ko ba haka ba Dady?"
Momy ta yi tambyar tare da duban dady.
"Tabbas haka ne" cewar Dady.
"Ok ke nan dai haWe man kai za ku yi, to shi ke nan na san abun da zanyi sai kawai ya gudu ya ce "Idan kin isa ki zo ki karSa."
Aikuwa ita ma ta bi shi suna ta zagayen parlon da gudu kamar daga sama suka jiyo salati cikin Waga murya suna jiyowa suka ga ashe BABA LARAI ce mahaifiyar Zahra.
Ita dai Rahma bata santa ba amma ganin su tare da Zahra shi ne ya bata tabbacin ita ce mahaifiyar ta, duk su ka tsaya kallon ta.
Sai cewa take yi "Yanzu saboda ALLAH Hajiya Saratu lalacewar har ta kai haka za ki bar Wanki ?waya Waya tak yana wasa da 'yar aiki kamar wani marar ga ta?"
Tana juya wa sai kawai ta ga Dady zaune a gurin aikuwa ta ?ara rabka wani uban salati "Au dama Yaya kana parlorn ake wannan sha shancin?"

Karaf Zahra ta ce "Umma bana sanar dake cewa duk ta shanye su ba? a kanta fa suka kora ni daga gidan nan."

Dady ya ce "Yanzu don ALLAH Hajiya Larai yaushe za ki yi hankali? ku shigo gida daga ke har 'yar ta ki ba wacce ta yi sallama kuma kun tsaya kuna ta faman aibata wata don ALLAH wannan hali ne mai kyau?"

"Yaya ka yi ha?uri raina ne a Sace shi ya sa, na manta da sallama."

Rahma ta ce "Momy ni zan je Waki idan ki na bu?atar wani abun za ki iya kirana."
"To shi ke nan Rahma."

Rahma har ta zo, za ta wuce Hajiya Larai ta ce "Ke baki iya gaisuwa ba ne, da za ki wuce baki gyada ni ba?"
Rahma ta yi kamar bata ji abun da take cewa ba ?o?arin sake tafiya ta yi, Hajiya ta sake ri?o ta ta ce "Me kike ji da kanki ne? ki na 'yar matsiya ta kuma 'yar aiki sannan marar gata amma har zanyi maki magana ki yi kamar ba ki jiba."

Rahma ta juyo ta cire hannun Hajiya Larai daga jikin ta sannan ta ce,
"Kin faWi gaskiya a cikin wata maganar ki Waya, tabbas ni ?ar aiki ce sannan ?ar talaka amma hakan bai hana ni sanin abun da ALLAH da manzon sa suka sanar da mu kuma suka koyar da mu ba."
"Addinin mu ya koyar da mu idan mutum ya je a guri sannan ya tarar da wasu to ya yi masu sallama idan kuma har bai yi ba, to su waWanda aka tarar kar su yi masu magana idan kuma suka yi to tabbas su ma masu laifine, ni kam bana son na zama mai laifi a gurin mahalicci na."
"Sannan kin kira ni marar gata, tabbas wani na iya zama gatan wani, amma wanda ALLAH ya zama gatansa shi ne mai cikakken gata, don haka ni Win mai cikakkiyar gata ce saboda ALLAH yana tare da ni."
Tana gama faWar hakan ta wuce Wakin ta.
Sufiy??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????an ya ce "Jira ni Rahma mu tafi tare."
Hajiya ta ce "Kuje ina? Dalla zo nan ka zauna magana na zo, mu yi kuma a kanka ne."

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
('Yar gatan mama)
' 08160726558
PAGE 1?? 4??

Baba Larai, ta gyara zama sannan ta ce,
"Yaya ya ku ka bawa wannan yarinyar dama haka da har za ta gaya man magana kamar sa'arta?"

Dady ya ce "To me ta faWa wanda ba gaskiya ba?"

"Yanzu dai ba wannan ba Yaya na zo ne a kan maganar auren yaran nan Zahra da Sufiyan na ga ya dace a yi komai agama tun da dai ba abun da muke jira?"

Dady ya ce ban katsi hanzarinki ba amma su yaran sun fahimci juna ne, ma ana suna son junansu ko kuwa zancenki ne wannan?"

"Ah Ahh Yaya sai da na tabbatar Zahra na son shi sannan na zo da maganar."
Dady ya ce "To shi kuma Sufiyan me ye ra'ayinsa ko kin sani?"

"Yaya na san ba zai ?i Zahra ba kuma ai mu muka haifesu don haka umurni kawai za mu, ba su kuma dole su bi,
"Ko bayan haka ai yaron nan ya girma sosai ya da ce, a ce zuwa yanzu ya yi aure haka nan."

"To ni kam ba haka nake ba dole sai yana so za ayi inko baya so to sai lokacin da ya samu wacce yake so."
"Sannan komai girman da ya yi a gurina yaro ne kuma ba zan yi ma sa dole ba."

Kallon Sufiyan ya yi sannan ya ce "Kai sanar da ni kana son wannan haWin tsakanin ka da Zahra?"
A take Sufiyan ya ce "Don ALLAH Dady ku daina maganar nan bana so, ni a matsayin ?anwa na ke kallon Zahra ba wani abun da ya wuce wannan, Dady idan ka yi man izini zan wuce?"

"Za ka iya tafiya" sannan ya juya gurin Baba Larai ya ce, "To kin ji don haka abar wannan zancen ALLAH ya haWa kowa da rabon sa."

Mi?ewa tsaye ta yi, ta ce "Amma wannan wane irin cin fuska ne Yaya ni da nake da 'ya mace ba ta ce bata yi ba sai shi da yake namiji?"
"To wallahi matu?ar ina raye auren nan kamar an yi angama."

Hannun Zahra ta ja suka bar gidan cikin Sacin rai.

*********************
Kwana biyu da faruwar hakan Sufiyan ya shigo parlorn da sauri ya ce Momy in sha ALLAH gobe da yaranki za mu kwana a gidan nan kuma har da su Momy'na da su Dady amma sun ce, ba su son ku san da su, za su zo saboda suna son baku mamaki sosai."

Momy ta ce "Shi ne matsalar ku ba'a sirri da ku, yanzu sunyi sirri da su su kuma sun sanar da kai, kai kuma ka zo kana sanar da mu yanzu."

"Ke kuma Momy sam ba ayi maki gwaninta wallahi."
Ya Wan Sata fuska irin ran sa ya Saci Win nan.

"Shi ke nan amma na yi matu?ar farin ciki da wannan labarin, ka ce dai gobe gidan nan zai ?ara haske sosai."

Dady ya ce to zaman me muke haka ya da ce mu fara shiri."

Sufiyan ya kalli Rahma ya ce "Ba ki ce komai ba,
"Me za mu yi masu ne goben?"

Allah ya kai mu goben ba abun da zai ga gara in sha ALLAH, amma kamar ?arfe nawa kake tunanin za su shigo?"

Ina ga zuwa ?arfe huWu suna gidan nan in sha ALLAH."
To ba matsala yanzu dai mu je lambu mu sha iska."

Shi ke nan mu tafi saboda yau ina cikin farin ciki komai kika nema kin samu da yardar ALLAH."

Suna isa lambu Rahma ta ce Yayana zan iya tambayar ka?"
"Ina jinki ?aunata."
"Yaya su waye waWan nan ba?in a gurin ka na ga tun da, ka samu labarin zuwansu kake cikin nishaWi sosai?"
Ya ce "Kina son ki san waye su?"
Rahma ta ce "Sosai ma kuwa Yayana."
"Shi ke nan saurara ki ji yadda muke da su."

WAYE SUFIYAN DA IYAYEN SA ???

~GARIN KADUNA~

Alhaji Suraj mahaifin Sufiyan asalin 'yan garin Kaduna ne, ya nada abokai uku shi ne na huWun su idan mutum bai sani ba zai yi tunanin 'yan uwan juna ne,
Alhaji Nura, Alhaji Ahmad, Alhaji Munir, Alhaji Suraj,
Su ne abokan junan sun ta so tun suna yara ka san cewar duk'kan su 'yan anguwa Waya ne kuma makaranta Waya tun daga boko har islamiya, sannan tun daga ?aramar makaranta har babba tare su ke idan kuskure ya sa aka sauyawa Wayan su makaranta to fa tabbas dole sai an sauyawa dukansu idan kuma ba haka ba, za su rin?a fa shin zuwa dukan su.
Tun iyayen na jin haushi har suka yi ha?uri su ma suka haWa kansu, duk abun da za su yi, sai sun yi shawara musamman abun da ya shafi yaran na su..

A haka dai har suka gama makaranta sannan suka samu matan aure aka yi auren su rana Waya.

Wata biyar da yin auren aka fahimci matar Alhaji Nura na Wauke da juna biyu ma'ana Hajiya Aisha.
Bai fi sati Waya ba tsakani ita ma matar Alhaji Ahmad aka gano na ta juna biyun Hajiya Nafisa ke nan an yi farin ciki sosai ka sancewar su ma matan sun zama ?awayen juna saboda ala?ar da ke tsakanin mazajan su,
Ashe ita ma Hajiya Saratu tana da, na ta juna biyun a lokacin.
Bayan wani lokaci Hajiya Aisha ta fara haihuwa ta samu Wanta namiji,
Ba a kai gayin suna ba Hajiya Saratu ita ma, ta haifi na ta Wan namiji.
Kwana biyu tsakani Hajiya nafisa ta samu na ta rabon na Wa.

Aiki ya tararwa Hajiya Zainab wato matar Alhaji Munir saboda ita ce kawai ba ta taSa ko da Satan wata ba,
Shi ya sa suka yi shawarar tun da duk sati daya ne haihuwar to a haWa taron sunan rana Waya kuma guri Waya.

Haka kuwa aka yi ranar suna Suka bawa Alhaji Munir damar ya sanya ma yaran suna,
?an Alhaji Nura yaci suna Salim,
?an Alhaji Suraj yaci sunan Sufiyan,
?an Alhaji Ahmad yaci sunan Samir.

Shekara biyar da haihuwar yaran Hajiya Aisha ta sake haihuwar 'ya mace.
Wata Waya tsakani Hajiya Nafisa ta samu wani Wan namiji,
A lokacin kakar Sufiyan ta sanya masa suna tilo saboda shi ne kawai ba ayi wa ?ane ba da ?yar Momy ta rabasa da sunan ganin shi ma baya so.

Watanni shidda da haihuwar ?annen su ?anwar Samir ta yi wata jinya daga ?arshe dai ta rasu,
Shi ma ?anen Salim daga jinyar fitar ha?ori shi ma aka rasa shi tun daga kansu ba wacce ta sake haihuwa.
Yaran sun ta so kansu ahaWe kamar ma sunfi iyayen na su son juna, ko wannen su zai iya sadaukar da komai a kan Wan uwansa.

Hajiya Zainab na matu?ar son yaran su ma kuma suna son ta, mutu?ar suna ?asa Waya to fa suna gidanta, idan ta yi tafiya ta dawo to duk tsarabarta a kan yaran za ta ?are sun sha?u sosai da ita idan tana aguri ko kulawa ba sa yi da iyayen na su, da Aunty suke kiranta ita ce ta zaSi hakan.

Amma sai dai kash ita har yanzu bata haihu ba sun je ?asashe da dama amma ba adace ba kuma duk gurinda suka je lafiyar su ?alau ake cewa adai jira lokaci kawai.

Wata rana an tura yaran ziyara gidan Aunty Zainab kamar yadda suka saba lokacin su na da shekara shidda da watanni uku.

Wannan ziyarar bata yi wa yaran daWi ba saboda yadda suka tarar da ita ba lafiya sosai sannan Alhaji munir baya ?asar ya je Italy wajen wani aiki, duk da ta so ta Wan nuna dauriya saboda ganin zuwan yaran amma sam ta gaza.

Hakan da suka ga ni, ya sa suka yanke shawarar kiran su Momy lokacin suna Nigeria dama duk lokacin da yaran na so zuwa gurin Auntyn ta su idan iyayen ba su shirya zuwa ba sai kawai su haWasu da wani ya kai su,
Dalili kuwa ita ba su fiye zaman ?asar ba.

Suna kiran Momy Aisha aikuwa hankalinta ya ta shi duk ta sanar da sauran da kuma mazajen su adaren ranar suka sauka kafin su je har sun kira mijinta sun sanar da shi, shi ma haka ya zo cikin daren nan.
Suna isa gurin ta, kowa da kalar faWan da yake mata,
Mai gidanta ke tambayar me ya sa bata sanar da shi ba, ko kuma ta kira Doctar ya duba ta?

Sai kawai ta ce bata son ta tsayar da shi a kan aikin sa kuma ta san idan har ta sanar da Doctar to fa sai ya sani.

Momy Nafisa ta ce, to me ya hana ta kira wani daga cikin su?
Momy Saratu ta ce,
"Ai kin san wani lokacin haka take yin abu kamar wata yarinya wallahi."

Nan dai ran Sufiyan ya fara Saci ga mata na cikin ciwo amma sun ta sata agaba sai faman faWa suke yi mata.

Ya ce "Wai yanzu don ALLAH za ku kai ta asibiti ne ko sai kun gama yi mata masifar tukunna?"

Sannan kowa ya ce haka ne gaskiya, da sauri suka tafi da ita asibiti....

PAGE 1?? 5??

Bayan dogon bincike Dr ya gane cewa ta na da juna biyu na tsawan sati huWu.
Ba wanda bai yi farin ciki ba marar musultuwa daga duk'kan Sangarorin, ba ma kamar Alhaji Munir da Aunty Zainab.

Bayan sun dawo gida kulawa take samu daga ko ina saboda ciki ne mai matu?ar laulayi shi ya sa duka familyn suka tare a gurin ta har yaran ba abar su a baya ba wajen bata kula.

Kwanci ta shi asarar mai rai cikin Aunty ya kai wata goma amma ba zancen haihuwa,
Ana gobe birthday Win yaransu na cika shekara bakwai Aunty ta tashi da wani matsanancin ciwon ciki ta sha wuya sosai a asibiti suka kwana asubar farko ALLAH ya sauke ta lafiya ta samu ?a mace mai kyau sosai idan mutum bai san iyayen ta ba, za ka rantse ka ce ba ?ar hausawa ba ce.

Daga nan gida suka wuce cikin farin ciki ranar birthday ranar zuwan sabuwar Baby,

Ranar suna yarinya ta ci sunan Sufanyya kowa na son yarinyar saboda ba ta da hayaniya tun kafin ta cika shekara Waya ta iya magana da tafiya duk da maganar ba wani fita take yi ba sosai amma a na Wan fahimta,
Akwai wani abu da iyayen suka fahimta ga me da ita duk ta faWi magana sai ta tabbata gaskiya.

Akwai wata rana duka yaran suna parlorn Momy Nafisa, sai kawai Salim ya ce shi dai harabar gida zai je ya yi wasa ya nemi sauran yaran da su ta so suje tare.
Sai kawai Sufanyya ta ce "Yaya karka fita idan ka fita sai ka faWa ruwa kuma ka ga za fitowa, lokacin tana da shekara uku su kuma mazan nada shekara goma.

Aunty Zainab ta ce "Me kike cewa haka?"
"ALLAH Aunty da gaske nake yi."

Duk sai a ka Wauki maganar shirme ta yarinta haka a ka bar zancen.

Hankalin kowa yabar kan yaran sai can aka lura Salim baya cikin yaran duk aka tambaye su amma ba wanda ya san gurin da ya je.

Ana cikin nemansa sai ga mai gyaran filawa ya zo da gudu yana faWin ga yaro can cikin ruwa kamar ma ya mutu,
Ai kuwa da gudu kowa yabar parlorn a ka je gurin ruwan Dady Ahmad shi ne wanda ya faWa ya fito da shi,
Duk an Wauka baya raye saboda yafi minty goma kafin a samu ya yi aman ruwan da ya zu?a sannan hankalin kowa ya Wan kwanta.

Aunty Zainab ta je gurin Suffanya ta ce,
"Sanar da ni waya sanar dake cewa idan Salim ya fita zai faWa ruwa kuma har ya gaza fitowa?"

Ta ce ba wanda ya faWa.
Duk kalar tambayar da za a yi mata amsar dai Waya ce.

Irin hakan ya sha faruwa hankalin iyayen ya yi matu?ar ta shi sosai duk gurin da suka ji mai magani sai an je amma abun yaci tura tun ana tunanin ko aljanu ne har aka daina wannan tunanin duk aka yarda cewa halittar ta ce haka.

Ta ku sa cika shekara huWu Dady munir ya ce, ta faWi duk abun da ta ke so ya siya mata na birthday,
Duk an yi tunanin irin su ?ar tsana ko wani abu dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login