Showing 51001 words to 54000 words out of 123822 words

Chapter 18 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3434

ce "In sha ALLAH ?aunata na yi maki al?awarin ri?e sa a tare da ni, ?aunata Waya tak ta yi man kyau ta ai dole na ri?e shi da kyau."

Sai da ta yi kusan wata uku kafin ta iya anfani da ?afar sosai, hakan ya sa yanzu ta hana Inna zuwa kasuwa sai dai ita da Furaira su tafi ita kuma ta yi aikin gida kafin su dawo, idan kuma sun dawo za su je Wibar ruwa sai sun cika komai na gidan sannan za su samu hutu.

Su Baffa har mamakin ta, su ke yadda take faman ?o?arin ri?a masu aiki ba gajiya tun suna hanawa har su ka ha?ura.

Yau suna zaune gurin da suke zama sai da nono Rahma ta siyar da nata tana jiran Furaira ta siyar ita ma su tafi gida.

Furaira ta ce "Addah kin taSa zuwa makarantar boko?"

Rahma ta ce "A mana, ke fa?"

"Humm na taSa zuwa har ma na gama primary amma su Baffa sun ce ba zan shiga secondary ba saboda wai aure za su yiman ni da Ado daya dawo daga tafiya, kuma wallahi Addah ina son na yi karatu sosai."

Rahma ta ce "Daina kukan mana, ba ke kika ce baki son ina kuka ba, kuma shi ne kike yi? dai na bana so, in sha ALLAH zan yi ?o?ari sai naga burin ki ya cika ?anwata."

Bayan sun dawo gida su na cikin cin abincin dare Rahma ta kalli Baffa ta ce.

"Amma Baffa me ya sa, ba ku sa Furaira makaranta ba kuma na ga tana da ?o?ari sosai?"

Baffa ya ce, "Ai ta yi wannan ?aramar don haka ya isa haka nan aure za mu yi mata da Ado Wan wajen yayana."

"Aure kuma Baffa, Furairar shekarar ta nawa da za'a yi wani zancen auren ta? sai nake gani har yanzu ?aramace."

"A gurin ku kenan, aimu a gurinmu ?atuwar budurwace don ma an san akwai wanda zai aure ta da yanzu an fara gulmur mun bar yarinya tana ta girma a gabanmu."

Rahma ta ce "A to Baffa kana da gaskiya bai kamata ka sauya al'adarku ba, akan wani dalilin can.

Amma sai nake ganin me ya sa tun da tana da ra'a yi asan ya ta, ta fara da Adon ya dawo sai a fitar da ita a yi auren.

"Wata?il idan an yi nasara ma yabar ta, ta cigaba bayan auren tun da shi ma ya shiga birnin."

"Yanzu ya san darajar karatun, don ALLAH Baffa ka yarda,
Kar ka man ta iyaye suna rayuwa ne saboda cikar burin ?a ?an su."

Baffa mutum ne mai sau?in kai nan take Rahma ta shawo kan shi ya ce,

"Hakane kuma amma fa karatun bokon nan yanzu sai ki ji sun faWi kuWi da yawa wanda har sai an ce na siyar da mara?ata."

Dama ta san hakan zai iya faruwa ga shi kuma ta, yi wa ?anwar ta al?awali tsoron kar ya canja ra'ayi da sauri ta ce,

"Ah ah Baffa na yima al?awari ba za ka siyar da komai ba ni zan Wauki nau yin komai in sha ALLAH zan shiga cikin gari neman aiki wanda zan samu na rin?a biyan kuWin makarantar."

"Baffa ni dai kawai kace ka amince ni kuma zan yi iya ?o?arina in sha ALLAH."

"Shi ke nan ku bari na yi shawara da Wan uwana duk abun da, ya ce shi ne abun da zai faru."

Kamar daga sama su ka ji ance "Na amince wannan shi ne hukuncina tun da shi Ado har yanzu bamu san lokacin dawowar shi ba, ka ga kenan bai dace mu tauye hak?in yarinya ba, fatan mu ALLAH yaba da sa'a."

Ashe yayan Baffa ne ya shigo ya ji suna magana shi ne ya tsaya sai da ya gama jin komai sannan ya yi magana.

Sunyi farin ciki sosai ita da Furaira, hakan ya sa tun da safe su ka fita neman makaranta sai dai sunyi rashin sa'a don sun je makaranta ku san uku amma sun ce sai ?arshen wata za su Wauka, a ta ukun ce Furaira ta ce

"Addah mu yi ha?uri har ?arshen watan ai kamar gobe ne."

"Hakane to ALLAH ya kai mu."

Sai dai kuma makarantar sun ce idan za su koma sai sun zo da dubu ashirin tukunna saboda da su za'a bata komai wanda zai nuna ta zama ?ar makaranta.

Hakan ya sa, ta shiga cikin gari sosai neman abun yi amma bata samu ba sai ta koma cikin kasuwa."

"Da?yar ta samu jiran shago a wani ?aton kanti, zata rin?a zuwa 11:am ta ta shi 2:pm saboda akwai mai zama irin wannan lokacin amma yanzu ya samu karantarwa sai biyu zai rin?a zuwa.

Da sauri ta amince, mai gurin ya ce "Sai dai dubu uku zan rin?a biyan ki tun da kinga akwai mai gurin taimaka ma shi kawai za ki yi."

"Ba komai na gode in sha ALLAH zan zo goben."

Sannan ta bar gurin da tunanin ta ya zata haWa dubu ashirin kafin wata Waya.

Wani shagon salon ta hango kamar za ta wuce sai kawai ta tsaya ta yi masu sallama su ka amsa sai da ta shiga sannan ta fahimci ba musulmi ba ne.

Daga nan ta sanar da su aiki take nema, mai gurin ta yi dariya sosai wai ta ya wannan ?ar yarinyar za ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? iya wankin kai da kitso.

Rahma ta ce "Wallahi na iya idan kina so ki gwada ni, ki ga ni."

Gashin kanta ta warwale dama ba Wan kwali akan ta ce "Zo ki wanke man kai na."

Cikin hausar ta marar fita sosai.

Cikin ?an?anin lokaci ta gama, a haka sai da ta, yi wa mutum uku sannan ta ce.

"Kai amma gaskiya kin ba ni mamaki ban za ci, za ki iya ba, kuma kina da sauri sosai irin ki nake so don haka ki fara zuwa gobe."

Rahma ta ce "Amma sai dai 2:30 zan rin?a zuwa saboda ina zuwa tallah sai na ta shi 5:pm saboda muna da, ni sa, da cikin gari."

Dariya sosai mai gurin ta yi, ta ce "Ko wanne ma aikaci idan aka Wauke shi aiki uban gidan ke sanya ma shi doko ki da lokaci.

"Amma ke na ki aikin na, da ban ne ke, ke sanya lokaci da kan ki, to shi ke nan, na amince amma sai dai kullun zan rin?a biyan ki ba sai ?arshen wata ba saboda kin ga ba wuni za ki yiman ba."

"Na amince" shi ne abun da Rahma ta faWa.

Tun da safe idan sun fita talla ko da sha Waya ke yi sun siyar sai ta bawa Furaira kayan ta je gida ita kuma ta wuce shago daga nan kuma tana ta shi sai gurin salon.

Mai shagon ya ga irin wahalar da take yi saboda sauran yaran duk sai su rin?a bada uzuri ganin ta na ?o?arin yin aikin ta ko ina.

Da tazo za su fara faWin Rashida bari na Wan je can yanzu zan dawo, da haka sai su jima ba su dawo ba.

Aikin duk ya yi mata yawa a she ogan ya na sane da duk abun da ke faruwa saboda haka ma ya ?ara mata albashi ya koma dubu shidda, ta yi godiya.

Ita ma mai salon ta na jin daWin aikin ta sosai idan za ta tafi gida tana bata dubu Waya wataran kuma har dubu biyu, ya danganta da cinikin da aka yi.

Furaira ta fara zuwa makaranta sai dai dubu sha biyar kawai ta samu ta biya, ta ro?i alfarmar za ta ciko nan da Wan lokaci an yi nasara sun amince.

Hankalin Baffa bai kwanta ba har sai da ya je guraren da take aiki ya ga ni sannan ya samu natsuwa.

Idan ta ta shi daga aiki koda zata je gida ita ma Furaira ta koma, ruwa za su Wai bo sai kuma wata goben.

Furaira na fahimtar karatu sosai kuma makarantar haWe take da islamiya shi ne abun da ya ?ara birge Rahma da makarantar.

*BIRNIN ABUJA*

Tun da aka samu Salim da Samir su ka farfaWo daga dogon suman da, su ka yi, ba su sake lafiya ba.

Hakan ya sa iyayen, su ka sake raba su da ?asar don neman lafiyar su.

Samir ne ya kalli Sufiyan ya ce "?an uwa wai har yanzu ba wani labarin a kan ?aunata?"

Ya na maganar sheWar shi na yin sama kamar zai sake wani suman.

Don ALLAH ku tausaya man ko dan ni, ku rage damuwa in sha ALLAH za'a same su nan ku sa.

Kun san ba zan juri ganin ku a wannan halin ba idan ni ma, ba so ku ke, na kwanta jiyar ba."

Salim ya san halin Sufiyan sam baya da juriya, da sauri ya ce.

"Kar ka sanya damuwa a ran ka Wan uwa, in sha ALLAH za mu samu sau?i nan ku sa, amma gaskiya ya dace mu koma gida nigeria."

"Ah ah gaskiya ba yanzu ba sai kun ?ara jin sau?i, ku dubi yadda ko tsayuwa bakwa iya yi akan ?afar ku sosai,.sai da Wan jagora, a haka za ku ce, mu koma gida."

Momy Saratu ce ta same su ita da sauran iyayen, ka na ganin su ka san, duk ba sa cikin hayyacin su saboda rashin lafiyar yaran na su.

Momy'n ta ce "?ana tun da an samu ka Wan fara magana ka daure ka bamu photos yariyar hakan zai iya taimaka mana wajen neman ta."

"Ka ga irin wannan matsalar aka samu rashin photos, ta wajen Salim hakan ya sa har yanzu bamu same ta ba."

Hawaye ne masu zafin gaske su ka fara zuba a idon sa, kuka ya fara sosai da?yar aka samu ya Wan tsagaita da kukan."

"Cikin muryar kuka ya ce,

"Momy wannan shi ne babban kuskuren da na aikata, ban taSa tunanin Waukar photon ta ba."

"Saboda a nawa tunanin na same ta, me zan yi da photo, idan ina son ganin ta kuma sai dai mu yi video call."

"Hakan ya sa ban taSa damuwa da zancen photo ba."

Momy Nafisa idanun ta cike da hawaye ta ce.

"Amma me ka aikata haka, a wannan zamanin a ce kun yi, ku san wata uku a tare amma baka taSa yi mata photo ko Waya ba a wayar ka."

"Yanzu don ALLAH daga ina ka ke son mu fara kuma?"

Sufiyan ya ce "Tsawon lokacin nan kai muke jiran ka dawo hayyacin ka mu samu photo, ko ka Suye su guri mai mahimmanci tun da duk mun duba ko ina babu, ashe ba haka ba ne."

Dady Nura ya ce "Shi ke nan ku daina damuwa za mu same su duk'kan su in sha ALLAH."

*PAGE* 3?? 4??
Yau dai Rahma jin ta take duk sai a hankali bata jin ta daidai haka ta kwana, a haka dai ta Wauki talla ita kuma Furaira ta wuce makaranta, ta gama tallar ta je shago amma kuma duk bata da natsuwa.

Oga ya ce "Lafiya kuwa, me ke damun ki? na ga kamar hankalin ki baya kan aikin yau."

"Wallahi oga yau bana jin daWi ne."

"Assha to kin ga, ki je gida kawai har gobe, ALLAH ya baki lafiya."

Haka ta Wauki hanyar tafiya gida ko ta kan gurin salon bata bi ba.

Da isar ta gida ta tarar da Furaira sai faman kuka take da sauri ta ?arasa gurin ta duk kayan makarantar ta sun Saci da jini ga duk'kan alama ita ma dawowar ta kenan.

Gefen ta kuma su Baffa ne shi da Innah kwance duk an yanyanka jikin su idan ba, ka matsa gurin su ba, sai ka Wauka sun mutu.

Ta na zuwa ta yi tambayar abun da ya faru da su sai mutanen gurin su kace ?an fashine su ka shiga gurin da Baffa yake kiwo ya yi masu gardama shi ya sa, su ka sassara shi.

Ita kuma Inna ta je kai ma sa fura abun ya rutsa da ita, bayan sun kora shanun sun tafi, aka samu mutane masu wucewa su ka taimaka su ka Wauko su aka kawo su gida.

Da sauri Rahma ta ce "Kuma shi ne, ku ka sanya su gaba kuna kallo ba wanda ya yi tunanin kai su asibiti?"

Baffa ne ya ri?o hannunta ya ce,

"Kar ki wahalar da kan ki ?ata ni kam ba ta shi zan yi ba, ita ma Innah ta ri?o Wayan hannun duk'kan su, su ka haWa hannunta da na Furaira."

Sannan su ka ce, "Mun yarda da ke mun yarda za ki kula da ?anwar ki ko da bama raye, don ALLAH ga amanar ?aunar ki nan ke da ita yanzu kun zama marayu don ALLAH ku haWa kan ku ALLAH ya yi maku albarka."

Kuka su ke sosai Rahma ta ce "Ku bari muje asibiti in sha ALLAH za ku samu sau?i."

Ashe lokacin duk bada mutane su ke magana ba, sai da Yayan Baffa ya ce "Sai dai ha?uri fa amma sun rigamu gidan gaskiya."
Rungume su, su ka yi suna ta kuka duk sai kallon su ake ba mai lallashi.

Sati biyu da rasuwar, su na zaune duk sun fita hayyacin su kana ganin su kaga abun tausayi, sai ga yayan Baffa ya zo gurin su ya ce,

"Dama na zo sanar da ku lokaci ya yi daya ka mata, ku ta shi daga gidan nan saboda dama can ba gidan Baffa ba ne, nawa ne na ara ma shi kuma yanzu ba ya nan."

Rahma ta ce "Haba Baffa ina ga kai ma uba ne kai mai ri?e mu ne koda Baffa na raye balle kuma yanzu da baya raye."

"Ni kam ba uban ki bane ko ita da na san waye uban ta ba zan ri?eta ba balle ke tsintarciya, kuma ba kiga ko shi da zai mutu ke yabawa amanar ta ba?"

"Ba ki yi mamaki ba, ga ni a raye amma ya ba ki amana to saboda ya san wane ne ni, shi ya sa."

"Don haka ku hanzarta tun ban yi maku wula?anci ba."

"Furaira ta ce "Kowa a rugar nan ya san sai dai kanemi abu a gurin Baffa na, ba dai shi ya nema a gurin ka ba."

"To marar kunya nuna man kina makarantar boko kin lalace kin fitsare ?afafun ki, to wallahi na ma fasa Waga maku ?afa yanzu za ku bar gidan nan, kuma na fasa haWa auren ki da Wana tun da kin zama ?ar iska."

Ya na maganar sai faman kun far baki yake yana Waga sanda kamar zai rabka masu ita a kai.

"Ya isa haka nan gida dai kake son mu bari to za mu tafi ka yi duk abun da zaka yi da shi, kai ma dai mutuwar zaka yi, ka bar shi a nan duniya, amma zancen kiran ?anwata da ?ar iska bai ta so ba, don wallahi zan manta da tsufan ka, na yi ma abun da sai ka yi dana sa ni."

"?an ka kuma idan ya dawo ka aura ma shi mata huWu lokaci Waya shi da, ba Wan iska ba."

Hannun Furaira ta ja bayan sun haWa ?an kayan su, su ka bar rugar amma kuma ba su san ina suka nufa ba.

Can ta ce "?anwata mu je gurin oganmu ko zai iya taimakon mu."

Su na zuwa ya ce "Ya na dai na ganin ki kwana biyu?"

Nan ta sanar da shi duk abun da ya faru da kuma dalilin zuwan su gurin shi, ne man taimako don ALLAH ko gurin mahaifiyar shi ya kai su, za su rin?a yi mata aiki, su dai gurin zama kawai suke ne ma.

"Ayya gaskiya ni ma iyayena duk sun rasu kamar ku Win nan, amma kuma akwai mafita Waya wace zan iya taimakon ku, mafitar kuwa ita ce ki aure ni, ni kuma na yi maki al?awarin ri?e ku."

"Ba ki yi mamaki ba a matsayin ki na ?a mace na baki aiki a nan? to saboda na ganki kuma ina son na aure ki, ina ta tunanin yadda zan sanar da ke, don haka me ye shawarar ki, amma fa ina da mata biyu ?a ?a shidda."

Hawaye ne na zubo mata a fuska, mutumen da take yi wa kallon yana da kir ki ashe ba haka ba ne, ga kuma kalmar da yake ta maimaitawa ta yana son ta, ji take kamar ta matse ma shi wuya ya mutu ta huta da jin kalmar saboda ta tsani ta, sannan ta tsani duk wanda zai sanar da ita kalmar.

Amma kuma akwai bu?atar ta amince ko dan Furaira, ya dace a ce ta samu guri Waya ta natsu akan karatun ta domin ta cika burin ta.

Tun da nata burin bai cika ba ya dace na ?anwarta ya cika, shi ne tunanin ta.

Da ace ita kaWai ce bata da matsala ko a rumfar kasuwa za ta iya rayuwa, sai dai bata yi wa Furaira wannan fatan.

Jin muryar oga ta yi yana faWin kinfa barni a tsaye ba amsa, tunanin me, ki ke yi haka?"

"Ba komai yi ha?uri kuma na amince."

Furaira ta kalle ta cikin sauri ta ce "Wallahi Addah ba zai yuyu ba kina ta Sata rayuwar ki saboda ni, ko yanzu na tabbata saboda ni, ki ka yarda."

"Mutane nawa ki ka kora a baya waWan da ma su kafi wannan komai shi ne yanzu za ki Sata rayuwar ki haka?"

"To jira ki ji Addah in dai saboda ki samaman rayuwa mai kyau ne da kuma farin ciki shi ya sa, za ki yi wannan auren to ni kam bana so,
saboda ba zan taSa farin ciki ba har abada,
Mu tafi hanyoyin ALLAH yawa ne da su, ke ki ka sanar da ni hakan bai dace yanzu ki manta ba."

Haka dai su ka bar gurin, gurin madam su ka je, ita ma dubu biyar ta ba su, ta ce "Daina ma sana'ar zan yi saboda zan koma gida Enugu da ace kun wuce yau ba za ku, same ni ba."

Godiya suka yi sannan su kabar gurin, sun yi yawo har sun gaji amma ba mafita, Furaira ta ce.

"Addah ni fa yunwa nake ji sosai."

"To ki jira ni a nan."

Ta siyo mata abincin kenan sai ta ji wata mata na ihu tana faWin, "Don ALLAH ku taimake ni zai gudan man da jaka Sarawo ne."

Amma kowa harkar ga ban sa yake mutanen ko ajikin su, ita kuma yana zuwa ku sa, da ita ta samu wani icce ta sanya a tsakiyar ?afar shi, nan ya faWi warwas, bata bari ya ta shi ba, ta dinga buga ma shi iccen har sai da matar ta zo ita ma, ta mare shi sannan ta Wauki abincin ta tafi bayan ta bawa matar jakar ta.

Furaira na fara cin abincin matar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login