Showing 48001 words to 51000 words out of 123822 words

Chapter 17 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3444

ki, da yaron gidan nan ba sai dan ?aruwar kansu, ke baki yi mamaki ba lokaci Waya a tsinto ki kuma a ce za ki auri Wan wannan gidan babba irin haka?"

"To bari ki ji na gaya maki gaskiya tun kafin na tafi gida nake da labarin cewa malamin su yaba da kalar yarinyar da za'a ne mo kuma idan an samu a aura ma Samir ita to lalle ba za su taSa tsiya ba, kuma arzi?in su zai yi ta ?aruwa ba yanke wa, amma ki sani duk soyayyar da suke nuna maki ta ?arya ce musamman shi Samir."

"Kin gama zan iya tafiya ko da saura? Kin ba ni mamaki ki na zaune da mutane tsawon lokaci ki na ci ajikin su amma kike faWar irin wannan muguwar kalmar game da su, to saurara ki ji, na yarda da su fiye da kaina kuma wannan maganar da ki ka faWa ita ce ta ?ara sa man son auren Samir."

"Sannan bayan na aure shi ko da jinina su ke sha zan yi masu uzuri na Wau ka suna da dalilin yin haka."

"Kuma ki sani ni ba'a kawo man jita jita don haka daga yau kar ki sake, ki ri?e girman ki ina fatan kin fahimta?"

"Kin rufe idanun ki kin ?i ganin gaskiya to ki sani kwanan nan za ki yi, da na sani saboda Hajiya ta na shirya wani abu akan ki don ta ce ko, za ta yi tafiya tsira ra akan ta lauci, ba za ta bari Wan ta ya auri marar asali ba...

*PAGE* 3?? 2??
A daren ranar Dady ya sanar da su tafiyar da zasu yi shi da Samir duba sauran yaran shi dake Germany amma ba da Momy zasu yi tafiyar ba saboda Rahma.

Samir ya ce "Dady kawai mu tafi da su duka don gaskiya bana son na tafi na bar mata ta a nan."

Dady ya ce "To marar kunya Ta ya, za mu tafi da ita bayan zancen auren za mu yi da ?an uwana bayan na duba yaran nawa, in ko na fasa tafiyar shi ke nan ka hutar da ni."

Da sauri Samir ya ce "Ah ah Dady da ma can wasa nake, ALLAH dai ya kaimu lafiya."

Momy ta ce "Ohh ni Nafisa Alhaji ban san lokacin da Samir ya za ma marar kunya haka ba."

Shi ma dariyar ya yi, ya ce "Humm sanadin ?ata ne."

Tun da safe su ka shirya tafiya Samir ya ja Rahma gefe Waya don su yi sallama, Rahma gaba Waya sai ta ji bata son ya yi tafiyar jikin ta duk ya yi sanyi ?iris take jira ta sanya kuka.

Ya lura da hakan, ya ce "?anwata ko baki son na tafi ne?"

Cikin rawar murya wace ke shirye da yin kuka ta ce "Ba na son na rasa ka dai, sam ba na son na rasa wannan soyayyar ita ma."

Cikin matu?ar razana wace har sai da ta nuna akan fuskar shi ya ce "Kin taSa rasa wata soyayyar ne a can baya?"

Ganin ta yi shuru ba amsa ya sa shi cewa kar ki da mu, in sha ALLAH ba za ki rasa ni ba muna tare har abada, ke ki ma ?addara wani dalilin ya sa, ba mu yi aure ba to in sha ALLAH ba zan taSa yin aure ba a rayuwa ta saboda ni Win na ki ne, ke Waya bawa ta."

Haka kawai ta tsare shi da ido saboda kalaman shi sun yi mata kama da na Yaya Salim Win ta.

Har sai da ya kai ga cewa "Lafiya kuwa ?anwata?"

Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce.

"Yaya a baya na Wauka son Wan mai kuWi ga ?ar talaka kuskure ne, hakan ya sa na tabka wani babban kuskuren a baya amma yanzu na gane ba haka bane shi ya sa nake son na gyara akan ka, saboda ban san ina zan je na gyara wan can ba, amma na ro?e ka yayana kar ka bar ni, na yi zaman jiran ka, ka dawo a kan lokaci."

Ya ce "Amma gaskiya na ji daWi sosai yanzu na ?ara tabbatar wa ina da matsayi a ran ki, zan tafi hankali na kwance saboda na san na samu gurbi a zuciyarki kuma in sha ALLAH zan dawo a kan lokaci, sannan kar ki rin ?a yin ni sa da wayar ki saboda mu rin?a magana a koda yaushe."

Muryar Dady suka jiyo yana faWin "Momy ina ga tafiya ta kawai zan yi saboda na ga kamar sallamar ba ta ?arewa."

Rahma ta ce "Ah ah Dady mun fa gama tun Wazu kai kawai ya ke jira, ko Yayana?"

Samir ya ce "A haka ne Dady."

Bayan kwana biyu da tafiyar su, a koda yaushe tana ma?ale da waya ko aiki zata yi zai ce ta ajiye wayar ku sa da ita yana taya ta fira har ta gama.

Ranar gama wayar su kenan ya ce "Ki jira ni yanzu zan dawo su Dady na ki rana." hakan ya sa ta fito parlor gurin Momy.

Momy ta ce,
"Ya bar ki kin fito kenan? idan kina biye masa sai ya ?ona maki kunne akan zafin waya."

Murmushi ta yi wanda shi ne Wabi'ar ta a koda yaushe ta ce "In sha ALLAH Momy ba abun da zai faru."

Suna cikin firar su aka kira wayar Momy tana Wagawa sai ta ce "Hajiya Larai me ke faruwa ne, na ji muryar ki haka?"

Sai kuma ta ce "Shi ke nan, gani nan tafe yanzu."

Kallon Rahma Momy ta yi, ta ce "?ata ko za ki shir ya mu tafi tare? wai ?ar gidan Hajiya Larai ce Aziza ba lafiya."

Da sauri Mama Ladidi ta ce "Ah ah Hajiya ai da kin bar ta gida tun da ina nan ko Bilkisu?"

Rahma ta ji duk bata yarda da kalamanta ba har za ta ce Momy zan bi ki sai kuma ta tuna Samir ya ce zai kira kuma tabbas zai kira tun da shi ya faWa kuma bai dace taje asibiti tana waya ba.

Kawai sai ta ce "A momy ki tafi kawai ALLAH ya bata lafita lafiya.

"Shi ke nan amma ki zauna ki huta sannan idan kin ji kaWaici ki kira yayanki ya taya ki fira, kin ji ko?"

"A Momy na ji, har ta kai ku san fita sai ta ji kuma kamar ta bita kawai sai ta tsayar da ita, ta rungume ta sannan ta ce "Momy ki kula da kan ki sosai."
Ita ma Momy abun da ta ce kenan.

Ko minty biyar Momy bata yi, da fita ba sai ga Mama Ladidi da lemu a kofi ta ce,

"?ata don ALLAH ki sha man lemun nan ki ji, na yi daidai ni dai ina son na iya kalolin lemun da kike yi."

Haka kawai Rahma ta ji sam ba ta yarda da zancen ta ba, ta ce "Mama Ladidi kin manta yau ina azumi sai dai wata rana amma dai ko a ido na san ya yi in sha ALLAH."

"Hakane to ALLAH ya bada lada."

Har zata tafi sai kuma ta ce "?ata amma don ALLAH kar ki rufe Wakin nan na yi ta bugu kamar Wazu amma ba ki jiba."

Ta ce "To shi ke nan."

Tabbas ta so rufe Wakin saboda sam ba ta yarda da ita ba, sai dai tana zuwa kusa da ?ofar kiran wayar ta ya shigo, garin sauri ta Waga kar ta tsinke hakan ya sa, ta manta zancen rufe Wakin suna ta wayar su hankali kwance, can kuma ya ce bari na kira ki video call,
yau dai na haWa ki da waWan nan natattun surakan na ki tun da kin ce Momy bata nan balle ta hana ki.

Bari na kira yanzu, kinga muna tare da su, in kuma ba haka ba, na san ba za su barmu mu yi soyayyar mu hankali kwance ba."

Dariya ta yi, ta ce "Ai suna da gaskiya bai da ce ace yadda kake yawan zancen su ba ace har yanzu ba su san ni ba, ni ma kuma haka."

"Shi ke nan na ji tun da kare su kike bari na kira ki yanzu, yanzu fa zan kira kar ki yi, ni sa."

Ya na ka she wayar kafin wani kiran ya shigo sai ji ta yi, an watsa mata wani abu a jiki gaba Waya ta ji ko hannun ta bata iya Waga wa jikin ta duk ya yi sanyi, jikin kamar ba nata ba.

Ta na iya fahimtar komai amma kuma ba ta iya yin komai akan idon ta Samir ya yi ta kiran ta amma ba damar Wagawa ?arshe ma sake turata suka yi can ta ?ara yin ni sa, da ita.

Akan idon ta mata biyu da maza da Mama Ladidi haka su ka sanya ta cikin ?aton zanen gado suka naWeta a ciki sannan suka fita da ita.

Sun yi tafiya mai ni san gaske wanda misilta lokacin ba abu ba ne mai sau?i, wani guri su ka samu kamar dai irin kasuwar ?auye haka, nan suka jefar da ita, su kace.

"To nan ne gurin da ya dace dake ba gidan Alhaji ba."

Da?yar ta iya ri?o ?afar Mama Ladidi cikin jigata ta ce,
"Don ALLAH me ya sa kika yiman haka?"

Wata dariya ta yi mai kama da mugunta ta ce,

"Bana sanar dake Hajiya bata son ki ba amma kin ?i yarda, to ita ce ta san ya ni, sannan ta ce na tabbatar kin fita rayuwar Wan ta, ga baki Waya."

Idanu ta rufe hawaye masu zafi su ka zubo tana son ta yarda amma zuciyar ta ta?i aminta sam, sai hango irin soyayyar da family'n suka nuna mata da tsantsar kulawa.

Bayan tafiyar su ta ce, "Gaskiya Momy ba zata iya cutar da kowa ba."

Tana cikin wannan tunanin sai ta ga mutanen gurin nata gudu suna faWin doki ya kufce kowa ya gudu, ga shi kuma ya na tun karo ta amma bata iya guduwa tana kallon sa yabi ta ?afar ta ya wuce ?ashin ?afar sai da ya amsa amma ta ma gaza yin kuka saboda tsabar azaba.

?ASAR GERMANY
Samir ne keta faman kiran wayar amma ba ta Waga ba ?an uwan shi ya duba ya ce

"Me ke faruwa kuma yanzu fa nace karta Waga ko ina ta jira na haWaku amma kuma ji bata Waga ba.

Yanzu haka wani aikin ta hango cikin gidan ta ce zata yi kafin Momy ta dawo ita ko gajiya bata yi da aiki."

Sufiyan ya ce "Wata?il cikin yaren ku na soyayya ka ce idan ka kira kar ta Waga har sai mun bar gurin."

Sannan ya kalli Salim ya ce "?an uwa ka shirya satin nan mu je nigeria sai mu ga yadda zai hana mu haWuwa da ita."

Salim wanda har yanzu bai gama dawo wa hayyacinsa ba ya ce "Hakane Wan uwa ni ma duk na gaji da ?asar nan ina son na koma na dage da neman khadija wata?il ALLAH ya ji tausayina ya bayyana man ita."

"Samir ya ce ALLAH ba haka ba ne yau dai na so ace kun gaisa haka nan, tun da ita ma tana son hakan amma, ban san me ya sa, ba ta Waga ba har yanzu.

Kuma a gaskiya ina jin jikina ba daidai ba kamar akwai wani abun marar kyau zai faru.

Kallon su ya yi da sauri ya ce kuna ganin anya kuwa, mata ta tana lafiya kuwa?"

Sufiyan ya ce "To mai mata na ga dai yanzu ku ka gama magana da ita kuma na ji kace har azumi take to mai ?arfin yin azumi ne za'a ce ba shi da lafiya?"

Baza ka fahimta bane saboda kai har yanzu kana nan kamar dutse bawa ni motsi, ba wace ta yi wuff da zuciyar ka, amma na san Wan uwa Salim zai fahimce ni."

To fa abun har da gori, to na yi shuru sarkin soyayya yanzu dai kira Momy ka ji ko ta dawo sai ka ji meke faruwa da matar ta ka ta?i Waga wayar ka."
Cikin murmushi ya yi maganar.

Salim ya ce ALLAH ba shi kaWai ba, ni ma yau ina jin kamar tawa matar ba ta cikin lafiya."

"To fa yau group Win na masu aure ne kenan ni dai yau ina ganin abubuwa."

To kai ma sai ka yi matar kawai ka huta da gorinmu, yanzu dai bari na kira Momy ko zan samu natsuwa."

ABUJA NIGERIA
Shigowar Momy kenan ta fara kiran, "?ata kina ina, ina kika shige?"

Wayar ta ce ta yi ringing tana Wagawa Samir ya ce "Momy mata ta lafiya take? tun Wazu na ke kiran ta amma ba ta Waga ba."

"Ni ma yanzu na shigo gidan ka ga sai faman kiran ta na ke amma shuru, bari na duba Wakin na ta ko bacci ne ya yi awon gaba da ita."

"Ok Momy tafi da wayar ba sai na ka she ba, mu ji me ke faruwa."

Wasa wasa ba gurin da Momy ba ta duba ba a gidan amma ba Rahma, ?arshe ma ta hango wayar ta can ?asan gado, nan take hankalin ta ya fara ta shi shi ma Samir duk ya ruWe ko ina cewa yake Momy taje amma ba alamar ta sam.

Tana cikin binciken gidan sai ga Mama Ladidi ta dawo, da sauri Momy ta ce,

"Yawwa Mama Ladidi don ALLAH ina kika ji ?ata ta ce zata shiga?"

Sai cewa ta yi "Ah ah, gida ko nabar ta na Wan je nan na siyo katin waya saboda duk masu aikin gidan sun shiga masallaci sallah."

Momy ta ce "kamar ya? yau she kuma duk aka fara watsewa du ka abar gidan ba tsaro, na dai ga raba kansu su ke idan waWan nan sun dawo waWan nan su tafi?"

Ganin magana da ita ba shi da wani amfani hakan ya sa da sauri Momy ta fita waje tana tambayar duk wani ma ai kacin gidan ko ya ga ?arta amma sai su ce, ba su ganta ba.

Cikin tsanani ta shin hankali Samir da ?an uwan shi suka fara haWin kayan su da shirin barin ?asar a lokacin.

Su Dady ne na tarar da su kowanne ba natsuwa.
Tambayar su suka yi, nan suka sanar da su duk abun da ke faruwa.

Hakan ya sa, duk su ka shirya tafiya har su Dady Win.

Suna sauka gidan suka tarar da Momy duk ta fita hayyacin ta ga shi har dare ya yi amma ba labarin Rahma.

Samir da yaga tabbas bata nan fa, a gurin ya faWi sume, shi ma Salim nan take komai ya dawo masa sabo.

Ya na ?o?arin Waga Samir shi ma nan ya faWi a sume, hankalin duka families ya ta shi.
Musamman Sufiyan ganin ?an uwan shi a wannan yanayin,
kuma ga shi ba'a san ina za'a samu ?an matan ba.
Do min shi ne kaWai babban maganin su.

Cikin ruWewa hawaye shar a fuskar shi, da ma can duk yafi su raunin zuciya.
Ya fara kiran su nan su ya na faWin.
"Don ALLAH ku ta shi, in sha ALLAH za mu gansu."

*PAGE* 3?? 3??
Bayan wani Wan lokaci Rahma ta ji kamar ?arfin jikinta ya fara dawo wa ga duk'kan alama komai ne ne, su ka zuba mata ya fara sakin jikin ta.

?o?arin ta shi ta fara yi duk da yanzu kam bata san ina ta dosa ba, sai dai kuma ta gaza ta ka ?afar ta.

Jan ?afar take yi, tana jin ?afar kamar ba, ta ta ba.

Tafiyar kawai take, ta fara ganin duhu a idonta, daga nan bata sake sanin a ina take ba.

Ta na buWe idanunta sai ganin ta, ta yi a cikin wata bukka.

?ar matashiyar yarinya ta gani wace shekarun ta, ba za su gaza sha hudu ba, da shigar fulani a jikinta.

Cikin farin ciki yarinyar take faWin "Baffa Innah ku zo, ta farka."

Wani dattijo ne ya shigo tare da shi kuma wata mata ce, dattijon ya ce "Sannu kin ji yarinya, ya jikin na ki yanzu?"

Ta amsa da faWin "Akwai sau?i in sha ALLAH."

Ta yun ?ura ta mi?e zaune ta gaza, da sauri ya ce "Ki yi ha?uri akwai karaya a ?afar ki."

Haka ta koma ta kwanta tare da faWin ina take ne nan?

Ya ce, "Ki na rugar fulani ne, yau kwana uku kenan da muka tsinto ki ni da ?ata Furaira"
Ya nuna wannan yarinyar.

Sannan ya ce "Ni dai sunana ?ahiru amma ana kira na da Baffa, ita kuma wannan mata ta ce Umaima su nan ta amma ana kiran ta da Innah, wannan kuma ?ar muce sunan ta Furaira."

Kallon ta ya yi, ya ce "To ke kuma me ye, su nan ki sannan daga ina kike kuma waye ya yi maki haka?"

Da sauri ta rufe idon ta sosai sannan ta ?i buWewa saboda ta san tana buWewa sai hawaye.

Ji ta yi an dafa ta ashe Furaira ce, ta ce "Idan ba ki son tuna abun da ya wuce a baya to ki bar shi kawai ba sai kin faWa ba amma don ALLAH kar ki yi kuka bana so."

"Kin ga tun da muka samo ki nake ta murna na samu Addah ni ma saboda ba ni da ?an uwa ni kaWai ce ina fatan za ki yarda ki zama Addah ta."

Murmushi Rahma ta yi, ta ce "Sai dai ban san me kalmar Addah ke nufi ba."

Innah ta ce "Addah yana nufin yayar ta ko Aunty."

Ta ce "ALLAH sarki to ki sanya aran ki daga yau na zama Addah a gun ki."

Cikin farin ciki ta ce "To me ye sunan ki?"

"Sunana Rashida."
Amsar Rahma kenan.

Haka ta cigaba da rayuwa a rugar suna bata kulawa sosai, kafin su tsinto ta Inna da Furaira ke zuwa talar nono cikin gari shi kuma Baffa ya je kiwo idan sun dawo akan lokaci sai ita Furaira ta same shi gurin kiwon su dawo tare.

Amma tun da, su ka tsinto ta, su ka dena tafiya su duka sai dai Waya ya je da safe Waya kuma da yamma shi kuma ya je kiwo duk dan abar ta ita kaWai.

Lokaci na tafiya ?afar ta na samun sau?i don har ta fara koyon tafiya.

Wata rana Furaira ta dawo daga kasuwa ta je gurin Rahma da gudu ta ce "Addah muga hannu ki."

Ta ja hannun ta sanya mata wani awarwaron duwatsu ta ce.

"Shi ne kyau ta, ta ta farko a gurin ki don haka don ALLAH ki ri?e shi sosai ki rin?a tunawa da ni akoda yaushe musamman idan bana ku sa dake duk'da ba wani mai tsada ba ne amma ya zama mai mahimmanci agurin ki.

Rahma ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login