Showing 81001 words to 84000 words out of 123822 words

Chapter 28 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3426

wanda ya yi baccin daWi, su kuma jigon tafiyar ko baccin ba su samu ba.

Tun da safe suna yin sallah ko wannen su ya yi wanka cikin sauri babu wani dogon shiri, ya ri?a hannunta sai gidan Dady Ahmad aikuwa sun yi sa'a saboda kowa na gidan, kuma duk suna parlor tun da suka dawo daga masallaci sun ka zauna gurin ga duk'kan alamu suna magana ne a kansu Win.

Suna shiga suka rin?a yin sallama kamar sabbin musulunta da ?yar aka samu masu amsawa sannan suka gaidasu nan ma, ba kowa ya amsa ba, waWan da na amsar ma kamar an yi masu dole.

Momy Nafisa ta ce "Lafiya me ya kawo ku gidan nan, ba mun yi maku kashedi ba?"

Sufiyan ya daure ya ce "Ha?uri mu ka zo mu ?ara ba ku don Allah ku yi ha?uri ba za mu iya jurar ganin kuna fushi da mu ba."

Momy Aisha ta ce "Mu a suwa kuma? ai tun da har kunka iya jure fushin Allah a kanku, to namu fushin ba wani abu ba ne."

Momy Saratu ta ce "Me ya sa kuke Sata lokacin ku gurin yi ma sa bayani, ka ga malam don Allah ta shi kabar gidan nan tun ban rasa ha?urina ba, sannan ta kalli Sufayya ta ce "Ke ta so nan ki ci abinci na san tun jiya ba abun da kika ci."

Da sauri Aunty ta ce "Wallahi ko mutuwa za ta yi, ba za ta ci komai ba a gidan nan, yadda zai fita haka ita ma za ta, bi shi su fita."

Cikin sar?ewar murya kamar ta mai shirin yin kuka Sufayya ta ce "Momy ni bana jin yunwa, yafiyar ku nake so don Allah ku gafarceni na tuba wallahi."

Dady Nura ya ce "Ku je ku fara neman yafi yar Allah sannan ku nemi ta mu daga bi sani, yanzu dai ku ta shi ku Sace mana da ga ni" su Kaka na gefe amma ba su ce uffan ba.

Bayan sun dawo gidansu ya kalle ta ya ce "?anwata na san yanzu ba ki son wani doguwar magana, amma duk da hakan ina son na yi maki tambaya, shin wai kwana biyun da kike son magana da ni mene ne kike son sanar da Ni?"

Kallon sa ta yi hawaye masu matu?ar zafi suna zubar mata ta ce "Ah ah Yaya maganar ta wuce bata da wani amfani yanzu gaskiya, ka ga bari na tafi in haWa maka breakfast yanzu" tana gama faWar haka ta mi?e ta shiga kitchen.

Da kallo ya bita yana tunanin shin wai mene ne ta so sanar da shi kuma yanzu take faWin ba shi da amfani, haka kawai ya koma jin haushin kansa na rashin bata lokaci a lokacin da take ta son su yi magana.

Ita kuma tana shiga kitchen ta ce "Ka yi ha?uri Yaya, a lokacin na so in gyara ala?ar zaman mu ne, duk da na san cewa har yanzu ba wani jinka nake a raina ba."

"Amma kuma da na yi dogon tunani sai na tuna cewa tabbas za mu haWu da fushin ubangiji saboda kalar wannan zaman, ni kuma tsoron haka ya sa, na so in gyara komai ko da kuwa zan yi maka ?aryane na ce ina son ka."

"Tun da ka ce sai ranar da na fara kallon ka a mijina, kuma ina da tabbacin in sha Allah ba za ka sauya maganar ka ba, sai dai kuma ?addara ta riga fata yanzu na san komai zan faWa ba za ka yarda da ni ba, za ka yi zargin saboda ina son iyayenmu su yafe mana ne, ya sa na faWi duk wannan" hawayenta ta share sannan ta fito ma sa, da breakfast Win.

*******************
Haka rayuwarsu ta cigaba yau tsawon sati biyu ke nan yanzu Sufayya da ta dawo daga makaranta sai gidan ta, ta rage shiga gidajen iyayen na su kuma su ma ba mai kula da su sai ?an uwan su, bata jin daWin rayuwar ga ba ki Waya duk ta yamotse ta fita hayyacinta, ganin ta haka ya ?ara Waga hankalin Sufiyan sosai.

Yau ma kamar kullun ta yi wanka ta yi shirin kwanciya sai kuma ta gaza yin baccin, ta koma zaune tana tunanin duk wannan abun da ke faruwa fa laifinta ne.

A zahiri ta ce "Saboda mugun taurin kaina ga shi na sanya iyayenmu na fushi da mu, tabbas gaskiyar Aunty ce, da ace Yaya ya ga fuska daga gurina tun lokacin bikin da ba zai Waukar man wannan al?awarin ba, da kuma yanzu iyayenmu ba su yi fushi da mu ba, tabbas ni ce mai laifi kuma ya kamata in gyara ko da kuwa zuciyata za ta buga ne in mutum, in dai family's na, za su yi farin ciki kuma su gafarta mana."

Dukan gadon ta yi da ?arfi ta ce "Ya zama dole na ajiye duk wata damuwa ta na gyara wannan kuskuren ko zan samu in daidai ta komai" sai kawai ta ji hawaye na son zuwan ma ta, da sauri ta dakatar da faruwar hakan.

Tana shirin sauka daga kan gadon ta ji wayarta ta yi ?ara alamar shigowar sa?o, tana dubawa ta ga Salim ne ya turo mata text, kamar haka.

"Ina fatan kina lafiya? ?anwata akwai abun da nake son na sanar dake amma ina fatan za ki fahimceni da kyau, na san kina damuwa da irin zaman da kuke yi da iyayenmu na san kuma kina son kiga komai ya daidai ta, to ki sani akwai mafita."

"?anwata wannan damar tana hannunki ke ce kawai za ki iya dawo ma wannan family's farin cikin su, ba sai na yi wani dogon bayani ba na san kin san abun da nake nufi, don Allah ki yi ?o?arin ganin kin gyara komai saboda wallahi ina matu?ar damuwa ganin ku a wannan halin."

Ko dan saboda ni da soyayyar da kike yi man, da kuma tsoron Allah dake tare da ke, ki yi ha?uri ki gyara ?anwata, na gode Allah ya yi maki albarka ya kawo farin ciki mai Worewa a rayuwarki."

Tana gama karantawa ta ji wasu hawaye masu zafi sun zubo mata, wannan sa?on sai ya tuna mata da sa?on Samir wanda ya tura mata awa biyu da suka wace, shi ma ku san abun da ya faWa ke nan ban ban cin kaWan ne, haka ta sharesa bata mayar ma sa da amsa ba, yanzu shi ma Salim haka ta jefar da wayar tare da jan dogon tsaki, shi ma bata ba shi amsa ba.

Sauka ta yi daga gadon ta sake wani sabon shirin ta sauya kayan baccin jikinta zuwa wasu masu matu?ar Waukar hankali, zuciyarta ta riga ta dake haka ta fito yau babu ko aminin nata wato hijab.

Tana isa ?ofar Wakin nasa sai kuma ta tsaya tana nazarin shin ma ta ina za ta fara an ya kuwa zai yarda da abun da za ta faWa ma sa? ta ce "Ya Allah ka sa, ya yarda da ni ka sanya kar ya gano ni, ya amince da duk abun da zan faWa ma sa, ya Allah ka taimake ni."

Haka dai ta daure ta buga ?ofar Wakin gabanta sai faman faWuwa yake, shi kuma Kamar jiran bugun nata yake a take ya buWe ?ofar, dama can bai yi bacci ba tunanin ta kawai yake.

Yana ganin ta a tsaye ya yi saurin zuwa ku sa da ita yana tambayar "Lafiya me ke faruwa ko wani abun ne, ya tsorata ki?"

Kallon sa ta yi, ta ce "Yaya waWan nan tambayoyin fa, ta ina kake son na fara baka amsa, kuma ma wata nawa ina cikin gidan duk can ba abun da yake tsorata ni sai yau?"

"Wannan Waukar zafi haka fa ?anwata? kin ga Allah ya huci zuciyarki dama ga ni, na yi kin fito ba ko hijab sannan kuma ga dare ya yi, shi ya sa, na yi tambayar ko wani abun ne ya tsorata ki."

"To ba haka ba ne ina sane da yadda na fito" kallon sa ta sake yi sannan ta ce "Yayana ya naga kana kallona haka kuma ka tare ?ofar, ko ba za bar ni shiga Wakin naka ba? kaga karka da mu magana kawai na zo mu yi in kana da lokaci yau."

Da sauri muryarsa na rawa ya ce "Me zai hana ki shiga Wakina ?anwata? bayan kin san duk gidan mallakinki ne kina da damar yin duk abun da kika ga dama, sannan kuma sanin kanki ne duk lokacina naki ne don haka mu je, ki sanar da ni me ke faruwa."

A kan kujera ta zauna shi kuma ya zauna bakin gado, ta sunkuyar da kanta ?asa, ta gaza magana sun kai minty Waya, ganin shuru ya yi yawa, ya sanya shi cewa "Ina jinki ?anwata ki yi magana."

Da ?yar ta buWa bakinta cikin muryarta mai sanyi ta ce "Dama Yaya na jima ina son sanar dakai wata magana amma ko da yaushe na yi yun?urin hakan sai naga kamar ba za ka yarda da ni ba, amma yau na shirya sanar da kai ko da kuwa za ka ?i yarda da ni Win."

"Yaya a lokacin bikinmu tabbas na shiga ruWani sosai ka sancewar idona ya rufe bana ganin komai sai cikar burina wato na yi karatu na zama doctor sai kuma ga maganar aure ya ta so lokaci Waya kai tsaye."

"Hakan ya sa na Waga hankalina duk da, na san aure ba zai hana karatu ba, amma ana wa ra'ayin nafi son na kammala karatun tukunna saboda nafi son duk abun da zan yi, ya zan na mai da hankalina duka a kansa kawai."

"Sai nake ganin kamar idan na yi aure hankalina zai rabu biyu ne, wannan dalilin ne ya sanya na kasa baka kulawar da ya dace har kake ganin kamar bana son ka a matsayin mijina."

"Bayan zuwana gidan hukuncin da ka yanke a kaina a lokacin farin ciki ya kamata na yi saboda na samu damar yin karatuna a natse, amma sai na samu kaina da jin saSanin hakan a raina, saboda a lokacin na ji ba daWi sai dai ba yadda zan yi na san ko da na sanar da kai ba lalle ka yarda da ni ba."

"Lokuta da dama sai na yi yun?urin sanar da kai cewa abun da kake tunani ba haka ba ne amma kuma sai na kasa, har muka Wauki tsawon wannan lokacin."

"A ranar birthday Wina ka yi matu?ar ?o?ari wajen ganin ka sanya ni farin ciki, don na san tabbas 80 cikin 100 duk shirin
ka ne, na ji daWi sosai hakan ya sa, na ?uduri a niyar taron na watsewa zan sanar da kai gaskiyar lamari."

"Sai ga shi cikin rashin sa'a wannan matsalar ta tunkaromu iyayenmu duk sun yi fushi da mu, hakan ya sa jikina ya yi san yi saboda na san tabbas duk yadda zanyi ma bayani ba za ka yarda da ni ba, za ka yi tunanin saboda fushin iyayenmu na yanke wannan hukuncin, yanzu ma ga ni na yi lokaci nata tafiya hakan ya sa, na yanke hukuncin zuwa na sanar da kai, duk abun da ke raina."

?ara sunkuyar da kanta ta yi sannan ta ce "Yayana ka ce duk ranar da na fara ganin ka a matsayin mijina to na sanar da kai, Yaya to yau ga ni a gabanka na zo gurin ka a matsayin matarka ba ?anwarka ko ?awarka ba."

"Sannan kuma ina mai neman afuwarka saboda halin zurfin cikina ya kai ga har iyayenmu na fushi da mu, kuma don Allah ka yafe man na rashin sanar da kai a kan lokaci, Allah ka ji dalilina amma yau ga shi, ina mai neman afuwarka."

Rufe idonta ta yi sosai saboda tsoron kar hawaye su zubo ma ta shirin ta ya lalace, cikin ?arfin hali."

Ta ce "Ina son ka, ina son ka, ina son ka, har cikin zuciyata, Yayana ka yarda da ni don Allah."

Shuru Wakin ya yi na tsawon lokaci sun Wauki kamar minty biyu ba Wanda ya ce uffan.

Ta gaji da shurun ta ce "Yayana yana ji ka yi shuru ne, ko kana ko konto ne, a kan abun da na faWa?"

Nan ma shuru ta ji ba alamar zai yi magana, Wago kanta ta yi nan suka haWa ido da juna, ta yi saurin kawar da nata idon saboda wani irin razana da ta yi, ganin duk ya sauya lokaci Waya idonsa duk sun yi jajir hawaye sun cika su sosai, ya kuma kafe ta da su, ko motsawa baya yi..

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
BY
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' * PAGE 4?? 9??

A razane murya na rawa ta ce "Akwai abun da na faWa ne daya Sata maka rai Yaya?"

Da rarrafe ya ?arasa gurin ta, ya ri?a hannayen ta hawayen da suka cika idonsa suka fara zuba, a raunane ya ce "Don Allah ki ?ara maimaita cewa kina so na, ina son jin kalmar daga bakin ki don Allah."

Shuru ta yi kamar ba za ta yi magana ba, ita ma hawayen ke son zubo ma ta saboda tsoron kar ya gano gaskiyar abun da take Soyewa, hakan ya sa cikin dakewar zuciya da ?arfin hali ta ce "Ina son ka, ina son ka, ina son ka mijina."

Ba wani dogon shiri ko tunanin komai da sauri ya rungume ta yana ta faWar "Allah na gode maka wace nake matu?ar so, yau ita ma ta fur ta man kalmar so, na gode maka Allah da ka nuna man wannan ranar."

"Kin san mene ne ?anwata? tabbas na sha jin kina faWar cewa kina so na, amma a zahirin gaskiya ban taSa yarda ba irin yau, saboda na ji wannan kalmar har cikin zuciyata, kuma zuciyata na sanar da ni cewa na yarda dake gaskiya kike faWaman" cikin farin ciki yake duk wannan maganar, hawayen sa na cigaba da zuba.

Cikin zuciyarta take cewa "Ina ma ace da gaske duk abun da na faWa gaskiya ne, ni ma zan so hakan saboda na tsani wannan ?arya a rayuwata" hawaye ne keta faman zubar ma ta.

Sun jima a haka yana rungume da ita kafin daga bi sani ya fara sauya salon rungumar daya yi ma ta, sai faman sha fa ta yake ta tako ina, a ransa bai so ya kulata ba, ya so ya ?ara bata wata damar su ?ara sha?uwa, amma kuma yana rungumar ta ?amshin turarukan jikinta ya da ki hancinsa tuni tunaninsa ya sauya.

Ganin yadda yake ma ta, ya yi matu?ar Waga hankalin ta, gaban ta sai faman faWuwa yake nan take jikinta ya Wauki rawa, tsoro ?arara ya bayyana a gurin ta, amma haka ta dake saboda tabbas idan har da gaske tana son daidai ta komai to lalle dole ta jure wannan yana yin.

Shi ma ya lura da yadda take a razane, sai dai ya san dole hakan za ta faru saboda wannan sabon yana yi ne, da bata saba da shi ba, amma ganin bata yi wani yun?urin kwatar kanta ba hakan ya tabbatar ma sa cewa ta amince da ?udurin sa, ya ?ara rungume ta a jikinsa sosai, duk ya gama fita hayyaci sa kamar an ce wani zai zo ya Wauke ma sa ita.

NI KUMA ( *?AR GATAN MAMA*) GANIN HAKA NA HA?A NAWA INA WA, NA BARO MASU GIDAN SU DA SAURI.....

?arfe 3:am Salim ya farka daga bacci a firgice yana kiran sunan Sufayya haka ya fito yana shirin fita yabar gidan kana ganin sa kaga wanda baya cikin hayyacin sa cikin sauri har ya bige mahaifiyar sa ba tare daya lura ba.

Ita ma haka kawai ta ji baccin ya gagare ta, hakan ya sa take a farke daidai wannan lokacin, muryar Salim da ta jiyo da ?arfi ya sa, da sauri ta fito ta hango shi cikin wannan yana yin, ba shiri ta ri?e shi ta ce "Kai Salim lafiya kuwa ina za ka je haka cikin dare kuma a firgice haka?"

Cikin yana yi na rashin sanin a wane hali yake kuma da rashin sanin me yake faWa kai tsaye ya ce "Gurin Sufayya zan je Momy na ji tana kiran sunana cikin halin neman taimako, wallahi tabbas ba lafiya ba, tana cikin matsala akwai abun da yake faruwa da ita na ji hakan a jikina, Momy don Allah ki bar ni, na tafi na duba ta."

Wannan hayani yar ce ta fito da Dady Nura, kuma duk ya ji komai muryar sa suka jiya yana cewa "Ba inda za ka je Wana, karka manta ita fa matar aure ce yanzu, koma me ke damun ta mijinta zai kula da ita."

"Shin wai ma mene ne naka a ciki na sanya ta a ranka har ka ji cewa bata da lafiya akwai abun da ke damun ta? bayan sanin kanka ne tana tare da mijinta kuma ina da tabbacin zai kula da ita sosai saboda shi ma yana son ta."

Cikin rashin natsuwa "Dady ka san wacece ita fa a rayuwata ina matu?ar son ta, ba zan iya dai na son ta ba, kuma idan har wani abun ya sameta ba zan taSa jurewa ba, sannan ni ma tawa rayuwar na cikin hatsari, don komai zai iya faruwa da ni."

A take Dady ya Waga ma sa hannu, "Kana cikin hayyacin ka kuwa Salim, matar aure kake wannan tunanin a kanta, ashe dama sadaukarwar da ka yi bata gaskiya ba ce? karka manta ita fa matar Wan uwanka ne kuma aminin ka, sannan tun farko sai da muka ce ba za ka iya ba, kace za ka iya jurewa, yanzu kuma shi ne za ka zo kana wannan zancen, gaskiya sam ban ji daWi ba, ka ba ni kun ya Salim."

Cikin hanzari ya faWa jikin Dady yana wani irin kuka mai tsuma zuciya "Ka yi ha?uri Dady don na yi sadaukarwa ba shi ke nuna zan iya cire son ta a raina ba, karka manta ba ni na sanya wa kaina son ta ba, Allah ne ya jarabceni don haka ba zan iya cire saba, kuma Dady son da nake yi ma ta ne, ya sanya duk abun da ya same ta marar daWi ko akasin haka zan sani, tabbas za ku ce na faWa maku wannan" cikin kuka sosai yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login