Showing 105001 words to 108000 words out of 123822 words

Chapter 36 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3433

nan kici abinci, amma ga duk'kan alama bata ma jin su baccin ta kawai take.

Kaka ta ce "Wai Sufiyan meke damun yarinyar nan haka ni dai ban san ta da lalaci ba, amma tun da muka zo na lura bata da wani aiki sai bacci ga rashin cin abincin, duk ta yi rama da fari sosai sai kace mai sha fa mai?"

"Wallahi Kaka ban sani ba kuma ta?i barin na duba ta" Kaka ta kalli Yayunta ta ce "Kai kuzo nan ku Wauko kayan ku na aiki kuduba man ita, yau nake son sanin abun da ke damun ta."

Salim ya ce "Akwai abun da nake tunani bari na duba idan ba shi ba ne sai abin cika muga mene ne matsalar" hannunta ya ri?e ya matsa jijiyar da ?arfi sannan ya saki yana murmushi, kallon Sufiyan ya yi ya ce "?an uwa zo ka matsa ?asan marar ta da ?ar fi."

Kamar ba zai yi abun da aka sanya shi ba sai kuma ya daure ya ?ara matsawa gurin ta, baya son ya ta da, ta daga baccin shi ya sa, da ?yar ya matsa gurin da ?arfi, ai kuwa ba shiri ta saki wata irin ?ara sannan ta koma baccin ta.

Da sauri Salim ya mi?e tsaye ya kalli Samir ya ce "Kai Malam mun ku sa zama uncle Wan uwa kuma Papa."

Da sauri suka yo kan shi suna faWin "Wai don Allah da gaske kake?"

Ya ce "Ku Wauki jininta ku gwada don ku ?ara tabbatar wa idan ba ku yarda ba" cikin farin ciki suka rungume juna suna faWin "Mun yarda doctor Mata" su ma iyayensu farin ciki sosai suke tare da yi wa Allah godiya.

Assalim da baya ga ni bai magantu ba ya ce "Wai Papa mene ne kuke ta farin ciki haka?" Samir ya Waga shi sama yana juyawa da shi "Yarona kun ku sa girma Mami za ta haifa maku wata ?anwar."

Su ma haka suka rin?a farin ciki sosai saboda duk aboka nan su, na makaranta suna da ?annai Amma ban da su, a haka har suka yi bacci aka mayar da su Wakin su.

Sufayya dai sai da ta yi bacci mai isar ta sannan ta farka, ganin duk suna kallon ta suna murmushi sai da ta gama kallon kowa sannan ta ce "Meya faru kuma ku ke kallo na haka, ba dai faWan cin abinci za ku yi man ba daga ta shi na?"

Sufiyan ya ce "Ko Waya amma ina son na sani shin wannan karon ma kin san komai kika yi shuru ba ki sanar da mu ba?"

Ganin yadda take kallon kowa da rashin fahimta, shi ya sa ya ce "Kar ki ce man ba ki gane me nake nufi ba? to ina nufin wannan karon ma kin san zan zamo uba amma ba ki yi ?o?arin sanar da mu ba?"

Ba shiri ta mi?e zaune a razane ta ce "Me kake nufi, ba dai kana son kace man akwai wani abun a jikina ba, kai ina hakan ba zai yuyuba in sha Allah na gama haihuwa har aba da, shin wama ya faWa maka wannan maganar? ni da nake da jikina ban sani ba, to wallahi idan ma da gaske ne sai ya zube don ba zan sake haihuwa ba, na ma gama magana."

Fizgota da ?arfi ya yi ta matso ku sa da shi sosai "Sanar da ni me kalaman ki ke nufi ba ki son ki sake haihuwa hakan na nufin ba ki son na zama uba ke nan? Wan dakata ma kar dai ace tsayin lokacin nan da ba ki sake haihuwa ba kina sane ma'ana tsari kika yi Koh?"

Cikin farin ciki ta kalle shi ta ce "Lah Yaya wallahi ka kawo shawara mai kyau me ya sa tun farko tunanina bai kai can ba? ka ga dana yi planning da duk hakan ba ta faruba."

Cikin tsawa da ?arfi Sufiyan ya ce "Wai haihuwar ce bakya so ko kuwa dai ni ne, ba ki so?"
Ido a rufe ta ce "Duk yadda tunanin ka ya baka hakan ne."

Kawai ya saki hannunta da ya ri?e ya rin?a ja baya kamar wanda baya cikin hayyacin sa.

Momy Aisha ta Waga ta sama ta mi?e tsaye ta wanka ma ta mari "Kina cikin hayyacin ki kuwa, kin san wa kike faWawa waWan nan kalaman? buWe idonki ki ga ni mijin ki ne fa."

Rungume Momy ta yi tana faWin "Wallahi bana cikin natsuwata amma ba rashin kunya nake yi ma sa ba, Momy bana son na ?ara haihuwa ina jin tsoro sosai don Allah ku fahimce ni" kuka take sosai da gudu ta wuce Waki ta rufe ?ofar da ?arfi kamar wani ya biyo ta.

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
*PAGE* 57

Sai bayan la'asar sannan ta fito lokacin duk suna ta ?o?arin cin abinci amma Sufiyan ba shi da wannan alamar, ta yana son ya ci wani abu.

Tana tafe kamar wata munafuka cikin sanWa, Dady Nura ne ya hango ta ya ce "?ata zo nan, me kike so, kin ci abinci kuwa?"

"Ah ah Dady ban ci komai ba, amma nafi son fruit a kan abincin."

"Shi ke nan zo nan ku sa, da ni kici abincin ko ka Wan ne sannan na yarda ki sha fruit, tun da amaryar tawa da son fruit ta zo."

Murmushi ta yi, ta sunkuyar da kanta ?asa "Don Allah ku gafarceni na san ban kyauta ba Wazu, Allah na razana ne shi ya sa."

Dady Ahmad ya ce "Me ye abun razana tun da ba cikin haramun ba ne a jikin ki, kuma duk abun da kika ga Allah ya bawa bawon sa, to ya san zai iya ne."
"Irin wannan damar da kika samu mutane da dama na neman ta daga ciki har da mu iyayenki, mun yi lokacin da muke son muga ana ta haihuwa amma Allah bai nufi hakan ba har ya kai mun ha?ura, tun da muna da ku a raye fatan Allah ya ?ara sanya maku albarka.

"Amma ?ata ya dace ki san kalar maganar da za ki rin?a faWa idan kina cikin fushi, ko kuma ki koma yadda kike ada, idan ranki ya Saci ba ki cewa uffan har sai kin huce, kin san fa mafi yawancin maganar ki tana zama gaskiya Koh? to don haka ki kiya ye, yanzu ta shi ki bawa mijinki ha?uri don shi kika yi wa laifi."

Jiki ba kwari ta ?arasa gurin sa ta zauna, amma ta gaza magana sai faman wasa take da yatsunta, sai can ta buWa baki da ?yar cikin sunkuyar da kai ta ce "Don Allah Yaya ka daure ka yi ha?uri in sha Allah ba zan sake irin haka ba, kuma na yi maka al?awarin kulawa da abun da yake jikina fiye da yadda zan kula da kaina, zan yi iya ?o?arina na ga cewa na zama uwa tagari in sha Allah."

Cikin sauri ya rungume ta, ya ma manta cewa iyayensu da ?an uwansa na gurin, faWin yake "Na gode sosai ?anwata dama abun da nake son na ji kin furta ke nan, kuma ba fushi nake da ke ba, ni ma da laifi na, bai dace na biye maki ba, bayan na ga cewa ba ki cikin hayyacin ki" sai jin murya Jawad ya yi yana cewa "Uncle ka sake Mami haka nan ka matseta da yawa kuma kaga ta ku sa kawo mana ?anwa."

Aikuwa da sauri ya sake ta ya ja baya yana susar kai, duk mutanen gurin suka saka dariya.

********************
Yau ita ce ranar taron, tun cikin dare ake abu Waya, don su dai wannan families a duniya suna son su ji abu ya samu na yin taro, suna girmama shagali komai ?aran cin sa, saboda suna jima wa, ba su yi ba.

Taro ya yi matu?ar kyau sun yi gayyata ta ko ina ?an makarantar su sun zo sosai duk da bata fiye shiga cikin mutane ba amma su kuma suna matu?ar son ta, shi ya sa mafi yawanci sun zo har da wanda kati bai sama ba, su ma yaran ?an makarantar su da iyayensu duk sun zo, taro dai ba laifi ya ?awatar sosai.

Duk mutanen gidan sun yi wa jama'a sallama sannan sun yi masu godiya sosai na samun halartar taron, shi kam Sufiyan bakinsa har kunne a kan farin ciki duk wanda ya mi?a ma sa hannu da ni yar su yi sallama sai ka ji ya ce "To sai kun zo taron suna kuma, nan da wata biyar in sha Allah, saboda ni ma na ku sa zama uba kamar ?an uwana" abun har dariya yake ba mutane, da haka dai aka salllami kowa.

Cikin tsokana Samir ya ce "?an uwa abun ko kara babu, abun ka bari mu mu sanar da mutane shi ne da kanka kake yi?"

"A Win, ai kuma lokacin naku yaran ni ma ba ku yi man kara ba don haka ni ma yanzu bazan yi ba" haka dai aka ta Tsokanar shi, sai ku san magrub sannan ya tsaya ya Wan huta lokacin mutane duk an watse.

Hango Sufayya ya yi tana shirin shiga kitchen, ai nan take ya manta da gajiyar sa, ya je gurin ta ya ce "Ina kuma za ki je, ba dai fruit za ki sake sha ba? kin ga zauna a nan faWa man me kike so sai na je, na Wauko maki?"

"Yaya ke nan don Allah ka barni na tafi faten kuskus nake son na yi, ka ga ke nan wannan aikin mata ne."

"Waya ce aikin mata ne ka Wai, kin manta duk kin ko ya mana kalolin girki? to don haka yau ranar ta zo yanzu zan haWa maki in sha Allah."

Sauran Yayunta ma suka ce aikuwa muma za mu bada tamu gudun mawar, za mu taru mu uku mu haWa maki yanzu nan."

Dariya ta yi ta ce "Yanzu a kan Wan fatan shi ne za ku taru har ku uku sai ka ce wani aikin gayya? to kun ga bari na ?ara maku wani aikin, ku haWa man da kunun gyaWa."

Momy Saratu ta ce "Kin yi man daidai, dama ace za ki sake tuna wani abun ki ?ara saka su."

Sauran iyayen suka ce ai yanzu aka fara mu dai namu kallo ne kawai, sai kuma fatan Allah ya raba lafiya."

*********************
Lokaci na tafiya watanni sun tafi cikin Sufayya ya shiga wata tara an fara dubin haihuwa, ba yadda su Momy ba su yi ba, a kan ya bari su mayar da ita gurin su har ta haihu, amma sam ya ?i bari ya ce shida ?an uwansa sun isa in sha Allah za su bata kulawa kamar lokacin baya, dole haka suka barta tare da sharaWin suna ganin alamar haihuwa to su kira kar su yi irin wan cen karon, suka amsa da to in sha Allah.

Yau ma duk suna parlour zaune babu alamar za ta je gurin bacci, su kuma sai jira suke su ji tace tana jin bacci amma shuru har 10:30pm.

Kallon su ta yi, ta ce "Ina son na je Waya daga cikin gidajen iyayena wata?il can ya fi nan sanyi don na ji nan ya fiye zafi da yawa."

Duk'kan su zuba ma ta ido suka yi suna kallon ganin cewa duk AC Win gurin a kunne suke, Sufiyan ya ce "?anwata bari mu duba ko ba a kai su ?arshe ba ne sai mu ?ara su kai ?arshe, kin ga yanzu 10:30pm idan muka tafi za mu iya Waga masu hankali su yi tunanin ko ba lafiya ba."

Cikin tsawa da Waga murya ta ce "Ka dai ce so kake na mutu ba damuwar ka ba ce, baka da asara, ko 3:am ne ba za ka kai ni ba, su yi tunanin ba lafiyar mana dama lafiyar ce da ni? na ce maka gidan zafi kamar ana hura wuta, amma ko ajikin ka, kai dai burin ka kawai na mutu ka huta."

A sanyaye ya ce "Me ya sa, za ki faWi hakan don Allah, ta ya zan so ki mutu ki barni? ai daga ranar ni ma mutuwa zan yi wallahi."

Salim ya ce "Shi ke nan ya isa haka nan daina kukan ta shi mu bar gidan nan ni ma na ji zafin ya yi yawa kina da gaskiya, ai wannan zafin tsaf zai iya ki san kai, ta shi ma za mu fita" kallon sa ta yi ta ce "Ai kai ka san gaskiya Koh?"

"Sosai ma kuwa na san gaskiyar" ya bata amsa, haka suka bar gidan, su kuma suka biyo bayan su.

Gidan Momy Nafisa suka tsaya saboda shi ne a ku sa, Dady Nura na jin tsayuwar mota ya fara tunanin su waye yanzu cikin daren nan, yana le?awa ya ga yaran su ne, da sauri ya tada Momy ya ce "Ta shi ga yaranmu nan" ai kuwa firgigit ta mi?e ta fito, ko da suka fito har sun ?araso cikin parlorn.

Ai ko gaidasu bata yi ba, ta fara ?o?arin komawa waje da sauri tana faWin "Momy wallahi ke ma gidan ki zafi kamar gidanmu."

Samir ya ja Momy gefe ya sanar da ita dalilin zuwan su, Momy ta ce "To Samir kana ganin ba haihuwa ba ce kuwa?"

"Mu ma tunanin mu ke nan, amma yanzu dai ki yi wani abu ki tsayar da ita, idan ta Wan huta sai mu je asibiti."

Da sauri Momy ta ri?e ta tana faWin "Kin ga wata?il dan na kashe AC ne shi ya sa amma yanzu duk za'a kunna su" haka dai ta daure ta zauna.

Bayan wani Wan lokaci ta ce "Dady don Allah kira man sauran iyayena nafi son ko mutuwar zan yi na mutu a gaban duk a halina."

Da sauri Sufiyan ya ri?e hannuta ya kalli Momy ya ce "Don Allah Momy ki ce ta daina zancen mutuwar nan bana so."

Su Momy Aisha na zuwa suka ga yana yin ta, tu ni suka sanya su Dady da Yayunta su fita waje tun da sun ga alamar haihuwar ta zo gab kafin su kai asibiti da matsala.

Da ?yar Sufiyan ya yarda ?an uwansa suka fita da shi, suna fita suka jiyo ?arar ta tare da kiran sunan Allah aikuwa sai kukan jariri suka jiyo, da sauri Sufiyan ya yi yun?urin koma wa, amma su Dady suka ri?e shi.

Sun fi minty 30 sai ga Momy Saratu ta same su a Waya parlorn a razane ta faWin "Ku zo don Allah kuduba ta tun Wazu ta haihu amma bata cikin hayyacin ta, har wanka mun yi ma ta amma numfashin ta bai dawo ba, mun yi duk abun da za mu iya amma har yanzu shuru.

Ai kafin ta gama bayanin har sun fice sun tarar da ita har an gyara ta, kai tsaye Sufiyan ya Wauketa sai asibiti, nan ma an yi duk abun da za'a yi har asuba shuru ba wani sau yi.

Sufiyan ya ri?e hannunta yana faWin "Don Allah ki ta shi mana ?anwata na san duk laifi na ne, sai da kika ce kina jin tsoron haihuwa ba za ki sake haihuwa ba, amma ni kuma sarkin son ?a-?a idanuna sun rufe na?i sauraran ki har da ganin laifin ki, don Allah ki yi ha?uri ki ta shi."

Sai ?arfe 7:am san yin safiya ya sauka jikinta, sannan ta ja dogon numfashi tare da ambaton Allah, abun da ke ?ara sa tana birge mutane ke nan shi ne yawan ambaton Allah.

Da ?yar ta samu buWa idanunta, buWar bakinta tambayar ta "Momy me na haifa, ina abun da na haifa?"

Ai sai lokacin Sufiyan ya tuna bema ga abun da ta haifa ba har yanzu, kallon ?an uwansa ya yi su ma babu alamar sun san me ta haifa.

Momy Nafisa ce ta kawo ma ta yaro ta ce "Allah ya a zurta mu da ?an biyu Maza rungumar su ta yi a jikinta Waya bayan Waya sannan ta ce Allah ya yi wa rayuwar ku albarka" duk suka amsa da Ameen.
Taslim ta ce "Mime kar ki bawa uncle ?anenmu tun Wazu ba su kulamu ba mu da ?annemu, sai kuka suke suna faWin don Allah ki ta shi."
Kallon iyayensu ta yi "Momy me yaran nan suke a asibiti kuma?"
"Ba kowa a gidan duk muna nan kuma kin san ba ki son ana barin su gurin ma su aiki shi ya sa" cewar Momy Aisha.
"Ok ba damuwa Jawwad Salim ku ri?a hannun ?annenku ku fita waje muma yanzu za mu fito mu tafi gida."
?o?arin sauka daga kan gadon ta fara da sauri Sufiyan ya yi yun?urin taimaka ma ta ganin za ta faWi, da ?arfi ta fizge hannunta ta ce "Karka taSa ni" kallon sa ta yi sosai ta ce "Me ka faWa lokacin da na ce na daina haihuwa ba zan sake haihuwa ba?"

"Cewa ka yi bana son ka bana ?aunar ka bana son ka zama uba, har mutane suka ta yaka faWa, to yanzu faWa man wannan shi ne kalar jiran da kake yi wa yaran na ka? ina da tabbacin in sha Allah tun da suka zo duniya ba wanda ya runmesu daga kai har ?an uwanka, wannan ita ce taku kalar soyayyar uba a gurin ?a-?an sa ko?"

"Tun da dai ba ni da lafiya shi ke nan ku kuma ba ku da lokacin yaran ku, da mutuwa ma na yi haka za su ta so, ba tare da samun kulawar ku ba saboda kuna jimamin rashin ?ar zinari Koh?"

Rufe ma ta baki ya yi cikin sauri "Kar ki ce haka don Allah, wallahi muna matu?ar son ?a-?anmu sosai, ganin suna gurin Momy's kuma ba kuka suke yi ba, shi ya sa duk muka raja'a gurin ganin kin dawo hayyacin ki."

"Kuma ?anwata su idan mun rasa su za mu iya sa ran samun wasu in sha Allah, ke kuma idan muka rasa ki to fa tabbas sai dai mu bi ki don mun tabbatar mun rasa ki ke nan har abada."

Kallon sa take baki sake har ya gama bayanin sa ya ce "?anwata ya naga kina kallo na haka?"

"Ba dole na kalle ka ba, idan dai na fahimce ka da kyau so kake yaran nawa su mutu, tun ban ma gama fita daga jin yar haihuwar su ba, tun da kana tunanin kana da hanyar samun wasu Koh?"

Girgiza kai yake da sauri yana faWin "Ba haka ba ne wallahi ina son yaran nan sosai kuma ba zan so wani abu marar kyau ya faru da su ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login