Showing 27001 words to 30000 words out of 123822 words

Chapter 10 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3414

ku ko da baku yi man tambaya ba dama na shirya zan baku labarina kafin na tafi, amma tun da kun nema a yanzu to duk ku zauna kai da Aunty dama duk wanda ke gurin nan za ku samu duk'kan amso shin tambayoyin ku in sha ALLAH."

"Amma idan ka ji labarin za ka barni na yi rayuwata, za ka daina zancen so na?"

"Idan har dalilin ya nada ?arfi to zan yi yadda kike so in sha ALLAH."

*WAIWAYE*
~JAHAR ZAMFARA~

Jahar zamfara jaha ce mai kwanciyar hankali ga kuma daWin zama mutanen jahar na son karrama ba?i daga cikin jahar akwai wani garin mai suna TALATAR MAFARA shi ma wannan garin akwai tarin natsuwa sosai a cikin sa, to ita ma a cikin wannan garin take, kafin daga bi sa ni jahar ta hargitse Sata gari suka shiga jahar amma duk da hakan gidan su, na cikin farin cikin sa da kwanciyar hankali kamar ko da yaushe.

Talatar Mafara nan ne garin su, sunan ta Rahma kamar yadda ku ka sani mahaifinta sunan sa Malam Musa malami ne na addini sosai kowa ya san shi, mahaifiyarta kuma sunan ta Hassana amma suna kiran ta da Mama, ta nada ?annai biyu maza Idris da Kamal, iyayen na matu?ar son su, su na kula da su sosai gidan su gida ne na farin ciki da girma ma juna.

Tun ta na ?arama mahaifin ta ke koyar da ita ilimin addini tun daga Qur'an har littafai kuma mafi ya wan karatun duk har da ce, ma'ana a kai yake yi mata kuma cikin ikon Allah da ya yi mata karatun take ri?ewa haka ma ?an uwanta suna ?o?ari ba laifi.

Ta taso ta na mai matu?ar son kiwo sosai hakan ya sa Baba ya ware mata wani guri a cikin gidansa, ya zuba mata kaji da tantabaru kuma sai Allah ya sanya masu albarka ko da yaushe cikin ?aruwa suke, ?ar baiwa shi ne sunan da iyayenta suke kiran ta da shi musamman Baban ta.

Ta na son karatun boko sosai duk'da Baba ba shi da ra'ayi amma haka ya daure ya sanya ta ita da ?anen ta Idris, a lokacin Kamal yaro ne bai isa shi ga ba, a gida suke barin sa idan sun dawo kuma sai suyi sallah suci abinci sannan su fara karatun addini wannan shi ne kawai aikin su ko wacce rana.

Akwai wani yaron ma?waftan su mai suna Sa'idu yana shiga gidan su sosai ya mai da gidan kamar na su ko yaushe ya shigo zai kirata da matar sa ita kuma a lokacin ba ta san ma'anar hakan ba.

Wata rana sun ta so daga makaranta kan hanyar su suka ga an buWe wata sentar ana koyar da abubuwa da yawa,
Suna zuwa gida ta tasa Mama gaba akan ta kaita ta koya Baba na jin maganar ya ce.
"To yanzu don Allah wanne za ki yi karatun ko kuwa Win ki."
"Baba ni dai ko wanne ina so kuma zanyi ?o?ari in sha Allah."

Baba baya son ya ga cewa ta rasa komai a rayuwa shi ya sa matu?ar yana da halin abu idan ta ce tana so yake yi mata yau ma hakan ce ta faru.
Baba ya ce "shi ke nan zan kaiki."

Ta yi murna sosai da farin ciki.
Kwana biyu da yin maganar Baba ya kaita ya biya komai sannan ta fara koyan Winki, idan sun ta so boko ta tafi can shi kuma na addini sai dare take.

Ta na zuwa gurin sai kuma ta ji ba iya Winkin take son koya ba aikuwa da ta faki idanun mai koyar da su sai kawai ta gudu ita ce bata nan bata nan kuma cikin ikon Allah duk gurin da ta je sai ta iya wani abun,
Har dai mai koyar da su, ya ga ji ya kai ?arar ta gurin Baba ya ce,
"In dai ?o?ari ta nada shi amma bata jin magana bata zama guri Waya."

Baba ya ce "?ata wannan ba halin ki ba ne rashin natsuwa me ya sa yanzu kike son koyon hakan."

"Ni fa Baba ina so kawai na ko yi duk abubuwan da ake a gurin shi ya sa nake zuwa, kuma Baba ba Winki ka ce suko ya man ba?
Baba ya ce "A mana" sai ta ce To ba kowa ne kala suke ko ya man ba na mata suke ko ya man bada na maza ba."
Baba ya yi dariya ya ce "Ke kuma me ye haWin ki da Winkin maza."

Ita kuma ta ce "Baba don Allah ina so ni dai."
"Wai ke har kai nawa ne dake ga karatu ga kuma duk waWan nan abubuwan da kike son yi?"
Ganin ranta na son Saci shi ya sa Baba ya ce "To shi ke nan yanzu kai bawon Allah kana ganin za ta iya kuwa?"

Mutumen ya ce "Gaskiya ban sani ba sai dai mu gwada mu ga ni malam."
Baba ya ce "Zan ?ara biyan kuWi kina ga ni idan kika bari na yi hasara ba zan sake baki wata damar ba."
Rahma ta ce "Na yarda Baba kuma in sha Allah ba zan baka kunya ba."

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' *PAGE* 2?? 0??

A kwana a ta shi asarar mai rai yau ita ce ranar yaye Waliban farko Kuma Rahma na daga cikin su, izuwa yanzu ta iya abubuwa sosai ba laifi saboda nacin ta a kai,
Hakan ya sa ta samu kyautuka sosai daga ciki har da keken Winki lokacin tana junior secondary school class 3.

Tun daga lokacin ita ke yi wa mutanen gidan su Winki amma Baba ya ce, ba za ta yi, na kuWi ba saboda zai iya Waukar mata hankali a kan karatu.

Wata rana suna firan su kamar yadda su ka saba,
Rahma ta ce "Baba ka san mene ne? na fa za?u na gama wannan makarantar na tafi University domin na ci ka burina na zama Doctor, ka san da hakan ko Baba?" ta ?arasa maganar tana duban Baba.
Baba ya ce "Amma a Wakin mijinki ko ?ata?"
"Ban fahimce ka Baba ka san fa wannan shi ne burina me ya sa, za ka faWi hakan kuma?"

"Ai idan har kinga kin wuce wata makarantar bayan secondary to ki tabbatar a Wakin auren ki ne, so kike duk gurin da na wuce arin?a ga malamin da yabar ?arsa ba aure saboda karatun boko, ke baki san ana yi wa ?an matan babbar makaranta kallon ?an iska ba, ke ma haka kike so a rin?a kallon ki ke nan?"

Kuka ta fara sosai sanin halin Babanta idan ya kafe akan magana Waya, amma bai hana ta yi ma sa magiya ba tana faWin
"Baba don Allah ka yi ha?uri karka biyewa zancen mutane, kuma ai kai kasan halina to me zai sa ka Wauki jita jitar mutane?"

Tsawa ya daka mata wacce bata taSa jiba ya ce, "Tun da kike kin taSa tambaya ta wani abun kin rasa?"

Girgija kai ta yi alamar ah ah.
"To tun da kin ji na ce ah ah ta tabbata kin ji na faWamaki, kuma ma har mun yi magana da Baban Sa'idu za su kawo kayan baiko ki na gama secondary shi ma lokacin ya gama za mu haWa auren ku."

Duk inda hankalin Rahma yake sai da ya ta shi ta ce "Baba Sa'idu kuma?"
Yaushe ya dawo ma daga lagos kuma yau she yabar shaye shaye? kuma wallahi Baba bamu taSa zancen soyayya tsakani na da shi ba."

"To yanzu dai magana ta ?are kuma zancen soyayya shi dai yana son ki, shi da kansa ya sanar wa mahaifinsa shi kuma ya zo ya sanar da ni, dan haka kema ya dace ki fara son sa daga yanzu."

Mama ta ce, "Amma Malam baka ganin ya dace abar ta ta zaSi wanda take so?"

"Ya kalli ta ya ce "Ban isa na saki abu ba Rahma kuma ban isa na zaSa maki miji ba?"

Daga jin yadda ya faWi sunan ta, yau babu ?ar baiwa, da kuma yadda ya yi maganar, hakan ya sa ta san zancen ya girmama da sauri ta ce "Ka isa Baba kuma in sha Allah zan yi duk abun da kake so, na daina zancen karatun kuma zan so Sa'idu in sha Allah."
Baba ya ce "Madallah ta shi ki tafi Allah ya yi maki albarka."

Ta amsa da ameen.

A ranar Sa'idu ya shiga gidan wai ya je zance harda wani jin kunya abun mamaki ma ya bata,
"Ba ina ki ranki matata ba amma ba ki amsa wa, to yanzu kins an dalili ko?"
Ita ce maganar da ta fito daga bakinsa ko sallama babu.
"Yawwa kuma don Allah ki saki jikin ki, da ni wallahi na yi maki al?awarin duk abun da ba ki so zan daina don Allah ki so ni kin ji?"

Rahma ta ce "Na ji amma zan aureka ne kawai idan kai Win ?addarata ce sannan kuma dabin umurnin mahaifina, zancen kuma za ka bar duk abun da kake yi saboda ni, to bana son ka daina, nafi son ka daina saboda tsoron Allah."

To shi ke nan zan yi duka biyun zan yi saboda Allah sannan kuma da ke."
Bayan wani Wan dogon lokaci,
watarana Baba ya tara Mama da duka ?a_?anta ya sanar da su cewa shi fa aure zai ?ara kuma ba kowa bace face Hajiya Hajara kuma za ta zo da ?arta Waya tak Asiya.
Ba Mama ba har yaran sai da hankalin su ya yi matu?ar ta shi.

Hajiya Hajara mace ce marar mutunci mafi yawan mutane duk sun santa ta yi aure har shidda wannan auren shi ne na bakwai kuma duk gidan da ta shiga sai ta tarwatsa farin cikin gidan sannan ta fice, tana da ?a Waya da ta haifa a auren ta na biyu, ta auri wani Alhaji yana da dukiya sosai ba laifi sai dai bai taSa haihuwa ba ba shi da wani burin daya wuce ya ga jinin sa.

Tun da ta samu labarin halin da yake ciki ta Wauki alwashin sai ta shi ga gidansa kuma sai ta haifa ma sa magaji ta ko wace hanya.
Sai ga shi yana auren ta, ba jimawa ta samu haihuwar Asiya, akan haihuwar yarinyar sai da ta saka Alhaji, ya kori duka matansa kuma ita ma daga bi sani ta ce ba zata zauna ba kuma da ?arta za ta je babu kalar magiyar da bai yi ba amma ina haka ta fice tabar gidan, duk gidan da ta shiga da manufar shigar sa.

Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce,
"Malam ba zan hanaka yin aure ba tun da Allah ne ya baku wannan damar amma don Allah ka sauya matar aure kai fa malami ne kasan cewa wajibi ne kazaSawa ?a ?anka uwa ta gari, kuma kai ma ka san wacece Hajiya Hajara don Allah Malam karka tarwatsa gidanka da kanka."

Duk wannan dogon sharhin da Mama ke yi ko ajikin Baba tana gamawa ya ce "To idan kin gama ki kwashe yaranki ku wuce ba shawara na zaunar daku kubani ba, na sanar daku ne saboda na fitar da hak?in ku sannan kuma gobe jumu'a za'a Waura kuma a goben za ta tare in sha Allah."

Mama ta ce "Shi ke nan Allah ya sanya alkhairi."
A sanyaye suka bar gurin Rahma ta ce "Mama me ya sa Baba duk ya sauya yanzu baya jin maganar mu?"

"Allah shi ya barwa kansa sani mu dai namu addu'a ne kawai."

An Waura aure Amarya ta tare amma cikin ?an ?anin lokaci komai ya sauya a gidan, yanzu Baba baya sanin baccin iyalin na sa, ko tashin su sannan komai ya koma hannun Amarya abinci ma sai ta ga dama ake ba su, duk'kanin su, suna iya jurewa amma banda kamal saboda shi yaro ne bai san babu ba sun sha sanar da Baba amma sai ya ce, rashin godiyar Allah ne kawai, wannan baiwar Allah ta na ?o?ari idan har ba su gode ma ta ba ai bai dace suzage ta ba.

?arta kuma sai abun da, ta ga dama ta ke yi a gidan ga masifar yawon tsiya ga kuma shigar banza .

Ga shi dama Baba baya barin sana'a a gidan sa saboda ya gama yarda cewa zai iya Waukar nauyin gidan sa hakan ya sa Mama bata sai da komai.

Sa'idu ya daina shigowa sosai gidan koma ya shiga to baya sakar ma ta fuska sosai wata?il ko yana tunanin za su Waura mai wani nauyi ne, mutumen da ko wata babbar sana'a ba ya yi abinci ma sau tari a gidan ya ke ci.

Rahma ta fara tunanin nai ma masu mafita amma kuma ta ya? Baba ya hata Winkin kuWi, sai kawai wani tunani yazo ma ta ai ta iya kitso da kunshi, sai kawai ta fara kuma ta fara asa'a mutane sai zuwa suke,
Da ta dawo daga makaranta aikinta kenan shi kuma Idris ya je yi masu cefane sai ya zama basa rasa abinci har sutura lokacin kuma tana ajin ?arshe a secondary sun ku sa yin candy.

A she Al'amarin ya yi wa Hajiya Hajara ba daWi saboda ita a wula?ance take son ganin su, sai kawai ta sanar da Baba ta ce yanzu duk anguwar cewa ake yi gidan Malan ya zama gidan tara mata.

Baba ya ce da Rahma in dai ya isa da ita ba za ta sake kitso da kunshi ba kuma idan ta sake ko bayan idon sa bai yafe ba Allah ya isa, cikin raunin murya Rahma ta ce, ya yi ha?uri in sha Allah ta daina.

Rayuwar su ta koma kamar ta baya Wan abun da suka tara shi ma ya ?are Baba kuma ya zama kamar photo duk abun da Hajiya Hajara ta faWa ta zauna ko bincike ba zai yi ba.

Wata rana Rahma taje gurin Baba ta sanar da shi zancen kuWin makaranta za su fara jarabawar ?arshe,
Har ya Wauko kuWin ke nan zai bata Amarya ta zo da sauri ta hana shi ta ce ?arya take ba wasu kuWi da akace su kawo,

Rahma ta ce "Wallahi Baba da gaske na ke."
Sai ya ce "Ke nan ?arya ita Hajiya take ko? Ta shi ki bani guri ba zan ba yarba."

Ta je Waki ita da Mama duk sun yi shiru sun rasa mafita ga rashin abinci gana matsalar kuWin makaranta, Sa'idu ya shigo gidan ya ce yana ganki kamar wacce akayi wa mutuwa, nan ta sanar da shi matsalar su,
Ya ce "Kuma har nawa ne kuWin?"
kamar abun Allah haka ya yi tambayar.

Ta ce 60k, sai cewa ya yi "Kai ashe da yawa haka gaskiya dole Baba ya hana ki kuWin sa, to kibar zancen karatun kawai tun da ba dole ba ne, dama karatun ?a macce ni banga anfanin sa ba, ni kam kinga tafiya ta."

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' *PAGE* 2?? 1??

Haka ya tafi ya barta nan zaune kamar an dasa ta.

Mama ce ta fito ta dafa ta, ta ce "Kar ki fiye tunani Rahma, komai na Allah ne, da man can na san ba ku dace ba saboda ba mutum ba ne wanda zai iya kare maki mutuncin ki ko Kuma ya yi ?o?arin fitar dake cikin matsala idan kin shiga, amma ke kin dage sai kin yi wa Baban ki biyayya."

Rahma ta ce "Kar ki damu Mama in sha ALLAH biyayyata ba za ta zama a banza ba, sannan kuma Mama na gama yanke shawarar sai da wasu daga cikin kaji na sai mu samu abinci kuma na biya makaranta."

"Haba Rahma duk yadda kike son kajin nan kike son kiga sun taru sun yi yawa shi ne za ki siyar da su kuma?"

"Mama duk yadda na kai ga son su, ba kamar ku ba, da kuma karatu na, in sha Allah wata rana duk burina zai cika kar ki samu damuwa."

"Shi ke nan Allah ya sa hakan shi yafi alkhari" cewar Mama.

Haka suka tattara ka ji da tantabaru masu yawa ita da ?anenta Idris su ka siyar, sun kuwa yi kuWi ba laifi dan ta samu kuWin kai wa makaranta sannan har sun samu na siyan kayan abinci kaWan ba laifi ranar dai sun yi farin ciki.

Kwana biyu da faruwar hakan Amarya ta sanar da Baba cewa yanzu kullun sai Rahma ta Wibi kaji ta siyar.

Baba ya ce "Yanzu Rahma har kin yi girman da za ki rin?a yanke shawara ba tare da kin sanar da ni ba? to ki sani yanzu kaji da duk abun da yake gurin ya ta shi daga naki sannan na mayar da kulawar su hannun Hajiya."

Da Wa yanzu kam dubara ta ?are masu mafita ta buwaya tunani duk ya toshe.

Haka ta rin?a yin yadda ta so da kajin kullun cikin yanka su take idan Baba ya yi magana sai ta ce rashin lafiya ce ta kama su ita kuma tana gudun su mutu ayi asarar su.

Yau sun ta shi kamal sai faman kukan yunwa yake shi ma Idris ?arfin sa ya fara ?arewa kwana biyu da suka wuce har tallar ruwa ya fara amma Baba ya ce ba zai ja ma shi zagi ba agari.

Ganin zaman ba zai yiba ga shi ita ma Mamar kamar dauriya kawai take, haka Rahma ta je gurin Amarya ta ce "Na ro?e ki, ki taimaka ko da ?annaina ne ki basu abinci wallahi yunwa suke ji sosai."

Ta yi wata irin shu'umar dariya ta ce,
"Wuya ba daWi yau ?ar baiwa ce ke ro?on abinci, to shi ke nan na ji zan ba ku abinci amma da sharaWi ba zan bakiba sai kin yi man wankin kayana da na Asiya idan kin gama sai na baki."

Da sauri Rahma ta yarda,haka ta kwaso kayan kamar wata jaka.
Rahma ta ce "Amma kayan sunyi yawa fa."

"Ba abinci kike so ba ke nan" cewar Asiya tana maganar tare da jefa mata wasu kayan.

Tun 1:pm har 8pm sannan ta gama kwano Waya na abinci ta tura mata,

Rahma ta ce "Don Allah ki ?ara masu wannan ba zai ishe su ba."
"Idan baki son wannan ki zubar ki Waga man daga ?ofar Waki."

Haka ta kai masu su kaci badan sun ?oshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login