Showing 6001 words to 9000 words out of 123822 words

Chapter 3 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3429

na yi mata tambayar sannan naga rashin dacewar hakan."
Daga zuwana na fara neman sanin wani abun da ya shafeta in sha ALLAH hakan bazai sake faruwa ba."

Rahma ce, ta shigo cikin Wan sauri sauri ta yi sallama sannan ta ce "Don ALLAH ku yi ha?uri yau na makara."

Zahra wace yanzu take shigowa parlorn ta ce "Bawani can matsiyaciya illar talaka kenan bai iya cin arziki ba wallahi."
"Yanzu tun da kinga ansakar maki fuska dole ki rin?a fitowa a makare."
Koda yake bama wannan ba ne matsalar, ba'asaba shan?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? AC ba shi ya sa, ai dole a makara matsiya ciya kawai."

Sai faman kumfar baki take amma Rahma ko gurin da take bata kalla ba aikin ta kawai take.

Ganin bawan da yakula ta hakan ya sa, ta har zu?a ta nufi har gurin da Rahma take jera kayan breakfas.
Taci gaba da cewa sun iya faWar cewa za su iya aiki amma a banza malama idan ba za ki iyaba ki sanar sai a can ja wata, matsiyanta suna da yawa, banza kawai."

Sufiyan ya gaji dajin kalamanta mi?ewa ya yi, ya Waga hannu da niyar marin ta.

Cikin sauri Rahma tari?e hannunsa tare da girgiza masa kai alamar kar ya yi haka.

Cikin yanayin ta narashin son hayaniya ta ce, "Da ni take bada kai ba, don haka kabar hukuncin aguna."
"Bugu da ?ari kuma kai Win namiji ne bazai, yi maka kyau ba ace kana dukan mace."
"Sannan ka san hausawa na cewa idan kare na haf shi ba'a tanka masa" ?ara jinjina hannunsa ta yi wanda har yanzu take ri?e da shi sannan ta ce "don haka ka kula da wannan ba girman ka bane kaji koh?"

Tun da ta ri?e hannunsa yake kallonta,
kallon sani ya kema fuskar ta amma har yanzu ya gaza fahimtar ina ya san wannan fuskar, sannan abun da yafi ba shi mamaki shi ne idan ta yi magana har cikin zuciyar sa yake ji.
Sai da ya nisa sannan ya ce "Shi ke nan na fahimta kuma maganar ki gaskiya ce na gode da kika tunatar da ni.
Komawa ya yi, ya zauna ita kuma ta cigaba da aikinta.

Cikin Sacin rai Zahra ta nufi gurin Rahma tana ?o?arin kaimata duka tare da faWin "Wa ki ke kira da Kare?"
Kaucewa Rahma ta yi, da sauri Zahra ta faWi ?asa sai ji kake tibbb kamar kayan wanki.
Murmushi irin wanda koda yaushe shi ne a kan fuskar Rahma shi ta yi sannan ta du?a ku sa, da Zahra gurinda ta faWi ta ce
"Zahra kenan ina bawa mutum girma amma fa sai ya girmama kansa tukunna, kwana Wayan nan duk kin sauya man to bari kiji ni Win ba ni da sau?i kamar yadda kike tunani."
"Da ace Momy'n ce, ta sanar da ni abubuwan da kika sanar da ni yanzu dako minty biyar bana tunanin zan ?ara a gidan nan saboda zamanta nake."
Idan kin yi zaton cewa ni Win filawa ce za ki murza ni yadda ki ke so, to kin yi kuskure domin kuwa ni Win WUTA ce, idan kika yi ganganci ?ona ki zan yi."
?an dafa kafaWar ta Rahma ta yi sannan ta ce "Idan kika yi ha?uri kamar yau ne za ki nemi Rahma ki rasa saboda ni Win ba mai zama bace guri Waya har in Wauki lokaci, don haka ki yi farin ciki dan kar ki samu hawan jini ki zama ko oho da Rahma, kinji koh?"
Ta faWi hakan tare da mi?ewa ta shiga jera sauran kayan.

"Momy ta ce maa sha ALLAH abun da nake so kenan, Rahma ta fara mai dawa Zahra magana shi ya sa tun Wazu ban yi magana ba."
Murmushi kawai Sufiyan ya yi saboda shi ma, ya ji daWi sosai.

Mi?ewa Zahra ta yi tsaye ta har'zu?a sosai, "Duk wannan rainin ku kuka jaman shi agun ?ar aiki, wai har da kai Yaya komai sai kuce Rahma Rahma kamar ba ni bace wace za ka aura."

Nan take ta ji wani irin wawan mari na yatsa biyar a kan fuskar ta ya ce.
"Waye zai aureki Win?"
To bari ki ji ko, a mafarki kika sake ganina a matsayin mijinki sai na Salla ki wallahi."

WATA ?ADDARA

PAGE 5??

Zahra cikin har gagi ta ce,
"Momy yanzu kina gani a kan idonki ya mareni kuma bazakice komai ba saboda bake bace kika haifan ba koh?"
"Amma ba komai Kuma kasani wallahi sai na aure ka Kuma sai ka zauna da ni a matsayin matar ka."

Sufiyan baya Waukar rainin hankali nan take ya sake yun ?urin kai mata duka, da sauri momy ta dakatar da shi ta hanyar Waga masa hannu.

Ransa a Sace ya ce "Momy ki duba fa rainin har akan ki taya kike tunanin zan iya tsayawa ina daukar wannan rashin tarbiyar nata?"

Momy'n ta ce "Idan ita ban isa da'itaba ban haife ta ba kai kuma fa, za ka biye mata ne?"

"Ba haka ba ne Momy ki yi ha?uri don ALLAH."
Zahra barin gurin ta yi da sauri tana ta kuka kamar wace uwarta ta mutu.

Shi kuma gurin Momy ya koma ya ce "Ta so mu je Momy mu yi breakfast saboda ina son idan mun gama mu yi magana dake mai mahimmanci."

Bayan sun gama su ka koma cikin parlon dukansu shi da Momy Wan kinshiWa ta yi akan kujera.

"To ina jinka cewar momy'n."
"Hmmm Momy kenan dama dai maganar da kuke yiman ne duk lokacin da nazo shi ne naga wannan karon baki taran da zancen ba?"
Cikin mamaki momy'n ta ce "Wace magana ba Sufiyan?"

?ata fuska ya yi sannan ya ce "Haba dai ta ya, za ki manta bayan wannan maganar ita ce koda yaushe a baku nan ku, ke da sauran iyayena."
"Ba ku gajiya da yi mana zancen ni da 'yan uwana?"

Cikin rashin fahimta Momy ke kallon sa. Ita dai iya sanin ta magana Waya ce suke yi wa yaran su koda yaushe ita ce, ta aure.
To me ya sa yau da kansa yake Wauko maganar bayan iya sanin ta basa son zancen.

?an nisawa ta yi, ta ce "Ni dai zancen aure kawai na san muna yi maku kuma ganin baku so shi ya sa muka dai na."
Yanzu kuma ga matsalar da 'yan uwan ka ke ci ki duk shi ya sa wannan karon bance da kai komai ba."

Da sauri ya ce "Yawwa Momy anzo gurin wannan maganar na ke nufi."
Nan take Momy ta mi?e zaune sosai ta ce "To ina jinka me ya faru kuma?"

Susar kansa ya fara kamar marar gaskia ya fara "umm amm dama umm."
Cikin za?uwa Momy ta ce "Wai za ka natsu ka yi man magana ko kuwa saika gama susar kan naka tukunna?"

"A zanyi magana, dama fa inaga nafa samu wace nake so kuma yanzu babu kowa akusa da ni sai ke shi ya sa nake son ki ba ni shawara tun da iyayena basa nan kuma 'yan uwana suma basa ku sa."

Razana Momy ta yi, ta rin?a taSa wuyansa ko zata ji zazzaSi amma ga duk'kan alama lafiyar sa ?alau.

HaWe ransa ya yi sannan ya ce "Momy lafiya ta ?alau fa."

"To na ji, amma ina ga mafarki nake UBANGIJI ka sanya wannan mafarkin ya zama gaskia "cewar Momy'n.

"Momy ki dena yiman haka shi ya sa nake kewar iyayena da sune ba za su yiman haka ba, za su Wauki maganar da gaske."
Ya faWi hakan tare da ya mutsa fuska irin ransa beji daWi ba.

Momy'n ta ce To idan da gaske ne wace ce ita kuma a ina take suwaye iyayen ta tun yaushe kahaWu da ita?"

Fuskar sa fal farin ciki Ya ce "Momy duk waWan nan tambayoyin wanne zan fara amsa maki?"

"To ni ma dai ban san komai a kanta ba kuma watakil kin ma fi ni sanin wani abun a kanta."
"Sannan ban jima da haWuwa da ita ba amma jinake kamar ita ce mahaWin rayuwata idan babu ta kamar zan shiga matsala?"

"Babbar damuwar ita ce kamar yarinyar babu alamar wani abu wai shi SO a tare da ita, ina jin tsoron kar ta?i karSar soyayya ta saboda ALLAH ne shedata yadda nake ji bazan iya jure amsar Ah Ah ba."
"Kadena faWar hakan my son."
Ka san har yanzu bamu fita matsalar 'yan uwanka ba, bana son ina jin wannan kalmar a bakin ka, in sha ALLAH babu abun da zai faru dakai, kuma wace yarinya ce zakace kana so har ta ce Ah Ah? sanar da ni ita yanzu na za?u na san 'yar tamu."

Cikin farin ciki da samun ?wairin guiwa ya ce "Momy bafa kowa bace face ?arki Rahma ALLAH ya sa, za ki aminci ba za ki dubi cewa ita Win ?ar aiki bace duk da na san hakan zai yi wahala saboda iyayena basa gudun ko kyamar kowa, koba haka ba Momy'na?"
Ya?arasa maganar cikin fuskar tausayi.

Momy'n ta ce "Me kake faWane haka? ni kam wannan abun ma farin ciki ya sanya ni sosai."

Kallon sa, ta yi cikin gaskiya da gaskiya sannan ta ce "Ni dai ALLAH ya sa wannan maganar da gaske kake bawai tausayin yarinyar bane a ranka ya sa kafaWi hakan."

"Ah Ah. Momy iya gaskiya ta kenan ki yarda da ni."

"Shi ke nan amma fa, ni ma ina ganin akwai aiki a gabanka gaskiya fatana dai ALLAH ya sa komai yazo da sau?i kuma kayi saurin sanar da ita don kasan matsayinka a gunta."

"Na gode na gode sosai in sha ALLAH kwanan nan zan sanar da ita komai ba zan bari a Wauki lokaci ba."

"ALLAH ya baka sa'a zan yi ta, yi maka addu'a kacire tsoron komai a ranka kai fa namiji ne, ka je in sha ALLAH Rahma taka ce sai ka aure ta ubangiji ya sa alkhairi ce a gunka."

A haka ko wannen su ya nufi Wakinsa cikin farin ciki da samun natsuwa.

Yamma na yi Rahma ta fito domin yin aikin ta ma'ana girki.
Sh ima Sufiyan lokacin ya fito da nufin zuwa lanbun gidan shan iska.
Can ne gurin da yafi zama saboda yana jin daWin gurin sosai bakajin motsin komao sai na tsuntsaye.
Hango Rahma ya yi da sauri ya nufi gurin ta.

"Sannu Rahma har an fito aikin? Sufiyan ya yi tambayar cikin kulawa"

"A nafito saboda lokaci ya yi shi ya sa."

"Ni zan tafi lanbu idan ba damuwa ko zan iya samun lemu kuwa."

"To shi ke nan zan kawo yanzu in sha ALLAH."
Na gode, ya faWa tare da nufin hanyar waje fuskar sa Wauke da murmushi.
Yanzu har mamakin kansa yake yana yawan magana da murmushi babu dalii...

SHIN SUFIYAN ZE IYA SANAR DA RAHMA ABUN DA YAKE ZUCIYAR SA KUWA?
KUMA ZATA AMINCE IDAN HAR YA SANAR DA ITA?
IDAN KUMA TA AMINCE YA ZAHRA ZATA YI?
SHIN WACECE RAHMA?
AM SO SHIN TAMBAYAYOYIN SUNA CIKIN
WATA ?ADDARA
BY
SUWAIBA M AMIRU
(Yar gatan mama)
' 08160726558

PAGE 6??

Rahma ta tarar da shi ga duk'kan alama yana Jin daWin gurin sosai ganin yadda ya lumshe idanunsa,
Ita ma haka ta tsinci kanta da wani ni shaWin wanda ta jima ba ta yi ba saboda ita ma tana son shuke shuke da dabbobi suna sanya ta nishaWi fiye da komai.

Alama ya ji kamar da wani aku sa da shi Wago kansa ya yi ganin ta a tsaye tana ta kallon fararen tsun tsaye murmushi ya yi sannan ya ?ara sa gurin da take.

"Rahma kinzo kenan, halan baki taSa zuwa nan gurin ba?"
"Ban taSa zuwaba ko yanzu sai da na sanya aka nuna man inji yaya mai gyaran filawoyi."

"Ok idan ba damuwa ki zo mana kiWan huta ki samu ganin tsun tsayen da kyau."

"Ba zance Ah Ah ba idan aka zo zancen dabbobi, amma sai dai in zo wani lokacin tun da naga gurin yanzu saboda ban gama aiki ba."
"Shi ke nan zuwa anjima sai ki zo."

"Ah Ahh ba dai yau ba saboda koda zan gama komai dare ya yi kuma akwai abun da nake yi a daidai wannan lokacin yafi man zuwa nan mahimmanci."
"Shi ke nan ALLAH ya kai mu safe lafiya."

Ameen cewar Rahama.

Bayan sallar isha Rahma ce ke sanyawa momy'n abinci kamar yadda ta saba bayan ta gama ta ce "Momy akwai abun da ake bu?ata kuma?"

"Ah Ahh Rahma bana bu?atar komai ki dai tambayi sauran 'yan uwanki."
Kallon Zahra ta yi.
"Aunty Zahra kina bu?atar wani abun kuma?"

"Bana bu?atar komai, kuma daga yanzu kar ki ?ara kirana da Aunty a gidan nan idan ba haka ba sai na yi matu?ar saSa maki wallahi."

"Kallon Sufiyan ta yi kai fa Yaya?"

"Bana bu?atar komai ?anwata sai dai ina son ki yi ta ha?uri da aikin jahilci."
Murmushi kawai ta yi tabar parlorn.

Kallon Momy ya yi sannan ya ce "Momy ubangiji ya sa abun da ke cikin raina alkhairi ne."

"Ameeen ya ALLAH, Ni ma fatana kenan."

Ni kam ina ta son yi maka tambaya a can baya naga baka son cin abinci sosai musamman idan ba ni, na yiba ko iyayen ka amma yanzu na ga an samu sauyi miye sirrin ko ka sha maganin cin abinci ne?"

"Hmmm Momy kenan ni ma ina mamakin kaina a kan abubuwa da dama, ina jin abincin kamar naku shi ya sa, amma duk waca ke yin girkin nan gaskia ta iya sosai."

"Momy am amma ba wannan Rahmar ke yin saba koh?"
Ya ?arasa maganar cike da son jin amsa daga gurin Momy.

Girgiza kai Momy ta yi tare da "Cewa ita ke yin sa mana, me ya sa ka tambaya halan?"
"Kawai dai na ga kamar ta yi yarinta da yawa ne bana tunanin ta wuce shekara 18 ko 19 fa."
Har ta ya ta koyi abinci haka?"

"Hmmm rayuwar Rahma abun da na fahimta akwai sirri sosai a ciki sai dai bata da niyar faWar wannan sirrin a yanzu."
"Ina ga mu bita a hankali in sha ALLAH wata rana zamu san komai."

Basu an karaba sai jin tsaki su ka yi suna juyawa su ka ga wai ashe har yanzu Zahra nagurin, a zahirin gaskiya sun manta da ita sam.
Mi?ewa ta yi tabar gurin da sauri tana huci kamar zakanya.

Momy dubanta ta mayar a gun Sufiyan ta ce "Wai har sai yaushe ne zaka sanar da Rahma burinka?"
"Ina nan ina shiri Momy Wazuma na yi yun ?urin sanar da ita amma wani dalilin ya hana.
"ALLAH ya bada sa'a ya sa a dace, yanzu ka ta shi kaje dare ya yi haka nan."

"Na ji zan tafi Win amma ba dan rai na ya so ba kin san idan ana zancen Rahma bana son a daina."

To na ji idan ba tsoro ba kanuna man kana ?aunar ta da gaske ka sanar da ita."

"Ai kuwa zan nuna maki ni Win Wan iyaye nane musamman Aunty kin koga ba zanji tsoron komai ba,
Idan naji tsoro ma ba za su yafe man ba HAJJIYA Momy."

Ya ?arasa maganar cikin zolaya tare da barin gurin cikin gudu gudu yana Wan dariya.

Ita ma dariya ta yi tare da faWin "Da kam yafi nan ne zaka nuna man kai Win ka cika sarkin soyayya."

Bayan shigar sa Waki ya rasa abun da, ke masa daWi tunani kawai yake shin ta wace hanya ya dace ya sanar da ita abun da yake ransa.

Kawai kamar an min tsine shi, ya ta shi ya fito daga part Win sa, bai tsaya ko ina ba sai part Win Rahma.

Muryarta ya jiyo ?asa-?asa tana karatu sauraron muryarta mai za?i ya tsaya yi can kuma kamar an ingiza sa kawai ya fara ?wan?wasa ?ofarta.

?an tsayawa tayi da karatun sannan taf ara tambayar waye waye?
Ni ne Rahma."

BuWe ?ofar ta yi ta ce "Yaya lafiya kuwa ko kana bu?atar in haWama wani abun ne yanzu?"

Ya rasa mai zai ce duk ya daburce sosai cikin rawar murya ya ce.
"Ah Ahh Raha ma cikin daren nan zan sanya ki wani aikin? kawai dai na jiyo kamar wani abun na ?onewa shi ya sa nazo nan, ke ma kinji ?aurin ko?"

"Ah Ahh ban ji komai ba gaskiya, amma kaduba har Wakin Momy da Zagra duk lafiya?"
"A na duba duk ko ina ba cikin su ba ne, bari kawai na wuce inaga tunanina ne kawai sai da safe."
"Am gobe kuma da safe ina son magana dake idan ba damuwa."

"To Yaya ALLAH ya kaimu" Rahma ta faWa.

Ko wannen su ya wuce ita ta shiga Waki shi kuma ya wuce part Win sa.
*******************
Tun misalin ?arfe 7:30am Sufiyan ya fito sanye cikin farar shadda mai Win kin ?aramin hannu ya sanya takalmi ba?i hakama hular kansa ba?ace sai faman ?amshi yake wanda dama chan kullun cikin ?amshi yake duk gurin da, ya wuce sai ka san ya wuce.
Momy ce ta kallesa sannan ta ce "Wannan kwalliyar fa ko, za ka je Waurin aure ne?"
Murmushi ya yi, yace "Momy banda sa ido fa, ni dai kima bari mu gaisa tukun na."
Bayan sun gaisa ya ce "Momy ina Rahma, ta fito kuwa?"

Tana kitchen tun Wazu ta fito"
da sauri bai jira wata maganar ba, y anufi hanyar kitchen Win.
Ganinta ya yi tana ta faman goge goge gurin da ta Sata,
Sallama ya yi mata.
Amsawa ta yi cikin kulawa ta ce "Yaya za ka je wani taro ne, na tsayar dakai koh? ka yi ha?uri nama gama yanzu zan fito da komai in sha ALLAH."

"Me kika gani ne halan daya baki damar tuna nin zan tafi taro yanzu?"
Ba komai na ga yau ka yi shigar manyan kaya kuma ban taSa ganin hakan ba shi ya sa, na yima tambayar."
Hmmm ba inda zan tafi amma yau ina da wani abun mai mahimmanci sosai, amma idan kina so zan rin?a sakawa kullun."

Shuru ta yi na Wan lokaci kamar ba, za ta yi magana ba can kuma ta ce "Me ya sa, za ka rin?a san yawa saboda ni, wane matsayi nake da shi?"
Hmmm yanzu dai idan kin gama ki same ni parlorn sama, kin san jiya na sanar dake za muyi magana koh?"
To nazo maka da breakfast Winka a chan Win?"

"Ah Ahh ki barshi zan neme sa daga bi sani saboda yanzu bana jin yunwa."
"Shi ke nan in sha ALLAH zanzo nan da minty goma haka."
Rahma ta gama komai sannan ta nufi parlorn sama da sallama ta shiga.
Sufiyan mi?ewa ya yi tsaye, ya yi mata iso da cewa ta shigo ciki.
Shiga ta yi ta zauna a ?asan carpet.
"Ki zauna a kan kujerar mana Rahama."
"Ah Ahh nan ma ya yi yaya."
"Ina jinka ka sanar da ni ko meye, kasan ni fa lokaci na duk akwai abun da nake yi da shi bana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login