Showing 93001 words to 96000 words out of 123822 words

Chapter 32 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3452

kun fara sauya man."

Samir ya ce "Sam ba haka ba ne Wan uwa, ban san me ke damun Wan uwa Salim ba amma tawa damuwar babba ce bana son kakira ni da mai son kai ko kuma ka kalli maganar da wata manufa da ban shi ya sa ban taSa yun?urin sanar da kai ba."

Idanun Sufiyan nan take suka sauya zuwa ja sosai tsananin Sacin ransa ya bayyana sannan ya ce "Kun ba ni mamaki wallahi, da har kuke tunanin akwai maganar da za ku faWa man na kalle ta da wata manu fa."

Samir ya ce "Ka yi ha?uri Wan uwa zan sanar da kai" cikin rawar murya ya ce "Dama ina so ne don Allah ka ba ni abun da ?anwar mu za ta haifa, na ka sance uban sa, ba Wan uwan uba ba, ya zama nau yin sa a kaina yake, ya ka san ce duk wani kulawar da uba ke bawa Wan sa nine zan ba shi, ina son ace ko a makaranta sunana zai rin?a amsawa amatsayin ubansa wannan shi ne ro?ona Wan uwa" ya ?arasa maganar cikin rauni sosai tare da sunkuyar da kansa ?asa.

Sufiyan ya rufe idanusa na tsawon wani Wan lokaci sannan ya buWe ya kalli Salim ya ce "Kai kuma fa me ye damuwar ka?"
"Ba komai Wan uwa yama wuce bar shi kawai" cewar Salim.

Murmushi Sufiyan ya yi, ya ce "Ga duk'kan alama matsalar ku iri Waya ce, to shin ba an duba ana tunanin ?an biyu ba ne a jikin ?anwar ta mu?" su kace a haka ne."

"To shi ke nan Allah ya tabbatar da hakan, ba yara biyu ba ko goma ne, na yi maku al?awarin zan raba su tsakanin ku in sha Allah."

Da sauri sun ka rungume shi suna ta yi ma sa godiya suna faman hawayen farin ciki, daga bakin ?ofa suka jiyo muryar Kaka yana faWin wannan hukuncin bai yi man ba, ni dai ban yarda ba, karka manta ba kai ka Wai ba ne mai hakki ga abun da za'a haifa ba."

"Uwar su ma tana da hakki don haka ka je ka fara yin shawara da ita tukunna" cikin mutuwar jiki Sufiyan ya ce "To bari na je, na ga ni, ko ta farka daga baccin."

"Yana shiga Wakin ya tarar har ta yi wanka tana shiryawa, gefen gado ya zauna sannan ya ce "?anwata ina son mu yi magana mai mahimmanci in ba damuwa."

"Ina jin ka Allah ya sa lafiya naga yana yin ka sai a hankali?" "?anwata lafiya ?alau" nan dai ya sanar da ita komai yadda suka yi da ?an uwansa da kuma abun da Kaka ya faWa.

Ta yi shuru tsawon lokaci tana ta gyaran gashin ta kamar bata ji abun da ya faWa ba, sai can ta ce "Bayan kai da Kaka waya san da wannan maganar?"

"Ba wanda ya sa ni bayan mu" juyowa ta yi ta kalle shi sannan ta ce "To maganar ta tsaya iya nan saboda ban amince ba Yaya."

Cikin tsananin mamaki yake kallon ta baki sake tare da tambayar me ya sa?..

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
BY
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' PAGE 5?? 3??

A Yaya abun da na faWa haka ne, Yaya idan har kana son ?an uwanka su yi aure to karka ba su yaranka, idan ma so samu ne, ka je ka sanar da su cewa idan suna son ?a-?a to su yi aure kawai, na san hakan zai iya sa ran su ya Saci su yi aure cikin ?an?anin lokaci in sha Allah."

"Wace magana kike faWa ne haka me ye haWin wannan maganar da zancen auren su kuma? sannan ta ya kike tunanin zan iya Sata ran ?an uwana har haka ban ba su yara ba kuma na yi masu zancen aure bayan na san ba wannan maganar a tare da su yanzu?"

"Yaya ka ga ne mana wani lokacin sai an Sata wani abun ake samun wani abun, iyayenmu burin su duk ku yi aure amma su kuma yanzu ba wannan lissafin a tare da su, shin me zai hana mu taimaka ma su ganin wannan burin ya cika?"

"?anwata aure lokaci ne, ya kama ta ki Wauki darasi ko a aurenmu, ba zato ba tsammani komai ya tabbata, sannan ?anwata iyayenmu ba za su, so auren su ba matu?ar ba za, su yi farin ciki ba."

"?anwata ni dai kawai mu yi masu addu'a amma gaskiya wannan ba hanya ba ce da zai sa, su yi aure sai dai ma mu ?ara Sata lamarin, don Allah ki taimaka man ?anwata mu yi masu sadaukarwar domin na samu ganin farin cikin su da kyau" ya zama abun tausayi lokaci Waya, har da haWa hannunsa guri Waya alamar magiya.

"Shi ke nan Yaya abun da kake so bazan iya yi maka musu ba sai dai kawai na bi umurni, Allah dai ya shige mana gaba, yanzu ka ta shi mu tafi sai mu sanar da kowa burin na ka Koh."

"Allah ya sa ?anwata har zuciyarki wannan sadaukarwar ba tursasa ki, na yi ba, saboda na ji kin ce wai burina, ma'ana ni ka Wai ba da ke ba?"

"Sam ba haka ba ne Yayana, shi ke nan to burin mu hakan ya yi ma?"

Murmushi ya yi ma ta tare da addu'ar Allah ya sa kar ta sauya ra'ayi, da haka har suka ?arasa parlor."

Suna shiga gurin ta ce "Ma sha Allah na ji daWin ganin kowa a nan saboda akwai magana mai mahimmanci da muke son sanar da ku, dama game da abun da zan haifa ne, ni da Yaya mun yanke shawarar idan har Allah ya sa da gaskiya ba yaro Waya ba ne kuma na sauka lafiya, to za mu raba su tsakanin ?an uwanmu Yaya Salim da Samir."

"Kuma muna son daga lokacin da yaran suka shiga hannunsu ba wani mai ikon kiran su da wani sun uban bayan na su sunan, duk wata kulawa da uba ke bawa Wansa to su nake son su, ba su ko a makaranta da sunan su za su rin?a amfani."

"Daga lokacin da wani ya kira su cewa su Win ba yaran su ba ne, suna da damar yin shari'a da shi ko da kuwa mu ne, don haka ko da wasa bana son wani ya yi gangancin ta da wannan maganar saboda bana son wani tunanin ya shiga cikin kan yaran."

"A takaice dai Yayuna ne uwanyen shi kuma Yayana uncle Win su, ina fatan za ku yarda da tayinmu, ba mu yi laifi ba."

Sufiyan ya ri?a hannayen ta sannan ya ce mun gode mun gode sosai ?anwata ubangiji Allah ya sanya ki farin ciki har ?arshen rayuwarki kamar yadda kika sanya mu a yau."

Su ma ku san abun suka ce ke nan cike da farin ciki "Momy Saratu ta ce Allah ya yi maku albarka ya ?ara korar sheWan tsakanin ku" duk suka amsa da ameen.

Zuciyar Sufiyan kuma fal take da farin ciki saboda yana tunanin yanzu ?anwarsa shi ka Wai take so kuma take kishi, tun da ga shi yanzu har tana fatan uwansa su yi aure ba tare da wani War ba, kai tsaye ta sanar da shi hakan.

**********************
Tun daga lokacin kulawar ta ya koma hannun Yayunta ukun ba su da lokacin komai sai nata, suke kai ta makaranta sannan a nan za su tsaya har sai ta fito su koma da ita gida, duk abun da take son ci ko sha kuma suke haWawa wani lokacin har sai sun gama girki a wahale tace kuma ta ji bata son shi wani abun da ban kuma take so.
A part Win na gidan suke rayuwa yanzu hakan ya sa iyaye duk suka koma gidajen su sai dai ko yaushe cikin kiran waya suke su ji komai lafiya.

*********************
A kwana a ta shi cikin Sufayya ya ku sa fita daga wata goma hankalin duka families a kanta yake an hanata zuwa ko ina har makaranta yanzu duk yawon ta baya wuce cikin gida zuwa gidan gonar gidan ko shi don ba'a son mai juna biyu ta zauna guri Waya.

Tausayi take bawa kowa ganin yadda cikin nata ya girma sosai da ?yar take tafiya duk ta kunbura, har ita ce mai ?o?arin nuna ba komai hankalin a kwance, duk sun fara tunanin ko dai CS za'a yi ma ta a cire cikin, amma ta Waura hannu a kai ta fara kuka tana faWin ita wallahi ba wanda zai yanka ta tun da dai lafiyar ta ?alau lokacin ta ne bai yi ba, da ?yar aka samu ta yi shuru tare da yi ma ta alkharin an daina zancen, Allah ya raba lafiya.

Yau wata sha Waya ke nan duk sun da mu sosai sannan da an yi zancen CS duk sai ta Waga hankalin ta, yau dai har ta fara bacci can kuma ta farka, shi ma Sufiyan da sauri ya ta shi ya ce "Lafiya dai ?anwata?"

"Parlor nake son na tafi" haka ya ri?o hannuta suka fito a ?asa ta zauna, suna zauna wa sai ga sauran Yayunta sun fito da sauri suna tambayar Lafiya.

Sufiyan ya ce "Wai nan take son zama shi ya sa muka fito, su ma sai suka zauna a gurin, 2:am amma sam ba alamar bacci a idonta.

Can kuma ta kalle su ta ce "Ina son yougot mai sanyi sosai da cake, da sauri suka mi?e duk'kan su amma sai ta ri?e hannun Sufiyan ta ce "Don Allah ka zauna da ni kaga ?afa ta ma ciwo take man sosai, aikuwa a take ya dawo yana matsa ma ta.

Bayan ta gama cin komai, suka ce yanzu kuma sai me akwai abun da kike so?"
"Ba komai sai dai ku zauna tare da ni karku yi ni sa, ku tsaya a tare da ni."

"Kar ki damu in sha Allah ba za mu je, ko ina ba muna nan, amma bayyane yake cewa suna cikin damuwa saboda yana yin ta duk ya sauya ga kuma kalaman ta kamar na mai yin ban kwana.

A nan gurin ta kwanta bacci ya yi awon gaba da ita, amma su kuma sun gaza yin ko dogon motsi, 3:30am kuma ta farka da wani matsanan cin ciwon ciki da baya sai faman gumi take tun tana dauriya har ya kai ta fara faWin "Ku taimakeni don Allah baya na zai balle ciwo yake man."

Da sauri suka yo kanta Salim ya ce "Lokacin haihuwar ne yazo ya dace mu je asibiti yanzu, suna isa asibitin aka shiga da ita Wakin haihuwa da yake an san su waye su Win hakan ya sa doctors da dama suka tsaya kanta.

Su kuma Yayunta ba mai ?warin giuwar shiga gurin ta don har sun fara rauni.

Wasa wasa haihuwa ta?i zuwa har asuba ganin hakan Samir ya ce "Ya dace mu sanar da gida, duk suka ce a haka ne, sai lokacin suka fahimci ashe ba wanda ya fito da wayar sa hakan ya sa suka je domin Waukar wayar asibiti su kira.

A can gida kuma iyayen ganin ba su gansu a masallaci ba hakan ya sa kai tsaye gidan na su suka wuce sun duba ko ina amma basa nan ga kuma wayoyin su ajiye hankalin su a ta she suka kira iyayen na su mata, suna tunanin ina suka tafi sai ga wayar Dady Nura ta yi ?ara da sauri ya Waga duk da bai san number ba.

Muryar Samir suka ji a nan ya sanar da su asibitin da suke, aikuwa da sauri suka tafi su ma, sai dai har suka tafi bata haihu ba, a raunane suka ce "Kun ga fa har yanzu bata haihu ba."

Dady Suraj ya ce "Yanzu addu'ar mu take bu?ata, suna cikin wannan yana yin sai ga Waya daga cikin doctors ta fito ta sanar da su "Ya kamata ku cike waWan nan takardun domin a shigar da ita CS saboda gaskiya ?arfinta ya fara gazawa sosai.

Sufiyan har zai sanya hannun Salim ya dakatar da shi ta hanyar ri?e hannunsa ya ce "?an uwa duk'kan mu nan mun san ba abun da ?anwar mu ta tsana irin ayi mata zancen CS kuma ba tsoro ba ne ita dai burinta shi ne ta zama uwa ta hanyar haihuwa domin ta ji yadda ko wace uwa ke ji yayin haihuwa."

"Don haka ya kamata mu yi ?o?arin cika ma ta wannan burin na ta, ta hanyar bata kwairin guiwa tun da dai kaga muma wannan aikinmu ne musamman ni Sangare na ne, kuzo mu shiga gurin ta ina da tabbacin in sha Allah za mu sanya mafarkin ta ya zama gaskiya."

Haka dai suka shiga Wakin ganin yana yin ta sai da jarumtar su ta so gushewa, amma a haka suka tattaro duka natsuwar su, bayan wani Wan lokaci sai ga su sun fito amma ba tare da Sufiyan ba.

Suna isa gurin iyayensu suka mi?e tsaye suna tambayar "Ya ake ciki ina ita Sufayyar tana lafiya kuwa?"

Murmushi suka yi sannan suka ce ku kwantar da hankalin ku yau Wan ku Sufiyan ya yi jarumta don ku san shi ya karSi haihuwar yanzu ma shi ka Wai mu ka baro ya gyara ta, kuma albishir na biyu ta sauka lafiya mun samu yara kyawawa har huWu biyu mata biyu maza cikin ikon Allah."

Ai kafin su rufe baki su har sun kai Wakin cikin sauri, suna shiga Wakin suka Wauki yaran suna faWin maa sha Allah kuma yaran barakallah ko wannen su da girmansa wata?il shi ya sa ta sha wahala haka "Ku dubi ikon Allah muna dubin ?an biyu sai kuma Allah ya azurta mu da ?an huWu" Momy Aisha ta yi maganar cikin tsananin murna.

***********************
Ta Wau lokaci tana bacci a Wakin hutu sannan ta fara ?o?arin farkawa daga baccin tana buWa idanunta sai a kan Sufiyan shi ka Wai ne a gurin ta saboda ba'a son a takura ma ta sosai.

Da sauri ya ?ara matsawa ku sa da ita, ya rungume ta yana yi ma ta sannu tare da yi ma ta godiya, cikin rashin kuzari ta ce "Yaya ka sake ni ga su Momy nan bayan ka" waskewa ya yi kamar bai gansu ba ya Wan sake ta sannan ya ce "Sorry na takura ki koh? to koma ki kwanta ki Wan huta."

Har an gyara yaran sun yi kyau sosai, su Kaka ta hango ta ce "Sau kar yaushe Kaka?"

"Yanzu nan muka sauka an sanar da mu tun jiya kina asibiti ni har nace idan nazo ba ki haihu ba zan sanya kawai a shiga dake a cire maki su."

"Kun fiye tsoro wallahi baku son ku rasa amaryar ta ku, yanzu ba ga shi cikin ikon Allah na sauka lafiya ba."

Kaka ya ce "Kuma fa haka ne, yanzu dai ina Sufiyanu yake ya zo, ya yi masu kiran sallah?"

Sufiyan ya ce "Ah ah karka ce man ka manta ?an uwana ne masu wannan ikon, tun da suna ku sa a matsayin su, na iyayensu su ya dace su fara yi masu kiran sallah ni kuma daga bi sani sai na yi masu nawa a matsayina na uncle Win su."

Haka kuwa aka yi duk ya dam?a yaran a hannunsu ya ce "Ga al?awarina ni ma ina ro?on Allah ya nuna man na zama uba kamar ku watarana" cikin farin ciki suka ce "Ameen ya Allah Wan uwa, mun gode sosai Allah ya sa ka maku da gidan aljanna."

Salim ya ce "?anwata kin tuna lokacin da na sanar dake cewa na yi mafarkin kin haifa man yara biyu ina ri?e da su, a lokacin kallon marar hankali kika rin?a yi man, to yanzu ga shi dai mafarkina ya zama gaskiya."

Samir ya ce "To ai ko ni bata yarda da ni ba don a lokacin da na sanar da ita, cewa ta yi na raba ta da shirme nan" ita dai murmushi kawai ta yi.

Nan dai suka yi masu kiran sallah da huWuba sannan suka sanya masu suna, Sufiyan shi ma sai farin ciki yake ganin ?an uwansa a haka, saboda ya jima bai gansu cikin tsantsar farin ciki ba haka, kallon su ya yi, ya ce "Wane suna ku ka sanya masu?"

Samir ya ce "Suraj da Saratu" iyayen Sufiyan ke nan, cikin farin ciki Dady ya je gurin sa ya ce "Maa sha Allah kace dai mu aka yi wa haihuwa, ubangiji Allah ya albarkace su" duk aka amsa da ameen.

Salim kuma ya ce "Munir da Zainab" iyayen mai jego ke nan, su ma sun yi farin ciki sosai tare da yi masu addu'a.

?a-?an Samir su ake kira Jawwad da Jawahid, na Salim kuma su ake kira da Assalim da Taslim.

Momy Nafisa ta dage gidan ta za'a zauna saboda ita ke son kulawa da mai jego, haka aka bi ra'ayinta.

Kulawa sosai take samu ta ko wanne Sangaren duk sai kiran mutanen su suke suna sanar da su har mutanen Nigeria.

Ranar suna an yi shagali sosai idan ka ga bakin iyayen Salim da Samir baya rufuwa a kan farin ciki, sun yi Sarin naira kamar ba su san zafin ta ba, shi ma Sufiyan ba'a barshi a baya ba ya yi ?o?ari sosai, yara da mai jego sun sha photo da video kuma sun yi matu?ar kyau, jikin Sufayya ya walwale sosai ya koma yadda yake ada duk kunburin nan ya fita daga jikinta idan ba ka sani ba, ba za ka ce ita ce ta haifi waWan nan yaran ba.

*********************
Akwana a ta shi wata ukun da su Momy suka ce sai ta yi sannan ta koma gidanta har ya ku sa cika an fara yi ma ta shirye shiryen koma wa, yaran kuma maa sha Allah sun ?ara girma.

Kwana biyar da komawar ta gidanta suna zaune su biyu kawai ita da Sufiyan, ?an uwan nasu kuma suna can part Win su da yaran dama sai dai idan yaran sun so uwarsu suke shigowa na su part Win, idan ma sun ba su madara sun karSa to basu da mu da kai ma ta su ba, sai su wuni basu ga juna ba.

Kallon Sufiyan ta yi sannan ta Wan yi murmushi ta ce "Don Allah na yi maka tambaya Yayana?"

?an jan hancinta ya yi cikin murmushi ya ce "ina jinki ?anwata."

"Wai don Allah har yanzu kana so na?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login