Showing 96001 words to 99000 words out of 123822 words

Chapter 33 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3453

na ji ance wai idan mace ta haihu mijinta na daina son ta sannan ya yi ta, yi ma ta wula?anci amma kai naga har yanzu ba abun ya sauya, sai dai har yanzu a tsorace nake gaskiya."

Kallon ta ya yi cike da kulawa da kuma hango gaskiyar maganar ta cikin idanunta ya ce "Haba ?anwata me ya sa, za ki Wauki wannan ban zar maganar a ranki? to bari ki ji ita soyayyar gaskiya ba abun da ke sanya ta rauni, kuma bari na sanar dake mafi yawancin ma'aurata soyayyar su na ?ara ?arfi ne idan sun haihu."

?ara ri?a hannunta ya yi, ya ce "Ki sani ?anwata ko da ana mutuwa a dawo ba zan taSa cire son ki a raina ba, a ko wace rana son ki ?aruwa yake a zuciyata bana tunanin akwai abun da zai sauya wannan."

"?anwata ke Win nake so ba wani abu ba don haka naro?e ki, ki daina Waukar zancen mutane, da ilimin ki da hankalin fa ?anwata."

********************
Tun daga lokacin ta ?ara daidai ta komai tsakanin su tana iya ?o?arin ta wajen nuna mai soyayya, sannan tana yi ma sa matu?ar biyayya komai ya ce to ta zauna babu ko musu, a yanzu shi kansa ya gama yarda cewa tana son shi, sannan kuma yanzu ne ya ?ara sanin daWin aure, hankalin duka families ya kwanta sosai na ganin irin zaman da suke abun gwanin birgewa.

Sai dai Salim da Samir suna ji a ransu kamar Sufayya har yanzu tana yin duk wannan ne a bisa biyayya, amma sun Wauki alwashin gano gaskiya, saboda su ba haka suke so ba, sun fi son ace tana yin hakan ne har zuciyarta,
Yara kuma sai ?ara wayo suke sun girma sosai don yanzu suna wata shidda ne.

*********
Yau ma misalin ?arfe 11:pm yara sun yi bacci sun mi?a su gurin iyayen su, zaunawa ta yi ku sa, da shi yana ta faman aiki a lopton kwanciya ta yi a kan kafaWarsa ta ce "Mijina don Allah idan ba damuwa ina son neman wata alfarma a gurin ka."

Yana yin kalmar mijina da kuma yadda ta yi maganar ya san cewa abun da take nema ba ?arami ba ne "Hmm gimbiyata ke nan ki ba ni umurni kawai in sha Allah zan yi maki koma mene ne idan bai fi ?arfina ba."

"Yayana dama ina so ne mu tafi Nigeria satin nan saboda ina son na tafi ZAMFARA can garin da na girma."

Da sauri ya ture lopton gefe ya gyara zaman sa, yana fuskantar ta, da kyau ya ce "Zamfara kuma ?anwata me zai kai ki can Win?"

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' PAGE 54
Hannunsa ta ri?e ta ce ina so ne kawai na je tun da jimawa na yi kewar su sosai, bana son ranka ya Saci ne shi ya sa ban sanar da kai ba, amma yanzu na ga cewa shurun ba ya da wani amfani, don Allah Yaya ka bar ni, na tafi karka ce ah ah" ta ?arasa maganar da fuskar tausayi.

"Shi ke nan daina damuwar in sha Allah sati mai zuwa idan kin samu hutu sai mu tafi Win, amma kafin nan zuwa safe zan sanar da iyayenmu komai mu ji, ta su shawarar."

Da sauri cikin tsananin farin ciki ta rungume shi tana ta yi ma sa godiya, ita ma a lokacin sai da ta sanya shi farin ciki.

Da asuba cikin ni shaWi ya farka daga bacci ya yi ma ta kiss a goshi sannan ya ce "A ta shi haka nan my love ki samu yin azkar Win ki a kan lokaci, kin san za mu shiga gurin iyayenmu mu sanar da su zancen tafiyarmu kafin lokacin shiga makaranta ya yi."

Haka ta shirya tsaf sannan ta shirya yaran suka fito duk'kan su zuwa gidan Momy Aisha dama da yaje masallaci ya sanar masu cewa don Allah duk su haWu a nan gidan akwai maganar da yake son sanar masu, hakan ya sa ko da sun ka tafi kowa ya hallara.

Bayan duk an gama gaisawa duk aka yi shuru, Dady Nura ya ce "Kai fa muke saurare Wana."

Sufiyan ya ce "Am Dady dama muna neman izinin ku ne muna son za mu yi tafiya zuwa Nigeria idan ?anwata ta samu hutu zuwa sati mai zuwa, saboda tana son ta kai ziyara garin da ta girma."

Bai ?arasa maganar ba Aunty ta katse shi da cewa "Garin da sun ka wula?anta ki suka zagi kima da mutuncin ki suka kora ki, yanzu kuma can kike son zuwa saboda ba ki da zuciya?"

"To meye ma abun sha'awa da birgewa a cikin garin da har kike son zuwa? to ki sani ba inda za ki je, ki ma cire wannan tunanin a ranki kin ji na faWa ma ki" ranta a Sace take magana.

Sufiyan ya ce "Don Allah karku ce za ku hana ta tun da tana son zuwa kuma ma tare za mu je na raka ta."

Momy Nafisa ta ce "Ka yi shuru kawai Sufiyan amma ni ma ban ga dalilin zuwa wannan garin ba."

A sanyaye Sufayya ta fara magana "Momy kar ka sancewar ku iyaye ya sa ku manta alkharin da suka yi maku, su Win mutane ne masu mutunci suna da matu?ar kir ki, sun raine ni sun ba ni tarbiya sun ba ni kulawa da tsantsar soyayya, sau Waya ba su taSa barin na ji cewa suba iyayena ba ne, duk abun da nake so shi ake yi."

"Amma lokaci Waya saboda kuskuren da ko wane mahalu?i zai iya aikata shi idan ya sa mu kansa a wannan yana yin, sai duk ya goge wannan alkharin na su?"

"Karku manta da fa ace ba su karon ba, da har yanzu ba ku haWu da ?arku ba, ni kuma da har yanzu ban san cewa ba su, ba ne iyayena ba, don Allah ku aje ye komai a matsayin ?ADDARA ta ce tazo da hakan, ku daure ku yi man izini na tafi" ta ?arasa maganar har ?an hawaye a fuskar ta.

Dady Ahmad ya ce "Wannan gaskiya ne bai kamata sharrinsu ya sa a manta alkharinsu ba don haka ni dai ta gurina na amince ta yi wannan tafiyar ko don ta tabbatar masu cewa abun da suke zargi a kanta ba haka ba ne, don na san in sha Allah yanzu zuciyar su ta yi san yi a shirye suke da su saurare ta."

Dady Nura ya ce "Ni ma dai ina bayan maganar ka, kuma ta gurina ga wata shawara, ina ga ya dace duk'kan mu ayi wannan tafiyar da mu, domin mu ga gurin da ?ar mu ta yi rayuwa sannan mu yi wa mutanen godiya a kan irin alkharin da su ka, yi mana na kulawa da ita."

Haka dai kowa ya amince a kan maganar Dady Nura, cikin farin ciki Sufayya ta ce "Na gode na gode sosai iyayena" Sufiyan ya ri?o hannuta ya ce "Kin yi farin ciki kuwa?"

"A mana Yayana ina cikin farin ciki sosai, yanzu dai ta shi mu tafi makaranta na ku sa makara."

Samir ya ce "Amma gaskiya ina da magana, ba wai yin tafiyar ba ne matsala, matsalar ita ce na ji fa ance har yanzu Zamfara ba su da filin jirgi, kuma tafiya a mota zai sa yaranmu iskan motar ya takura masu."

Dady Ahmad ya ce "To uwanyen yara to bari ka ji, ku ma lokacin da kuna yara haka muke yin tafiyar mota da ku kuma ba abun da ya taSa samun ku, sai yanzu wani abun zai samu naku yaran? to shi ke nan saboda tafiyar ta zo da sau?i sai mu sauka Kaduna ko Sokoto, ina ga tafiyar ka Wan za mu ?arasa a mota, hakan ya yi maku Koh?"
Duk suka ce "A hakan ya yi Dady."

********************
Cikin satin duk in da kaga Sufayya tana cikin farin ciki sai faman shirye shirye take sosai.

Yau ta kama ranar tafiya a Kaduna suka sauka gurinsu Kaka, sun ji daWin ganin su sosai musamman da suka ji dalilin zuwan na su, kwana biyu suka yi sannan suka Wauki han yar tafiya Zamfara.

Sun yi tafiya sosai a mota saboda rashin sabo duk sun jigata amma ita kam ko a jikinta ita dai fatan ta shi ne ta ganta a cikin garin.

Cikin ikon Allah ga shi suna cikin farkon garin Sufayya na ganin sun kawo garin da sauri ta ce "A tsaya dama su huWu ne ita da Yayunta sai direba shi ne na biyar.

Duk kallon ta suka yi bayan sun tsaya Sufiyan ya ganta duk a razane ya ce "Lafiya kuwa me ke faruwa ko da wata matsalar ne, duk kin yi wani figicewa haka?"

Cikin rawar murya ta ce "Yaya na tuna lokacin da nabar garin nan da kuma yana yin da nabar sa, kuna ganin za su karSe ni kuwa, kuna ganin mutane da yara ba za su sake taruwa suna zagin kima da mutuncina ba, kuna ganin za su karSe ni a mai daraja kuwa? ni dai wallahi a tsorace na ke."

Salim da Samir suka ce "Kar ki manta yanzu ba ke ka Wai bace kina tare da duk families ki don haka ki cire komai a ranki ba abun da zai faru da ke in sha Allah."

Sufiyan ya ce "Sannan zancen kima da mutunci kuma kar ki manta kina tare da mijinki don haka ba wanda ya isa ya zagi kimar ki kin ji koh?"

Sunkuyar da kanta ta yi sannan ta yi murmushi ta ce "Haka ne fa na manta cewa ina tare da ku don haka yanzu ba ni da fargabar komai za mu iya tafiya."

Kafin ta sake yin magana sai ga kiran wayar Salim ya shigo, yana Wagawa Dady Munir ya ce "Wai lafiya ku ka tsaya bayan kun san bayan ku muke bi?"
Salim ya ce "Ku yi ha?uri Dady yanzu za mu tafi tana Wan duba hanyar ne."

*******************
Da kwatance da misali har suka ?arasa ?ofar gidan ba ?aramin ?o?ari ta yi ba gurin gane gidan duk da gidan na nan yadda yake amma garin ya Wan samu sauye sauye sosai.

Samir ya ce "Kin tabbatar wannan ne gidan kuwa?" Salim da sauri ya ce "Kuma a ciki kika yi rayuwa ?anwata?"

Ta kalle su baki sake ta ce "Me ya sa kuke yi man wannan tambayar haka ko bai yi maku kama da gida ba ne?"

"Ni dai na tabbatar gidan muka zo kuma a nan na yi rayuwa, kun ga ku bari na fara shiga saboda na yi maku iso tun da, ba kowa a ?ofar gidan."

Tana ?o?arin shiga sai ga Idiris ya fito ga duk'kan alama aiken sa aka yi, tana ganin sa cikin farin ciki ta ce "Idiris ina zuwa haka kake sauri?"

Da sauri ya juyo ya matsa ku sa, da ita ya kafe ta da idanu sai can kuma ya ce "Baiwar Allah kin yi kama da Aunty na har da muryar ku iri Waya, amma sai dai yanzu bata tare da ni dana nuna maki ita, kullun sai dai ta zo man a mafarkina ta yi man al?awarin za ta dawo ko kuma ta yi man gizo amma har yanzu ta?i cika man al?awari ta dawo gurina" nan take idanunsa suka sauya yana shirin yin kuka.

Murmushi ta yi, ta ri?o hannunsa ta ce "Ba dai kuka za ka yi ba jarumin ?anena? to yau Aunty ka ce a gabanka ba gizo ba kuma ba mafarki ba."

Cikin Waga murya ya ce "Da gaske Aunty ke ce yau a ku sa, da ni? ya yi wani irn tsalle ya rungumeta yana ta faWin na yi matu?ar kewar ki, don Allah kar ki sake yin ni sa, da ni" hawaye ke zubar ma sa sosai.

Da ?yar Sufiyan ya raba su sannan ta kalli Idiris ita ma da hawayen a fuskarta ta yi murmushi ta ce "A fuska dai kamar ka girma amma a zahiri har yanzu kai Win yaro ne."
"Aunty me na yi kuma yanzu."

"Haka ya dace ka tarbe ni a waje kuma tsaye sannan ba ka ganni da mutane ba halan?"

"Ki yi ha?uri Aunty Waukin ganin ki ne ya sanya na manta duk abun da zan yi" kallon duk mutanen gurin ya yi, ya gaida su, sannan ya shiga cikin gida da gudunsa yana faWin "Mama Baba ku fito wallahi yau Auntyna ce ta zo da gaske."

Mama ta fito daga kitchen tana faWin "Idan ka gama shirmen naka to ba ni aiken da, na yi ma tun ban haWa ka da Malam ba yanzu."

"Wallahi Mama yau ba shirme ba ne, da gaske nake Aunty ce ta zo da wasu mutane masu yawa."

Ran Mama ya fara Saci saboda dama ya saba yi ma ta irin wannan wasar musamman idan ta aike shi ya yi shirme, cikin Sacin rai ta ce "Ka san Allah Idiris ka shiga hankalin ka."

Kafin ta rufe baki ta jiyo sallama ?ofar shigowa gidan, muryar da ba za ta taSa manta wa ba a rayuwa ce ta ji yau, sai dai fuskar ce ta sauya ma t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a saboda ta ?ara haske ta yi matu?ar kyau sosai.

Da sauri ta ?arasa gurin ta tana faWin "Da gaske ke ce ?ata" nan take ta fara hawaye ba shiri ta rungume ta a jikinta tana faWin "Ina kika shiga me ya sa, ba ki dawo gurinmu ba?"

?aga murya ta yi da ?arfi tana kiran Baba Malam "Malam ka fito yau dai da gaske ?ar mu ta dawo gurinmu."

Baba Malam ba ko hula a kansa ya fito yana faWin "Haba don Allah da gaske kike" yana ?arasowa shi ma suka haWa idanu da ita da sauri ya je gurin ta "?ata ke ce da gaske don Allah, ina kika shige ne haka?"

Shi ma rungumar ta ya yi yana ta kuka, Salim da tun Wazu suna gurin shi ne ya raba su, sai a lokacin suka lura da mutane a gurin, Baba ya ce "Ba za yi man ba ya ni ba, kice bake ka Wai bace?"

Cikin muryar shagwaSa irin wace ta saba yi ma sa, ta ce "To ai baku ba ni wannan damar ba."

Baba ya girgiza kai ya ce "Halin dai na ki na nan ?ata" sannan ya yi masu iso zuwa tsakar gidan aka shimfiWa manyan tabarmi.

Baba ya sa Idiris ya je siyo lemu mai sanyi da ruwa, ita kuma Mama ta kawo masu cincin da samosa wanda ta gama yanzu na siyarwa, duka ta juye masu, kana kallon fuskokin su ka san suna cikin matu?ar farin ciki.

Samir yana ?o?arin cewa "Ai da kun barsu saboda duk muna da su a mota" kafin ya ?arasa abun da yake son faWa da sauri Sufayya ta Webo cincin ta zuba ma shi a baki, dole ya gaza ?arasa maganar ya yi shuru suna haWa ido ta watsa ma sa harara, duk wanda ke gurin ya fahimci dalilin ta na yin haka amma ban da Malam da Mama su hankalin su ba ya ma gurin suna can suna shawarar abun da za'a dafawa ba?i.

Sufayya ta je gurin Malam ta kwanta a kan ?afafun shi, da sauri Aunty ta ce "To uwar son jiki."

Mama ta yi murmushi ta ce "Ki kyalesu kawai in dai tana ganin Malam a zaune to fa tabbas sai ta kwanta a jikinsa kuma shi ne ya ko ya ma ta hakan."

Malam ya ce "Ai sai ku yi kuma daga zuwan yarinya ko hutawa ba ta yi ba kin fara saka ma ta idanu so kike ku fara diramar yanzu, kinga ?ata kar ki koma kansu ba ni labarin dalilin da ya sa, ba ki dawo gurinmu ba duk tsawon wannan lokacin?"

Cikin raunin murya ta ce "Baba na yi ta yun?urin zuwa amma sai nake ganin kamar za ka sake korata kuma kamar tunanin ku a kaina har yanzu yana cikin ranku, shi ya sa ko na yi yun?urin zuwa sai na ji tsoro na fasa."

Baba ya ce "Allah sarki ?ata ai ko sati biyu ba ki yi, da tafiya ba gaskiya ta bayyana, ashe duk abun da ya faru shirin Hajiya Hajara ne da Sa'idu da ?arta Asiya, ni kuma na gaza yin komai ne saboda aikin asirin da ta yi man, ?ata na ?ara yarda asiri ba wanda ba ya kamawa shi ya sa a lokacin duk na watsar da ku."

"Bayan kin tafi da sati Waya labari ya zo mana cewa ?an fashi sun kama Sa'idu sun yi ma sa duka sosai har ya samu karaya sannan sun tafi da duk abun yake hannunsa."

"Ai kuwa lokacin ne Hajiya Hajara ta ce "?arya ne so yake kawai ya gudu da dukiyar ga ba ki Waya, nan fa ita da Asiya suka rin?a fallasa irin abubuwan da suka yi, suna faWin yanzu so yake duk wahalar da muka yi, ya ta shi a banza."

"Shi fa aikin kawo kwarto kawai muka sanya shi amma duk wani zuwa gurin boka ye mune masu yi ?auyuka kala kala kuma duk da kuWi na, bai fa san yadda na sha wahala ba kafin asa mu asirin da ya kama Malam, ita ba?ar matar sa da ta?i barin gidan duk wahalar da nake bata, ni ce na yi asirin da ya raba tsakanin ta da Rahma shi ya sa bata goyi bayanta ba lokacin da ake zargin ta."

"Amma shi ne yake son cin amanar mu, ko fa gurin da zai je ya siyar da Rahma da taimakona ni ce, na ba shi kuWin mota, kuma ni ce nan fa na yi sanadin kashe Wan Malam ?arami, yana nufin yanzu ya siyar da ita shi ne yake son ya gudu da kuWin to wallahi bai isa ba."

"Ba su san duk abun da suke faWa ba a kan kunnemu ni da Mama duk mun ji sannan kuma lokacin ne hankalin mu ya dawo jikinmu har ina mamakin yadda na auri wannan matar, a take na fito na sha?i wuyanta har sai da Mama ta ga cewa da gaske zan iya kisan kai hakan ya sa ta nemo jama'a waje da ?yar aka kwace ta daga hannuna."

"Sannan na ce sai ta sanar da ni gurin da suka siyar da ke azaba ya sa ta sanar da ni a nan gurin na yi ma ta saki uku sannan na haWa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login