Showing 63001 words to 66000 words out of 123822 words

Chapter 22 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3441

da dama can zamanmu yafi ?arfi musamman su Aunty shi ya sa muka yi shawarar kawai ita ma ta je can, ta cigaba da karatun, Allah dai ya sa mun yi shawara mai kyau Dady."

Dady Ahmad ya ce "Ma sha Allah yarana sun girma sun fara tunanin manya, to ina fatan Allah ya yi maku albarka."

Aunty ta ce "To sai ku sanar da ?ar ta ku, ta ko yi cire wannan ?aton hijab Win, kafin ta fara zuwa makaramtar."

MurguWa baki ta yi, ta ce "To fa ?an sa ido sun fara sakaman idanu tun a gida, to ba zan cire ba idan na je a haka ki ce, su koro ni ehee."

Aunty ta ce "Sai na matse bakin marar kunya yanzun nan."

Momy Aisha ta ce "Idan bama kusa kenan, ai yarinyata gaskiya ta faWa ba zata sauya yanayin ta saboda wata makaranta can."

Kwana biyu Rahma wace ta zama Sufayya yanzu saboda shi ne asalin sunan ta, tana cikin farin ciki sosai kullun sai Yayunta sun fita da ita ganin gari, suna bata kulawa sosai."

Su Dady sun kira Kaka Alhaji, sun sanar da shi cewa nan da wata biyu Sufayya za ta koma Germany ta cigaba da karatun ta a can.

Kaka Alhaji ya ce "Ma sha Allah ita Sufayyar ce za ta je karatun koh, kuma nan da wata biyu komai zai kammalu koh? to ma sha Allah ai haka ake so Allah ya sanya alkhairi" suka amsa da ameen Alhaji.

An yi magana da Kaka yau, safiya na yi kowa na shirin komawa gidansa cikin satin suna ta firar su, Sufayya ta haWa masu kayan ciye ciye tare da taimakon ?an uwanta ta je jikin ?afafun Momy Saratu ta kwanta.

Aunty har ta fara mita tana cewa "Wai ke, ba ki iya zama da kan ki sai kin kwanta jikin mutane kamar wata mage?"

Momy ta ce "Yau na ga ikon Allah amma dai na ga kamar ba ajikin ki, ta kwanta ba koh?"

Sufayya ta ce "Ni dai don Allah Momy idan za ku tafi ku tafi da ni don idan ku ka bar ni, a gurin matar nan kafin wata biyun su yi na je makaranta mitar ta, ya gama illata ni."

Muyar Kaka Alhaji suka jiyo yana faWin "Kwantar da hankalinki matata, ni da kaina zan Wauke ki kafin wani abun ya same ki don na ga wannan Aunty ta sanya maki idanu sosai."

Sannu da zuwa aka shiga yi masu, shi da matar shi Baba Kulu, bayan sun huta Dady Munir ya ce jiya kuma mun jima muna waya amma ba ku sanar damu zuwan ku ba."

Kaka Alhaji ya ce "Ai ka san tafiya zuwa take to ko yanzu zuwan ta yi, ya kama ne dole sai mun zo, shi ya sa."

Dady Ahmad ya ce "To Allah dai ya sa lafiya Alhaji?"

"Lafiya ?alau biki dai muka zo kuma muna nan har sai angama komai."

Dady Suraj ya ce "Ma sha Allah wa zai yi aure halan Alhaji?"

Kaka ya ce "Kamar ya, kuna nufin ba ku sani ba? to auren Sufayyatu muka zo kuma muna nan sai an yi komai a kan idonmu tukunna."

Sufayya ba ta san lokacin da, ta sa ki dariya ba ta ce "Wallahi Kaka rikicin tsufa ya fara kama ka shi ya sa, su Yaya ke ta ba ku shawarar ku wuce kawai musha gumba."

Dady Ahmad ya ce "Amma Alhaji zancen karatun ta muka sanar da kai ba aurenta ba."

"Kai rufe mun baki can ai tun da ku ka iya sama mata makaranta har wata ?asa ai kuwa kun shirya aurar da ita kenan."

"Don haka wallahi ka ji na rantse in dai har za ta je makaranta nan da wata biyu to ku sani lalle za ta yi aure kafin wata biyun, ta je da mijin ta idan kuma ba haka ba to a fasa zuwa karatun kawai."

"Kai bari ku ji ko fasa karatun aka yi sai kun aurar da ita saboda ita ?a mace ce, ba na miji ba lokacin ta kaWan ne, yanzu fa idan ba manta wa na yi ba shekarunta sha tara."

"To kallon me za ku tsaya yi mata, don haka komai za ta yi, ta yi shi Wakin mijin ta, na gama magana fa?at."

Sufayya da ke jikin Kaka Kulu har ta koma zaune sai hawaye ke bin fuskarta, kallon kowa take, nan ta tuna da maganar da ?an uwan ta, sun taSa sanar da ita cewa duk maganar da Kaka ya yanke to ba mai yi ma shi musu magana ta zauna kenan.

Ta na tuna hakan ta ?ara sakin wani sabon kukan ta ce "Na ro?e ka Kaka kar ka, yi man haka na yi al?awarin ina gama karatun zan yi auren tun da shi ka ke son, na yi Win."

Kaka ya ce "Da yake ke kike da rayuwar ki a hannunki koh."

Za ta sake magana kenan Aunty ta ce "Ke Sufayya" da ?arfi har sai da ta razana saboda tsawar.

"Kaka Alhaji na magana kina yi ma shi musu, to ki sani ko yau ya ce za'a Waura auren ki ta zauna, don haka ki dawo hayyacin ki."

"Kuka take sosai ta ce "Ba musu nake yi ba ha?uri nake ba shi, amma don Allah ku yi ha?uri ba zan sake ba" gefe ta koma kamar wata marainiya.

Kaka ya ce "Yanzu dai duk ba wannan ba, ba tare da Sata lokaci ba ki sanar damu wanda ki ka zaSa a matsayin mijin ki daga cikin ?an uwan ki?"

"Sanin kanki ne duk'kan su suna son ki sosai, to don haka yanzu zaSi ya rage na ki, ki sanar damu ina da tabbacin akwai wanda ki ke so a cikin su."

"Kuma ina son kar ki ji kunya ko tsoro ?an uwan ki suna ?aunar junan su sosai don kin zaSi Waya daga cikin su hakan ba zai kawo rabuwar kansu ba in sha Allah."

"Kin ga da ace kece na namijin, su kuma mata da sai duk ki aure su ko?"

Hankalin Sufayya a matu?ar ta she, take kallon Kaka, duk sanyin AC gurin amma ita gumi take.

*WATA ?ADDARA*
*ANOTHER DESTINY*
By
*SUWAIBA M AMIRU*
(?ar gatan mama)
' *PAGE* 4?? 0??
Shuru ta yi babu alamar za ta yi magana haka ma mutanen parlorn ba wanda ya yi magana daga cikin su, sai can Kaka Alhaji ya ce "Da ke nake magana fa, to ku iyayenta ku yi ma ta magana ko za ta bamu amsar da muke bu?ata."

Dady Ahmad ya ce "?ata ki yi magana kina ji Kaka na jiran amsar ki."

Ko yanzu kamar ba, za ta yi magana ba har sun fara tunanin ko, ba ta jin maganar da ake yi ne, sai can ta Waga kai duk fuskarta ta ji?e da hawaye, ta kalli duk Yayunta sannan ta ce "Ni na bar muku zaSi dukan su ?an uwana ne ina da tabbacin duk wanda ku ka zaSa man daga cikin su zai kula da ni sosai in sha Allah."

Ta na gama faWar hakan ta rufe idanunta da ?arfi hawaye na ta fita ta na jin wani ?ona a cikin zuciyarta.

Salim Sufiyan Samir duk'kan su idanunsu sunyi ja sosai suna jin zafi ?asan zuciyarsu saboda hawayen da suke ga ni daga cikin idanunta da kuma tsantar damuwar da suke ga ni atare da ita, ko wannen su, ji yake kamar ya rungume ta ya yi ta lallashin ta.

Kaka Alhaji ya ce "To kun ji, yanzu dai ku muke jira mu ji wa za ku zaSa mata ku iyayenta."

Dady Suraj ya ce "Ai mun baku wannan damar Alhaji duk wanda ku ka zaSa ya yi."

Kaka ya ce "To ni kam iya sanina ba maganar auren ta, ya taSa yin ni sa ita da Samir? to don haka ina ga kawai Samir shi ne mijin ta ina fatan ba wani mai ja a kan haka."

Duk'kan iyayen su ka ce "Bamu da wani ja, ubangiji ya sanya alkhairi a cikin auren."

Da sauri Samir ya Wago kansa da alamar razana ya kalli ?an uwansa Waya bayan Waya, zai yi magana kenan ?an uwansa suka dakatar da shi ta hanyar mi?a ma shi hannu su gaisa.

Suka ce muna ta ya ka murna Wan uwa, shi dai kallon su kawai yake, ya sake yun?urin magana Sufiyan ya dafa hannunsa shi ma Salim haka dole ya yi shuru.

Dady Suraj ya ji gurin ya yi shuru ya ce "?ata kin ji hukuncin da muka yanke ko?"

Shuru ba magana ba amsa kamar ma bata ji abun da ake faWa ba, Dady ya kalli Momy Aisha ya ce "?an girgiza ta kamar bata jinmu."

Momy ta girgiza ta firgigit ta mi?e ta ce "Na am Momy kina magana ne?"

"Me ya sa kina yarinyar kike son yawan tunani ?ata za ki iya kamuwa da wata matsalar fa, tun Wazu ana ta magana amma kamar baki tare damu."

"Shin kin ma ji wanda muka zaSa maki kuwa? to bari in sake maimaita maki mun yanke Samir ne mijinki in sha Allah."

Da sauri ta Waga kai ta kalli Momy sannan ta kalli gurin da yayunta suke zaune sai kawai ta sun kuyar da kanta ?asa jikinta na rawa, hawayenta ba su daina zuba ba.

Cikin sar?ewar murya ta ce "Shi ke nan momy na gode Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi, amma idan ba damuwa zan iya tafiya Waki an gama da ni?"

Kaka ya ce "A za ki iya tafiya amma ki sani auren zai ka san ce nan da sati biyar kin ga lokacin ya rage saura sati uku kenan ki fara zuwa makaranta."

"To Allah ya kai mu, tana faWar haka ta yi yun?urin ta shi amma ina, ta gaza kamar wata ?ar maye sai jin kanta take yana juya mata, da?yar ta mi?e tabar gurin.

Kaka ya ce "Ku ma duk za ku iya tafiya yanzu, kuma kufara shirye shiryen bikin tun yanzu."

Samir na barin gurin Wakin Sufayya ya wuce yana bugawa ta ce "A buWe ?ofar take" tana nan kwance ko motsi bata yi ba, ya ce "Ko nazo lokacin da bai dace ba ?anwata?"

Mi?ewa ta yi zaune ta ce "Me ya sa, ka faWi hakan?"

"Saboda na ga kamar kina bu?atar yin bacci."

"Ka taSa ganin ina bacci irin wannan lokacin? kawai dai na Wan kwanta ne saboda kaina da na ji yana Wan ciwo amma na san zai daina in sha Allah."

"Haka ne ta bari na tafi kawai har ki samu sau?i kar na cika ki da surutu, dama magana na zo mu yi amma na ga kamar ba za ki iya ba yanzu."

"Kana tunanin ni Win raguwa ce da ba zan iya jure wannan Wan zafin ciwon ba? ka yi maganar ka ina jinka."

"Shi ke nan ?aunata dama ina son na san wannan hukuncin da aka yanke ya yi maki kuwa, ma'ana har yanzu kina jin son aurena?"

"Don Allah kar ki Soye man komai na yi maki al?awari duk abun da kike so shi zan yi maki ni na san hanyar da zan biyo ma iyayenmu in sha Allah, ni dai bana bu?atar ganin ki cikin damuwa ?anwata."

"Yaya kenan ni kam ba ni da damuwa da wannan hukuncin sai dai idan kai ne, ke da matsala a kan hakan wata?il ka sauya tunaninka a kaina in kuwa haka ne ka sanar da ni a kan lokaci don Allah."

Da sauri ya rufe mata baki "Don Allah ki dai na faWar haka ki sani ko da ace mutuwa na yi, na dawo ba zan iya dai na son ki ba ?anwata, ke ce rayuwata, kawai dai ina jin tsoron kar ace yanzu baki son wannan haWin namu, amma ina matu?atar ?aunar ki a cikin zuciyata."

Rufe ido ta yi, da sauri ita a tunanin ta, ya ce a haka ne ya fasa auren amma sai ta samu amsa saSanin tunanin ta.

Da ?yar ta ce "Idan kuwa haka ne to, ka dai na ko wane tunanin ka je ka fara shirye shiryen ka."

"To shi ke nan ki kula man da kan ki kin ji ko????? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?"

Yana fita ta ji sam ta fara gazawa da dauriyar da take sai kawai ta saki wani sabon kukan sosai hakan ya yi daidai da isowar Salim ?ofar Wakin nata da ni yar wuce wa.

Da sauri ya shiga ya tarar da ita a parlorn dakin sai faman kuka take, bata ma san mutum ya shigo ba, ya rufe ?ofar sannan ya ja hannunta ya kaita cikin Wakin, nan ma ya sake rufewa, ya zauna kusa da ita ya ce "Meye haka kuma ?anwata, har tsawon wane lokacin za ki Wauka ki na wannan kukan don Allah?"

Da sauri ta faWa jikin shi ta ?an?ame shi tana ta maimaita don Allah ka taimakeni ka yi wani abun wallahi na fara gazawa ba zan iya ba, ka yi shuru ka yi magana mana yayana."

"To me kike so, na ce ?anwata? don Allah ki cire wannan tunanin a ranki saboda ba abun da zai yuyu ba ne, da ace wani ne can da ban, ba Wan uwana ba, to ki sani sai gurin da ?arfina ya ?are ko da kuwa zan rasa raina gurin faWan samun ki to zanyi, amma yanzu ba ni da wannan ?arfin sam ?anwata."

Ta janye jikinta daga na shi ta ce "FaWan yafi ?arfin ka, ko kuwa ka daina so na? ka sanar da ni idan haka ne, ba zan tursasaka ba."

Cikin razana ya ce "Me kike faWa haka? ba na tunanin za ki bar zuciyata ko da a mafarki, bugun zuciyata da naki yake gudana, ina rayuwa ne saboda ke ?anwata, ki sani ba wata ?a mace da za ta samu gurbi a cikin zuciyata bayan ke."

"To idan haka ne ka zo mu je mu sanar da kowa cewa ba za mu iya rayuwa ba tare da juna ba don Allah ka ta shi mu je yayana."

Ta na maganar ta na jan hannusa ta na ?o?arin jan shi su tafi waje.

Zaunar ita ya yi sannan ya kalle ta ya ce yaushe kika sauya ne ?anwata?"

"Iya sani na dake, ki na sadaukar da rayuwarki da fari cikin ki saboda wasu, amma yanzu ga shi lokaci Waya kina son sauyawa."

"Bayan kin san abun da kike shirin aikatawa zai taSa zukatan mutane da yawa don Allah ki fahimce abun da nake son ki ga ne, kin ji ko ?anwata?"

Cikin kuka ta ce "To ni yanzu ya kake son na yi, da tawa zuciyar kenan? ni tun farko da na san ba za su zaSa man kai ba, da na yi magana da kaina, na yi tunanin za su fahimci soyayyata a gareka kai ne masoyina na farko."

"Ko lokacin da na yarda da soyayyar Yaya Samir ai dan ban san ina zan sameka ba, yanzu kuma gamu tare."

"Yadda za ki yi, da zuciyar ki shi ne ki bata ha?uri na san za ta fahimce ki, kuma wani lokacin soyayya ta biyu tafi ta farko ?ar?o."

"?anwata ya kamata ki san cewa Allah bai ?addara za mu, ka san ce tare da juna ba shi ya sa muka rabu tun farko, don haka don Allah ki yarda da Samir, ki ba shi kulawa saboda yana matu?ar son ki shi ma."

"Ba za ki taSa da sanin auren shi ba kuma don Allah ki yi man al?awarin ba za ki taSa barin ya san har yanzu akwai ni a ranki ba."

Kuka suke sosai yama gaza cigaba da magana, ita ma ta ri?e hannunsa sosai kamar numfashinta zai fita.

Suna cikin wannan yana yin suka ji bugun ?ofa, Salim a ruWe yake kallon ?ofar.

*WATA ?ADDARA*
*ANOTHER DESTINY*
By
*SUWAIBA M AMIRU*
(?ar gatan mama)
' *PAGE* 4?? 1??

Cikin razana Salim ya ce "Ki na tsammanin wani ne yanzu?"
Kallon sa ta yi cikin sar?ewar murya ta ce "Yaya me ya sa, ka razana haka? ni fa nafi son koma waye ya ganmu tare wata?il na samu sau?in matsalata."

Cikin Wan Waga murya ya ce "Ki na cikin hankalin kuwa, wai ba ki san abun da hakan zai haifar ba ?anwata? sanadin hakan zai iya lalata wannan zumunci mai kyau, don Allah ki yi shuru."

"Ah ah bana cikin hayyacina na haukace saboda kai."

Girgiza kai ya yi sannan ya je gurin ?ofar.

?ofar ya buWe yana dubawa mahaifiyarsa ya gani wato Momy Aisha, a razane ya ce "Momy ki ce?"

"Way, ba ka so ganina ba halan?"

"Me kike faWa haka ne Momy, me zai sa na ji ban so ganin ki ba?"

Rahma na jin muryar Momy da sauri ta fito daga Wakin ta faWa jikin Momy kuka take sosai da ?yar Momy ta samu ta yi shuru, sannan ta ce "Me ya faru ?ata?"

Kamar jira take wani sabon kuka ya zo mata, cikin kukan take faWar Momy don Allah ki taimake ni wallahi ji na ke kamar zan mutu zuciya zafi take man, Momy idan ban samu yaya ba wallahi akwai matsala sam ba zan jura ba" idanunta sun rufe bata ma sanin abun da take faWa, ganin hakan Momy ta yi saurin rufe mata baki.

"Ki yi man shuru ba na son jin irin wannan maganar daga bakinki, na fahimci komai amma ki sani a wannan gaSar ha?uri kawai za ku yi daga ke har shi yayan na ki."

"?ata Yayunki duk abu Waya ne, Samir zai kula dake kamar Salim ina da tabbacin za ki yi farin ciki sosai in sha Allah."

"Sannan a matsayina na uwa ina son ki yi man al?awarin ba za ki sake haWuwa da yayanki a irin wannan yanayin ba, a matsayin masoyinki, kar ki manta yanzu akwai sa rana a kanki don Allah ku ki ya ye kun ji koh."

Ba zan iya ba Momy wallahi ba zan yi maki wannan al?awarin mai girma ba, ki gafarce ni."

Cikin Sacin rai Momy ta ce "Ke nan ban isa dake ba, kike son nuna man koh? shi ke nan na gode sosai."

Murya na rawa ta ce "Ba haka ba ne, ki yi ha?uri in sha Allah zan yi yadda kike so Momy."

"Allah ya yi maku albarka ya sanya farin ciki a rayuwar ku."

***********************
A haka ta kwana zaune da safe har ku san 12:pm bata fito ba kuma Kaka ya hana kowa zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login