Showing 78001 words to 81000 words out of 123822 words

Chapter 27 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3448

ta shi, tana ?o?arin buWe idanunta aikuwa sai ta ga Wakin kamar an sauya mata shi duk an yi ma shi kwalliya an rubuta happy birthday dear Sufayya.

Cikin nishaWi ta mi?e zaune sai ta ga duk families a cikin Wakin cikin tsantsar murna ta ce "Yau birthday Wi na ke nan?"

Momy Aisha ta ce "A mana don haka ki ta shi ki shirya ki fito akwai sauran surprise da Yayunki suka shirya maki har da mu kan mu."

Cikin farin ciki ta diro daga kan gadon har ta manta cewa kayan bacci ne a jikinta kuma ba hijab, da sauri Yayunta suka bar Wakin ta ce "Ke nan su ma Yayuna yau ne birthday Win su ko?"

Duk suka ce "A mana su ma yau ne" haka suka ba ta guri don ta shirya ta fito.

Suna fita ta yi murmushin farin ciki ta ce "A gaskiya ya dace yau tun da kowa na cikin farin ciki na yi ?o?arin sanar da Yaya gaskiyar komai, duk ma abun da zai faru sai dai ya faru amma na ga ji, da Soye ma sa gaskiya."

Da wannan tunanin ta shige wanka...

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
BY
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
'
PAGE 4?? 7??

Bayan ta fito parlorn a fuska kowa ya ganta ya san ta yi kyau amma sai dai wannan shegen ?aton hijab Win kamar na gado na nan a jikinta.

Tana ?arasowa ku sa d???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a su, Momy Aisha ta mi?a mata hannu "Ciro hijab Win nan ki ba ni yanzu" har za ta yi magana Momy ta ce "Kinga alamar wasa ne a tare da ni?"

Ganin yadda Momyn ta haWe rai ba alamar wasa kuma ta duba sauran iyayen ta ga cewa ba mai niyar hanawa hakan ya sa, ba shiri ta cire hijab Win ta bata, gashin kanta da ta yi gammo da shi a take ya walwale dama kuma ba Wan kwali a kan nata.

Babban tashin hankalinta shi ne yau ba duguwar riga ta sanya ba, riga da sikit ne a jikinta na les duk sai ta ji, ta takura sosai saboda dirin surar jikinta duk ya bayyana, da sauri Sufiyan ya kawar da fuskarsa a kanta su ma sauran Yayunta haka.

Cikin sanWa ta fara ?o?arin juyawa ta bar gurin, hakan ya sa Momy Nafisa ta ce "Ina kuma za ki je?"

Murya a sanyaye "?aki zan je na Wauko Wan kwalina" Momy ta ce "Ah ah ba sai kin Wauko ba dawo kawai kin yi kyau a haka, kuma na ga cewa duk mu ne dai to wa kike jin kunya halan? ke ban san me ya sa ba, ko gajiya ba kya yi da zama cikin hijab gida da waje" ita dai shuru ta yi bata sake cewa uffan ba amma dai yau malama Rahma jinta take kamar tsirara.

Haka suka cigaba da gudanar da shagalin su basu gayyato kowa ba sai su Kaka da matarsa da nazo tun jiya amma ita bata sani ba sai yanzu, duk'da tana jin ta a takure amma ta yi matu?ar farin cikin ganin su.

Duk wanda ke gurin ya yi mata kyau ta sannan ta yanka cake wanda aka ?awata ya yi matu?ar kyau, su ma Yayunta sai ta dage sai an kawo masu na su cake Win sun yanka tun da su ma yau ranar su ce, dole haka akabi umurnin ta su ma suka yanka.

Dady Ahmad ya ce "?ata komai na ce kice ameen kin ji ko?" ta ce "To Dady."

Ya ce "Allah ya sa shekara mai zuwa ko da, za mu haWu kamar haka wajen murnar cika shekarun ki 21 ya zama da jikana ko jikanyata, ma'ana mata ko abokina lokacin."

Da sauri ta kalle sa cikin razana har sai da wayarta ta faWi ?asa, shi ma Sufiyan irin halin da ya shiga ke nan sai dai ba wanda ya fahimta saboda yana can tare da ?an uwansa guri Waya, ?an uwan su kaWai suka fahimci na shi tashin hankalin, ba su ce dashi komai ba sai girgiza kai kawai da suka yi, a ransu suna mamakin ke nan har yanzu bai gyara zaman su ba.

Dady ya ce "Lafiya kuwa ?ata, ya na ga kamar kin razana?" Ta ce "Lah Dady ba haka ba ne waya tace dai ta faWi ?asa shi ya sa."
"Ok na ji yanzu dai ki ce ameen, gumi ne ya fara fito mata ta cikin kai duk sanyin parlorn, cikin rawar murya jikinta na kyarma ta ce "A A ameen Dady."

Dady Nura ya ce "Kuma surprise na gaba shi ne yau duk'kanmu a gidan nan za mu kwana sai gobe mu tafi gidajenmu."

Ku san a tare ita da Sufiyan suka ce "Nan gidan kuma me ya sa too?" Cikin razana suka yi tambayar.

Sai da duk suka kalle su sannan Momy Nafisa ta ce "Ya na ga kamar ba ku yi farin ciki ba?"

Sufiyan ya ce "Ah ah ba haka ba ne dama mamaki kawai abun ya ba ni ?anwata ta jima tana cewa mu yi maku magana ku kwana gidan nan ko da sau Waya ne, ni kuma na ce sam ba za ku amince ba, sai kuma ga shi yanzu cikin sau?i kun cika mata burinta."

Momy Aisha ta ce "To ai mun sanar da ku yau aikinmu shi ne mu sanya ?armu farin ciki saboda yau ranar ta ta ce."

Haka dai duk kowannen su ya fara shirin shiga Wakin da zai kwanta ita ma Sufayya da sauri ta shige Wakinta, ba ta jima ba sai ga Sufiyan ya shigo, da sauri ta kalle shi ta ce "Yawwa Yaya kamar ka san kai nake jira."

Ya ce "Na san kina jirana ai shi ya sa, na shigo na san son kike ki yi man tambayar me ya sa, na sanar da su hakan saboda za su iya gano ba Waki Waya muke kwanciya ba ko?"

"To kar ki da mu, in sha Allah ba za su gane ba, tun da kinga kwana Waya ne za su yi sai dai kuma ya zama dole yau mu kwana Waki Waya.

Ta buWa baki za ta yi magana ya ce "Kar ki da mu kuma kar ki razana ki sani ba zan taSa karya al?awarin da na Waukar maki ba in sha Allah, ba zan taSa kallon ki a matsayin matata ba har sai kin fara jina a zuciyarki a matsayin mijinki, don haka ki kwantar hankalinki."

"Ki je ki yi kwanciyar ki a kan gado ni kuma zan kwanta a kan kujera" cikin ?aguwa da zancen na shi marar yankewa ta ce "Koma haka ne sai dai ni na kwanta a kan kujera kai kuma a kan gado tun da nafi ka sabo da kwanciyar kujera, kuma ba wannan ba ne maganar da nake son mu yi, amma ka?i barin na yi magana tun Wazu."

"Shi ke nan yi ha?uri na yi tunanin abun da kike son faWa ke nan amma tun da ba haka ba ne sanar da ni mene ne?" yana maganar tare da sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya yi tseren gudu, kana ganin shi za ka fahimci a razane yake.

"Yaya tun da jimawa nake son mu yi wannan maganar kuma jiya kai kace mu bari har zuwa yau, shi ne nake son sanar da kai maganar yanzu"
"To ina jinki ?anwata tun da yanzu mun samu lokaci."

"Yaya don Allah ka yarda da magana ta karka yi mata wata fassara ta daban, Yaya dama dama ummm" haka muryarta ta rin?a rawa kamar wace take a tsorace "Yaya ina son dama ala?armu..... kafin ta ?arasa ta ji saukar mari a kan fuskarta har sau uku, tana Wagowa ta ga ashe Aunty mahaifiyarta ce, cikin razana su biyu ke kallonta."

Ashe ko da suke wannan maganar ?ofar Wakin bata rufuba sosai, Aunty ta zo za ta wuce kawai ta ji suna wannan maganar duk'da ?asa ?asa suke maganar amma ta ji komai hakan ya sa ta shiga Wakin ta wanke ta da mari, kafin Rahma ta gama da wowa daidai Aunty ta ja hannunta har cikin babban parlor ta jefar da ita.

Ta je ta ciro wayar chaja har uku ta haWa su guri Waya tayo kan Sufayya da su ganin haka da sauri Sufiyan ya shiga tsakani ya ce "Don Allah ki hukunta ni wallahi ni ne mai laifin ba'ita."

Aunty ta ce "Waya sanar da kai cewa kaima kyaleka na yi bari na yi, na gama da ita tukunna na dawo kanka."

Ganin da gaske gadan gadan ta yi kanta hakan ya sa da sauri ya je ya faWa jikin Sufayya ya yi mata rumfa duk dukan da ta yi mata sai yake tsayawa a jikinsa ganin haka ya sa ta yi ?o?arin cireshi daga jikinta saboda a daina dukansa amma ta gaza.

Sufayya sai kuka take ta yi kamar ranta zai fita zuwa lokacin kuma kowa ya fito ya zo gurin da suke.

Kaka ya ce "Zainab kar ki sake dukan su kuma ki sanar da mu laifin su mu ji."

Ita ma kukan ta fara hakan kuwa ya ?ara Waga hankalin Sufayya da Sufiyan sosai, ganin cewa sune sanadin wannan kukan nata, Aunty ta ce "Baba Alhaji yaran nan sun muna furcemu sun yaudaremu sannan sunci amanar yardar da muka yi da su."

Da rarrafe Sufayya ta je gurin Aunty ta ri?e ?afarta tana kuka ta ce "Don Allah kar ki ce haka ki daina kuka na tuba wallahi na yi maki al?awarin zan gyara."

Cikin tsananin Sacin rai Aunty ta dam?o gashin kanta da ?arfi sai da Sufayya ta yi ?ara saboda azaba, ta ce "Har kina da kwarin guiwar zuwa ku sa da ni, ba ni ha?uri duk irin abun da kika yi saboda kin raina ni koh?"

Kafin Sufiyan ya ?arasa gurinsu har Salim da Samir sun je gurin da ?yar suka cire hannun Aunty daga kan Sufayya, aikuwa da sauri ta Suya bayansu jikinta nata rawa, ta rirri?e su sosai.

Sufiyan yana kuka ya ce "Aunty na ro?eki don Allah ki daina hukunta ta wallahi duk laifi na ne, wannan duk shiri na ne, kafin ya rufe baki ta wanke shi da mari shi ma.

Kowa a gurin ya yi mamaki sosai saboda sanin yadda Aunty ke son yaran ba mai sa masu hannu da sunan duka matu?ar tana ku sa, ita ma kuma bata sanya masu hannu tun suna yara.

Ta kalli Kaka ta ce "Baba wannan yaran da kake ga ni, ba zaman aure suke ba."

Duk suka zuba mata ido da alamar tambaya, Kaka ya ce "Ban gane ba shin sakin ta ya yi bamu sani ba ko kuwa?"

"Da ma ace sakin ta ya yi zai fi sau?i da irin zaman da suke yi yanzu, Baba ba su fa taSa haWa ko da Waki Waya ba balle kuma shinfiWa Waya ko wanensu Wakinsa daban."

Momy Saratu ta zo gurin Aunty da sauri ta ce "Kuma shi ne kike hukunta Sufayya a laifin da ba nata ba, ta juya gurin Sufiyan ta rin?a wanka ma sa mari tana cewa "Irin yaudarar da za ka yi mana ke nan ina ka koyo wannan halin na yi imani ba laifin Sufayya ba ne saboda kai ne namiji duk hanyar da kabi da ita nan za ta bi."

Ganin haka ya sa Sufayya ta ?ara razana sosai ta sake ri?e Yayunta sosai jiki nata faman yi mata rawa.

Can kuma Momy ta Wan yi shuru ta ce "?an da kata na tuna wani abu yanzu, me ya sa tun farko ba mu tsaya mun yi nazarin maganar Sufayya? ranar bikin su ta taSa sanar da mu cewa tana ganin kamar ya dai na son ta, amma muka Wauki zancen wasa ashe da gaskiyar ta."

Momy ta ri?o shi da ?arfi ta ce "ka sanar da mu yanzu, shin da gaske ka daina son ta ne, hakan ya sa kake hukunta ta haka, ko kuwa kana da wani dalilin da ban?"

Shuru ya yi yana ta zubar da hawaye, Sufayya tana ?o?arin yin magana sai kawai ya girgiza mata kai alamar ta yi shuru, saboda ya san idan yabar ta ta yi magana wutar za ta ?ara ruruwa ne.

Dady Munir ya zo ku sa, da su Samir ya ce "Sufayya fito daga bayan su zo nan ku sa da ni" jikinta na rawa ta je gurin shi, ya Kalle ta sannan ya yi murmushi cikin muryar sa mai sanyi ta rashin son hayaniya ya ce "Na gaza yarda da abun da na ji yanzu saboda na gama ba ki duka yarda ta."

"Don haka yanzu ki sanar da ni cewa duk abun da ake faWa ba gaskiya ba ne" shuru ta yi tare da sunkuyar da kanta ?asa tana zubar da hawaye.

Ganin haka ya sa ya rufe idanunsa sannan ya buWesu, ya ri?o hannuta ya ce "Mu Wauka cewa da gaske mijinki ne ya kawo wannan shawarar, amma kuma akwai hanyoyi da dama da mace ke bi don sauya namiji, ki sanar da ni, ke a matsayinki na mace wace hanyar ki kabi don sauya Na ki mijin?"

Nan ma bata yi magana ba steel kanta na ?asa ta gaza Wagowa su haWa ido, "Yanzu Dady Ahmad ya gama yi maku fatan zama iyaye kafin wata shekarar, ashe ku ba ku ma shiryawa hakan ba."

Da ?arfi ya saki hannunta sannan ya nuna ta da yatsa ya ce "Ki sani yanzu na janye imanina a kanki, tabbas wannan ba laifin kowa ba ne sai na ki."

"To ki sani daga yanzu har zuwa lokacin da za ki gyara kuskuren ki kar ki sake kallona a matsayin mahaifinki" ya kalli Aunty ya ce "Wuce mu tafi ba zan taSa zama gidan waWan da mala'ikun rahama ke tsine masu ba."

Muryar Sufayya har ta fara dishewa saboda kuka haka tabi su tana magiya tana ba su ha?uri, amma suka ture ta gefe Waya suka fi ce, a nan ta faWi dur?ushe kukan ma ya daina zuwa sai na zuci duk ta yamotse lokaci Waya.

Dady Suraj ya kalli Momy Saratu ya ce "Ke Kuma zaman me kike? ki ta shi mu tafi ni ma banga abun da zan yi a wannan gidan ba, gidan da Allah ke fushi da mutanen cikin."

Sannan ya kalli Sufiyan ya ce "Ina fatan ka ji dai abun da Dadyn ku Waya ya faWawa ?anwarka koh? to ni ma hakan take a gurina daga wannan lokacin karka sake kallona a matsayin mahaifi" yana gama faWar hakan suka bar gidan

Dady Nura cikin Sacin rai ya ce "Ku zo nan" jiki ba kwari suka ?arasa Ku sa da su, ya kalle su ya ce "Yanzu kuna ganin abun da, Ku ka yi kun yi daidai ke nan? ba zan iya cewa ga mai laifi a cikinku ba, saboda duk'kan ku masu laifi ne."

"A gaskiya ranmu ya yi matu?ar Saci, don haka ku sani kamar yadda sauran iyayenku suka faWa muma haka za mu gaWa shirinmu da ku shi ne gyara wannan kuskuren na Ku."

Cikin rawar murya Sufiyan ya ce "Don Allah Dady ku yi ha?uri karku yi fushi da mu."

Kaka ya ce "Sufayya saboda na matsa sai kin yi aure sannan za ki zo makaranta shi ne yanzu kin ka nuna man iyakata koh? Ke nan idan na san wata ban san wata ba koh? to ai shi ke nan na gode."

Ita dai Sufayya bata ma iya magana ko kuka, sai dai faman girgiza kanta take alamar ba haka ba ne, haka su ma duk suka ta shi da niyar tafiya, Sufayya ta yi saurin ri?e ?afafun su Momy tana girgiza kai alamar ban ha?uri.

Momy Aisha ta ce "Kamar yadda ba mu isa da ku ba har kun ka bamu kunya irin haka, to kuma ba za ku, ne mi ko wace alfarma a gurinmu ku samu ba" haka su ma sun ka fizge ?afarsu suka fita.

Kaka kulu har ta kai ba kin ?ofar fita ta ce "Kai Salim Samir ku ta so, mu tafi zaman me kuke yi a nan?"

Haka dai suka ta shi ba dan ransu ya so ba saboda yana yin da ?an uwan Na su suke ciki ya sanya su ma suna jin wani ?ona a ransu, idanunsu sun yi matu?ar yin ja, a raunane suka kallesu suka ce, ku yi ha?uri kowa da kalar jarabawar sa."

Sufiyan idonsa a rufe ya ce "Ba komai ?an uwa ku ta shi, ku tafi karku zama masu laifi kamar iri na, na zama mai laifi sannan na sanya ana ganin laifin ?anwata."

Ita dai Sufayya bata ma san abun da suke faWa ba, haka su ma suka fita aka barsu su biyu kawai....

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' PAGE 4?? 8??

Ba wanda ya motsa daga in da yake, sai can bayan wani Wan lokaci Sufiyan ya yi ?o?arin ta shi ya nemo ruwa mai sanyi sosai ya bata ya ce "Daure ki sha kin ji."

Ba musu ta karSa ta sha, shi ma ta zuba ma shi ya sha, sannan ta Wan kwanta a kan kafaWarsa suka jin gina jikin kujera, cikin raunin murya ta ce "Yaya ni mai laifi ce mai saSo ce don Allah Yaya ka yafe man, sannan ka daure ka taya ni bawa kowa ha?uri har da su Kaka" magana take hawaye wasu na bin wasu haka suke zubar mata.

Ya ce "Me ya sa kike Worawa kanki laifin da bana ki ba, na san tabbas a lokacin da na nuna ina bu?atar ka sancewa dake a matsayin mata ba za ki taSa gujewa hakan ba, Na sanza ki yi ?o?arin sauke nauyin da ke kanki."

"Sai dai gaskiya bana bu?atar mu gina rayuwarmu a kan iya biyayya kawai na fi son mu fara rayuwa ne a kan tsantsar soyayyar juna, saboda na gama yarda cewa tabbas akwai wanda kika yi wa biyayya wanda ya sanya ki amince wa da aurena."

"Don haka ki natsu ?anwata komai zai zama daidai in sha Allah, duk za su yi ha?uri kuma za su yafe mana" a haka dai ya yi ta lallashin ta har ya samu ta Wan natsu.

A nan gurin suka kwana a wannan ranar duk family's ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login