Showing 54001 words to 57000 words out of 123822 words

Chapter 19 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3446

ta same su, ta yi mata godiya ta ce "Amma baki ji tsoron ya fi ?arfin ki ba zai iya cutar dake ai."

Rahma ta ce "Ba sai kin gode man ba yi wa kai ne, maganar tsoro kuma a lokacin da mutum ya yi ni yar yin alkhairi tsoro guduwa yake a cikin zuciya."

Matar ta ce "Haka ne kuma, amma kar ki ce, na fiye tambaya me kuke yi a nan zaune ita wannan ?ar uwar ta ki har da cin abinci a rumfar kasuwa?"

"Tana jin yunwa ne shi ya sa, ba za ta iya ha?uri ba, nan kuma da kika ganmu nan ne kaWai muke da shi gurin zuwa, idan kin gama tambayar za ki iya tafiya."

"Ki yi ha?uri idan na Sata maki rai amma ina iyayen ku, su ke?"

Ran Rahma ya fa fara Saci da yawan tambayoyin matar, cikin alamar Sacin rai ta ce "Iyayenmu sun mutu ba sa raye."

"ALLAH sarki to idan ba damuwa ku zo, mu tafi gidana ina da gidan abinci cikin gari kuma a gidan nake yin komai na rayuwata, ku Wauke ni a matsayin uwa."

Da sauri Rahma ta ce "Ni, ni ce uwa kuma uba ga ?anwata ni kuma bana bu?atar wata uwa zan iya kulawa da kaina in sha ALLAH, ku ne irin matan nan masu kai ma Alhazai ?ananun ?an mata koh? to ba inda za mu, na san irin ku."

Subuhanalillah wallahi ni ba haka na ke ba, duk da ni Win mai sai da abinci ce amma na san darajar kaina kuma na haifa ni ma yadda bana son a Sata rayuwar su haka ba zan so na yi sanadin Sata rayuwar wasu ba, amma za mu iya tafiya idan kun ga abun da bai yi maku ba sai ku bar ni, na yarda."

"Na yarda za mu je amma sai idan aiki za ki Wauke ni, saboda ina bu?atar kuWin da zan rin?a biyawa ?anwata makaranta."

"Shi ke nan mu je sai ki duba abun da za ki iya da kan ki."

Gidan abincin babba ne, ku sa da shi akwai wani madaidaicin gida Waki uku ne a gidan, ta ba su Waki Waya daga ciki, ta nada masu aiki sosai kowa da abun da yake, haka su ka fara rayuwa a gurin.

Furaira na zuwa makaranta tun safe Rahma za ta kai ta da kanta da yamma kuma ta je Waukar ta, komai take ajeye shi take sai ta dawo, har Mama mai abinci ta saba da hakan.

Suna zaune da Mama mai abinci ta ce "Rashida Wan zuwan ki gidan nan kin kawo cigaba sosai yanzu costomer ta ko ina zuwa suke, har sai nake ganin kamar bana yi maki adalci bana biyan ki yadda ya dace."

"Ah ah ba haka ba ne, abun da, ki ka yi mana a rayuwa ba zan iya biyanki ba, kin bamu gurin kwana sannan kina bamu abinci, ki sani wannan kuWin ina karSa ne kawai saboda karatun ?anwata ba dan haka ba wallahi ba abun da zai sa in karSi wani abu na ki."

"Don haka kar ki damu, ni bari na tafi Wauko Furaira sai na dawo."

Mi?ewa tsaye ta yi tabar gidan da sauri saboda ta makara kaWan.

Tafi son koda a ke ta shin su, ta na bakin get sam bata son Furaira ta jira ta sai dai ita ta jira....

*PAGE* 3?? 5??
*?ASAR GERMANY*
Kaka Alhaji ne ya yi masu waya akan dole wasu daga cikin su, su dawo Nigeria saboda shi kam ya gaji da zama baya jin motsin su a tare da shi.

Hakan ya sa Dady Suraj da Momy Saratu su ka shirya komawa gida domin bin umunir Kaka Alhaji.

A lokacin a ka nemi Salim a kan wani aiki ?asar Misra amma sai dai sam ba abun da yake iya yi a wannan lokacin shi ya sa, ya ro?i Sufiyan da ya je saboda ya san zai iya duk abun suke bu?ata ka san cewar duk abu Waya su ka karanta.

Da ?yar su ka samu ya yarda zai je amma sai sunyi masa al?awari za su kula da kansu kuma su rin?a shan magani a kan lokaci, tun da dama shi ne mai matsa masu a kan shan maganin.

Sun yarda da sharaWin sa, shi ya sa ya fara shirin tafiyar domin yin aikin Salim, ya je a matsayin Salim Win.

*NIGERIA*
Rahma ta Wauko Furaira sun dawo gida kenan daga bayan su, su ka ji ana ta kiran Furai Furai Furaira suna dubawa Furaira ta ce Ado.

Ku sa, da su yazo ya ce "Furai ina ki ka shiga ina ta neman ki? don ALLAH ki yi ha?uri na ji duk abun da Baffa ya yi maku amma ya gane ya yi kuskure don haka ku zo mu koma komai zai yi daidai."

Furaira ta ce "Ni kam ba inda zan bika ina jin daWin rayuwata a nan ni da Addah, sannan kuma ga karatu na ina yi."

"Kuma dai na ga abun da ke tsakaninmu zancen aure ne, Baban ka kuma ya hana to ba shi ke nan ba?"

"Ni wallahi sai da, ya ce anfasa aurenmu na san ya yi man babban gata don haka sai anjima."

Saurin tare su ya yi, ya ce "Don ALLAH baiwar ALLAH ki bata ha?uri na ga tana jin maganar ki bai dace ta yanke man hukunci ba a kan abun da Baffa ya yi."

"Ka sani duk abun da ta faWa da ni, na fara magana tun farko ni ma abun da zan faWa kenan wata?il har sufi haka don haka kar kama Sata lokacin ka."

Su na shiga Furaira ta ce "Addah ni wallahi da na gan shi har tsoro na ji, ya yi wani iri kamar kafiri duk jiki sar?a ni kam na gode ALLAH da haka ta faru kinga shi ke nan, na huta."

"Dama fa ni ba son shi nake ba, to ni lokacin da, aka ce shi ne mijin da zan aura na ma san so ne, ai ban ni ba?"

Maganarta take kanta tsaye ba abun da ya dame ta, ita kuma Rahma sai faman kallon ta take.

Rahma ta ce "To yanzu kenan kin san mene ne so koh?"

"Ah ah wallahi ban san komai ba kawai dai na ji ?an makarantarmu senior su na firar soyayya amma bayan haka ban san komai ba."

"Shi ke nan daga yanzu kar ki sake zama gurinda ake yin irin wannan firar, idan ba so, ki ke na fitar da ke daga makarantar na aurar da ke ba."

"Du ka shekarun ki nawa, sha biyar fa har ki ke zama irin gurin da ake wannan firar, kin gan ni nan har na gama secondary ba ni da, ko ?awa duk da bana son ki yi rayuwa irin tawa, amma ki ki yaye kin ji ?anwata, duk lokacin abu a yi shi."

IKON ALLAH SU RAHMA GIRMA FA YA SAMU.

"Don ALLAH Addah ki yi ha?uri in sha ALLAH zan ki yaye."

Kwana biyu kullun sai Ado yazo gurin ko da, ba yada lalurar siyan abinci amma Rahma ta ka sa, ta tsare ta hana haWuwar su, da Furaira, dama can ita ma Rahma bata fiye fita gurin customer ba, sai da babban dalili iya kar ta kitchen, furaira kuma ko aikin bata fiye barin tana yi ba.

*GARIN KADUNA*

Dady Suraj da suka shigo Nigeria ba su tsaya Abuja ba Kaduna su ka wuce gidan kaka Alhaji.

Kwana biyu da zuwan su shi ma Dady Munir ya shigo ?asar sam baya cikin na tsuwar shi ya ce Dady Suraj yazo su tafi gidan gona ankira shi dabbobin sun ka mu, da annoba.

Su biyu su ka tafi saboda sauran su na can gurin kula da su Samir.

*********************

Yau ta kasance Alhamis ranar da tana Waya daga cikin ranakun da Rahma ba za taSa manta wa ba, masu haWa kwanukan da customers na gama anfani da su sunyi ?aranci hakan ya sa, ta fita, tana zuwa a kan wata kujera ta ga wata jaka an manta a gurin.

Ta ga kamar tana da mahimmanci a gurin mai ita hakan ya sa, ta buWa jakar ta samu katin mai jakar a ciki ta je gurin Mama mai abinci ta ari wayarta ta samu wani layin ta saka sannan ta kira mai jakar gudun kar ya san inda take hakan ya sa, ta ce sai dai ya yi mata kwatancen gurin da yake ta kai masa.

Bayan ta kai masa ya nemi sanin sunan ta saboda ya ji daWin karamcin ta, haka kawai ta ji zai fa iya neman ta, kuma idan ta sanar da shi sunan da mutanen gurin na sani to fa zai gano ta cikin sau?i, ita kuma a yanzu sam bata son wata mu'amula da irin waWan nan mutanen masu kuWi ko inuwa Waya bata son su haWa.

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Sunana Sadiya, Dady Suraj ya yi mata godiya sosai.

Ta na barin gurin ta wuce makaranta don Wauko Furaira.

Tun da, ta do shi makarantar take jin faWuwar gaba, ta duba duk gurin da take zama jiran ta amma bata nan, da sauri ta je gurin mai gadi ta tambaya ko ya ga Furaira amma ya ce duk an watse ba wanda ya rage.

Gida ta je, ko ta koma da kanta duk da bata taSa yin haka ba, amma ta na zuwa ta tambayi Mama mai abinci ina Furaira?

Mama ta ce "Ba ke kika je Waukar ta ba, ke ya dace na tambaya."

Aikuwa hankalinta ya yi matu?ar ta shi, ku san hauka ta yi gurin neman ta sai can yamma sosai ta dawo amma kamar bata cikin hayyacin ta.

Da gudu Rahma ta je gurin, ta rungume ta, zubewa ta yi ajikin ta nan su ka faWi ?asa jikin Furaira ya yi sanyi sosai kamar ?an?ara, cikin rawar murya Rahma ke tambayar.
"Lafiya me ye faru da ke?"

"Addah yau na gama Exams a kan lokaci na tsaya gurin da nake zama jiran ki, sai ga Ado ya zo, ya ce ke, ki kace ya zo Wauka ta, da fari na?i yarda amma sai ya yi ta rantsuwa ganin kin Wauki lokaci baki zoba har aka watse hakan ya sa na yarda da maganar sa saboda na san baki saba jimawa haka ba."

"Adda wani guri ya kai ni kamar kan gon mashaya ya ce bake kika aiko shi ba kawai ya ga bani da, ni yar auren shi, shi ya sa, ya yanke shawarar Wauko ni ya karSi abun da yake na shi ne, don haka na yarda cikin ruwan sanyi ko inrasa raina."

"Shi ne na ce ko zan rasa raina bazan yarda da wannan ba?in ?udirin na shi ba, saboda Addah ta ce na yi faWa koda da numfashi na ne, na ?arshe gurin kare mutumcina."

"Ah ah ni kam bazan tsaya wani faWa dake ba, amma zan aika ki gurin da na aika iyayen ki, kin yi mamaki koh?"

"To bari kiji ni da Baffana muka shirya komai mune muka yoma iyayen ki ture har su ka rasa ran su don haka ke ma, ki shirya bin su yau."

"Wata kwalba ya buWe, ya matse bakina ya zuba man wani magani sannan ya turo ni waje ya ce, na je na mutu a hankali."

"Addah da?yar na dawo gida, Addah na bada rayuwata a kan mutuncina kamar yadda kika ce, mutuwa zan yi saboda wani zafi nake ji a cikin cikina, Addah zan mutum ba tare da na cika burina ba, amma don ALLAH ke ki yi ?o?arin cika naki burin ina son ki Addah."

A kan kuka muryar Rahma har ta fara dushewa ta ce "ki daina maganar shirme, za ki ta shi, za mu rayu tare ba za ki bar ni, ni kaWai ba in sha ALLAH."

Mama mai abinci ta kallah ta ce "Mama kulaman da ita na samo mota mu je asibiti."

Suna zuwa asibiti Doctor ya ce "Ai gubace kuma ta gama yi mata illah saboda duk ta yanyanka kayan cikinta, sai dai ku yi ha?uri za mu ce."

Wuyan rigar Doctor Rahma ta sha?e ta ce "A yi ha?uri da me kenan, ba dai so ka ke, kace man zan rasa ?anwata ba?"

"Kana Doctor amma ka ke faWar irin wannan kalmar ta cire tsammani a kan majinyaci, to ka sani ?anwata za ta rayu ba za ta bar ni ba."

Kuka take sosai da?yar aka cire hannunta daga jikin Doctor, a she ko da hakan ke faruwa Furaira ta jima da rasuwa.

Rahma ta girgiza ta a kanta ta shi, ta yi magiya ta yi ro?on ta a kan kar ta Sar ta ita kaWai a wannan duniyar, amma ina Furaira ita ma ta barta, Rahma ta ?ara zama marar kowa.

**********************

?agaren Dady Suraj kuwa tun lokacin da su ka rabu da Rahma yake neman ta har ya gaji su ka bar garin, Dady Munir ya koma Germany gurin sauran families, shi kuma Dady Suraj ya wuce Dubai, Momy Saratu kaWai su ka bari a Kaduna saboda nan da sati uku za ta wuce Abuja.

************************

Kwana arba'in da mutuwar Furaira amma kullun Rahma jin mutuwar take kamar sabuwa ta gaza samun farin ciki, Wan murmushin ma da ake gani a kan fuskar ta yanzu sam babu.

Ta daina wani dogon aiki yanzu aikinta bai wuce wanke wanke ba, wata rana kuma ta Wan shiga kitchen ri?a wani abun.

Yau tana zaune cikin gida ko ?ofar waje bata yi ba, ta yi ni sa sosai cikin tunani, Mama mai abinci ta zo da sauri ta na girgizar Rahma ta na faWin.

"Ki ta shi mu gudu akwai babbar matsala ?an bindiga sun ziyarcemu sai ka she mutane suke don haka kizo mu tafi."

"To ki yi sauri ki gudu mana Mama, ni kam ba inda zan tafi saboda sau?i ne yazo man har gida, ni fa na jima da son ka she kaina amma sanin hukuncin hakan a addinina shi ya sa har yanzu nake a raye."

"Ki faWa man don ALLAH me zai sa naji ina da dalilin rayuwa a yanzu ba ni da kowa wanda zan kira nawa sannan komai na ga, ya zama nawa sai wani dalilin ya zo wanda zan ra shi, don haka ki wuce kawai ki ceci ranki Mama."

"Don ALLAH ki daina wannan tunanin, yanzu ba lokacin shi ba ne, na ro?e ki koda sau Waya ne ni ma, ki kalle ni a matsayin ta ki, sannan ba ki san abun da ALLAH yake nufi da ke ba, bai dace da iliminki amma ki rin?a ?o?arin gujewa ?addarar ki ba."

Duk wannan bayanin ta na yin shi tana jan hannunta har su ka je, ku sa da wata ?aramar ?ofa sannan ta SuWe su ka fita.

Gudu take sosai tana ri?e da hannunta har ta fara bawa Rahma tausayi ita ma ta fara gudun da ?arfinta don ta ragewa Mama aiki.

Sunyi ni sa sosai har sun gama yarda da cewa sun goje masu, sannan Mama ta zube ?asa tana mai da numfashi ita ma Rahma haka take.

Mama ta ce "?ata ban san ki ba, ban san daga ina ki keba amma na gama yarda dake sosai, na san ki nada zuciya mai kyau musamman yadda naga kin ri?e ?anwarki Furaira kamar kun fito ciki Waya, wallahi na yi mamaki sosai lokacin da na fahinci cewa baku haWa komai da ita ba, da haka nake son na ro?e ki wata alfarma ni ma don ALLAH kar ki manta da ni."

"Daga nan za mu rabu, ni mutuniyar nijar ce, dalilin da ya sa, ba zan je dake ba, ni ma bajin daWin garin nake ba, duk ?a ?ana sun rasu bayan mutuwar mijina shi ne ?an uwa su ka taso ni gaba shi ya sa, na dawo Nigeria na fara sana'a, yanzu kuma ga wannan al'amarin daya faru dole na koma gida."

Rahma ta ce "To me ze hana mu samu wani gurin sai mu rayu tare koh?"

Cikin raunin murya take magana ?irjinta sai faman bugawa yake, tunanin ta badai ita ma Mama barinta za ta yi ba.

"?ata ba zai yuyu ba wallahi duk hankalina ya koma gida, ?ara ko mutuwar ce ta same ni a ?asata, ke dai ki yiman al?awarin za ki kulaman da kan ki kuma idan ALLAH ya nufi akwai sauran ganawa tsakaninmu in sha ALLAH wata rana za mu haWu kar ki damu."

Da haka ta wuce ta barta nan tsaye ta na tafe ta na waiwayen Rahma har ta Sace mata, wasu hawaye ne masu zafi su ka zubo mata, cikin sar?ewar murya ta ce.
"Kenan ita ma mun rabu."

*PAGE*3?? 6??
Momy Saratu ce cikin mota ta na waya, ga duk'kan alama da Dady Suraj take magana saboda sai faman faWa yake a kan me ye dalilin yin tafiya tun daga Kaduna har Abuja, Momy ta ce.
"Bafa ni ke tu?en motar ba, ka san duk ba zan iya tu?in mota ba, tun daga Kaduna har Abuja, tare da direba na ke, don haka kar ka damu in sha ALLAH lafiya ?alau za mu je."

"Shi ke nan amma za mu rin?a waya dake har na ji saukar ki lafiya sannan zan samu natsuwa."

"Na amince ranka ya daWe."
Ta yi maganar cikin zolaya ta na yin dariya.

RAHMA
Rahma ta ga cewa tsayuwar ba mai yuyu ba ce, hakan ya sa ita ma, ta cigaba da tafiya, ta yi tafiya sosai cikin dajin har ta fara fita hayyacinta ko hanya bata ganewa sosai.

Hakan ya sa har tafito titi bata sani ba, tafiya kawai take idon ta rufe ?afafunta duk sun kumbura da?yar take Waga ?afa.

A yayin da Su Momy su ke tafiyar su hankali kwance ba damuwa ko matsala direba na jan motar cikin natsuwa, sai hango Rahma ya yi idonta rufe duk yadda ya so kwace mata amma hakan ya gagara dole sai da, ya kaWeta.

Momy na waya da Dady daidai lokacin ya ji tana ta salati, hankali a ta she Dady ke tambayar lafiya kuwa.

Momy ta ce "Wallahi mun kaWe yarinya ne bari mu je asibiti za mu yi waya."
Ka she wayar ta yi da sauri su ka Wauki Rahma.
**********************
A lokacin ne haWuwar Momy da Rahma, bayan Momy ta zo gida da ita a bisa umurnin Doctor na cewa abata kulawa sosai, sai ta ga gidan kamar gidansu Yayanta Samir banbancin kaWan ne.

A zuciyarta ta ce "Na koma faWawa gidan masu kuWi kenan, lalle ya zama dole na yi gaggawar barin gidan nan ko ta wane halin."

Sai dai Momy ta?i barin hakan ta faru a bisa bin sharaWin Rahma na sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login