Showing 120001 words to 123000 words out of 123822 words

Chapter 41 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3431

ita ba uwata ba, bayan ta san ina da aure, kuma ta san yadda nake son ki sosai, duk muka haWu sai na yi masu hirar ki, don Allah ki yarda da ni kin ji ?anwata."

"Na yarda da kai sosai Yayana" Allah sarki Sufiyan yau ya samu natsuwar da ya jima bai samu ba, saboda yanzu zai iya sanar wa duniya cewa tabbas matarsa na son sa 100%, a daidai lokacin bai barta ba sai da ya tabbatar sun raya lokacin da farin ciki tare da samun ladar juna ga ubangiji....

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
*PAGE* 61

Suna kwance a kan gado ya ?ara janyo ta jikinsa "?anwata na gama yarda yanzu ni ka Wai ne a zuciyarki amma me ya sa lokacin da nace mu je cikin families ki sanar da ni kina so na kika tsaya jayayya, sannan kuma ?anwata wannan kishin naki ya yi yawa har sai da natsorata Wazu, hakan na nufin ko abokiyar aikinmu na ga ni, na daina magana da ita gudun samun matsala koh?"

Gyara kwanciyar ta yi a jikinsa ta ce "Yaya a lokacin ban yi tunanin hakan zai zama wata matsala ba, kuma na?i yin hakan ne a lokacin saboda na gama shirya maka kalolin surprise a ranar anniversary kamar yadda kake jin daWin yi man ba za ta, ni ma haka na so na yi, da naga lokacin kana son Sata man Waya daga cikin shiri na shi ya sa, na tsaya yi maka yawo da hankali, amma tabbas da na san hakan zai faru da ban tsaya wani jan aji ba gaskiya."

"Humm ni kuma na ji daWi sosai da hakan ta faru saboda ba dan haka ba, ba zan ga wannan kalar son da ake yi man ba har sumewa aka yi saboda wata tsohuwa can da har su Momy ta girma" cikin zolaya ya yi maganar.

Turo baki ta yi kamar za ta yi kuka, da sauri ya ce "Don Allah rufa man asiri kar ki fara kukan nan yanzu fa da ?yar na samu kika yi shuru."

Ri?o hannunsa ta yi "Shi ke nan ba zan yi kuka ba, Yayana ina son na sanar da kai wani abun, kar kishina ya zame maka rauni a zuciyarka, tabbas Yaya ina matu?ar son ka hakan kuma ya sa bana fatan ganin ka da ko wace mace, amma hakan ba zai sa na haramta abun da Allah ya hallata ba, saboda ni musulma ce kuma renon hausawa kaga ke nan na gaji kishiya ta ko wace hanya, amma don Allah duk rintsi karka yi abun da zan ji ka daina so na wallahi ba zan jure ba Yaya."

?an?ame ta ya yi sosai a jikinsa ya ce "?anwata ina sake yi wa Allah godiya daya ba ni mace irin ki, duk da tsananin kishin ki hakan be hanaki tunawa da hukuncin Allah a kanki ba."

"?anwata ina ?ara matu?ar son ki, sannan na san ko wane mutum da kalar ?addarar sa, ni dai ina ro?on Allah ya sa babu ?addarar yin mata sama da Waya, saboda ba zan taSa yin adalci tsakanin ku ba, dalili kuwa ke ce zaSi na, ba wanda ya isa ya sauya hakan, ki daina damuwa in sha Allah, ni naki ne har abada."

A gogon wayarsa ya duba da sauri "Lokaci ya tafi ?anwata an ku sa magrub bari na je sallah amma zan Wan jima a waje saboda ina son na koma gurin ?an uwana dazu na yi masu laifi zan tafi na daidai ta komai."

Bata ne mi sanin me ya yi masu ba cewa kawai ta yi "Yaya to don Allah karka daWe sosai ina jin tsoron zama ni ka Wai" kiss ya yi ma ta a fuska "Kar ki da mu in sha Allah yanzu zan dawo."

Cikin sauri sauri ya yi wanka ya shirya ya fita tare da yi ma ta "Bye Baby ki kula man da kanki" murmushi ta yi ita ma hakan ta maimaita ma sa, kana ganin su kaga waWan da ke tsananin farin ciki.

Salim Samir zaune a parlor duk sun yi shuru suna tunanin rayuwa Salim ya gaji da shurun ya ce "?an uwa bana jin daWin wannan rayuwar sam dole cikin abu biyu mu yi Waya, ko mu yi aure duk tsananin tsanar auren da muke kuwa, ko mubar ?asar mu yi ni sa sosai da families mu wata?il Wan uwanmu ya samu natsuwa sosai."

Samir ya ce "Ni ma kamar ka binciki zuciyata Wan uwa, sai dai wallahi ba zan iya yin aure ba, saboda na san illar da hakan zai hafar ko matar ta kai ni wuta ko ni, na kai ta wuta ko duk mu shiga wutar, dalili kuwa wallahi ba zan iya sauke hak?in iyali ba, na zaSi mu yi ni sa sosai da su amma kuma yaran mu fa, ko kana ganin mu tafi da su duk lokacin hutun makaranta sai muna tura su su yi hutun a gida saboda ba za mu iya raba tsakanin uwa da ?a-?an ta ba Koh?"

"A to gaskiya wannan shawarar tafi don ni ma muddun na yi aure a haka tabbas matsalar ke nan, narasa fahimtar me ya sa Wan uwa ya manta cewa kafin mu haWu da Sufayya bamu taSa ganin wata muka ji son ta a ranmu ba, kuma tun da suka yi aure sai rayuwar mu ta dawo kamar ta baya, me ya sa ba zai yi wannan tunanin ba, ya yi mana addu'a mafita a gurin ubangiji?"

Kamar daga sama suka jiyo muryarsa yana faWin "Cikin biyu ba za ku yi ko Waya ba" ?arasawa ya yi gurin su ya zauna ku sa da su "?an uwa don Allah ku gafarceni wallahi idona ne a rufe kwana biyun, amma na yi al?awarin in sha Allah ba zan taSa barin irin haka ya faru ba, ba zan bar sheWe ya sake ziyartar zuciyata ba."

Banza suka yi da shi kamar ma ba su son ya zauna gurin ba, cikin yana yin damuwa ya ce "Wai don Allah ba za ku yi man magana ba, ni ne fa Wan uwan ku, haba don Allah ku kula ni ?an uwana."

Nan ma shurun suka yi daga ?arshe ma Samir laptop ya Wauko ya fara duba wa kamar mai wani aiki ciki, mi?ewa ya yi "To shi ke nan tun da, ba za ku kula ni ba, ni nata fita" har ya kai ?ofar fita ba su kalli gurin da yake ba, ya ?ara cewa "Kuna fa ganin na ka wo bakin ?ofar fita kuma tafiya zan yi" nan ma dai shuru.

Da gudu ya dawo ya fizge laptop Win hannun Samir ya rungume su, ya ce "Don Allah ku hukunta ni duk yadda ku ke so amma don Allah karku yi man shuru ban saba da wannan yana yin naku ba, na san fa na yi kuskure kuma na baku ha?uri, ko Allah muna yi ma sa laifi mu nemi afuwar sa kuma ya gafarta mana, ku yi ha?uri ?an uwana" kuka yake sosai.

Salim ya ce "Me ya sa hakan ya faru, lokacin da har ka san gaskiya, ba zargin mu ya dace ka tsaya yi ba, zuwa ya dace ka yi mu zauna ka yi mana tambaya mu baka amsa, idan har baka gamsu da amsar ta mu ba sai ka yi duk hukuncin da kake ganin ya dace, yanzu daina wannan kukan sanar da ni yaushe kuma a ina ka san komai a kan wannan maganar?"

?an sassauta kukan na shi ya yi sannan ya fara da cewa "Tsawon kwanaki ina Wan cikin damuwa haka kawai nake jin zuciyata ba daidai ba kamar akwai abun da gurbin sa be cika ba a rayuwar aurenmu sai dai ban san mene ne shi ba, ranar kuna firar yadda aurenmu ya kasan ce a lokacin ba ku san ina ?ofar parlorn ina jin duk abun da kuke faWa ba."

Hakan ya Waga man hankali jin yadda ?anwata ta tsaneni sosai, zuciya ta rinjaye ni na je gurin ta nace ta zo mu tafi cikin families mu ta sanar a gaban kowa tana so na kuma ina son hakan ya fito daga ?asan zuciyar ta, ba wai don bin umurni ba, inda aka ?ara samun matsala shi ne tsayawa da ta yin tambayar me ya sa, da yi man musu haka kawai na ji cewa har yanzu babu so na a zuciyarta, to kun ji mafarin komai, amma don Allah ku yi ha?uri."

Samir ya ce "Shi ke nan Allah ya cigaba da tsaremu daga sharrin sheWan dana zuciya" duk suka amsa da Ameen.

Salim ya ce "Sannan gobe in sha Allah tun safe za mu koma Nigeria kaga ba zai yuyuba a ce duk'kan mu bama tare da yaranmu ba, kai kuma ka ?ara samun lokaci da Sufayya a nan kaga ba takurawar families babu ta yara" cikin murmushi ya ?arasa maganar.

Shi dai Sufiyan sunkuyar da kansa ya yi don har ga Allah kunyar su yake ji sosai saboda yana jin abun da ya yi sam be kyauta ba, Samir ya kalle shi ya fahimci yana yin da yake ciki ya ce "?an uwa idan wannan halin za ka fara mana na jin kunyar mu sai kace wanda ya aikata zunubin, to za mu daina kula ka gaskiya."

"Shi ke nan na daina in sha Allah" haka dai suka kasan ce suna ta zolayar juna sai 9:pm ya mi?e tsaye da sauri "?anwata ita ka Wai ce a gidan fa, kun ga ni kam na tafi sai da safe sai mun yi waya."

Dariya suka yi Samir ya ce "Ai na Wauka ka manta sahibar ta ka, shi ya sa ka shirya kwana a nan cikin mu gwauraye."
"A haba dai ai da kun hukunta ni idan har na manta da ?anwarku, ku ma dai Allah ya nuna man ranar da zan mayar maku da wannan gorin" sallama ya yi masu ya fice sai gidansa.

A parlor ya tarar da ita ta yi girki ta chaSa ado mai matu?ar Waukar hankali, tsayawa ya yi ya kafe ta da idanu sallamar ma gaza ?arasa wa ya yi, saboda a zahirin gaskiya ita Win ba wata masoyiyar kwalliya ba ce, sai dai akwai yin kalolin Win ki mai Waukar hankali, amma yau kam har da kwalliyar ta yi.

Cikin rawan murya ya ce "Ke ce da gaske matata?" banza ta yi da shi cikin muryar shagwaSa ta ce "Ai da ka kwana a can ka yi wani manta da ni kuma sai da nace karka daWe."

"Haba haba matar mijinta ta ya don Allah zan manta da ke cikin sau?i haka, ?an uwanki ne dai da ?yar na samu suka yafe man kuskurena shi ya sa, na kai wannan lokacin amma yanzu dai tuba nake" har da ri?e kunnesa alamar ban ha?uri "Shi ke nan komai ya wuce ta shi muci abinci tun da naga dai kallon ba zai ?are ba, ka yi wani tsare ni da idanu haka" murmushi kawai ya yi.

********************
Cikin sati biyu rayuwar su ta sauya kwanciyar hankali ya wanzu tsakanin su, ?aunar juna haWi da soyayya mai ?arfi ita ce ke gudana tsakanin waWan nan ma'auratan, Sufiyan har wata ?ar ?iba ya yi ya ?ara kyau, yanzu kuma sai shirye shiryen koma wa Nigeria suke saboda ya ransu da kuma anniversary Win su daya zo gab saura sati biyu.

Cikin jirgi suke zaune Sufiyan ya ce "Wai kin san wani abu ?anwata wallahi sam bana jin daWin tafiyar nan da za mu yi don ya zama dole ne kawai saboda mun Wauki tsawon lokaci bamu samu dama irin wannan ba, lokacin da muka taSa samun dama irin wannan, a lokacin kuma bamu zama cikakkin miji da mata ba, don haka bamu mori wancen lokacin ba sosai."

Ita dai bata ce da shi uffan ba tana lafe a ?irjinsa yana dubawa ya ga har bacci ya fara Waukar ta murmushi ya yi, ya gyara ma ta kwanciyar, ya yi ma ta uzuri saboda ya san tabbas kwanan nan duk a gajiye take, a haka har suka sauka.

Sun sauka lafiya an yi murnar zuwan su sosai musamman yaran su har da kuka suka yi saboda sun tafi sun barsu da ?yar aka lallashe su.
**************************
Bayan sati biyu da zuwan su an yi shagalin anniversary party Win su an gama lafiya duk mutame an watse su kuma duk suna parlor daga iyayensu har su Kaka da mutanen Zamfara, Sufiyan ya ce "Ni fa na gaji da jira ke kika ce kina son yi man surprise ranar anniversary Win mu amma har yanzu na ji shuru."

"Au kana nufin kai nan wani surprise kake jira lalle ma wannan Yayan to yi ha?uri yallaSe, ai ka lalata komai tun da jimawa ni kam kaga bari na shiga Waki ina da abun da zan yi."

?ata fuska ya yi ya ce "To ai na ba ki ha?uri ko kina nufin ba ki yafe man ba?"

Ita dai bata sake kulawa kan shi ba, ku san minty 30 bata fito ba ya ce "Kun ga ?an uwana ku zo mu fita mu bar gidan nan ban ga amfanin zaman ba gaskiya" har sun kai ?ofar barin parlour ya jiyo muryarta tana faWin "Yaya fita za ku yi?"
"Ina ruwan ki kuma? a fita za mu yi kuma sai gobe za mu dawo gidan don ma ki sani, Allah ya sa muna da guraren zuwa da yawa."

To ku tafi Win idan kunga dama ko goben karku dawo ku bari har wata goben, ni kam na ga ji da wannan wula?ancin naka don ka san ina son ka, kuma ina ?aunar ka, shi ya sa duk abun da kaga dama shi kake yi, dama na san har budurwa kake da ita mai ce maka dear."

Jin kalmar ina son ka, ina ?aunar ka, ya sanya shi juyowa da sauri yana kallon ta har ta gama maganar ta, ga wata sabuwar shiga da ta yi, doguwar riga ce har tana ja da ?asa ku san ma tafi wace ta saka lokacin party ko mayafi babu balle kuma hijab, gurin ta yaje da gudu.

"Me kike fada ne haka wai ba ki yarda da duk bayanin da na yi maki a kan wannan matar ba?"

"To idan haka ne me ya sa baka juyo ka kalle ni ba, shi ne kuma ka shirya fita ko sanar da ni baka yi ba?"

"Yi ha?uri na fasa fitar" duk taron mutanen gurin ya kalla, ya sake kallon ta cike da mamaki yana tunanin "Wai a gaban kowa ta iya furta man wannan kalmomin babu ko War a cikin idonta."

Samir ya ce "Ka barmu fa a tsaye kai muke jira kazo mu je" hararar sa ya yi "To na hana ku zama ne? ku yi zaman ku don ni kam na fasa fitar."

Salim ya ce "Ai kuwa Allah ba ka isa ba, Malam kai ka kawo shawarar fitar nan fa kuma har mun zo ?ofa kace wani abu wai ka fasa fitar."

"To sai me, ni na kawo shawarar amma kuma yanzu na janye magana ta, kin ga ?anwata zo mu je, mu yi fira" baki Salim ya saki ya kallon ikon Allah, shi kuma Samir da gudu yabi bayansa ya ce "Allah Malam fita dole sai mun yi kuma sai goben za mu dawo."

Bayan Sufayya ya Suya "?anwata yi wa wannan Yayan na ki magana don Allah kar ya takura man, wai don Allah Samir me ya sa kake Wan hana ruwa gudu, wai ko kunya ta baka ji? ni fa surukin ka ne mijin ?anwarka."

"Au sai yau ka tuna mu surukan ka ne ke nan to mun ?i wayon, Salim tare man shi nan ka yi tsaye kana kallon mu."

"Ah ah Wan uwana Salim, babban Yaya magajin Uba don Allah karka biyewa wannan yaron mai ?urciya har yanzu."

"Au ke nan sai yau ka tuna ni Win Yayanka ne ko? to ri?e girman bana so" duk suna maganar suna zagayen parlour da gudu, ?o?arin ri?e shi suke.

Momy Saratu ta ce "Ku daina bin shi kar ya karya man ku, kun san fa yanzu ba kunya bace da shi" ni kam har nagaji da wannan rashin kunyar ta shi dama zai haWa ya bar gidan nan da yafi."

Momy Nafisa ta ce "Kaga Sufiyan Wauki matar ka ku tafi gidanku ko yaran ku bar su a nan, a daina kiran ka marar kunya don ka kula matar ka."

Cikin farin ciki ya ce "Ina son ku iyayena to mu kam mun tafi sai da safe" hannun Sufayya ya ri?a yana faWin "Zo mu je matar mijinta."
Momy Saratu ta rabka salati ta ce "Kai dama rashin kunyar ta ta kai can ikon Allah?'
"Ni kam gaskiya ki daina yi man haka, kina ji fa da kunnenki iyayena suka ce na tafi da matata to don na bi umurnin su me ye laifina, ni dai kin ga tafiyar mu, a daina kirana marar kunya sai na jima banzo gidan ba balle a kira ni marar kunya" hannunta ya ri?e ya ce "Mu tafi amaryar Sufiyan."

Baki duk suka ri?e suna kallon sa, shi kuma ko a jikinsa, yanzu kam ya fitsare ?afafunsa ya sanya wa idonsa yaji.
Fizge hannunta ta yi ta ce "Amma dai ba a haka zan fita ba ko?"
"A to da gaskiyar ki bari na Wauko maki hijab" da gudu ya Wauko hijab Win ya yi masu sai da safe, a haka dai suka bar gidan ana ta, yi ma sa dariya.

Momy Aisha ta ce "Ma sha Allah, Allah ya ?ara sanya natsuwa da farin ciki, a rayuwar su, ya kore sharrin sheWan" duk ameen suka ce.

Salim da Samir suka ce "Yanzu kam mun samu natsuwa ganin su haka Allah ya tabbatar da alkhari."
************************
Suna shiga cikin gidan su ya ce "Barka da zuwa gidanki matata" murmushi ta yi ita ma ta ce "Barka da zuwa gidanmu dai."

?ar ?aramar dariya ya yi, ya ce "Ga duk'kan alama dai yanzu families mu sun yarda mun girma mun yi hankali, shi ya sa suka turo mu gidanmu mu ka Wai yau."

"Humm ba dole su yarda ba kana nuna masu rashin kunya ?arara"
"Ohh ni ne marar kunyar ko? to ki tsaya in ri?a ki."

Da gudu tabar gurin tana dariya Wakin ya bita ya tarar har ta cire hijab tana ?o?arin rage kayan jikinta don ta shiga wanka, ri?e hannunta ya yi, ya tsareta da idanu ya ce "Ai ban kalli wannan kwalliyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login