Showing 57001 words to 60000 words out of 123822 words

Chapter 20 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3425

dai ta Wauketa aiki kuma ta amince da hakan.

Ranar da ta fara karSar kuWin albashin ta a ranar ta nemi izinin Momy a kan tana Wan son fita, Momy ta yarda duk da a lokacin ta na jin tsoron kar ta gudu.

Kasuwa ta je bayan ta gama siyayya za ta koma gida ta haWu da telan Mama mai abinci wanda su ke aron keken shi tana yi masu Winkin kayan su.

Bayan sun gaisa take tambayar shi, me yake a nan kuma? nan yake sanar da ita cewa ai suna da wani reshen a Abuja shi ne babban reshe ma.

Ta nemi ya nuna mata gurin saboda za ta rin?a zuwa hayar keken kamar yadda ta saba in sha ALLAH.

WANNAN SHI NE ASALIN KUMA TUSHEN LABARIN RAHMA DA KUMA WANNAN FAMILIES..

CIGABAN LABARI.....

Duk mutanen da ke cikin parlorn fuskarsu hawaye ne, duk'kan su kallon tausayi suke yi wa Rahma, ita ma kukan take sosai wanda har numfashinta na neman barin jikinta, ganin hakan ya sa da sauri Salim ya je gurin ta tare da cewa sauran ?an na shi, su kawo ruwa da sauri.

Da?yar su ka samu ta natsu ta dawo hayyacinta sai mai da numfashi take da?yar, kallon Momy Saratu ta yi sannan ta ce.
"Momy a gidan nan ne kaWai ban sauya suna ba, na yi anfani da sunan da Baba Malam ya sanya man saboda na gaji sosai da sauya sunaye daga nan zuwa nan, hakan ya sa nace ko nabar gidan nan ba zan sake sauya suna ba."

"Momy kuma wannan ne dalilin da ya sa duk yawan tambayar ki a kan wace ce ni, na gaza baki amsa saboda bana son tuna abubuwan da su ka faru a rayuwata na san matu?ar zan baku labarina to fa sai na tuna da ?anwata da kuma abun da ya faru."

Kallon Aunty ta yi, ta ce "Don ALLAH ki faWa man ni da ban zama Yaya ta gariba a gurin ?anwata ba, ta ya zan zama mata ta gari kuma uwa ta gari?"

"Sakacina ya sanya na rasa ?anwata, da na je a kan lokaci da wani mummunan abu bai faru ba."

Bayan haka kuma FIYAYYEN HALILTA ANNABI MUHAMMAD (S A W) ya ce, ku aurawa ?a ?anku uwa ta gari, to ni kaina ban san wace ce, ni ba."

"Ba wanda zan nuna nace shi Win family na ne, ga kuma ya won cikin duniya idan na faWa nan, na ta shi nan."

"Ta ya zan yi tunanin son Wanki? Hmm kuskuren da na yi abaya ya isa hakan nan don ALLAH kar ki hanani tafiya."

Dady Suraj a rauna ne ya ce "Ki yafe man don ALLAH ?ata, saboda ni ne sanadin rasa ?anwarki da ban yi mantuwa ba, na san da baki makara gurin Waukar Furaira ba."

Da sauri ta ce "Haba dai Dady ni kuma bana tunanin kai ne sanadi, na gama yarda cewa lokacin ta ne, ya yi a wannnan ranar Furaira dole zata bar ni."

"Kuma bawai ina jayayya da hukuncin ALLAH a kaina ba ne, kawai dai idan na tuna ta hanyar da, na rasa ta sai na ji duk ba daWi kamar na gaza rike amanar da su Baffa na barman, don haka don ALLAH kar ka sake tunanin hakan."

Sannan ta mai da kallon ta a kan Salim ta ce "Yaya Samir don ALLAH ka daure ka yafe man na aikata babban kuskure a gunka duk da, na yi tunanin kamar shi ne mafita a gunmu baki Waya, ban yi tunanin hakan zai cutar da kai ba, har a yi maka kallon wanda ya yi gamo."

"Sam ban yi tunanin masu kuWi suna soyayyar gaskiya ba, na yi tunanin kawai ka so ni ne saboda muna wata duniyar da bamu da kowa sai junanmu."

"Shi ya sa nake ganin kamar na yaudari kaina soyayya da kai, a lokacin da na fahimci ko kai waye na ?ara tabbatar wa kafi ?arfina."

"Hakan ya sa, na gudu saboda kar na kai kaina gurinda za'a wula?anta ni, amma yanzu na fahimci duk ba haka ba ne, na yi babban kuskure don ALLAH ka yafe man."

"Yaya Samir kai ma ina fatan za ka yiman afuwa, ba wai na?i dawowa gurin ka ba ne saboda ina tunanin Momy bata so na, sai dan kawai ba zan iya sanar da kai cewa Mama Ladidi da ku ka gama yarda da ita, ta zama kamar Waya da cikin familyn ku, ita ce ta fitar da ni daga cikin gidan ku ba, na san za ka cutu sosai haka suma su Momy shi ya sa ban dawo gurin ka ba."

"Amma ka yarda da ni wallahi ban taSa tunanin cewa hakan zai cutar da kai ba har ya kai ka kwanta rashin lafiyar da ake tunanin kamar ba za ka rayu ba, duk a tunanina za ka manta da ni cikin ?an?anin lokaci, don ALLAH ka daure ka gafarce ni."
"Yaya Sufiyan kai ma ina fatan samun afuwar ka, ka jefa rayuwar ka cikin hatsari don ka ga cewa na samu farin ciki da mahallin zama, ka ku sa mutuwa saboda ni."

"Amma ka sani da na san ka Wauki wannan riskin tun farko dana dakatar da kai saboda akwai masu bu?atar ka a rayuwa kamar iyayen ka, da ?an uwanka, sannan kuma wannan awarwaron ba wani namiji ba ne, ya ba ni, ?anwata Furaira ce ta ba ni, da na san zancen zai cutar da kai, da na sanar da kai ko mai a kan shi,
Amma ka yi ha?uri don ALLAH."

Shuru parlorn ya yi, na Wan lokaci can ta ce, ina fatan duk wanda ke gurin nan ya samu amsar tambayoyin sa, kun san dalilina na?in auren Yaya Sufiyan."
"Zan iya tafiya yanzu ko ba komai yanzu duk yaranku sun ji sau?i zan tafi ba tare da fargabar wani abu zai samu Wayan su saboda ni ba."

Aunty ta yun?ura za ta yi magana kenan su ka jiyo sallama daga ?ofar parlor'n suna dubawa su kaga Mama Ladidi ce kamar a razane take, ido huWu su ka yi, da Rahma.

Cikin rawar murya ta ce "?ata kece da gaske? ALLAH na gode maka da kasa ina da rabon sake ganin wannan baiwar ta ka."

"Don ALLAH na ro?eki daki yafeman abun da, na aikata agun ki tun da lokacin da hakan ya faru ban sake samun natsuwa ba sannan ga shi ina ta haWuwa da kalolin jarabawa, don ALLAH ki yi ha?uri."

A gaskiya son zuciya da son kuWi su ne, su ka sanya ni aikata hakan, amma Hajiya bata san komai ba a kan hakan, wannan duk shirin Hajiya Luba da Hajiya Larai uwar Zara, kuma sunyi haka ne saboda Samir ya?i amincewa da auren Aziza, sannan su ka ce, ko ta wane hali na tabbatar na Sata sunan Hajiya a zuciyarki yadda ko kin rayu ba za ki yi tunanin sake neman su ba.

Murmushi Rahma ta yi, ta ce "A tunanin ki kin yi nasarar Sata sunan Momy a guna? to kin yi kuskure domin ban taSa jin tsanar Momy ba, saboda zuciyata ta gama yarda da su."

"Kuma idan na yarda da mutum abu ne mai wahala a sauya man tunani a kan shi, idan baki manta ba na taSa sanar dake wannan, dama can tun farko ke ce ban yarda da ke ba, kuma ga shi tunanina ya zama gaskiya a kan ki."

"Sai dai akwai abu Waya daya Waure man kai shi ne, a kan kuWi ?azantar duniya abun da duk yadda za ki tara su a nan za ki bar su, amma kika cutar da mutanen da su ka gama yarda dake a rayuwa a kan su."

"Amma gaskiya kin ba ni mamaki sosai, kin raba faruwar aure, kin raba tsakanin iyaye da ?arsu, duk saboda kuWi."

Mama Ladidi ta ce "Ah ah bawai wannan kaWai ba ne kuskusren da na aikata, anyi laifuka da dama ina sane amma na yi shuru saboda suna biyana,

Laifuka kamar su..........

WA?AN NE LAIFUKA NE, KUMA WAYA DACE RAHMA TA AURA, SHIN WAI A WANE HALI MALAM SU KE IYAYEN RAHMA?
DUK AMSAR NA CIKIN CIGABAN
WATA ?ADDARA
KU BIYO NI AKWAI SAURAN CAKWAKIYA A NAN GABA.

*WATA ?ADDARA*
*ANOTHER DESTINY*
By
*SUWAIBA M AMIRU*
(?ar gatan mama)
' *PAGE* 37

~RANAR TONON ASIRI~
Duk wanda ke gurin kallon ta yake da alamar tambaya a kan fuskar su, Rahma ta ce "Ban fahimta ba waWan ne laifuka kuma aka yi kina sane amma kika yi shuru saboda son zuciyarki?"
***********************
Mama Ladidi ta fara da cewa "Hajiya Larai ?anwar Alhaji Suraj, da Hajiya Luba ?anwar Hajiya Nafisa, Alhaji Isha ???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????anen Alhaji Nura, Hajiya Binta Yayar Alhaji Munir."

"Kinga waWan nan mutanen huWu ba suda wani burin daya wuce su ga bayan ?an uwan su saboda sun fisu rufin asiri, ka sancewar burin su yazo Waya hakan ya sa, su ka haWa kansu gurin cimma manufar su."

Ita Hajiya binta tun farko bata so ?anen nata Alhaji Munir ya samu haihuwa ba shi ya sa, ta dinga shayar da su magani na rashin haihuwa har na tsawon shekaru."

"Amma da yake komai na Allah ne sai ga shi sun samu haihuwa, aikuwa sai ta ji kamar za ta mutu don tsananin takaici, amma bayan sun haWa hannu da sauran sai su ka samo mata mafita."

"Wata rana su ka sanya a cire birkin motar ?anen nata, suna cikin tafiya su ka yi hatsari da man suna biye da su lokacin da abun ya faru ganin kamar yarinyar tana da sauran rai shi ne su ka Wauke ta a fakaice kafin mutane su zo, lokacin iyayen na sume sannan saura motocin sunyi gaba ko da, su ka dawo har sun tafi da yarinyar."

"Wani mutum su ka bawa ita domin ya ?arasa kashe ta, shi kuma ya ce sai dai ya jefar da ita amma ba zai kashe ta ba, domin shi baya ka she ?ananun yara, sun amince duk yadda ya ga dama ya yi kawai, su dai burin su karsu sake ganin ta har abada."

"Sannan mutuwar yaranku mata ba rashin lafiya ba ne sanadin mutuwar su, su ne sanadi ta hanyar sanya masu guba a baki, tun daga lokacin su ka yanke shawarar Waukar mataki kar su sake haihuwa, shi ne fa, su ka rin?a shayar da su magani cikin lemu ba tare da sun sani ba kuma dak'kan su daga mazan har matan."

"Suma yaran maza sunyi ta neman hanyar da, za su kawar da su amma daga bisa ni, su ka canja ra'ayi su ka yi shawarar barin su, za su yi masu anfani shi ya sa suke son haWa auren su da ?a ?ansu mata saboda wannan ce hanya mafi sau?i da, za su bi gurin mallakar duk abun da suke so sai dai an yi rashin sa'a duk yaran sun?i amince da haWin."

"Na jima ina neman hanyar da zanbi na gyara kuskurena sai ga shi kwana biyu da su ka wuce sun kira ni, a kan wani aiki wai na samo masu wata mai aikin da za su kawo gidan nan domin ta yi masu aiki a kan wata yarinya da Sufiyan ya dage a kanta baya ganin kowa sai ita kamar dai Samir."

"Shi ne suke son ta shigo gidan domin ta yi masu aiki irin wanda na yi a kan ki."

"Na ce gaskiya su nemi wata ni kam ba ni da wace zan kai masu saboda na tuba laifinda na yi abaya ina ro?on Allah ya yafe man."

"Sunce na yi gaggawar sauya ra'ayi, idan kuma ba haka ba tabbas na shirya ma hukuncin da za su yiman."

"Ni kuma nace ko za su kashe ni, ba zan sake yin abun da suke so ba, shi ya sa na yi tunanin zuwa kawai na faWi gaskiya."

"Wannan shi ne irin abubuwan da su ka faru ina sane amma na yi shuru saboda suna biyana, sai na gaza faWar gaskiya, amma yanzu ashirye nake da nakarSi duk kalar hukuncin da za ku yiman, amma don ALLAH ku yafe man."

Da sauri cikin zafin rai gwarazan samari ukun sukayo kanta suna son kai mata duka, Rahma ta shiga tsakani dama ita ce, ku sa da ita.

Kallon su ta yi, ta ce "Me kuke shirin aikatawa haka? kuna maza za ku Sata lokacin ku gurin dukan mace, macen ma irin wannan kudube ta fa sai naga kamar hannunta ya samu matsala ma."

"Duk da wannan matsalace ta family bai dace na sanya baki ba, amma sai nake ganin kamar ku barta da hukuncin ALLAH shi ne wanda zai yi mata hukunci fiye da naku, amma fa shawara ce ba umunir ba, a yanzu ALLAH ya dace ku yi wa godiya a ?alla kun san irin mutanen da suke tare da ku."

Suna nan tsaye sun gaza yin komai sai faman kallon ta suke, Dady Ahmad ya ce "?ata gaskiya ta faWa yarana don haka kubarta ta wuce horon da duniya kaWai zata yi mata ya isa."

"Ke kuma ki fita daga gidan nan tun ban kira security ba, su fitar man dake mayaudariya mai fuska biyu."

Haka ta fita tana kuka sai faWi take "Don ALLAH ku yi ha?uri ku yafe man na tuba."

Tana fita ita ma Rahma ta nufi hanyar fita, da sauri Aunty ta ri?e mata hannu ta ce "Ina kuma za ki je?"

Rahma ta ce "Ai mun yi dake cewa dana sanar da ku dalilina za ku barni na tafi, kinga kenan yanzu sai tafiya koh?"

Aunty ta kalli mai gidan ta ce "Wai Alhaji ba za ka yi magana ba, har tsawon wane lokacin kake son mu ?ara jira kenan?"

Duk wanda ke gurin ya maida kallon sa gurin Aunty cikin mamakin me take son faWa ne.

Kallon Rahma Aunty ta yi, ta ce saurara ki fahimce maganar da zan faWa maki cikin kunne basira, tun ranar da na fara ganin ki na ji bugun zuciya ta ya daWu saboda fuskar ?ata da nake gani a tare dake, na sanar da Alhaji amma ya ce mu yi ha?uri har yaronmu ya ji sau?i tun da muna tare, don shi ma yana jin hakan a kan ki."

Sufiyan ya ce "Yes Aunty wallahi tun ranar da na fara ganinta nake yi mata kallon sani amma sam na gaza tuna ko fahimtar ina san fuskar."

Momy Nafisa ita ma abun da ta faWa kenan, ta ce "Jiya ma maganar da muke kenan muda yaran dukan mu sai tunanni muke kamar mun san wannan fuskar ba tun yanzu ba amma kuma a ina, sai yanzu da kika yi magana sannan muka tabbatar da tammanin mu a kanta."

Rahma kallon ko wannen su take baki sake, can kuma ta fara wata irin dariya kamar wace ta zauce duk sai su ka koma kallon ta cikin mamaki, tunanin su dama ta san yadda ake dariya haka.

Ta kalli Aunty sannan ta ce "Tabbas yau na ?ara yarda cewa masu kuWi suna ganin duk abun da suke so a duniya za su samu, to ke kuma ta wannan hanyar kika biyo domin ki hana ni tafiya shi ne kike son kirana da ?ar ki wace ta Sata, koba haka ba ne?"

Cikin fargaba Aunty ta ce "Sam ba haka ba ne bari ma kiga ni" laptop ta Wauko ta rin?a nunama Rahma photos kala kala tun daga ranar da aka haifeta har zuwa ranar da ta Sata.

Ta ce "Duba nan ki ga ni, ranar da muka rasaki ne kuma na tabbata, wannan sune kayan da aka baki wanda akace da su aka tsince ki, don ALLAH ki yarda da ni, ke ?ata ce."

Kamar wace ta shiga jimami da gaske har Auntyta fara jin daWi, kar Sar laptop Win ta yi ta shiga duba photos da kyau sannan sai ta fara murmushi ta kalli Aunty ta ce.

"Amma gaskiya Aunty na tayaku jimami sosai rashin wannan ?ar ta ki mai kyau haka ina fatan ALLAH ya bayyana ta idan ta na raye."

Muryar Aunty na rawa zuciyarta ta fara karyewa yanzu kam, cikin razana ta ce "Tana raye kuma a yanzu ALLAH ya bayyana ta gurinmu, don ALLAH na ro?eki kar ki rufe idon ki, ki?i ganin gaskiya na tabbata yanzu daga ganin wannan shedar kin san cewa gaskiya nake faWa."

"She da kuma Aunty, wace she dar kenan? ni ban san waWan nan kayan ba kuma koda na san su, sai akace ?arku ce kaWai mai kalar su, kaya suna zuwa da yawa kasuwa duk wanda ya ga ni, yana so sai ya siya kawai."

Aunty ta ce "Ban da kayan yarana, ni ce da kaina ke bada zanen su, da hannuna daga ke har ?an mazan."

"Daga dai ?ar ki har yaran ki maza."

Dady Munir ya matsa ku sa da ita, ya ce "Sufayya me ya sa kike son Soye kan ki daga garemu, bayan kin fahimci gaskiya, don ALLAH ?ata ki daina wahalar damu haka, mun shiga damuwa sosai na rashin ki."

"Ikon ALLAH wai don ALLAH yanzu ?arya kuke son na yi maku, ya kuke son na kalleku lokacin da ?ar ta ku ta bayyana, duk fa wannan abun da kuke yi don kun ji labarina ne, ba ni da kowa kuma tsinta ta aka yi, shi ne kuke son yin anfani da wannan damar saboda idon ku ya rufe a kan son ?ar ku."

Salim ya ce "Koma mene ne gaskiyar yanzu za ta fito in sha ALLAH" ledar da ya karSa a hannunta ranar da za su rabu ita ya Wauko sannan ya ce.

"Kin sanya na yi maki al?awari ba zan SuWa ba, kuma har izuwa yanzu ban taSa buWawa ba, amma ki yi ha?uri yau a kan idon ki zan buWa saboda gano ainihin gaskiya."

Ri?e hannunsa ta yi, ta ce "Don Allah kar ka karya man al?awari, bana son ka buWe wannan ledar."

"Ni kam ba wani al?awari dana karya tun da a kan idon ki zan bude, ba bayan idon ki ba" Rahma har da hawaye gurin ro?on Salim amma ya ce sai dai ita ta yi ha?uri.

Shi ya ja ledar ita ta ja, a haka har ledar ta yage kayan ciki duk su ka zube ?asa, ?ananun kayan yara na ?an mata masu kyau...

*WATA ?ADDARA*
*ANOTHER DESTINY*
By
*SUWAIBA M AMIRU*
(?ar gatan mama)
'
*PAGE* 3?? 8??

Cikin tsananin farin ciki duk wanda ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login