Showing 21001 words to 24000 words out of 123822 words

Chapter 8 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3430

na yara haka za ta fada, amma sai ta bawa kowa mamaki ta hanyar cewa ita dai tafi son gurin kiwo babba sosai kuma ace nata ne.

Dady Munir ya ce "Chabdijam lalle kee ra'ayin ki na daban ne, to ina kike son gurin ya kasance?"
Ta ce koma ina ne tana so."

Iyayen suka yanke shawarar adawo Nigeria a samu guri mai kyau sai agina.

Haka ko akayi bayan sun dawo gida Nigeria su ka sanya cigiyar babbar gona, sai a wani ?auye dake can cikin jahar Kaduna aka samu gurin mai girman gaske, cikin ?an?anin lokaci aka kammala komai.

Ranar da tacika shekaru huWu su kuma yayun nata na da shekaru goma sha Waya a ranar duk suka shirya zuwa buWe gidan gonar.

Su na ?arasawa gidan gonar farin cikin Sufayya ya kasa Soyuwa da sauri ta rungumi iyayen ta cikin irin maganarta ta yarinta ta ce,
"Na gode sosai ina son ku."

Suna cikin wannan yanayin malamin da aka gayyato domin ayi wa gidan gonar sauka qur'anic ya zo, ku sa da su sannan ya sanar angama saukar inji almajiran sa.
Duka familyn suka yi ma sa godiya tare da yi ma sa kyauta sosai.

Har ya fara tafiya ya dawo gurinsu sannan ya ce idan ba damuwa ina son na Wan yi tambaya don ALLAH, da su nan waye a ka yi wannan gidan gonar?" a nan suka nuna masa Sufayya.

Ri?a hannunta ya yi sannan ya ce,
"Ku yi man aikin gafara idan har abun da zan faWa bai maku daWi ba, duk lokacin da wannan yarinyar ta ke cikin wata matsala ko damuwa to wannan gidan gonar tabbas zai yi annoba sosai."

Duk wanda yake gurin hankalinsa ya yi munanan ta shi,
Da sauri Aunty ta ce in sha ALLAH babu wata matsalar da za ta shiga, mun gode za ka iya tafiya kawai."

Wunin ranar a gurin suka wuni,
Lokacin da za su bar gurin Sufayya ta kalli Momy Aisha sannan ta ce, "Momy na ku sa barin ku, na yi ni sa, da ku sai na yi ta kuka sosai, koh?"

Da sauri kowa ya ce "Kamar ya fa, me kike faWa Sufayya?"

Ba ta sake magana ba sai kawai ta Wauki alawarta ta shiga mota ta zauna dama can ba mai yawan magana ba ce, amma idan ta yi Waya sai ta sanya hankalin kowa ya dawo kanta.

Amma wannan maganar nata ya Waga hankalin kowa musamman iyayenta, ga kuma abun da malan ya faWa, Aunty har da hawaye ta yi.

Sun shirya tafiya kowa da tunani a ransa, mota Waya yaran suke shiga amma wannan ranar ta ce ita kam motar su Aunty za ta shiga, Sufiyan daga jin hakan shi ma, ya ce motar zai shiga ba yadda ?an uwansa basu yi ba dan ya zauna tare dasu amma ya?i haka ya shige motar, dole suka ha?ura.

Suna cikin tafiya ba su fi minty talatin da fara tafiya ba, cikin ikon ALLAH motar su ta haWu da wata babbar motar sai kawai suka birkice mummunan hatsari ne ya faru wan da ba'a fito da kowa cikin su da rai ba.

Sai farkawa suka yi suka gan su asibiti har Sufiyan sai dai wata babbar matsalar ba'aga koda gawar Sufanyya ba, an yi nema duk gurin da ya dace birni da ?auye amma ba labari,
Mutane da yawa sun yarda cewa ta rasu amma Aunty da Dady ba su yarda ?ar su ta rasu ba.

Har yanzu tsawon shekara sha huWu ke nan amma ba wanda ya ga koda mai kama da ita kuma har yanzu basu cire ran dawowarta ba, har ?an uwan nata maza sun sha wahala rashin ta musamman Sufiyan dama shi tun yana yaro bai iya saka damuwa arai ba duk ya saka damuwa sai ya yi matu?ar wahala,
Kuma tun a kanta basu sake haihuwa ba, sannan duk shekara sai sunyi ba?in cikin rashin ta kullun addu'ar su ALLAH ya dawo masu da ita cikin aminci.

Wannan dalilin ya sa Sufiyan ya daina birthday ya ce sai ranar da ?anwarsa ta dawo sannan, jin hakan ya sa su ma ?an uwansa suka daina,
Idan ranar ta zagayo haka suke zama kamar masu zaman makoki, sannan har yanzu ana kulawa da gidan gonar ta sosai.

Watannin da suka wuce gidan gonar yayita haWuwa da annoba aikuwa hankalin Dady Munir ya ta shi saboda tunawa da zancen malam amma ya gaza faWama matarsa saboda matsalar hawan jinin da ta samu tun Satan yarinyar.

Wannan ke nan.

**********************
CIGABAN LABARIN...

Rahma ta sauke numfashi ta ce "Yaya amma gaskiya na tausaya ma su sosai, idan tana raye ALLAH ya haWa su cikin aminci..
Sufiyan ya ce ameen.

Rahma ta yi murmushi ta ce "Yaya ko dai ita kake jiran ta dawo ka aureta sha ya sa ba ka soyayya?"
Sufiyan ya ce "Ban taSa kawo wannan tunanin a raina ba, aurena lokaci ne bai yi ba idan ALLAH ya kawo lokacin sai ki ga na yi, kallon ta ya yi cikin yana yin son karantar abun day ke ranta ya ce "Amma Rahma bakya kishi na da kike faWar hakan?"

"Ki shi kuma, akan me zanyi kishinka ni ba matarka ba kuma ba wace za ka aura ba? ni kam ko kaWan ba na jin wani kishin ka, idan ita ma kake jira ALLAH ya bayyanata mu sha bikin."

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' PAGE 1?? 6??

A cikin zuciyar sa bai ji daWi ba amma sai kawai ya daure.
"Ya ce haka ne kuma ?anwata, amma ni ma ina son na yi maki tambaya idan ba damuwa."

"Amma dai ba akan rayuwata ba ne koh?"
"Ah ahh akan wannan a warworon hannun naki ne nake son dan ALLAH ki sanar da ni me ya sa, ya ke da mahimmanci sosai a gurin ki?"

"Kyautar sa aka ba ni, shi ya sa nake matu?ar son sa."
Sufiyan ya ce "Ke nan idan na fahimceki kina son wanda ya ba ki shi sosai?"

Rahma da sauri ta ce "Sosai ma kuwa, Yaya idan ka ji a na zancen SO Waya kenan, to ni idan akwai abun da yafi so shi nake yi wa mai wannan a warwaron."
"Ke nan ba za ki iya mantawa da shi ba?"

"Har abada kuwa, ko da mutuwa na yi, na dawo in sha ALLAH sai na tuna mai wannan a warwaron, kai Yaya bari ka ji, da wani na bada ran sa ya yi fansar wani to da zan iya bada raina fansa ga mai wannan abun hannun."
"Amma ke fa kika ce man ba ki soyayya koh?"

"A mana Yaya, amma ko da bana soyayya to ina yi ga mai wannan a warwaron, kuma ina son sa fiye da yadda nake son raina."

Za ta cigaba da magana, da ?arfi ta ji muryar Sufiyan yana cewa "Ya'isa haka nan dan ALLAH ki yi man shiru."

Cikin rawar murya ta ce "Lafiya Yaya ko na faWi wata kalma da bata yima ba? Idan haka ne don Allah ka yi ha?uri."

Rufe idanun sa ya yi sosai sannan ya sauke ajiyar zuciya, duk sai ya ji bai kyauta ba gaskiya me ya sa zai Waga mata murya haka.
A sanyaye ya ce "Kinga ?anwata ba abun da ya faru kawai dai na ga kamar lokaci na tafiya kuma tashin safe za mu yi saboda ba?inmu da zasuzo amma ki yi ha?uri na tsorata kin da na yi."

Rahma ta ce "Wallahi har kasa na tsorata na Wauka wani laifin na yi kuma."
"Ba komai mu shiga cikin gida kawai."

Yana shiga Waki kamar jira yake ya gansa a Wakin ya saki wani irin kuka sosai maimakon zuciyarsa ta yi ma sa sanyi sai ma ?ara zafi ta yi, haka dai ya kwana a wahale.

Da safe ya kasa fitowa, kowa ya yi mamakin rashin ganinsa ya fito duk yadda ya ke Waukin zuwan ?an uwan sa, sai can misalin 12:pm ya samu fitowa.

Rahma ta ce, "Na yi fushi sosai sai yanzu za ka fito?"

To me ya sa da ban fitoba ba ki je, ne mana ba?"
"Ai na yi tunanin kana yin wani abun ne mai mahimmanci shi ya sa."

Momy ta zo gurin su ta ce "?ata komai na tafiya daidai koh?"
Rahma ta ce "Momy na ma ku sa gamawa in sha ALLAH."

Kallon Sufiyan Momy ta yi, ta ce "Kai lafiya kuwa ka ke, duk ka yi wani sauyawa haka?"
"Lafiya ?alau nake Momy."

Parlor Momy ta wuce ta samu Dady yana duba jarida ta ce.
"Alhaji kwana biyun nan sai nake ganin kamar Sufiyan ba yada lafiya amma sam ya ?i faWa."

Dady ya ce "Ni ma na lura da hakan amma ai shi ba yaro ba ne, da wani ga garumin abu ne daya sanar da mu dan haka kar ki da mu don ALLAH."
Momy ta ce "Shi ke nan ALLAH ya kyau ta."
A kitchen Rahma ta ce "Yaya ka san mene ne kuwa?" Bata jira amsawar sa ba, ta ce a duk lokacin da kake cikin damuwa ka yi ?o?arin bayyana ta ga wani musamman iyayenka ko da basu Wauki wani mataki ba za su yi maka addu'a hakan kuma zai sa ka samu sanyi cikin zuciyar ka.
"Yayana ka yi wa ALLAH godiya kana tare da iyayen ka, kana da masu sha re maka hawayen ka duk lokacin da ka samu kanka cikin damuwa, saSanin wasu iri na cikin mafarki ma ina son suzo na sanar da su matsala ta amma ban samu wannan damar ba, to kai da kake da wannan damar me ya sa kake son barin damuwa ta illata ka?"
"Yayana damuwar da kake bari a cikin zuciyarka gab take da ta illata ka kuma a dalilin hakan duk wani na tare da kai zai shiga damuwa da tashin hankali."
Sufiyan ya ce "Shin waya sanar da ke ina cikin wata damuwa ko matsala ?anwata?"

"Karka da mu ba dole nake yi maka ba shawara ce na baka ya rage naka ka Wauka ko ka watsar, amma za kace na sanar da kai wannan in sha ALLAH."
**********************
Ba?i sun sauka gida ya cika da farin ciki sosai.
Aunty ta ce "?ana baka ji daWin zuwan mu ba halan?"

"Ah Ah Aunty ina matu?ar farin ciki kawai dai bari na yi kuhuta sosai shi ya sa kawai."

Momy Nafisa ta ce "Ikon ALLAH, Aunty yaran ki sun girma fa, kinga yadda duk suka natsu."

Momy Aisha ta ce,
"Wallahi ba wata natsuwa da suka yi kawai dai surukan mu ne suka sanya su wannan natsuwar musamman samir da ya fisu hayaniya,
Sai dai shi Sufiyan bamu san me ye matsalar ba me ya sa duk ya rame haka, ko shi ma baya da lafiyar ne?"

Salim ya ji hayaniyar na son fin ?arfin sa hakan ya sa, ya kalli ?an uwan na sa, ya ce mu je Waki mana muWan tattauna koh?"

Dady Suraj ya ce "Abincin kuma fa?"
Kusan a tare suka ce za mu tafi da namu a can Wakin karku da mu."

SUFIYAN da ?an uwan sa Samir da Salim a cikin part Win sa zaune duk sun yi shuru ba mai magana daga cikin su.
Sai can Salim ya ce "Sufiyan baka yi farin cikin zuwanmu ba ne?"
"Miyasa ka faWi hakan Wan uwa?"
Samir ya ce "Ba dole ya faWi haka ba tun da mukazo ba wata walwala a tare da kai."

"Zan sanar da ku amma kafin nan ku sanar da ni ya jikin na ku ina fatan yanzu dai kun samu sau?i sosai koh?"

"Wallahi har yanzu ba wai mun ji sau?i ba ne kawai dai muna dauriya ne saboda iyayen mu" cewar Samir.

To ni kam ina ma son na san me ya faru ne bamun taSa maganar kun ku sa fahimtar juna ba lokacin ina Germany gurin Salim ina kula da shi?"
Kai kuma Salim har yanzu baka samu ganin ta bane tun wancen lokacin?"

Samir ya ce a tunani na tarkona ya kama tsuntsu a she ba haka ba ne,
Ta barni lokacin da nake cikin tsantsar bu?atar ta, na nai meta ko ina amma na rasa ta har yanzu,
Sai dai ban cire ran za mu sake haWuwa ba in sha ALLAH."

Salim ya ce "Ni ma dai tun da muka rabu a wannan gurin ban sake sakata a ido ba, na sha ?udirin muna barin gurin zan aure ta amma sai na ?are a gadon asibiti, har ana yi man tunanin ko na yi gamo da aljannu ko kuma na samu ta Sin hankali, bayan ni na san ba haka ba ne."

Sufiyan ya nisa sannan ya ce,
"Wai me ya sa ?addarar mu ta ke son zama iri Waya koma na ce ta zama iri Wayan?"
A tare su kace "Kamar ya fa?"

Nan ya kwashe duk labarinsa da Rahma ya sanar da su,
Ya ce ?an uwana kun ji tawa jarabawar Rahma sam bata so na, na ga hakan a cikin idon ta."
Ya ?arasa maganar cikin rauni sosai.

Salim ya ce,
"Ya ALLAH amma me ya sa, za ta ?ika ko tana tunanin kana da wani halin ne marar kyau?"

"Wallahi ban saniba amma dai na san akwai wanda ta ke matu?ar so mai wannan a warwaron."
Yana cikin faWar hakan sai kawai muryar sa ta sar?e ya kasa cigaba da magana, tari kawai ya ke, a man jini ya fara sosai ya ri?e ?an uwan nasa ya nata faWar bata so na, kuce ta so ni ko sau Waya ne don ALLAH."

Cikin ruWewa Salim ke faWin za ta so ka don ALLAH ka natsu Wan uwa."

Ganin al amarin na son fin ?ar finsu shi ya sa Samir ya yi saurin fita ya je parlorn sama ya tarar da iyayen na su, cikin tashin hankali ya ke magana wallahi Sufiyan ne zai mutu."

Ai kuwa basu jira mai zai ?ara faWaba hanyar Wakin na su suka nufa.

Halin da ya ke ciki ya Waga hankalin su sosai Waukar sa suka yi sai asibiti suna shiga aka karSesa sai ICU domin ba shi taimakon gaggawa.
Sun fi awa Waya sannan suka fito.

Doctar ya bu?aci ganin iyayensa amma Dady Suraj ya ce koma mene ne ya faWa saboda nan duk iyayen sa ne.

Dr ya gyara tsayuwar sa sannan ya ce "A gaskiya sai dai ku yi ha?uri da abun da zan faWa, yaronku ya nada hawan jini sosai sannan ya kamu da ciwon zuciya mai tsanani a yanzu haka zuciyar ta kunbura sosai za ta iya bugawa a kowa ne lokaci.
"A ta?aice dai bama tunanin zai ?ara awa shidda a raye, sai dai kuma abun da ALLAH ya yi kawai, amma akwai mafita Waya ina ganin watakil za ta iya aiki."

Idan kun san akwai wani abun da yake bu?ata a rayuwa ko kuma abun da ya yi sanadin jefa shi wannan matsalar to ku yi ?o?arin samar masa da shi dan duk irin taimakon da za mu ba shi idan da wani abun da ya saka a ransa to fa aikin banza ne."
Yana gama faWar hakan ya wuce opis Win sa...

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
*PAGE* 1?? 7??

Dady Nura ya ce "Alhaji Suraj meke faruwa ne haka da Wan namu?
"Har yanzu ?an uwansa ba su gama jin sau?i ba sosai, yanzu kuma shi ma ga shi nan a wannan halin?"
"Ni ma ban san yana rashin lafiya haka ba saboda bai sanar damu ba, Wazu ma da safe Momy ke cewa ta gafa ya nata rama kamar marar lafiya."
Dady Munir ya ce "Amma dai ba za ku rasa sanin abun da ke damun sa ba, ko kuma wani abun da ya saka a ransa ba."
Dady ya ce "Tabbas na sani" nan dai ya kwashe duk labarin Sufiyan da Rahma ya sanar da su.
Nan suma su Salim da Samir suka sanar da abun da ya faru a yau Win bayan shigar su Waki.
Aunty Zainab ta ce "Wai su yaran namu duk jarabawar su a kan so ne?"
Mun samu waWan cen sun Wan ji sau?i yanzu kuma ga wannan rayuwar ma gaba Waya ta ke son raba shi da ita lokaci Waya."
"Hajiya Saratu ina zamu samu yarinyar yanzu?"
Momy ta ce "Tana gida yanzu haka.
Momy Aisha ta ce "Amma me ya sa bamu ganta ba tun Wazu?"

"Bayan ta gama aiki ni ce, na ce taje ta zauna ta Wan huta, da ni ya ta sai zuwa anjima na kirata ku gaisa saboda dama can ba mai son hayaniya ba ce."

Dady Ahmad ya ce "Wai yanzu tsayawa za ku yi kuna mai da magana ba za mu yi sauri mu Wauko yarinyar ba?"
Duk'kan su suka nufi gida, da man ba'a ba su damar shi ga gurin saba,
Suna zuwa gida kai tsaye Wakin Rahma suka nufa.
Rahma kam bata san mike faruwa ba, ko yanzu gama sallar ta ke nan tana naWe sallaya sai kawai ta ji bugun ?ofa da ?arfi,
Hankalin ta, ya ta shi saboda bata saba jin irin wannan bugun ?ofar ba, cikin razana ta ce "Waye?"
Momy ta ce "Ni ce Rahma buWe ?ofar."
Da sauri ta buWe ta ce "Momy lafiya kuwa?"
Ina fa lafiya Yayan ki na can na neman mutuwa."

BuWe idanunta ta yi kamar za su faWo ?asa, "Mutuwa kuma Momy me ya same sa Wazu fa lafiya ?alau muka rabu da shi?"

Momy ta ce "Uanzu kuma yana asibiti bai san wanda ke kansa ba."
Hannun Rahma Momy taja da ?arfi ta na faWin,
"Don Allah ki zo mu tafi ki taimakemu ke ce kaWai mai maganin wannan matsalar ta Yayan ki."
"Ni kuma Momy meue haWina da rashin lafiyar sa?"
Idan mun tafi kan hanya zan sanar dake komai yanzu ba lokaci."
Haka ta ja Rahma har suka fito tsakiyar parlorn,
Su na fitowa da sauri Salim da Samir suka zo gurin su,
Samir ya ce Bilkisu."
Salim kuma ya ce Khadija dama zan sa ke ganinki?"
Hajiya Nusaiba ta ce "?ata ina kika shiga me ya sa kika barmu mun naimeki amma mun gaza samun ki?"

Dady Ahmad ya ce "Haba ?ata idan laifi muka yi maki ai sanar damu ya dace ki yi, ba ki barmu ba."

Salim ya ce "Dady wannan fa sunan ta Khadija ba Bilkisu ba, kuma ita ce wacce na keta nema."

Samir ya ce "Ah ah Wan uwa sunan ta Bilkisu ba Khadija ba kuma ita ce nake baka labarin ina nema."

Da sauri Aunty ta ce "Ku yi mana shuru koma mene ne za mu sani daga baya, yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login