Showing 42001 words to 45000 words out of 123822 words

Chapter 15 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3436

biyu."

Dady ya ce "Wai yanzu ma tunanin kike? ga matar gidan nan tana ta maki magana tun Wazu amma kin yi shuru."

Kallon Momy Nafisa ta yi, tana mata murmushi Rahma ta ce "Don ALLAH ki yi ha?uri ban jiki ba, ina kwana?"

"Ba komai hakan na faruwa wasu lokutan, lafiya ?alau, kinga duk kin ji?e muje ciki ki sauya kaya."

"To amma baki sanar da ni abun da zan yi maki ba, ko aiki kike so na yi maki?"

Momy ta kalli Dady ta ce "Kuna nufin baku sanar da ita ba?"

"A naga cewa kamar bata cikin natsuwar ta shi ya sa, na bari muzo gida ta Wan huta sannan mu sanar da ita."

Momy ta ce "A to hakan ma tunani ne amma kuma a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, don haka ?ata zo muje ki cire wannan kayan da suka ji?e sannan na sanar dake dalilin da ya sa muke neman ki."

Bayan ta fito Momy ta zaunar da ita ta ce "Ni sunana Hajiya Nafisa."

Dady ya ce "Ni kuma sunana Alhaji Ahmad sai dai kuma yarana suna ki rana da Dady ita kuma mai Wakin tawa Momy."

Samir ya ce "Wai sai wani gabatar mata da kanku kuke amma ni baku ce komai akai na ba."

Momy ta ce "Wai mun ga kana da baki shi ya sa muka bari ka gabatar da kan ka."

Matsawa ya yi kusa da ita ya ce "Shi ke nan ALLAH dai yasa ina da baki, kin ga ni dai sunana Samir su kuma iyayena sannan basu kaWai bane ina da wasu iyayen masu so na sosai ba kamar waWan nan ba."

Yana maganar yana murguWa masu baki irin sun Sata masa rai basu gabatar da shi ba, yaci gaba da faWin "Ina da ?an uwana biyu duk za ki gan su nan da Wan lokaci kaWan, ke kuma me ye su nan ki?"

Har zata sanar da su, su nan ta, da ta sani wato Rahma amma sai ta fasa suma ta, ba su wani suna Bilkisu, sai da ya jima yana kallon ta har ta kai da yin magana ta ce "Mene ne kuma?"

"Ba komai na dai ga kamar baki yi kala da sunan ba amma kuma su nan ya yi daWi."

A ranta ta ce "Ko Yaya Salim sai da ya faWi hakan, shin ko dai ana fahimtar su nan mutum ne da an kalle sa?"

Can taji Samir na cewa "Gaskiya zan sanar dake ba zan iya ?ara Waukar wani lokaci ba, a can da sam ban yar da akwai wani abu soyayya ba amma gaskiya ganin farko da na yi maki na fahimce tunani na ba daidai ba ne,
Lokaci Waya naji cewa ina son ki kuma da aure ina fatan za ki amince da ni?"

Da sauri ta kalle sa ta ce "So kuma? yau she, a ina ka san ni da har kaji kana so na?"

Ya yi murmushi ya ce "to wace amsar kike so na fara yi maki bayani a kanta?"

"Da farko dai na fara ganin ki tun ranar da muka yi karo da juna amma kin san mene ne? tun kafin ranar na yi mafarkin ki har na sanar da su Momy amma sai suka rin?a yiman dariya suka mayar da maganar wasa."

"Yawan mafarkin ki ne ya sa, na baro ?an uwana Germany Wayan ko lafiya bayada haka na dawo gida ko zan samu ganin ki."

"Haka ma ranar da, na sanar da su na haWu da matata ta mafarki nan ma dai dariyar suka yi sosai sai da suka ga, na dage sannan suka fara Waukar zancen da gaske, tun daga ranar nake neman ki amma kuma ALLAH baisa na same ki ba sai yau."
Kana ganin yana yin Rahma zaka fahimci a matu?ar razane take...

*PAGE* 2?? 9??
Momy ta ce "Wannan gaskiya ne ?ata da fari mun yi tunanin ko ya yi gamo ne har mun fara tsorata, da yake shi ma Wan uwan shi ya samu irin wannan matsalar ya ce, ya haWu da yarinya amma har yanzu bamu same ta ba yanzu dai muna tunanin gamo ya yi."

"Shi ya sa hankalinmu ya ta shi sosai har muna tunanin kiran Wan uwansu muce kar ya dawo ?asar nan, duk da dama shi ba masoyin zaman ?asar ba ne sosai kamar sauran ?an uwan na shi, saboda muna tunanin zuwan su ?asar ne abun yake bibiyar su haka."

"Jiya ina faWa maki bamu yi bacci ba har asuba, ya matsa sai yaje neman ki wai kina bu?atar taimakon shi a yanzu, ya ji hakan a jikin shi da?ar Dady ya ba shi ha?uri akan ya bari har da safe da kansa zai rakashi neman ki, sai ga shi kuwa anyi dace cikin ikon ALLAH."

Dady ya ce "Amma fa duk wannan ba zai sa muce dole sai kin so shi ba saboda bamu san me yake cikin ran ki ba don haka za mu baki lokaci daga yau har zuwa sati Waya ki yi tunani in ya yi maki shi ke nan idan kuma bai yi maki ba, ba zamu tilasta ma ki ba kuma za mu cigaba da ri?e ki a nan a matsayin ?armu in sha ALLAH."

Da sauri cikin damuwa Salim ya ce "Amma kuma Dady."

Dady ya ce "Amma kuma me? so kake na tursasata ta so ka koda ranta baya so? kar ka man ta ita ma ?ace kamar kai tana da, damar zaSar abun da take so kuma tabar wanda bata so, don haka sai ka yi ha?urin jin amsar ta ko wace iri ce."

"Dama ni bance ku tilasta mata ba, kuma in sha ALLAH ni ne zaSin ta, ko ?anwata?"
Ya yi maganar ya kallon ta.

Ita dai binsu kawai take da kallo cike da mamaki a ranta ta ce "Ta yama hakan zai faru a so mutum lokaci Waya ba tare da an san juna ba har ?arama Yaya Salim duk da ya ce ya fara so na tun ranar da aka kai ni gurin amma ai mun Wan zauna tare ya Wan fahimce ni ni ma haka, amma shi wannan bai taSa zama da ni koda na minty talatin ba, kuma wai yana so na, to shin wai dama haka shi so yake ban sani b?"
Ta yiwa kanta tambayar da ba amsa.

Ta yi zurfi cikin tunani ta jiyo muryar Momy na cewa "Don ALLAH ka barta ta huta ta samu ta ci abinci kafin ka cigaba da yi mata zancen na ka."

"Shi ke nan Momy a kawo mana abincin tare zamu ci da ita yau ba da ku zanci ba, ko ?anwata?"

Momy ta ce "Ka ga ba yau ba ina ga kabar ta, yau taci ita kaWai sai mu ba ta guri kafin ta gama saboda na ga kamar tana jin kunyarmu ko ba haka ba ?ata?"

Cikin san yin muryar da rashin sukuni ta ce "Ah ah bahaka bane ni bana jin yunwa ne kawai."

Da sauri Salim ya ce "Wallahi Momy wannan ba gaskiya ba ne tana jin yunwa bata ci komai ba don ALLAH kisa ta ci wani abun."

Dady ya ce "ALLAH dai yasa ba ba?unta za ki yi ba nan fa gidanku ne ki yi duk abun da kike so kin ji ko?"

Kiran Sufiyan ya yi cikin farin ciki yana sanar da shi ya samu yarinyar yanzu haka tana cikin gidansu, Sufiyan ya yi murna sosai Salim ma haka.

Nan take muryar Salim ta sauya ta yi rauni ya ce "Ni ma dai ALLAH yasa na samu ganin tawa."
Amsawa suka yi da ameen.

Ba yadda ba su yi ba akan ya tura masu photo ta kosu yi video call kafin su shigo ?asar, amma sam ya?i ya ce "Yadda na sha wahala gurin neman ta kuma ba zaku ganta cikin sau?i haka ba, don haka ku shirya zuwa ?asar nan don ku gaisuwa guy's."

"Amma dai ka san ba za a bar ni zuwa ?asar ba yanzu ko."
Cewar Salim.

"To sai ka yi sauri ka ji sau?i ka dawo wata?il ma idan ka zo, mu samu sau?i gurin binciken ta tun da kace bata cikin wannan video dana tura maku wai hijab Win ta kawai ka hango, to kaga kenan ya dace ka zo mu dage da nema ko ALLAH zai ji ?anmu mu same ta."

"Shi ke nan to ka haWamu a waya mana mu gaisa."

Lalle ma to na?i wayon, ta nan kuma kuka bullo?"

Salim ya ce "Kaga Sufiyan ka barshi kawai mu sanya lokaci muje ?asar sai muga yadda zai hanamu ganin ta, ka san shifa har yanzu jin shi yake a yaro shi ya sa duk abubuwan yara su yake."

"Oho dai, yau ko jariri za kuce man ba zan damu ba, sai dai kun shigo ?asar, magana ta ?are fa?at."

*********************
Kwana biyu da zuwan ta gidan amma kamar ta yi wata Waya yadda iyayen ke bata kulawa abun har mamaki yake bata shi Samir ba'a ma maganar shi sosai yake janta ajiki.

Sai dai ta lura da abu Waya duk yawan masu aikin gidan Momy bata barin su yi mata girki da kanta take hakan yasa ta fara tunanin ri?a mata wasu abubuwan ko zata samu sau?i, ai kuwa shi ma Samir ganin haka sai ya fara shiga kitchen Win wai da su nan taimakawa,
Duk inda ta sanya ?afa shi ma ta shi na gurin, idan aka ce wannan abun na yanka ne ko bai iya ba to shi zai yi, a ce warshi wai kar ta yanka hannunta.

Ganin tana iya yin abubuwan da Momy ke so hakan yasa ta bar mata kitchen Win.

Ta sha tambayar ta, a ina ta iya girki haka, kuma daga ina ta zo, amma kuma amsa ta yi wahala saboda bata son tuna komai akan hakan,
Haka Momy ta dena yi mata tambayar a cewar ta idan ta saba da su zata ba su labarin ta in sha ALLAH.

Samir na bata kulawa sosai wani lokacin har mamakin yadda ya damu da ita haka take, idan ta yi la'akari da cewa bai rasa komai ba na rayuwa wanda ko mata huWu ya keda ra'ayin aura lokaci Waya zai iya amma ya tsaya yana Sata lokacin shi akan wacce ita kanta bata san wace ce ita ba.

Ranar da ta cika kwana biyar a gidan, ta shi ta yi, da wani matsanancin ciwon kai kuma hakan na da nasaba da dukan ruwan da ta sha ranar da suka samo ta saboda duk son ta da ruwa idan ruwan sama ya same ta tofa sai ta yi wannan ciwon kan, wannan karon har mamaki ta yi ganin an yi kwana biyar tana lafiya ?alau, a she dai abun na zuwa.

A ranar sai taji kamar ciwon ya mafi na kullun sai dai bata son Momy ta fahimci hakan saboda ta san hankalinsu zai ta shi amma ina tun tana iya jurewa har ta fara gazawa ?arshe dai Momy ta gano bata cikin hayyacinta sosai.

Tambayar ta ta yi meke faruwa? nan ta sanar da ita matsalar ta.

Momy duk ta ruWe sosai ta kira Samir ta sanar da shi wai yazo ya duba ta a tunaninta ta yi gwaninta, ai kuwa yana zuwa har sai yafi mai jinyar shiga damuwa duk yabi ya Waga hankalin shi ya Waga na iyayen na su ?ar she dai har da su kuka kai kace mutuwa aka yi masa.

Momy cikin Sacin rai ta ce "Don ALLAH ka natsu ka duba ta."

"Wallahi Momy bana iya tuna komai akan hakan kuma bana fahimtar komai, ni dai kawai ta samu lafiya don ALLAH Momy ki taimaka ki yi wani abun wallahi tana jin jiki sosai, duba fa ki gani."

Momy ta ce "Ta ya zan iya yi mata wani abun bayan kaine Doctor?"

"Ni kam ALLAH, na ma manta cewa ni Doctor ne Momy."

Sai da Dady yaga abun nata cigaba kuma shi baya da kwarin guiwar duba ta hakan yasa ya kira wani Doctor ya duba ta, ya bata duk abun da ya dace sannan ya ce, ta kiya yi shiga ruwa saboda jikin ta baya so.

Kwana Waya da wuni tana jinya amma Salim sam baya matsawa ko nan da can idan dare ya yi sai Momy ta yi da gaske sannan yake tafiya Wakinsa amma fa kafin safiya sai ya kira wayar ta yafi sau hamsin.

Ganin hakan dake faruwa ya sanya dole ta fara nuna taji sau?i duk da bawai ta warware bane sosai.

Da?ar ta samu Samir ya yarda taji sau?i har ya fara fara'a a fuskar shi, ada ko kana ganin shi kaga wanda aka yiwa mutuwa saboda yanayin fuskar shi.

Dady ne ya zaunar da su domin jin amsar ta, taji faWuwar gaba sosai ita yanzu tunanin ta mema zatace, idan ta ce bata son Samir tabbas Dady bazai tursasa mata ba kamar yadda ya yi al?awari amma kuma Samir zai iya shiga wani hali saboda yadda ya Wauki soyayyar ta kamar rayuwar shi.

"Kin yi shuru baki yi magana ba ?ata, kin san sati Waya naba ki, ki yi shawara ka san cewar bakida lafiya ya sa nabar maganar har zuwa yau, don ALLAH kar ki ji komai ki sanar da ni abun da yake ran ki."

Sai da ta kalli kowa a gurin musamman Samir daya gama za?uwa ya ji, mi zata ce sannan ta du?ar da kanta ?asa da?ar ta furta kalmar "Na amince."

Dady ya ce "Kin tabbatar kin amince har cikin zuciyar ki babu takura?"

"A babu takura a ciki na amince."

"Maa sha ALLAH na ji daWi sosai ALLAH ya yi maku albarka, in sha ALLAH zan sanar da ?an uwana komai sai su saka lokacin ayi komai a gama."

"Amma kafin nan sai na fara ziyarta yarana na ga halin da suke ciki yanzu, sannan daga bi sani na yima ?an uwana zancen ku, sai su zo nema ma shi auren ki a gurina, kinga kafin lokacin kun ?ara fahimtar juna, koba haka Momy?"

"Hakane gaskiya amma ni dai na so ace a rana Waya zamu aurar da yaran nan duka mu huta sai dai kuma duk abun da ALLAH ya yi shi ne daidai, wata?il ma kafin lokacin suma sai kaga sun samu cikin ikon ALLAH."
Dady ya ce "To ALLAH ya yarda, ni ma zan so hakan sosai."

*PAGE* 3?? 0??
Tana shi ga Wakin ta sai ta ji babu abun da take so irin ta yi kuka ko za ta samu sau?i a zuciyarta, faWin take,
"Me ya sa ?addara ta za ta ?are ga masu kuWi duk guje masu da nake? nabar Yaya Salim saboda hakan yanzu kuma ga Yaya Samir ni kam ya zan yi da rayuwata?"

Tana nan a dur?ushe kamar wata mai ro?on gafara kuka take sosai, sai ganin kofin ruwa ta yi a fuskarta an mi?a mata, tana Waga kai ta ga Samir.

"Ya ce karSi ki sha ruwan za ki ji san yi a zuciyar ki, sannan kuma ki sanar da ni gaskiyar baki so na, na yi maki al?awarin zan ha?ura da zancen auren ki duk'da na san zan cutu, amma kuma wannan ya nayin na ki zai fi cutar da ni, ba zan juri ganin ki a wannan halin ba, ba zan taSa tursasa ki, ki so ni amma na san a ?alla za mu zama abokai ko ba haka ba?"

Kallon cikin idon ta yake domin ya karan ce ta sosai.

Kunya ta ji sosai da jin kalaman shi duk'da juriya ce kawai yake, a cikin maganar shi, za ka fahimci hakan daga jin muryar shi.

?o?arin daidai ta kanta ta yi, ta ce "Waya sanar da kai haka Yayana? ka sani a ra'ayin kai na, na amince da zancen auren ka kuma bana jin a kwai tursasawa a ciki, sai dai akwai damuwa Waya yau na amince da wani har zancen aure ya shiga amma kuma bana tare da iyayena da kowa nawa."
"Yanzu don ALLAH akan wannan kike damuwa haba ?anwata kin manta yadda su Dady na sanar dake akan cewa sune iyayen ki kuma duk abun da iyaye ke yiwa ?ar su ina da tabbacin za su cika maganar su."

Dama sun jima suna neman ?a mace yanzu kuma ALLAH ya basu don haka ki dai na wata damuwa, kuma kar ki damu da ni saboda ni ina da iyayena ko yanzu dan ba su ?asar ne shi ya sa kika ganni gidan nan amma da sun dawo zanbar gidan nan sai dai na zo zance."

Maganar shi dariya ta bata ta ce "Zance kuma yayana?"
"A mana ai duk wasu al'adu na aure sai mun cika su in sha ALLAH, kuma ko ba haka ba ki na ganin waWan nan iyayen na ki, za su bar ni zaman gidan nan cikin salama? ai su Momyna na dawowa za su kora ni, kin ga ?ara na tafi kafin a yi man kora da hali."

"Ka ga gaskiya ba zai yuyuba kana son ?ar mutane kuma kana gaya masu magana akan idun ?ar, kar ka man ta fa suWin surukan ka ne."

"ALLAH ya baki ha?uri mai gadon zinari, yanzu dai na ji daWin yadda kika warwale domin cigaba da wannan farin cikin ki ta shi mufita shopping saboda tun da ki kazo gidan nan baki taSa fita ba, har na fara tunanin ko dai kin fara kullin ne irin na matan aure tun kafin a yi auren."

"Haba dai wane irin kulli kuma kawai dai bana son fita ne saboda ban san ina zan tafi ba."

"Yanzu kin samu Wan jagora don haka ki shirya mu tafi ki ga gari sosai."
"Gaskiya sai dai ka tafi kai kaWai saboda ba zan iya kallon Momy na ce mata wai za mu fita."

"Dama ban ce ki sanar da ita ba, ni da kaina zan sanar da ita kuma yanzu nan."

Sun shirya fita Momy ta ce "A dawo lafiya ?ata."
Dady kuma ya ce "A yo mana tsaraba ?ata."

Sun je gurare sosai duk gurin da suka wuce sai ta ji kamar su kaWai ake kallo saboda ko wanne saurayi da budurwa duk sun ci kwalliya an sanya ?ananun kaya amma ita ta sanya wani ?aton hajib kamar na mai karar kishiya, sai take ganin kamar ba su dace da shi ba sam.

Amma ta lura shi ko a jikin shi, sun je gurin ?arshe sun yi siyayya sosai sannan su ka fito da shirin tafiya har sun iso ku sa da mota, Samir ya ce "Ohh nafa yi halin nawa na baro ATM a ciki dole sai na koma.

"Kin san mene ne? a kan wannan halin nawa ya sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login