Showing 72001 words to 75000 words out of 123822 words

Chapter 25 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3423

"Na gode sosai."

Momy Nafisa ta ce "Salim Samir ku ne, za ku ja motar amarya da ango kamar yadda aka tsara, ku huWu ke nan ba direba."

Da sauri Sufayya ta ce "Ah ah Momy ni kam ku zan bi, ni fa nafi son na zauna duk gurin da ku ,ke ."

Momy Aisha ta ce "Ai kuwa mu kam duk nan da ki ka ganmu ko wace da mijinta za ta tafi, don haka ke ma mijinki za ki bi.

"Sannan in ban da wauta irin ta ki, kin taSa ganin ango da amarya sun tafi da ban da ban?"

"Ya isa haka nan mu je na raka ki mota kin ga lokaci na tafiya ba?inmu na can suna jira."

Haka ta shiga mota ba dan ranta ya so ba, suna isa event center Win, amarya ta kafe guri Waya ta ?i shiga ?o?arin koma wa mota ta fara yi, Salim ne ya ce "Lafiya kuwa ?anwata?"

Murya na rawa ta ce "Ba zan iya shiga cikin mutane a haka ba gaskiya, dubi fa shigar jikina Yaya."


Duk'kan yayun sun goyi bayan su koma gida kawai, ta sauya shigar jikinta, amma iyayen sun hana.

Momy Saratu ta ce "Da ku ka san ba ku son ta sanya me ya sa, ku ka kawo mata ita, don haka karku Sata mana lokaci ku shige mu tafi, kuma shin rigar ba ga mayafinta nan haWe da ita ba?"

Sufiyan cikin san yin murya ya ce "Amma Momy mayafin ya yi shar shar da yawa."

"Au sai yanzu kuka fahimci hakan, dallah ku wuce mu tafi" cewar Dady Ahmad.

Haka dai suka shiga taron Sufayya kuma ta cika al?awarin da ta yi wa Aunty, ta bada haWin kai sosai sai hakan ya ?ara ?awatar da gurin, kowa a gurin sai yaba irin tsarin amarya da ango ya ke.

Su na gurin da aka tanada domin su, ma'ana mazaunin ango da amarya sai ga doctor Umar ya zo, yi wa ango fatan alkhairi a lokacin, ya tsare Rahma da idanu har ya manta abun da ya kawo shi gurin, sai da Samir ya dake shi, ya ce "Kai malam lafiya kuwa?"

Da sauri ya dawo daidai sannan ya ?ara matsawa ku sa da Sufiyan ya ce "Guy dole fa ka nemi rasa ranka a kan wannan gimbiyar mata haka, na rantse ko ni ne zan iya shiga irin yana yin da ka shiga."

"Kai amma gaskiya ka yi dace, kuma wallahi ku na kama, sai dai kuma ta fika kyau gaskiya, kai amma gaskiya Allah ya yi hallita a gurin nan abokina za ka fa mori ?urciya sosai fa."

Magana ya ke ta rashin Wa'a, kamar wanda ya zauce sam ya gaza Wauke idanunsa a kanta.

Ba ran Sufiyan ba, hatta na sauran yayunta sai da ya Saci amma ita ba ta ma san abun da ke faruwa ba, saboda hankalinta na gurin su Momy da ke gabatar ma ta da ba?insu.

Cikin tsananin Sacin rai da kishi Sufiyan ya ce "Ya isa haka nan malam na gode za ka iya tafiya" Samir ya ce "Ba ka ji abun da ya ce ba, ko sai na daki bakin ka na zubar ma da ha?ori yanzu?"

Ya san halin Samir sarai zai yi abun da yafi hakan ma, duk a cikin su yafi su ya wan magana kuma yafi su zafin rai ba ya Waukar raini ko kaWan.

Ba shiri ya ce "Sorry boss dama na zo, ta ya murna ne kuma na yi bari na tafi Allah sanya Alkhairi" cikin sauri ya bar gurin.

Tsaki Sufiyan ya yi, ya ce "Wai har yanzu lokacin watse taron nan bai yi ba?" Salim ya ce "Ni ma abun da nake son faWa ke nan."

An taru sosai mutanen kowa sun zo Sufayya ba ta sha wahala sosai ba gurin gaisawa da mutanen da, ba su iya hausa ba, sai yaren na sa ra.

Haka dai aka yi komai lafiya a ka watse.

A daren ranar Rahma tana kwance a parlorn Wakinta ta yi kamar mai bacci, sai ga Sufiyan ya shigo tare da yin sallama.

Ta amsa tare da ta shi zaune, ya ce "Allah ya sa ba ki fara bacci ba, na tada ki."

Ta ce "Ah ah Yaya ba haka ba ne kawai dai na Wan kwanta ne."

"Ma sha Allah ?anwata dama ina son sake magana da ke a kan zancen aurenmu, har yanzu muna da sauran lokaci don Allah yau dai ki daure ki sanar da ni gaskiya kin ga yau ne yarage idan ba ki yi magana yanzu ba sai yaushe za ki yi?"

Tunawa ta yi da maganar iyayensu da kuma al?awarin da ta yi masu, kallon sa ta tsaya yi sannan ta mayar da kanta ?asa idanunta na son fitar da ?wallah amma ta?i ba su wannan damar, a raunane ta ce "Yaya ni fa gaskiya raina ya fara Saci da wannan maganar ta ka tun farko na sanar da kai idan ka daina so na, ka sanar da ni amma ba ka ce komai ba."

"Sai yau da ka ga cewa sauran a wanni komai ya zo ?arshe shi ne, za ka zoman da wannan maganar."

"To ka ga, mu yi wani abu Waya, ka je ka sanar wa kowa cewa ka fasa aurena saboda yanzu sam baka so na, shi ke nan ka ga magana ta ?are" cikin fushi ta bar shi nan gurin zaune ta shige Waki, haka shi ma ya girgiza kai yabar parlorn.

Lokaci ba ya jira, sannan rana bata ?arya yau dai misalin ?arfe 12:pm an Waura auren SUFIYAN ALHAJI SURAJ da amarya SUFAYYA ALHAJI MUNIR.

Bayan su Dady sun baro taron jama'a suka sanya a kawo masu amarya, ko da Momy Aisha ta je Wakinta ta tarar da ita ?asan gadonta ta rafka uban tagumi kai ka ce mutuwa aka yi mata.

Momy ta dafa ta, ta ce "Ta shi mu tafi ?ata ana neman ki Parlor, jiki ba ?wari haka ta mi?e tabi bayan ta har cikin parlorn, idan mutum bai san ita ba ce amarya, zai iya cewa ba ita ba ce amaryar ba, saboda duk ta fita hayyacinta, sai dai ba laifi ko yau ta yi kwalliya sosai kuma ta yi kyau, lufaya les ce a jikinta, hakan ya sa ana hangen gyaran gashin kanta shi ma ya yi kyau sosai ya ?ara kwanciya a gadon bayan ta.

Ku sa, da su Dady ta zauna sannan ta ?ara gaida su, bayan sun gama buWe taron da addu'a Dady Nura ya kalli amarya ya bata wata envelope ya ce "Ri?e nan ?ata."

Ba musu ta karSa da hannu biyu ya ce "Ma sha Allah kin san an ce ?arancin sadaki ya fi albarka a aure.

"To yau dai Allah ya nuna mana aurenki, sannan wannan envelope Win sadakin ki ne a ciki, saboda haka addini ya ce idan an Waura wa yarinya aure to a dam?a mata sadakinta a hannunta don hak?in ta ne."

Da sauri ta Wago kai ta kallesu tare da sakin kuWin a ?asa, jikinta na rawa ta ce "Dady an Waura aurena ka ce fa, ke nan kuma da Yaya Sufiyan Win?"

Dady Ahmad ya watsa mata wani kallo wanda sai da, ta yi saurin du?ar da kanta ?asa.

Duk wanda ke gurin kallonta yake cikin mamakin maganar ta amma ban da Sufiyan saboda ya gama yarda akwai dalilin da ya sa, ta amince da auren sa.

Dady Suraj ya ce "?ata me ya sa, ki ka ce haka ko kina tunanin wani abun ne da ban?"

Cikin rawar murya ta ce "Ah ah Dady dama na yi tunanin Yaya ya daina so na ne, shi ya sa, na Wauka na rasa shi saboda ko jiya sai da, ya yi ta yi man tambaya kamar mai son rabuwa da ni."

"To kwantar da hankalin ki wanda ki ke so, shi ki ka samu kuma shi ma yana son ki sosai, kawai dai tsokana ce irin ta sa" cewar Dady Nura.

Dady Ahmad ya ce "Kai yaran zamani, to ke nan da mun yi gangancin aura maki wanda ba shi ba, raba auren za ki yi ke nan" sai da duk mutanen gurin na yi dariya amma ban da mutum huWu, amarya da ango da kuma Yayunta.

?a ga kai ta yi, ta kalli Yayunta har da angon na ta sannan ta du?ar da kanta ?asa wasu hawaye suka biyo a kan fuskarta.

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' PAGE 45

~RAYUWAR GIDAN AURE da ?ALUBALIN RASHIN SO~

Momy Nafisa ta ce "Ta shi mu je tun yanzu ki fara shiri, kin san mu ne ?an matan amarya, tun da ?ar ta mu bata da ?awaye, don haka mu ne nan za mu raka ki."

Da sauri ta Wago kai ta ce "Momy za ku raka ni ina ke nan?" Cikin farin ciki kuma ta ce "Ko dai tun yau zan wuce makarantar?"

Baki sake duk wanda ke gurin yake kallon ta, Momy ta ce "Kamar ya fa ?ata? gidan mijinki za mu raka ki kamar ko wace amarya."

Za ta sake yin magana Dady Nura ya ce "?ata wuce ki shirya lokaci na tafiya, ba ma son dare ya yi, kai war yamma muke son yi maki" idanu cike da hawaye ta bar gurin da sauri.

******************
Ma sha Allah gidan amarya ya amsa su nan sa, ya yi matu?ar kyau kuma naira ta yi kuka a gurin, iyayensu ne suka raka su tare da ?an uwansu.

Bayan sun kai su, suka sake yi masu huWuba sosai, sannan sun yi mata kyautuka sosai daga ciki har da motoci biyu masu matu?ar kyau, ita dai in ban da zubar da hawaye ba abun da take.

Dady Ahmad ya ce "Wai wannan wane irin kuka ne haka? ba fa wata duniyar muka kai ki ba, kuma a hannun yayanki wanda kike so muka kawo ki, me kuma ya rage yanzu da kike cikin wannan yana yin haka?"

Cikin muryar kuka ta ce "Ni fa Dady kawai ina wannan damuwar saboda rabuwa da ku a lokacin da ya dace ace ina tare da ku, ganin cewa ban jima da sanin ku Win families na ne ba."

Kaka ya ce "Da yake an faWa maki cewa daga yanzu kin daina ganin su har abada koh? to bari ki ji kuna tare ba ku rabu ba in dai waWan nan iyayen naki ne, muma kuma za ki rin?a ganinmu lokaci zuwa lokaci ko da kuwa kun bar ?asar nan ne."

Dady Suraj ya ce "Wannan gaskiya ne ?ata ki dai na damuwa kin ji koh?"

Momy Saratu kuma ta ce "Idan kuma kika so ganinmu ya nemi hana ki, ki kira ni kawai da kaina zan zo in Wauke ki."

Duk suna wannan ne don su samu ta Wan samu natsuwa, Dady Munir ya ce "Ai ya dace mu tafi haka nan koh, kun ga har daren dai ya yi ma na a nan."

Haka dai duk aka watse aka bar su, su biyu, Sufiyan ya ce "Daure ki ta shi mu yi sallah muci abinci ko" ba musu ta mi?e ta bi shi, shi ya fara shiga yin alwallah ita kuma ta zauna gefen gadon Wakin, kafin ya fito ta yi saurin Waukar wayarta ta rubuta text kamar haka.

"Na gode sosai Yaya da wannan hukuncin na ka, na ?o?arin fitar da ni daga rayuwarka da kuma ?o?arin Wauke farin cikina saboda farin cikin Wan uwanka, a wannan gaSar ka nuna man son kanka ?arara, duk tsawon lokacin nan ban cire ran za ka sauya ra'ayinka ba amma sai na ga akasin hakan, na gode da wannan na mijin ?o?arin na ka sai anjima."

Bayan ta gama rubutawa sai kuma ta rasa wanda za ta turawa daga cikin su sai kawai ta tura masu su biyun, ya yi daidai da fitowar Sufiyan ta ajiye wayar ita ma, ta yi alwalla suka yi sallah tare kamar yadda muslunci ya koyar da mu, domin yi ma sa godiya da kuma nuna farin ciki da korar sheWanu.

Sannan ya Wauko kazar da aka kawo su da ita, ta ce ita dai lemu kawai take so, ko shi Win tana shan rabin kofi ?arami ta ce ya ishe ta haka nan, Sufiyan ya ce "Ni ma dai ya ishe ni haka nan, ki ta shi ki yi shirin kwanciya koh."

Shuru ta yi kuma ba alamar za ta yi shirin kwanciyar, kallon ta ya yi yai murmushi sannan ya ce "Kar ki da mu akwai Wakuna da yawa a gidan nan zan je in kwana a cikin Waki Waya, ina fatan ba ki da damuwa a kan hakan."

Tsayuwar sa ya gyara sannan ya ce "Kin ga ?anwata ko ki sanar da ni, ko kar ki sanar da ni, zuciyata na sanar da ni cewa tabbas kina so na amma ba son aure ba, don haka na yi maki al?awari in sha Allah ba zan taSa kallon ki amatsayin matata ba har sai kin fara so na a matsayin mijinki."

"Amma ina fatan za ki cigaba da kallona a matsayin aboki kuma Yayanki, in sha Allah za mu zauna lafiya cikin farin ciki kamar yadda mu ke a baya."

Kallon sa ta yi cikin raunin murya ta ce "Amma Yaya ba haka" sai kuma ta yi shuru ta gaza ?arasa maganar, ta sunkuyar da kanta ?asa, ta ce "To na gode sosai Yayana."

Har ya so, ya yi mata tambaya a kan me take son faWa ne, sai kuma ya fasa maganar, ya ce "Ba komai" daga haka ya fita ya bar Wakin.

**********************
Salim da Samir sune na ?arshe gurin dawowa gida sun rasa gurin zuwa hakan ya sa, ko wannen su ya faki idanun mutane ya nufi Wakin iyayensa.

Samir na zuwa gurin iyayensa ya faWa jikin Dady ya fara wani irin kuka mai tsuma rai, ba abun da yake faWa sai "Na rasa ta wallahi na rasa ta har abada Dady, yau za ta kwana gidan wani ba ni ba wallahi ji nake kamar mutuwa zan yi."

Kuka yake sosai ya ce "Dady ga shi ita ma har yanzu fushi take da ni sosai, kun ga ku duba sakon da, ta turo man, shi ne wani babban tashin hankalina sam ba zan juri fushin ta a kaina ba."

Dady ya ce "Ya isa haka nan natsu ka ji Wana" Dady kalli Momy ya yi mata alama da ta kawo ruwa, da sauri ta kawo ma sa ruwa ya sha, sannan ita ma ta zauna ku sa, da shi.

Dady ya ce tun farko sai da muka yi tunanin hakan zai iya faruwa shi ya sa, ka ji mun ta yi maka tambaya a kan za ka iya wannan sadaukarwa kuwa? ka ce tabbas za ka iya, to yanzu me ya kawo wannan sauyin haka?"

"Ya kamata ka tuna cewa yanzu fa ita Win matar aure ce, tunanin ta a gareka haramun ne kuma bana son karin?a Waukar zunubi a kanka Wana, saboda bana son ka haWu da mahallicinmu a mai laifi."

"Kai fa jarumi ne na san da haka, hakan ya sa nake son neman wata alfarma a gurinka."

"?ana na san cewa tabbas ba za ka iya cire son Sufayya a ranka ba, amma don Allah karka bada damar da za ta ji cewa har yanzu kana yi mata son soyayya, saboda ba na son ta samu rauni gurin yi wa mijinta biyayya" Momy ta ce "Ni ma abun da nake son na faWa ke nan Wana."

Cikin raunin murya ya ce "In sha Allah zan yi ?a?orin ki yaye hakan, amma don Allah ni ma ina neman alfarma ina son kubar ni, na yi nisa da su ma'ana ina son na bar ?asar na wani lokaci ko zan Wan samu sau?i a zuciyata."

Dady ya ce "Ni ma na yi wannan tunanin don haka na baka damar tafiya, amma sai nan da sati Waya saboda bana son Wan uwanku ya fahimci wani abun."

******************
Shi ma Salim ku san abun da ya faru ke nan bayan zuwansa gurin iyayensa, da ?yar suka samu ya natsu duk ya fita hayyacinsa, shi ma irin wannan hukuncin ya yanke kuma shi ma iyayensa ba su hana ba, amma kamar sun haWa baki da iyayen Samir saboda su ma sun ce ya Wan jira nan da sati Waya saboda Wan uwansu, kuma ya amince da hakan.

Haka dai ko wannen su ya kwana ba bacci kamar yadda suka ga rana haka suka ga dare da safiya.

Gidan amarya kuwa su ma, ba su yi wani bacci ba sosai ko wannen su da kalar tunanin da yake a ransa, Sufiyan har kuka ya yi yana mamakin wane irin aure ne wannan suka yi, ga shi dai ya samu wace yake so amma kuma yana yin yazo masu wani iri.

Da safe tana ta shi bayan ta yi sallah ta yi wanka, ta shirya cikin wani material mai matu?ar kyau riga ce da siket, ta gyara gashin kanta ya yi kyau kamar ta zauna a haka, sai kuma ta sanya hijab ta fesa turaruka sannan ta fito parlor da, ni yar shiga kitchen.

HaWuwa suka yi da juna tana ganin shi ta yi saurin sunkuyar da kanta ?asa sannan ta gaida shi, ya amsa cikin sakin fuska, shi ma ya yi kyau sosai ya sanya golden shadda.

"Ina ki ke shirin tafiya ne haka ?anwata?"

"Yaya dama so nake na shiga kitchen ne, na haWa breakfast."

Da sauri ya ce "Rufa man asiri ta ya zan barki ki yi aiki yau? ai sai ki sanya su Momy su kama ni da laifin na sanya masu ?a aiki a ranar farko gidanta."

?an turo baki ta yi cikin yana yi kamar na mai shagwaSa ta ce "To meye a ciki kai fa abokina ne kuma Yayana, ai naga ba laifi ba ne don na haWa maka breakfast."

Kallon ta ya yi, da yana yin yadda take magana a ransa ya ce "Ina ma rayuwarmu ta ka sance haka cikin so da ?aunar juna, amma sai dai kash duk tana yin wannan ne a bisa bin umurnin wani, kuma tabbas sai na gano ko waye in sha Allah."

"Yayana tunanin me kake yi haka?" ta yi maganar cikin sigar tambaya.

"Ba komai ?anwata" ya yi ajiyar numfashi ya ce "Maganar ki haka ne, amma sai dai mu yi aikin tare in kin yarda."

"Shi ke nan na yarda" haka suka jera tare gwanin ban sha'awa har sun ku sa shiga kitchen Win suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login