Showing 102001 words to 105000 words out of 123822 words

Chapter 35 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3443

ta wuce suka zo nan har Hajiya Luba ?anwar Hajiya Aisha, suka mana cin mutunci sosai har da shi ?aton banza mai biyewa mata Alhaji isah suka zage mu tas wai muna da masaniyar yarinyar Munir ta bayyana amma ba bu wanda ya yi tunanin sanar da su saboda ba a Wauke su da mahimmanci ba."

"Sannan har aka sanya ranar auren ta da Sufiyan har aka yi auren ba su sani ba, kuma maimakon su sauran yaran biyu ku ce, su auri yaran su a ?ara dan ?on zumunci tun da dai ba yarinya Waya za su aura ba duk su ukun, amma ba ku yi hakan ba saboda duk an tsane su."

"A lokacin mu kuma muka taka masu birki, muka bayyana duk irin abubuwan da suka yi, muka tambaye su cewa ko suna tunanin bamu san komai ba har yanzu, to su sani mun yi shuru ne kawai saboda Sufayya ta bu?aci hakan tace a bar ku da hukuncin Allah zai fi."

"Aikuwa nan suka ?ara haukace mana suna faWin ai sun ma ji daWi sosai daya zama na, mun san komai, to wallahi mu sani ba wanda zai samu kwanciyar hankali musamman wannan ba?ar munafukar yarinyar da ta ?i mutuwa tun tana ?arama har ta samu ta dawowa gida, wannan al?awari ne suka yi ko za su tafi tsirara sai sun tabbatar burin su ya cika" haka dai suka wuce ransu a Sace."

"To sati biyu da suka wuce aka kiramu ana sanar da mu cewa Hajiya Luba da Hajiya rabi da Larai suna cikin mota Waya sun yi hatsari kuma cikin rashin sa'a motar ta ?one da su a ciki, duk'kan su sun mutu amma ban da Hajiya Rabi ita ta samu nasarar fitowa jikinta na ci da wuta."

"To dai a yanzu su anjima da binne tukar su saboda sun ?one ?urmus, ita kuma tana asibiti kullun maganar ta Waya ce, ita dai a kawo ma ta Wan uwanta da ?arsa tana son ganin su kafin ta mutu."

"Shi kuma Alhaji Isah ?ar sa Zuhura da ya kai karatu Italy wace yake son Salim ya aura, ita ce a ka kira shi ya zo tana asibiti ba lafiya, ko da yaje aka sanar da shi cewa kayan cikin ta ne suka lalace sakamakon yawan shaye shaye da take, don haka yanzu sai an yi ma ta, da she kuma duk da hakan ba tabbas Win za ta rayu.

"Yana cikin wannan jimamin ya fito da ni yar tafiya masaukin sa aikuwa ya haWu da wasu turawa daya taSa cin amanar su ashe ba su mantuwa, aikuwa suka sanya a yi ma sa dukan tsiya suka bar shi a nan gurin.

"A yanzu dai ya samu shanyewar Sarin jiki, shi ma dai mun je mun duba shi da muka samu labari, ita kuma ?ar ta sa, da ta rasu mun ro?i alfarma da ?yar suka bari muka bunne ta, shi kuma muka dawo da shi wannan ?asar, matar sa ko tace ita kam ba za ta iya da jarabar wankin kashi ba, da yi ma sa wanka, don haka ta tattara komai ta gudu ita da babban Wanta, yanzu daga shi sai masu aiki."

Duk sun yi shuru suna jin bayanin Kaka cikin jimamin...

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
PAGE 56
Kaka ya Wan gyara zaman sa sannan ya yi gyaran murya ya ce "To kun ji duk abun da ya faru ba tare da sanin ku ba."

Cikin jimami Momy Saratu ta ce "To Alhaji su kuma sauran yaran ?an matan fa Zahra da Aziza suna ina ke nan?"

Kaka ya ce "Hmm ai su ma abun sam ba sau?i, ashe ba su da aiki sai na yin ciki kuma su zubar wannan ba komai ba ne a gurin su, to zuwan su na ?arshe sai da aka sanar da su indai ba haihuwar cikin za su yi ba, to kar su bari su ?ara Waukar sa saboda akwai matsala, amma ba su Wauki shawarar ba."

Cikin ikon Allah wannan karon suka samu cikin ku san lokaci Waya, sun je fitar wa doctor ya sanar da su akwai hatsari fa, suka ce ba abun da zai faru sun amince ya yi aikinsa kawai."

Zahra aka fara yi wa, sai aikin ya yi kamar ya yi kyau ashe ta kamu da matsalar yoyon fitsari kuma mahaifar ta, ta kamu da kansa, ashe duk samun waWan nan matsalolin nata da yawa tana Wauke da HIV ne, shi ya sa abun ya yi yawa."

Ita kuma Aziza cikin rashin sa'a gurin cire ciki sai da rayuwar ta, tu ni ta riga gidan gaskiya, Zahra kuma tana nan asibiti tana karSar magani."

To kun ji su kuma kalar na su hukuncin Allah, ba mu sanar da ku ba ne saboda bamu son ku yi tafiya cikin rashin jin daWi."

Dady Ahmad ya ce "Ikon Allah dama Sufayya tace mu barsu da hukuncin Allah ga shi kuwa Allah ya hukunta su ba tare da mun Waga muryarmu a kan su ba, to su waWan da suka rasu Allah ya gafarta masu, su kuma zuwa gobe kafin mu wuce Abuja za mu je duba su in sha Allah." da sauri Samir ya ce "Amma Dady bada mu ba ko, kuma bada Sufayya ba?"

"Duk da ku har da ita ?anwar ta ku, kai har da yaran ku saboda ina son su ga kowannen mu cikin ?oshin lafiya musamman Sufayya" su dai Yayunta ba haka suka so ba amma ba yadda za su yi.

Da safe duk suka shirya tafiya gurin Hajiya Rabi Yayar Alhaji munir, tana ganin su hawayen ta suka ?aru kuka take sosai tana faWin ina Sufayya don Allah kununa man ita ina son na nemi afuwar ta, ba alamar kam za ta samu ganin ta saboda Yayunta sun kai ta bayan su sun Soye kamar wace za'a gudu da ita.

Dady Nura ganin tabbas ba za su iya barin Hajiya Rabi ganin ta ba, shi ya sa da kansa ya ri?o hannuta ya je ku sa, da gurin da take ya ce "Kin ga ?armu Sufayya."

Ta kaalle ta sosai "Tabbas wannan ita ce ?ar Munir da Zainab ko shakka babu, wannan ?a lalle ke Win da shen Allah ce, duk kalar muguntar da na yi maki sai Allah ya tsiratar da ke har kika dawo gida a lokacin da ba mu yi tsammani ba, don Allah ki ya feman na san na aikata maki ba daidai ba, na cutar dake don Allah ki gafarce ni."

Har Sufayya za ta yi magana Sufiyan ya san za ta iya cewa ta yafe ma ta ai kuwa da sauri ya ri?o hannuta ya ce "?anwata mu je mota yara sun ta shi daga bacci" haka ita da Yayunta suka bar gurin, nan iyayensu suka yi ma ta fatan samun sau?i suka yi tafiyar su.

Suna shiga Wakin da Zahra take suka ji wani irin zarni fitsari yana ta shi duk sun gaza ?arasa wa ciki, tana ganin ta mi?e tsaye zaune daga kwanciyar take sai kallon kowa take Waya bayan Waya amma ta gaza magana, ta Wan Wauki lokaci sannan ta ce "Don Allah Sufayya ki daure ki zo ku sa, da ni."

Sufayya ta yi yun?urin zuwa da sauri Sufiyan ya ri?e ta ya ce "Ina za ki je halan? duk abun da take son sanar dake ta sanar kina daga nan za ki ji komai ba sai kin ?arasa gurin ta ba."

A take hawaye suka wanke fuskar Zahra ta ce "Yaya ban ga laifin ka ba dama bai dace ta zo gurin mace irina ba amma saboda son kai irin nawa sai na manta da hakan, don Allah Sufayya ki yi ha?uri ki yafe man, na yi maki abubuwa da dama na to zarta ki, na wula?anta ki na yi maki hassada ashe hassadar tawa takice a gurin ki, kamar yadda hausawa ke cewa hassada ga mai rabo taki."

Amma ki sani na yi hakan ne saboda duk a tunani na kin hana burina ya cika na auren Yaya Sufiyan na manta shi Allah ba azzalumin bawansa ba ne, dama tsabar son kai ne amma ni na san, sam ban dace da zama matar shi ba, don Allah ku yi ha?uri."

Salim ya ce "To mun ji tun da dai ke kuma nan son duniyar ya kawo ki, Allah ya kyauta ke kuma ?anwarmu wuce mu tafi lokaci na tafiya."

Haka duk suka Wauko ?afarsu suka fito sun barta nan kamar sauran, daga nan suka yi wa, su Kaka sallama suka Wauki hanyar filin jirgi zuwa Abuja.

********************
Kwana biyu da zuwan su garin Sufayya na saman bene tana shan iska ga duk'kan alama yana yin na yi ma ta daWi saboda har da cire hijab ta ajiye a gefe Waya, tana cikin rufe ido tana buWewa can ta mi?e tsaye tana hango ?asan gidan can gurin get na uku wanda daga shi sai cikin gidan.

Da sauri ta Wauki hijab Win ko tsayawa ta gaza yi sanyawa ganin kamar za ta rasa abun neman ta a hannu ta ri?e sa, sau?i Waya dai doguwar riga ce ajikin ta mai dogon hannu, haka ta fice da gudu ba tare da ta luraba har tana ban ka Wai Yayunta dake shiri hawa saman su ma, ganin ta a wannan yana yin haka suka bi bayan ta da gudu suna kiran sunan ta, amma ko kallon su bata yi ba.

Tana zuwa bakin get Win ba ta ga abun da take nema ba, da sauri ta nufi get na biyu nan ma ta gama dube duben ta tana ta ratsa mutane amma babu nasara, da yake duk ranar narba da jumu'a muta ne, na turuwa ?ofar gidan saboda rabon kayan abincin da ake rabawa da yamma kuma a raba dafaffe.

Ganin bata ga abun da take nema ba ai tuni ta nufi get Win farko kafin ta ?arasa ta hango abun da take nema cikin farin ciki ta ?arasa ku sa da wata mata tana faWin "Babah mai abinci da gaske ke ce?"

Matar da ta kira da Babah mai abinci ta juya da sauri ta ce "Rashida ?ata ke ce a nan?" rungume ta Sufayya ta yi tana faWin "Ni ce Babah" sun jima a haka sannan suka rabu da juna.

Babah ta ce "Kin yi kyau sosai ?ata ban da na san daga ke sai ?anwar ki Furaira ke kira na da wannan sunan da ba zan gane ki ba, me kike yi a nan kar dai kice man ke ma abincin kika zo karSa saboda jikin ki sam bai nuna hakan ba."

Sufayya ta ce "Kai Babah ni dai bari na saka hijab Wina ki zo mu shiga cikin gida kiga dangina."

"Maa sha Allah ke nan yanzu kinga danginki kuma kina tare da su, har da waWan nan matasan, dangin na ki ne, naga kuna kama da juna?"

Juyawar da za ta yi sai ganin Yayunta ta yi a tsaye sai lokacin ta fahimci ashe suna gurin, ganin duk ransu Sace hakan ya sa, ta yi fuskar tausayi.

Samir ya ce "Duk wata fuskar tausayin da kika yi, ba za ta kwaceki a gurinmu ba yau, wannan gudun da kika sanyamu, duk mun Wau ka cewa wani abun ne ya tsorata ki ashe ba haka ba ne, da kin sanar damu abun da kika hango ba sai a sanya security su duba ba."

"To don Allah ni dai ku yi ha?uri na yi gudun kar ta Sace wa gani na shi ya sa, kuma ban da abun ku, ba ga shi na sanya ku motsa jikin ba."

Da sauri Salim ya yi kanta kamar zai kai ma ta duka aikuwa ta Suya bayan Babah dole ya tsaya, Sufiyan ya ce "Ai sai ki wuce mu tafi tun da duk motsa jikin da muke ko wace rana bai isa ba sai kin sanya mu wani."

"Allah Yaya na ga ji ?afata sai zugi take ba zan ita koma wa ba, ku sanya a kawo mota don Allah."

Sufiyan ya ce "Ai kuwa ba ki isa ba yadda kika zo da ?afar ki, haka za ki koma, sai da suka ga tabbas ta ga ji kamar za ta yi kuka sannan aka kawo motar, haka duk suka shiga gida har da Babah mai abinci.

Suna shiga Dady Ahmad ya ce "Yanzu nake zancen mubi bayan ku mun ji an ce angan ku kuna ta gudu kamar za ku ta shi sama" Samir ya ce "A mana wannan ?ar taku ce ta samu gudu kamar wasu tsuntsaye mun yi zaton ko ba lafiya ba, shi ya sa muka bi ta."

"Dady ni fa Allah ban san sun bi bayana ba kuma ni fa Babah mai abinci na hango shi ne ina gudun ta Sacewa ganina shi ya sa na yi gudu don na samu na tsayar da ita."

"A to tafi ku gaskiya to yanzu dai komai ya wuce ku zo ku huta" cewar Dady Nura.

Nan dai kowa ya yi ta, yi wa Babah sannu da ?o?ari bayan Sufayya ta ?ara gabatar da ita, sai faman yi ma ta godiya suke, Sufayya ta ce "Babah tun yaushe kika dawo ?asar nan?"

Babah ta ce "Ai ko wata Waya ban yi ba, na dawo saboda can Win babu daWi, dangina sun addabi rayuwata don na koma bada komai ba, dama na sanar dake idan kika ga sun yi murnar zuwana to na je da wani abun ne, kuma yana ?arewa shi ke nan wula?anci ya ta shi ke nan."

Bayan na dawo na yi neman aikin da zan yi don rufin asiri na, da ?yar na samu aikin dafa abinci a wata primary to a nan nake samun abun da naci kuma ?arshen wata a bani dubu biyar, ganin cewa wace nake gidan ta, ta gaji da ni har ta fara habaici, sai na fara tunanin kama haya ko Waki Waya ne, dama na san matar ne lokacin da nake da gidan abinci muna mutunci sosai ashe lokacin don ina da madogara ne."

"Ina cikin neman hayar ne wata mata da muke aikin abunci tare take sanar da ni akwai gida masu shi sun gina shi ne kawai saboda irin irin mu marar sa mafaka na zo idan ina da bu?ata, da sauri na bita kuwa, tare muke zuwa karSar sadaka a nan gidan."

"Ita ce ta fara nuna man nan Win sannan ta sanar da ni Waya daga masu gidan da muke zaune shi ne mai wannan gidan kuma shi ke bada wannan abincin ga mabu?ata."

"Ta sanar da ni a can baya mai gidan ya kan fito da kansa wasu lokutan ya ce "?arsu ce ta Waura su a kan wannan aikin amma kuma yanzu ba su tare ta jima da Sata, don Allah a taya su da addu'a Allah ya bayyana ta."

Daga bayan nan kuma sai suka sanar ?ar su ta dawo cikin aminci ayi ma ta addu'ar samun farin ciki mai Worewa, to kin ji abun da zan iya tunawa bayan dawowa ta ?asar nan ?ata."
***************
Sufayya ta ce "Allah sarki Babah rashin sani to ai nan gidanmu ne, nan ita ma ta bata labarinta bayan rabuwar su.

"?ata kin ga jarabawar iri iri a rayuwarki amma yanzu ina ro?on Allah ya san ba wani abu na damuwa da zai ?ara shigowa rayuwarki har abada" duk suka amsa da Ameen.
**********************
Wata Waya tsakani Babah mai abinci ta warware sosai saboda kafin subar ?asar Sufayya sai da ta saka aka samo ma ta wani ma daidai cin gida ta siya ma ta, sannan ta ba ta jari, yanzu kasuwanci take sosai sai dai ba ta koma wa sana'ar ta ba ta siyar da abinci.

Dady Ahmad kuma yana ta ?o?arin cika al?awarin da ya Waukarwa ?ar su, don a yanzu har ya saka aka wo su Malam Abuja daga nan za'a wuce da su Germany gurin da suke.

A can zamfara kuma ya saka a rushe gidan a fara sabon ginin zamani saboda so yake ko da, za su koma Zamfara su tarar da gidan na su ya kammalu kuma ya saka a nema masu ?aton fili a fara gina masu don idan sun je ziyara garin.

Yau dai cikin ikon Allah su Baba Malam da Mama har da Idris sun sauka a Germany, lokacin da Sufayya ta gansu ji ta yi kamar za ta ta shi sama saboda farin ciki, su kuma su Malam sai War War suke tun Abuja suka fara tsorata ganin gidan da aka ajiye su, yanzu kuma ga su Germany, su dai kam ba dan sun ga ?ar su ba, da ba abun da zai hana su yarda cewa siyar da su za'a yi ba?"

A daddafe sai da su Dady suka sanya su yin wata biyu a ?asar saboda aikin gidan da suke yi masu a Soye, kuma suna son ko da zasu koma angama komai shiga kawai za su yi.

Yau ce ranar da za su koma, aikuwa Sufayya an sha kuka har suka tafi tana faman abu Waya, bayan kwana biyu da tafiyar su, suka kira waya suna ta zuba godiya na abubuwan alkharin da aka yi masu, su Dady suka ce ba komai yi wa kai ne.

***********************
A kwana a ta shi ba wuya a gurin Allah lokaci na tafiya abubuwa sun faru da dama yanzu yaran Sufayya sun kai saura wata Waya su cika shekara huWu, su???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n girma sosai kamar ?an shekaru biyar ko Shidda, ga su da matu?ar wayo, yanzu sai sun ga dama suke zuwa part Win su Sufayya ko idan suna bu?atar wani, ko da yaushe suna gurin iyayensu maza Salim da Samir.

Yanzu haka shirye shirye kawai suke na birthday Win yaran su nan da wata Waya da kuma munar kammala karatun Sufayya ta zama cikakkiyar doctor yanzu, shi ne suke son haWewa rana Waya, an sanar da kowa har da mutanen Zamfara Babah mai abinci ma Sufayya ta ro?i ta zo, ita ce za ta Wauki nauyin komai, don haka ta amince amma sai ya rage kwana goma za su zo tare da mutan Zamfara.

Su Kaka dai tun yau suka sauka ?asar saboda sun ce komai a kan idon su za'a yi abun da bai masu ba su yi magana.

Kwana uku da zuwan su duk suna parlorn gidan Dady Nura, Sufayya na ?afafun Kaka Kulu kwance duk sun juyin duniya a kan ta ta shi ta ci abinci amma ta?i, har da yaran sai da suka zo suna Mami ki ta shi hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login