Showing 60001 words to 63000 words out of 123822 words

Chapter 21 - WATA KADDARA Complete Hausa Novels By (Yar gatan mama).doc

24 Sep 2025

3442

gurin yake kallon kayan, Aunty murya na rawa ta ce "kun gani na ce maku Sufayya ce."

Salim ya ce "Me ye dalilin ki nayin haka ?anwata?"

"Baka da wani ikon yiman tambaya a yanzu tun da har ka iya karya man al?awari, idan kuma a kan wannan kayan kake magana ?one su a gurina ba wani abu ba ne mai wahala bari ma na samo ashana yanzu ka ga ni."

"Wata?il ma sauya man kayan ku ka yi saboda dama can kun shirya duk wannan Win."

"Ban karya maki al?awari ba ?anwata, sannan ban sauya maki komai ba, kuma ke ma kin san da haka."

Aunty ta ce "Duk wannan shedar ba ki yarda da ita ba sannan ki na tunanin da kin ?ona ta shi ke nan, to bari ki ji ina da wata shedar, ki cire hijab Win jikin ki a hannunki na hagu akwai tambarin kalmar sunan ki wato S, ke da yarana maza duk kuna da wannan kalmar a hannu."

"Idan har kin duba babu ita to na yarda cewa ke Win ba ?ata bace, amma ki sani shi jini baya Suya Sufayya."

"Tun farko ki ce dai giya ya dace na fara nema ba ashana ba" ta kalli yayun nata ta ce "Don Allah ina zan samu giya yanzu?"

Duk kallon ta suke da alamar tambaya, ta ce "Ya kuke kallona haka? to ba sha zanyi ba."

Runtse idonta ta yi da ?arfi ta cire hijab Win jikin ta, karo na farko kenan da duk wanda ke gurin ya gan ta ba hijab, duk sai anyana wa suke cewa ?ara da Allah ya yi ta masoyiyar hijab da ta zama masifa saboda zubin haliltar ta, duk da ba wasu kaya ba ne masu fitar surar mutum doguwar riga ce a jikinta kuma mai faWi sosai sai dai kanta ba Wan kwali.

Gashin kanta Waurin da ta yi masa ya walwale duk ya zuba ajikin ta, har yana rufe mata fuska saboda iskan na urorin wutar dake aiki a parlorn, idan baka san cewa ita Win ?ar hausawa bace kuma ba hausa, da mutum zai rantse ya ce ita Win ruwa biyu ce.

Ranta a matu?ar Sace ta yaga hannunta rigarta na hagu, sai kuwa ga tambarin ta tun sunanta ya bayyana, ta ce "Ba wannan kuke magana ba, tun da dai har na san cewa bada shi aka haifan ba yanzu zan fitar da shi ta hanyar goge shi da giya, kinga kenan shi ke nan na huta da zancen sheda."

"Sannan maganar jini da kike yi" wu?ar da ke kan kayan marmari ta Wauko ta yanka hannunta da sauri duk wanda ke gurin ya yo kanta.

Cikin razana suke tambayar me ya sa ta aikata hakan? hannu ta Waga masu alamar kar wanda yazo ku sa, da ita sannan ta kalli Aunty ta ce "Kinga wannan jinin duk wanda zai yanka hannusa a gurin nan to kala Waya zai nuna wato JA kinga kenan jinin kowa iri Waya ne."

Aunty ta ce "Me muka yi maki ne? kika tsanemu haka? tsawon shekaru ina dubin hanyar dawowar ki duk yadda mutane na so in yarda cewa kin mutu amma na gaza yarda da hakan kullun mafarkina na ga cewa kin dawo garemu, amma yanzu kina nuna cewa ba wanWan da kika tsana irinmu, me ya sa haka?"

Aunty ta ?arasa maganar cikin raunin murya har hawaye sun Wan fara zuba a kan idonta.

Rahma ganin haka sai ta ji cewa duk kamar hakan bai dace ba sam ta ce "Ni fa ban tsane ku ba, amma ni kam a yanzu nafi bu?atar rayuwata ni kaWai bana bu?atar kowa musamman masu kuWi irinku."

Yanzu fa na gama jin labarin saboda kuWin ku aka so kasheni sannan na rayu gurinda ba mahaifata ba, na tsawon shekaru."

"Ni dai don Allah ku fita hanyata kubar ni na yi rayuwa ni kaWai, kuma hakan zaifi maku sau?i, idan har ina son zama ?a, ta gari dole na yi ha?uri da nawa farin cikin domin baku tsaro."

"Idan ina tare da ku tabbas za asa ke yun?urin cutar da ni, idan kuma ba su yi nasara ba a kan ku za su koma, gaskiya ni kuma bazan juri hakan ba, matsalolin da na shiga sun isa haka nan, don Allah ku daure ku fita tayuwata."

Dady Nura ya ce kina da ilimi ?ata kin san cewa talaka da mai kuWi duk na Allah ne, sannan shi ne ya bamu wannan dukiyar ba yin kanmu ba ne, ko dubarar mu."

"Amma ki sani kin fiye mana komai na cikin duniyar nan, wallahi ?ata ashirye nake mu ajiye komai duk abun da muka mallaka saboda ke, sai mu zauna yadda kike so, amma don Allah ki daina gudunmu."

"Tabbas haka ne Dady don Allah ku yi ha?uri idan na Sata maku rai, tsoro nake ji kar wani abun ya sake faruwa saboda ni, amma yanzu na fahimci bai dace na rin?a jayayya da hukuncin ubangiji ba, ya dace na san cewa wannan ita ce ?addarata."

Can kuma ta Sata fuska ta turo baki kamar wata jinjira ta ce "Amma fa ka sani Dady zan yarda ku Win iyayena ne, da ?an uwana."

"Amma gaskiya banda wannan matar sam bata so na, tun ranar farko da muka haWu ta wanke ni da mari wai don bance ina son Wanta ba."

Duk wanda ke gurin sai da, ya so dariya amma ban da Aunty, ri?e hannunta ta yi da sauri ta ce "Ki yi ha?uri don Allah wallahi ni, na yi marin amma kuma ni naji zafin marin a zuciyata tun lokacin na ?ara yarda da abun da nake tunani a kan ki."

"Ki yarda da ni, lokacin na ji tsoro ne sosai ina gudun kar mu sake rasa, Waya daga cikin yaranmu kamar yadda muka rasa ki, amma ki yafe man, in sha Allah hakan baza ta sake faruwa ba."

Momy Nafisa ta ce "Sannan kuma ?ata, ai kaza na taka ?a ?anta ne ba don bata son su ba, sai don ta nuna masu hanya, don haka dukanmu muna baki ha?uri a madadin ta ina fatan kin ha?ura?"

"A Momy komai ya wuce" Dady Munir kamar jira yake da sauri ya rugume ta, yana ta hawaye ya jima sosai a haka sannan ya sake, kana ganin shi kasan yana cikin farin ciki sosai.

Haka duk sauran iyayen su ka rin?a rungume ta Waya bayan Waya cikin farin ciki da murnar ganin ?ar ta su, can Rahma ta kalli Aunty ta ga, ta koma gefe ta zama kamar abun tausayi, Rahma ta fara tunanin wace hanyar zata bi Aunty ta walwale, duk ta zama kamar mai wani babban laifi.

Ta ce "Ke ba za ki rungume ni ba, wannan shi ne jiran da kike yiman na tsawon shekaru?"

Wata irin ajiyar zuciya Aunty ta sauke, ta rugumeta sosai kamar wace za'a kwacewa ita, kuka take sosai sai faWi take Allah na gode maka.

Sun jima a haka ita ma Rahma kukan take sosai, tabbas shu?in iyaye na da ban ne a rayuwa, ji take bata taSa tsintar kanta a irin wannan shu?in haka ba.

Sun jima a haka sai can Rahma ta ce "Don Allah malama tun da ba'a ciki za ki mayar da ni ba, ki sake ni haka nan, ina ma hijab Wina yake?"

Samir ya ce "Au sai yanzu za ki tuna hijab Win, bayan da hannuki kika jefar da shi, kuma ki godewa Allah dama ta rugunme ki, sanin kan ki ne Aunty bata bu?atar wasu ?a ?an saboda tana damu, saboda haka ki je gurin iyayen ki kar ki karya mana uwa."

"Oh malam a haka dai aka gama zubar man da hawaye saboda anga sabon jini, ku kuma duk kun tsufa, shi ne aka lallSo gurina, to bana so, koba haka ba Momy's?"

Momy saratu ta ce "Tabbas haka ne ?armu don ko yanzu sai mu goya ki mu zaga gidan nan dake, idan ba tsoroba wata ta yi wa yaranta hakan."

Salim ya ce aimu muna tausayin Auntynmu ba za mu bata wahala ba" sai lokacin Sufiyan ya yi magana ya ce "Tabbas haka ne Wan uwa."

Momy Aisha ta ri?e hannunta ta ce "Kinga zo mubar parlorn nan idan kuma ba haka ba Uwa da ?a ?anta ba za su bar ki, ki huta ba."

*********************
Kwana biyar da bayyanar Rahma cikin families ta, duk wanda ka gani yana cikin farin ciki, Dady Suraj ya ce "?ata tun da kin huta yanzu ya dace mu fara shirin zuwa Kaduna ki gai da Kaka Alhaji, shi kaWai ya rage cikin iyayenmu sai matar shi."

Salim ya ce "Allah sarki har na fara jimamin rashin Kaka Alhaji, ?an uwa ko kun manta ya ce, ba zai mutum ba sai yaga dawowar amaryar shi" duk'kan su, su ka sanya dariya.

"Ku dai bi a hankali yara idan baku ga mutuwar shi ba, ku ga mutuwar iyayen ku" cewar Dady Ahmad.

Da sauri su ka ce "Ah ah Dady aiku da saura gaskiya."

****************

Kwana biyu da yin maganar su ka shirya tafiya Kaduna amma Rahma ta ce ita a mota take son ayi tafiyar, dole haka su ka amince, sun sauka lafiya, a gajiye duk su ka sauka garin.

Kaka Alhaji ya yi farin cikin ganin su sosai saboda sun jima ba su haWu guri Waya haka ba, Kaka Alhaji mahaifin Dady Nura ne ma'ana Kakan Salim, shi kaWai ya rage amma duk Waya yake kallon su da sauran, duk kai tsaye yake bawa ko wanne su umurni kuma dole a bi.

Kaka Alhaji ya ce "Ai ke Sufayyatu da ace ni ne, na fara ganin ki, da a ganin farko zan ce wannan jinina ce, na san daga lokacin waWan nan ?an uwan naki za su san nafi iyayen su, da su kansu gani, ko ba haka ba Mata ta?"

Rahma shuru ta yi ba alamar amsa sam jin firar ta su kawai, iyayen nata ya kalla ya ce "Shin ko dai Amaryar tawa bata magana ne tun Wazu ina ta magana amma shuru?"

Dady Suraj ya ce "Haka take bata fiye son yin magana ba, sannan ya kalli Rahma ya ce "Ki saki jikin ki da Kaka Alhaji ?ata za ku saba kin ji ko?"

Baba kulu ta ce "A she dai halin su Waya da yayun nata shi ya sa, tasu ta zo Waya tun farko?"

Murmushi Rahma ta yi, ta ce "Kaka gaskiya ka faWa amma sai na ke ganin sai dai kafi yuyun na wa gani, ba dai iyayena ba."

"Kuma dalilin da, ya sa ban yi magana ba tun Wazu, jikina ne ya yi sanyi sosai, na zo da Waukin zanga Angona wani shar shar da shi sai naga ashe ma duk ka tsufa, gaskiya ni kam ina ga na fasa wannan auren."

"Ah ahh yarinya ai sai dai ha?uri amma ki sani aurenmu na zobe ne, ba rabuwa."

Baba kulu ta ce "Ni fa tun da aka ce, za ku zo na ke ta fargabar kar dai ace kishiyar tawa ?atuwa ce kin san kishi da ?aton mutum yadda yake da abu ya haWa su sai su zaune mutum, amma sai na ga ashe ma ?ar firit ce koni na fita kumari don haka yanzu asherye nake yarinya."

Salim ya ce "Ah ah ?ar tsohuwa ban da cika baki abun ba ajiki yake ba, kar ki yi wasa da wannan ?awar tamu, idan ta zaune ki, ba za ki iya ta shi ba."

"To na ji masu ?anwa, lokaci zai nuna mana waye yafi ?arfi."
Haka dai aka yi ta zolayar juna....

*WATA ?ADDARA*
*ANOTHER DESTINY*
By
*SUWAIBA M AMIRU*
(?ar gatan mama)
'
*PAGE* 3?? 9??
Kwana biyu suka yi a Kaduna, suka fara shirin komawa, amma Kaka Alhaji ya ce sai an je gidan gonar Sufayya ta ga ni, haka ko suka Wauki hanyar tafiya.

Sun isa cikin gidan gonar da gudu Sufayya ta yi cikin kajin da tsuntsaye kala kala duk sai da ta zaga ko ina, kana ganin ta za ka fahimci ta na cikin farin ciki sosai."

Su ma dabbobin kamar sun san ta daga ?ananun har manya ba wanda ya yi yun?urin cutar da ita, hasalima su ma kamar suna cikin farin cikin ganin ta.

Iyayen da ?an uwan na ta ?an kallo su ka koma, suna ta kallon ta cike da farin ciki, yayun kuwa sai faman yi mata photos da video suke, da ta fahimci hakan, sannan ta Wan natsu ta dawo cikin su ta zauna.

Nan ma kwana biyu suka yi sannan suka Wauki hanyar koma wa Abuja har sun kai cikin gari, amma kuma motar su Sufayya na bu?atar ?arin mai, da yake ita da Yayunta ne a motar.

Waya suka yi wa iyayen a kan cewa za su tsaya gidan mai hakan ya sa su ma duk suka tsaya, bayan an gama zuba masu man, har za su tafi ta jiyo muryar wani ya na bara aikuwa ta hana su tafiya dole suma duk suka fito.

Salim ya ce "Ina kuma zuwa ?anwata?"
"Biyo ni ka gani Yaya."

Tana zuwa gurin mutumin ta ce "Ado ya kake yana ganka a nan ba dai har dukiyar ta ?are ba, ya kake kallona haka ko sai na yima bayanin kaina? to Rashida ce Yayar Furaira da ka, kashe."

Da sauri ya zube ?asa yana ta kuka yana faWin "Don Allah ko ke ce, ki ce kin yafe man wata?il na samu sassaucin wannan azabar da nake ciki, na san ba zan ga Furaira ba balle har na nemi afuwarta, amma na san yadda take son ki sosai na san idan har kin yafe man to ita ma za ta gafarta man."

"Na aikata laifuka da dama a rayuwata amma babban kuskurena a rayuwa shi ne abun da na aikata a kan iyayen Furaira, da ita kanta Furaira har da ke."

"Bayan na bawa Furaira guba tana barin gurin na je rugarmu na Wauki Baffana muka je siyar da duk dadbobinmu dana Baffan Furaira waWan da muka kwashe dama can mun siyar da gidanmu da gonankinmu har da na Baffa."

Mun gama haWa kuWin komai da ni yar mu koma birni mu gina sabuwar rayuwa muma mu more, amma aka yi rashin sa'a mun je tsallaka titi wata babbar mota ta Waukemu ni ta jefa ni gefe shi kuma Baffa ta malkaWe shi a kan titin, sai da ya zama ba'ama gane shi duk ya yi ?ire ?ire dole sai tattara naman shi guri Waya aka yi, aka binne shi haka nan."

"Ni kuma koda na farka na rasa ?afata da yatsun hannuna sannan babu kuWin, wasu sun sace, nan ake sanar da ni iran mutuwar da Baffa ya yi, na yi kuka sosai da dana sani amma a lokacin ba su da amfani."

"Bayan wani lokaci asibitin suka ga ji, da ni suka sallame ni saboda ba ni da kuWin da za su, yi man aikin ?afa, yanzu haka dai a cikin ta sha nake kwana idan safiya ta yi, na fito bara na samu abun da zan ci."

"Yanzu kin ga ?afar ta wa sai ruwa take fitarwa tana wannan warin haka, yanzu haka duk in da na je cikin mutane, sai kiga ana ta kora ta wai wari nake, don Allah ki yafe man wallahi na tuba na yi nadama."

Dariya ta yi sosai sannan ta ce "Ikon Allah, Allah na gode maka, tun ba'aje ko ina ba abubuwan alkhairi sun faru haka, amma gaskiya ina taya ka murna sosai malam Ado."

Du?awa ta yi kusa da shi ta ce "Na ji zan yafe maka amma da sharaWi Waya, za ka iya dawo man da su Baffa da ?anwata Furaira?"

"Ina har za ka dawo man da su, to ni kuma na yi maka al?awarin yafe maka har abada, amma ka sani rashin dawo man da su, shi zai sa na?i yafe ma, kuma ina da ya?inin su ma ba za su taSa yafe maka ba."

"Sannan bari na baka wani labari mai daWin ji, kafin ?anwata ta rasu sai da ta tsine maka sosai, ka ga kenan tsinuwar ta ce, ke bin ka da kuma ta su Baffa da ni kaina ba abar ni a baya ba, don ba zan taSa yafe maka ba, koda a kan idona za ka mutu."

"Sannan jarabawa baka gama ga ni ba in sha Allah, ka gama ganin ta duniya kuma ka je lahari ka gamu da ta can."

Ta na gama faWar hakan ta dubi yuyunta ta ce "Yaya ku wuce mu je don na fara jin amai sosai."

Hannunta suka ja ta, da sauri sai mota, su ma iyayen na su duk suka shiga motocin su, nan suka bar Ado yana ta kuka, mutanen gurin nata Allah wadai da halin shi.

Gidan Alhaji Nura suka sauka, Dady Ahmad y ce "Wallahi duk jikina ya yi sanyi sosai lalle duniya abar guduce sam bata da tabbas, yanzu ji yadda wannan yaron ya koma duk da ban san yadda yake ba can da, amma da gani ka san yana shan wahala."

"Sai dai tun da, na ji labarin abun da ya aikita na ji duk na tsane shi sosai."

Salim ya ce "A wallahi Dady ni fa da fari na Wauka Sufayya kyauta za ta ba shi, ashe shi ne Ado, amma abun da ta faWa ma shi ya yi man daWi" duk wanda ke gurin suka ce, to Allah dai ya kyauta.

*********************
An zagaya gidan kowa da ita gidansu ne, na ?arshe gidan Dady Munir kenan, suna zaune kamar ko da yaushe cikin parlor, Dady Nura ya ce "?ata yanzu me ki ka tsara za ki yi nan gaba Aure ko karatu?"

Du ka Yayun na ta sai da, su ka Wago su ka kalle ta, ?irjin su sai faman halbawa yake, ita ma su take kallon can kuma ta sun kuyar da kanta ?asa."

Shuru ta yi, na Wan lokaci can kuma ta ce "Dady karatu nake son na yi, ina fatan zaSina bai saSawa ra'ayinku ba, ni kawai ina son cika burina ne idan ba damuwa."

Dady ya ce "Ba wata damuwa Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhari, amma yanzu wace ?asar kika yanke shwarar yin karatun?"

"Ban yanke ko wace shawara ba Dady duk abun da, ku ka yan ke shi ne daidai aguri na."

Sufiyan ya ce "Idan ba damuwa Dady ni da ?an uwana har mun sama mata admission a Germany tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login