Showing 153001 words to 156000 words out of 161948 words

Chapter 52 - ABU - MALEEK Book Complete BY SARAUTA.txt

05 Jan 2025

6622

yanzu da kyau na da kwari na" ya faɗa cike da wasa, kunyar ɗaya bata ne yasa tayi saurin ɗura kanta a cinyarsa hakan ya tabbatar masa da cewa ta amince kanta ya shafa yace.
"Thank you for saving my family Roomana" girgiza masa kayi tace "it's my pleasure" Murmushi kawai yay mata kafin yace "You can go" tashi tayi ya bita da kallo kafin a hankali ya Lumshe idanunsa yana tunawa da matarsa masoyiyarsa Oumuu-Ayman.
Ana kiran sallar magrib Abu Maleek da Julde na farkawa da sauri ya miƙe yana dafe goshi, bathroom ya shiga yana ɗaura alwala yana fitowa ya shirya cikin tattausar jallabiya ya nufi Masjid, itama bathroom ta shige ta sakarwa kanta shower kafin ta ɗaura w ta fito ta shirya cikin Abaya Sallah ya gabatar, kana ta shirya kanta cikin wasu haɗaɗɗun falling rose pattern nightdress white colour wanda sukai mata masifar kyau, Lip balm ta ɗauka ta shafa a laɓɓanta, kafin ta turare jikinta da turaren Al'ajabu, fita Parlo tayi tana zabga ƙamshi ta fito a matar sarkin ta, zama tayi kan sofa tana jiran dinner domin yunwa ta keji sosai.
Tana nan a zaune ne wayarta tayi ƙara alamar notification ne, ɗaukan wayar tayi ta shafa haɗaɗɗan photon ta ita da Abu Maleek ya bayyana, ganin kuma kamar saƙon na whatsapp ne yasa kai tsaye ta shiga,prvt number ce, shiga tayi ta fara download na abinda ka tura mata, da wani irin sauri ta dafe ƙirjita, jikinta ya ɗauki rawa tashin hankali, firgici da kuma ladamar ganin abinda ta gani ya shige ta, wani irin ƙara ta sake lokacin da idanunta ya sauka akan....




Gonna missing🥲😍




*SARAUTAR MARUBUTA*










*_99-100_*
Wasu photos wanda ganin photo nan ya hadasa tsayawar komai nake mata yawo a tsakiyar kanta, tunaninta ya tsaya cak jiki na rawa ta shiga bin photo nan da idanu, a hankali ta sulale a ƙasa tare da sakin kuka, kukan da ita kanta ta jima ba tayi irinsa ba, kuka take da dukkan ƙarfinta wanda duk wanda ya ganta zai cewa tana cikin halin ƙunci baƙin ciki damuwa,da takaicin abinda ta gani, al'amarin ya ɗaure mata kai duk yadda takai data danne ta hana kanta kuka lamarin ya faskara.
Sai da tayi kuka for good 20mins kafin a hankali ta dinga sauke ajjiyar zuciya, gaba ɗaya ta fitar a hayyacinta idanunta sun kumbura sosai idan akwai mutum a parlo babu abinda zai hana shi jiyo yadda yake sauke wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya kamar ranta zai bar jikinta.
Abu Maleek a hankali suka fito daga masjid shida Adams da Baffa, sai Maleel da Khaleluddeen wanda ya sanya su a gaba, duk inda suka ratsa Fadawa ne ke zubewa suna gaida su, a haka suka isa parlo Baffa na part ɗinsa, suna zama kuma Queen Roomana ta shiga ajjiye masu cup of coffee sai tiriri yake, Baffa ne ya ɗauki coffee tare da kaiwa bakinsa ya sha kaɗan, a hankali Abu Maleek ma ya kurɓi coffee hankalin sa gaba ɗaya yayi kan matarsa, ya jima kafin yaji ɗumin Jikinta, gyara zama yay yana ɗan shafa kansa, lura da Baffa yay kamar da magana a bakin Abu Maleek yasa shi faɗin.
"Yadai Our king?" Marai-raice fuska yay yana ɗan lumshe idanunsa kafin a hankali cike da gajiya ya buɗe baki yace.
"Baffa daman akan kejera ne, tunda ka dawo sai ka ɗura inda ka tsaya ko Baffa?" Kallonsa sosai Muhammad Jalal yay yana ɗan Murmushi kafin a hankali ya kalli Abu Maleek yace.
"Saboda kai ba zaka iya ba ko mene?" A hankali ya girgiza kansa kamar zai kuka a shagwaɓe kuma yace.
"A'a Baffa, ina son ci gaba da buga ƙwallo na, ni bana son a takure ni" ajjiye Coffeen Baffa yay cikin nutsuwa da kamewarsa yace.
"Ball kana bugata ne domin me?" Shiru Abu Maleek yay yana rufe ƙofar Murmushi kawai Baffa yay yace "answering my question my friend" zamewa yay daga saman kujerar tare da zama wajan ƙafafuwan Muhammad Jalal yace.
"Baffa ball is my dream and hobby please allow to do it Baffa, and ban san komai na wannan mulkin ba, ga Adams nan sai kawai ya hau madadina ko Bro" ya faɗa yana kallon Adams, Shiru Adams yay tabbas yana son muƙamin Mahaifinsa amma daya tuna cewa bashi da wata power da freedom sai kawai ya girgiza kai yace.
"A'a kam Allah ya sawwaƙa min dole kayi fa Malam" a wannan karan dariya Baffa yay ganin yadda Khaleluddeen yake ta kallonsu kafin yace "look wannan shine zaki, bakai ba, Ni ban san wanda ya sanya maka wannan sunan ba, idan sai zaki ne kai ɗin ai sai dai ka zama fasa taro ba mai tsoran mutane ba" kwaɓe fuska Abu Maleek yay kamar zai kuka yace "haba Baffa, I'm hero ka tamabayi Mami i can handle everything" Baffa na shan coffee yana satar kallon Abu Maleek ɗin wanda komai irin nasa ya ɗauka komai, hatta wannan marai-raice war haka yake ma mahaifinsa da Mai Babban ɗaki, shi kam ai Malamin Alaafin ya gama dashi daya sanya aka sauya masa kamilalliyar fuskarsa, gyara zama yay yace.
"Eyee! Su hero manya idan haka ne sai ka shirya mulkar dubban jama'a, daman kuma naji Mamin naku na faɗin lokacin RAN GADI yayi, ba komai kake so kuma ka samu ba, sai kaga abinda kake gudu shine alkairi a gareka, Mulki yana da daɗi idan ka sanya tsoran Allah da kuma taƙawa a zuciyarka, ka sanya cewa Tabbas rayuka da duniyoyin jama'ar da suke ƙarƙashin kulawar ka zaka kare, kada ka sake ruɗin mulki ya ɗauke ka, abinda baka sani ba idan har akace jinin mulki na yawo a jikinka is hardly ace baka son mulki sai dai kawai wani abu ya ɗauke maka hankali"
Shiru Abu Maleek yay kafin ya kalli Baffa a sanyaye cikin mutuwar jiki ga wata fargaba data kamashi yace..
"Zanyi Baffa,amma what about my ambition?" Kallonsa sosai Baffa yay a karo na farko kallon da bai taɓa yi masa irinsa masa tunda suka haɗu cikin kulawa yace.
"Shima zakai ai, duk sanda buga ball ɗin ya tashi kayi bazan hana ba amma dai ƙato dakai da ball wai"
Dariya duk sukai har Khaleluddeen da bai san komai ba, suna cikin dariyar ne Mami ta shigo hannunta riƙe dana Maleek yana ganin Abu Maleek ya ƙwace hannunsa da sauri yazo wajan Abu Maleek ya faɗa jikinsa yana dariya, kallonsa Abu Maleek yana mamakin yadda yaron ke son shi haka, duk da cewa ya tabbata ba shine mahaifin sa ba, sassanyan Murmushi yayma yaron da yake faɗin "I miss You Bàami" Adams ne yace "kai Babanka kawai ka sani ko?" Dariya Baffa yay yace "Ai fa, gashi ko kakansa baya kulawa" zama Mami tayi nesa dasu tace "wanne mataki ka ɗauka akan mahaifiyar yaron? The you like to stay with her? Ko mene?" Da sauri ya girgiza kansa yana taɓe baki yace "No Mami! I'll devorce" jinina kai tayi kafin tace "Otun yace yana son Zubaida zai aureta" wani farin ciki ne ya kama su gaba ɗaya da sauri Adams yace "Mami kefa?" Juyawa Abu Maleek yay yana kallon Baffa kafin yace "Baffa you should marry her kaji a daina wannan mema sunansa ahha! Ƙwarƙwara wallahi Baffa ban so ni" Murmushi Baffa yay yana kallon Mami wacce kunya ta kamata yace "I love her ai ina sonta sosai and I'll marry her today" wani Ihu sukai Ihu Abu Maleek yay tare da Adams hakan yasa Maleek da Khaleluddeen kwanciya a ƙasa suna dariya da sauri Jalaluldeen ya miƙe yace "Yes!Yes! Thank you Baffa" ya faɗa yana rungome Mami wacce take murmushi, Adams wajan Baffa yay yana Rungome sa yace "Wow! What a beautiful couple Mami& Baffa, Wow! Wow! Thank you Mami kinyi dacan samun kamar Baffa wallahi ba duk kai ba" Murmushi Abu Maleek yay yace "Ohhhu! Mami na dai tafi Baffa ƙwari da kyau" Murmushi Baffa yay yana Rungome Adams yace "Malam sake min Iyali, kaje ka ɓoye matarka zaka kassara min tawa ko?" Murmushi Abu Maleek da sauri yace "Bye Baffa bye Mami good night"
Dariya Mami tai masa tace "ance mahaukaci baka duka yace har kun tuna min, wato sallar Isshā ɗin a ɗaki zakai kenan" baice komai ba ya fita, kai tsaye part ɗin Mai Babban ɗaki ya nufa bayan yaje ya gaida sosai, kana ya nufi wajan sashin Ayoola lokacin tana zaune sai kuka take yara biyu ta rasa kuma duk hukuncin kisa ya hau kansu ita kam ta shiga uku, haƙuri ya bata sosai kafin ya nufi sashin Bola tana zaune ita ɗaya tana ganinsa tai saurin ƙasa da kanta yana daga tsaye yake binta da kallo a hankali kuma a sanyaye ya fara bata haƙuri cikin lallausar Muryar da kamilalliyar lafazi, daga bisani kuma ya bata takardar sakin ta, Murmushi kawai tayi hawaye na zubu mata ta kasa magana har yaje bakin ƙofa ya tsaya yana faɗin.
"Maleek yana waje na har abada" yana faɗin hakan yay waje sai da yay sallar Isshā a gabansa kuma aka ɗaura auran Baffansa da Mami, dai kuma na Otun da Hadima Zubaida jiki a matuƙar gajiye ya nufi part ɗinsa yunwa ya keji sosai.
Masu tsaron ƙofar sa ne suka zube suna gaida shi a hankali kuma cike da nutsuwa ya shiga cikin side ɗin nasa, wata Lamintacciyar ajjiyar zuciya ya sauke lokacin daya sauke idanunsa akan to tana zaune akan kujerar idanunta a lumshe, a hankali kuma take sauke ajjiyar zuciya kamar wacce ta shekara tana kuka, walking slowly yake tafiya zuwa inda take zaune haka kawai yaji gabansa na faɗuwa sosai, yana zuwa ya zame tare da zama kusa da ita a hankali kuma yake binta da kallo jin yadda yake take ta sauke ajjiyar zuciya, hakan yasa a hankali ya miƙa hannunsa tare shafa fuskarta, idanunta ta buɗe fuska babu yabo babu fallasa ta ɗan kallesa cikin ƙasa da Murya tace.
"Sannu da zuwa" kallonta yay sosai nan take kuma yasan akwai abinda yake damunta domin jikinsa ya riga daya gama bashi something is feshin, a hankali a taushashe kuma yace "what wrong with you My Queen?" Ba tare data kallesa ba ta miƙe a hankali tare da durƙosa wa a ƙasa , hankali ta kama ƙafarsa tare zare masa takalmi bayan ta kama,ta kama hannunsa zuwa cikin part ɗin su kai tsaye bathroom ta shigar da shi, ta haɗa masa ruwan wanka a tube ta zuba turare, fita zatai yay saurin kamota ya manna ta da ƙirjinsa muryarsa na rawa yace "what i have done to Queen Hawwa'u Julde Muido? Me mai maki?" Wani irin killer smile tayi tace "me kuwa zakai min?" Girgiza kai yay kamar zai kuka yace "No! Wallahi akwai abinda nai maki i knw my wife nasan all good habit naki dan Allah kada ki rama dukkan wani abu da nayi maki ta hanyar hana kunne na jin sautin zazzaƙar Muryar ki, please ki gayan dan Allah" hawaye ne yake ƙoƙarin zubu mata sai kawai ta ƙwace jikinta tayi waje, yi yay kamar zai biyota sai kawai ya fara wankan Sharp-Sharp ya gama ya fito ɗaure da towel, yana jefanta da wani irin mayataccen kallo, mamakin sauyinta duk ya damu zuciyarsa, miƙewa tayi jiki ba ƙwari hannunsa ta kama tare da zaunar dashi a saman stool a hankali ta ware towel ɗin jikinsa ta basshi naked, wani body lotion mai ƙamshi ta fara shafa masa a saman fatarsa, wani irin sassanyan numfashi Abu Maleek ya sauke, lokacin da yaji saukar hannunta a tsakiyar ƙirjinsa tana gogawa a hankali tare da murza wajan.
A hankali yay ƙasa da kansa dai-dai fatar wuyanta ya manna bakinsa a hankali ya ware laɓɓansa tare da fito da tongue ɗinsa ya manna bakinsa sosai a wajan a hankali kuma ya bawa wajan wata Amintacciyar tsotsa yana wani irin jan numfashi.
Wani irin maraitaccen numafshi suka ja a tare a kuma lokaci guda suka sauke numfashin, yadda yake lasar fatar wuyanta yana tsotsa yasa, jikin Julde ya fara rawa da wani irin ɓari a hankali kuma ta fara kokawa da numfashinta dake ƙoƙarin barin ta, shi kuwa Abu Maleek wata Amintacciyar tsotsa ya ƙara yiwa fatar wuyanta a hankali kuma ya kauda kansa ya sauke wani irin fitinannan numfashinta yana jin yadda J ɗinsa ta fara harbawa.
Tsayawa tayi a hankali kuma ta fara dai-dai-ta Numfashinta, bayan ta kammala shafa masa ne ta nufi wajan wardrobe wasu Milk ɗin Pajamas masu kyau ta ɗauko ta ajjiye masa, tana gamawa ko abinci bata samu taci ba, ta haye gado abinta tare da jan duvet ɗin ta rufe jikinta.
Da sauri Abu Maleek ya miƙe bai ma tsaya sanya kayan ba ya nufi bed ɗin tare da shigewa cikin duvet ɗin, da sauri Julde ta miƙe tsaye tace.
"Don't touch me" da mamaki yace "why? Baki missing nawa bane? Kin san kewarki da nayi kuwa? Me nai maki?" Taɓe baki tayi tace "raguwar wata ne banso" da wani irin sauri ya miƙe zaune ya binta da kallon mamaki, murya can ƙasa yace "raguwa? As how?" Idanunta dake kawo ruwa tai saurin janyewa tace "eh raguwa, batun missing kuma wannan ba gaskiya bane tunda har zaka iya zuwa ka nemi baturiya" da sauri jikinsa na wani irin ɓari yasa hannunsu ya fisgota jikinsa tare matse ta sosai a jikinsa Murya na rawa yace "wallahi bani bane, ban san komai ba, bai taɓa aikatawa zina ba,ko wanda yake ina nisanta kai na dashi, dan Allah kada ki azabtar da zuciyata da soyayyarki, wannan abin nake gudu ga mace, ki tausaya min wallahi ko wanda na aikata a baya ƙuruciya ce da sharrin shaidan wallahi tun lokacin ban taɓa kallon wata ƴar mace ba sai ke da kike haliliya ta, wane ya faɗa maki?" Kuka ne ya kwance mata da sauri ya ƙara rungome ta a jikinsa tare faɗin.
"Believe me Queen Hawwa'u Julde Muido, wallahi ban taɓa zina ba, Yasubuhanallah Tayaya ma zaki faɗi haka akai na, bayan kin san waye ni? And mene yasa kika faɗi hakan?" Zame jikinta tayi tare da ɗauko wayarta kai tsaye wajan photos ɗin ta shiga tare da nuna masa da sauri ya amsa yana faɗin "What! Subuhanallah this gal" photonsa ne tare da Supia wacce yana manta da ita, zai iya tuna ranar daya bar wajan buga wasan su ya haɗu da ita a hanya, Tayaya akai ta samu number matarsa? Tabbas akwai dalili, wata zufa ce ta shiga keto masa Murmushi kawai Julde tayi tace "zaka iya ban wayata ai" idanunsa ne ya cika da hawaye yace "wallahi ban aikata komai bari kiji yadda abin yake" da sauri ta ɗaga masa hannu tace "bana ƙwai na sai da zakara" cikin sauri yace "eh ai nine nama zakaran" taɓe baki tayi tace "whatever, ni ban buƙaci jin komai ba, Allah ya kyauta kawai ni dai ban ƙara haɗa waje dakai" tana faɗin hakan tai wani bedroom cikin sauri ya biyo bayan ta, kafin ya isa tuni ta rufe ƙofar, zamesa yay a wajan tare da dafe kansa dake bala'in sara masa, ga wani irin ciwo da mararsa ke masa domin ya riga ya saba da jikin matarsa.
Cikin wata iriyar Murya wanda kuka ke shirin ƙwace masa yace.
"Wallahi Allah kenan ban san wannan Yarinyar ba? Tayaya ina da mata kamar ki zanje wajan wata? ko bani dake bazan taɓa aikata hakan ba, open the door I'll explain everything to you My Queen" a hankali itama kukan ya kwance mata ta yarda da Maganar sa amma menene matakin wannan photo nan? Da take ganin mace kwance a jikinsa? A wannan daran babu wanda ya runtsa a cikin su kuwa tunani yay masa yawa.
Washe gari da ƙyar ya miƙe tare da yin alwala ya shirya cikin farar Jallabiya kana ya nufi Masjid, bayan an idar bai iya dawowa ba a masjid ɗin ya zauna tunani fal ransa.
Abu fa kamar da wasa suka ɗauki sati har aka fara gabatar da shari'ar su Sharefddeen amma Julde ta ɗauke wuta, zatai masa komai amma ko rungome ta bata bari yayi, tashin hankali firgici ya shiga sosai, kullum sai yay mata kuka kamar yadda itama kullum take kukan kewar jikin mijin nata, a haka yake zama a fada fuska babu walwala,yin duniya kuma Mami tayi amma a banza.
A yau sun ɗauki good 1mnt kenan yana can wajan ɗaurin Auran Junaid da Bola.
A hankali ta fito daga cikin bedroom ɗin da take tana sanye cikin wani Maroon ɗin lace mai kyau ta murza ɗauri sai baza ƙamshi take, parlo ta nufa da sauri ta buɗe basket ɗin lunch ɗin da aka kawo masu, yawon bakinta har zuba yake plate ta ɗauka ta zuba zallar naman kazar sai da ta kusa cinye kaza guda tana lumshe idanunta, babu abinda taci ruwa ta ɗauka ta kura dashi kafin, ta miƙe akan kujerar tana jin wani ƙwaɗayin naman na tasu mata, a hankali kuma ƙarar waya ta karaɗe Parlo kamar ba zata tashi ba sai kuma ta miƙe, Wayarsa ce ya mance da ita, kira akai har wajan sau biyar a hankali tai answering zuciyarta na bugawa tana ɗagawa muryar mace ya daki kunanta.
"Hello! Abu Maleek nasan zuwa yanzu ka rasa gane kan matarka dalilin photon ƙawata dana tura mata, nice nan Kubraahh nasan ka mance da ni tun sanda ka sake ni, weel naje Madrid ko zan sameka sai na haɗu da ƙawata Supia a wayarta na samu photonka, kuma ta tabbatar min babu abinda kai mata domin baka cikin hayyacinka ne shiyasa ta kawoka gidanta, kawai kayi mata ne shiyasa ta ɗauki photo da kai, ni kuma hakan yay min daɗi sosai, na sami hanyar da zan muzanta rayuwar Auranku kai da wannan bafulatanar, Finally kuma naji daɗi"
Tunda ta fara magana hawaye ke zuba daga idanun Julde zuwa saman fuskarta, tausayin mijinta da haƙƙin sa data ɗauka ya shiga damunta, cikin dakewa tace.
"Ji banza, tun kafin ki turo min nasan labarin Supia a wajansa, rayuwar auranmu babu abinda ya faru dashi sai alkairi domin ina ɗauke da cikin mijina Abin alfahari na jagoran rayuwata, garkuwa ta Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal, dan haka abin wani jirgin Malama Kubraahh"
Tana faɗin hakan ta kashe wayar tana kuka, gyaran murya da taji a bakin ƙofa yasa ta miƙe da sauri shi ne yay tsaye a bakin door way, ya harɗe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login