Showing 45001 words to 48000 words out of 161948 words

Chapter 16 - ABU - MALEEK Book Complete BY SARAUTA.txt

05 Jan 2025

6592

hannun Julde, bayan ya finciki naman hannunta ne kuma ya kafa bakinsa ya shiga zuƙar jinin dake zuba ta jikin wajan daya cire naman wajan.


Zuciyar A.m ce ta buga da ƙarfi tare da wani irin harbawar daya sanya shi sanya hannunsa ya dafe tsakiyar goshinsa, tashin hankali ƙarara ya bayyana a saman fuskarsa.


"Innalillahi wa'inna ilaihir Arjun!" Shine kawa abinda yake fita daga ƙasan zuciyarsa tare da fitowa ta cikin bakinsa, yayinda wata ƙyakƙyawan zufa ta shiga yanko masa, jijiyoyin kansa suka shiga Miƙewa.


A hankali ya dinga jaa da baya, sai sauke Ajjiyar zuciya ya kamar wanda yayi tsere, bai taɓa ganin mutanan da suke cin naman mutum ko susha jinin mutum ƙarara a zahiri ra'ayin aini ba, sai yau, wanne kalar abu ne haka? Mene Amfanin shan jinin mutum? Waye wannan ɗin? Sune abubuwan da yake ta tunani a ransa amma babu amsa.


Wata kalar zabura yayi saboda tunawa da mutanan Birnin Bera, ƙara mai da idanunsa yayi kan mutumin daya dage yana shan jinin Julde, ba wasu sutturar arziƙi ne a jikinsa ba, sai wani jan bante daya sanya ya rufe al'aurar jikinsa, yayinda jikinsa yake baƙiƙirin.


A hankali ya juya ya shiga duba wajan, ga mamakin sa sai yaga babu kowa na dangane da mutanan Birnin Bera sai wannan mutumin hakan ya tabbatar masa cewa ƙwace wa yayi daga cikin Birnin Bera ya fasu jikin gari!.


Julde dake fidda wani kalar numfashi bakinta ya shiga fidda wata kalar Kumfa, mai yauƙi ga kuma yadda Jikinta ke ɓari kamar wacce take jijjiga, azabar data keji a cikin jijiyoyin dake Jikinta wacce jini ke gudana a cikinsu ɓata Lokaci ne, zuwa yanzu kam gaba ɗaya tunaninta ya fara sauyawa yayinda hancinta ya fara ɗauko mata wani kalar ƙamshi wanda bata taɓa jin maka mancin sa ba.


A sannu a hankali kuma ƙamshin data keji ya fara juyewa yana dawowa ƙarnin jini, da sauri kuma ta zabura tana ɗan buɗe bakinta yayinda ta ware idanunta akan A.m dake tsaye dukkan jikinsa yana ɓari tamkar wanda ake buga masa gangi.


Kwaɓe fuska yayi tare da marai-raice wa, ya ɗan langwaɓar da kansa gefe guda, saboda wani Irin kallo da yaga Julde ta nayi masa, wanda a zahiri shike Ganin hakan amma sam bata ganin komai kawai Ubangiji ne ya nufe ta da kallon saitin da yake tsaye.


Shiru Julde tayi saboda wani irin baƙon yanayi daya fara shigarta, yayinda gaba ɗaya ta kasa fahimtar komai, sosai taji zuciyarta na buƙatar wani abu, yayinda hancinta ke jiyo mata ƙamshin wani abu, wanda yake gigita mata lissafi,
A hankali kuma jijiyoyin jikinta suka fara saki, yayinda dukkan wani kuzarinta ta neme sa ta rasa, wani kalar numfashi take fesar wa yayinda take jan numfashi kuma da ƙyar.


A gigice Mutumin kuma ya cire bakinsa daga hannun Julde, yana wani irin gurnani, gaba ɗaya bakinsa ɗigar da jini yake,
Yana layi kuma ya janye jikinsa zuwa baya tare da Miƙewa tsaye, juyawar kuma da zaiyi ne idanunsa ya sauka akan Abu Maleek dake tsaye ya sunkuyar da kansa zuwa ƙasa.
Hangame bakinsa Mutumin yayi wanda zai iya bashi sunan (Arnan daji).
Kai tsaye kuma yana tan gaɗi da wata iriyar tafiya mai kama data ƴan shaye-shaye,
Gaba ɗaya bashi da kuzari saboda ya sha jini yayi bankas.


A.m kowa tuni jikinsa ya fara rawa, jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa, yayinda gargasar jikinsa ta shiga mimmiƙewa, yana jin kansa na wani irin harba masa tamkar zai tsage gida biyu.


A hankali mutumin yake nufar A.m yana tafe yana buɗe bakinsa, alamar a wannan karan jinin Abu Maleek yake nema, kai tsaye kuma yana zuwa ya fara ƙoƙarin kaiwa A.m cafka.


Karyar da wuya Abu Maleek yayi kafin ya ɗan buɗe bakinsa Murya can ƙasa bata fita sosai yace.
"O'ohhhh"
A dai-dai lokacin ne kuma Mutumin ya ƙara buɗe bakinsa tare da kusanto A.m kafin ya ida sauke bakinsa a damtsan A.m,
Tuni Abu Maleek yayi ƙasa tare da ɗaukan wani ƙaton Dutse ya miƙe a hanzarce kai tsaye kuma ya sauke dotsen akan Mutumin,
Nan take ya tsulale a wajan jini na zuba ta tsakiyar kansa,
A hankali shima Abu Maleek ya sulale a wajan, wanda tuni ya manta da shiga ɗaya duniyar tasa, hakan yasa gaba ɗaya yaga samaniya na juya masa,
Yana ganin taurari na sakkowa zuwa dab da idanunsa,
Idanunsa a shiga Lumshe yayinda fatar jikinsa ta ɗauki rawa sanadiyyar rawar da naman jikinsa yake,
Cikin rashin makama da kuma rashin sanin abinyi ya sanya tafin hannunsa dake fidda wani gumi ya manna a tsakiyar goshinsa, wanda ya kejin kamar zai rabe masa gida biyu, kunnuwansa kowa wani irin numfashi yake jiyowa wanda ya kasa tantance wanne kalar numfashi ne wannan ɗin.


Ƙara cure jikinsa waje guda yayi tare fesar da numfashi, ya shiga taune leɓansa, yana jin wata azaba na fincikar jijiyar kansa, kafin a hankali ya fara saki wani sound mai kama da gurnani, gaba ɗaya jikinsa ɓari yake, sanyi da kuma iskar wajan haɗi da haraɓar dake kwance a wajan bai hana,
Wata wahalalliyar zufa keto masa ba, sosai ya keji samun kansa a cikin a zaba muddin juyewar tunaninsa ya tashi.
Zuro sweet tayi da idanunta, yayinda ta rakuɓe waje guda.


1hour left
Ya shiga sauke wani Numfashin wahala yana ɗan jujjuya kansa, dake sara Masa, duk da cewa yaji ciwon yayi ƙasa, amma hakan bai yana yaji kansa yayi masa nauyi sosai ba.


Bakinsa ɗauke kuma da salati ya shiga buɗe narkakkun gajiyayyun idanunsa, wanda sukai masa nauyi, kafin a hankali ya yunƙura ya miƙe tsaye baki ɗaya,
Sweet dake gefe na ganin hakan ta fara tsalle tana kaɗa jela, a sanyaye fuska a narke ya kalli sweet suna haɗa idanu ya kwaɓe mata fuska, irin I'm tired ɗin nan, a hankali ya sunkuya zai ɗauki sweet domin suci gaba da tafiya domin Allah yana kallo ya mance da batun Julde, baya Sweet tayi tare da juyawa ta kalli Inda Julde ke yashe, slowly ya juya idanunsa zuwa ga direction ɗin da Sweet take kallo.


Idanunsa ne suka sauka akan Julde wacce take kwace, farar fuskarta ya tsorawa idanu ganin yadda ta ƙara wani mugun haske, tai fari fatt da ita,
Langwaɓar da kansa gefe guda yayi yana ya mutsa fuska tare da marai-raice wa baki ɗaya kafin ya juya ya kalli sweet yace.


"Kin gani ko? I can't Sweet ni bazan iya ba gaskiya aita wahalar da mutum, ko uban me take a kwance kuma ohhhhoo??"


Ya ƙare maganar yana ƙara mirgina kansa gefe guda, tare da ƙoƙarin juyawa, cak kuma ya tsaya, saboda kansa da yaji ya sara take kuma ya fara tuna abinda ya faru, cikin sauri ya juya kanta tare da cilla idanunsa akan Julde wacce take fidda numfashin wahala,
"Yasubuhanallah!"
Shine abinda ya zo bakinsa, Shikenan ta harbu yaya zai yi kenan? Anya bazai barta a nan ba, tunda daman neman kai yake da ita?
Wata zuciyar kuma tace.


"A'a Jalaluldeen, wannan dukkan haƙƙin ta yana wuyanka, kula da lafiyarta, cinta, shanta, sutturar ta, Wheel ba ita tace tana sonka ba,
Sanda za'ai auran itama bata sani ba a yanzu dukkan abinda ya sameta you're the reason behind, dan haka ya zama dole ka kula da ita, domin ita ɗin KYAUTAR ALLAH ce, KYAUTA CE DAGA ALLAH kare ranta kuma na nufin kare rayuka da dama wanda suke gab da salwanta"


Zuciyar ta ƙare maganar tana harba masa, tare da ƙara bashi umarnin zuwa ya taimake ta.


Kwaɓe fuska yay yana jan tsaki kafin ya kalli sweet yace.
"Sweet naje? I'm scared kada ta cijan na zama maye"
Karkaɗa jela sweet tayi, kafin tayi gaba zuwa wajan Julde taɓe baki Abu Maleek yayi yace.
"Uhm! Allah za muyi faɗa sweet, i don't know why kike son Fulani girl ɗin nan"
Ya ƙare maganar yana riƙe ququnsa da dukkan hannayensa, kafin kuma walking slowly ya marawa sweet ɗin baya, yana zuwa ya durƙosa dai-dai kanta ya kallo ƙyakkyawar fuskarta mai kyau wacce ta kasance zagayayyiya (Oval shape).


Wani irin fisgar numfashi Julde taja lokacin taji ƙamshin mutum kusa da ita, a hankali kuma Jikinta ya fara rawa ta shiga ƙoƙarin tashi zaune tana buɗe baki,
Zare ido A.m yayi a ransa yake faɗin "Mayya!!" Zanyi maganinki yasin,ji yadda take buɗe mitsitsin baki ko small yatsana bai shiga"
Ya ƙare maganar yana sanya duguwar yatsarsa ya dungure mata kai.


Julde bata san mene yake ba, burinta kawai ta samu abinda hancinta yake jiyo masa ƙamshin sa,gane abinda take so ne yasa ya ɗan saki Murmushi ƙiri-ƙiri an mayar da ita mayyar ƙarfi da yaji.


Idanunsa ya juya kaɗan cikin Sa'a idanunsa ya sauka akan wani yadi, kafin yayi magana sweet ta ɗauko yadin da bakinta ta kawo masa, kanta ya shafa cikin ƙaunar magen tasa yace.
"Love You!"
Zama yayi sosai yana mai ya tsuna fuska shi gaba ɗaya tsantsamin Julde yake,
bisa dole ya tattausan hannunsa ya ɗan jawota gefensa tare da ɗura kanta a cinya,
idanunsa kuma ya mayar wajan ciwon ganin yadda yake zubar da jini,
wani irin zabura Julde tayi tayo kan Abu Maleek duk da bata gani,
unexpected abun ya zuwa A.m hakan yasa yayi baya tare da faɗuwa Julde kuma tabi jikinsa ta kwanta tana buɗe baki tare da neman inda zata ciza,
ganin hakan yasa Abu Maleek neman yadda zai ƙwaci kansa dan muddin ya bari ta cijesa ya gama aiki,
hannunsa ya buɗe baki kasancewar mai faffaɗan ƙirji yasa gaba ɗaya ta rufta cikin ƙirjin nata,
da sauri kuma ya sanya hannayensa yayi mata rumfa dasu,
Kokawa suka fara inda take ƙoƙarin ganin ta kama hannunsa yayinda yake sun ganin ya riƙe fuskarta baki ɗaya, shi Abin dry ya basa,
Ganin kuma tana ɓata masa Lokaci ne yasa ya ɗan haɗe fuska sosai tare dasa hannunsa a saman karan hancinta ya ja,
Wata ƙara ta saki saboda zafin da taji sai kuma ta kwaɓe fuska ba tare kuma da tace komai ba kamar wacce aka bawa umarnin tayi ƙasa da kanta zuwa ƙirjinsa, tare da sauke ajjiyar zuciya,
Tana mai ƙara mannewa a jikin nasa ba tare kuma data kai masa cizon ba.
Lumshe idanunsa yayi sosai yana jin yadda take saukar masa da gajiya, kafin kuma
Ya ɗauki yadin ya shiga naɗe mata baki dashi, yana gamawa ya sauke numfashi tare faɗin.
"Ya Allahu Ya Rahamu"
Kana ya miƙe tsaye da ita a jikinsa tare da ɗan taɓe baki yana faɗin.


"Kawai aita wahalar dani, yarinya wallahi sai na rama, ƙwaffff"
Ya faɗa yana jan ƙwafa, kana ya cilla ta bayansa ya ɗauki sweet a hannunsa,
Ko takan nono da ruwan bai bi ba, ya kama hanya tare da suma tafiya, yayinda kuma Julde tai lubb a bayansa tana sauke ajjiyar zuciya da ƙarfi.


Yau ta kasance ranar juma'a, ranar da dukkan wanda yake Kanzaf bazai taɓa mancewa da ita ba, ranar data shiga tarin daga cikin ranakun tarihi, ranar da mutanan Kanzaf da mutanan da suke cikin Alaafi suka shiga cikin tashin hankali, tashin hankali mara fasaltuwa, ranar da Kanzaf ta zama kamar wani sansani na maƙabarta saboda Shiru da garin yayi baka jin motsin komai, Hatta tsuntsayen da suke shawagi kullum daga Cikin bishiyoyin Alaafin zuwa bishiyoyin Kanzaf yau babu su,
Sai wata dadɗar iska mai daɗi da kuma ratsa zuciya dake tashi, cikin ƙaramin lokaci kuma garin yayi duhu saboda tasuwar hadari daya haɗa da wata gagarumar iska mai ƙarfi.


Oumuu-Ayman ce tafe ita da Salimerh sun sanya Mai Babban ɗaki a tsakiya wacce Idanunta yayi jajurr, ga wani irin rawa da Jikinta yake, a haka suka nufi sashin King Tunde suna zuwa suka samu Queen Ayoola a kusa dashi riƙe da hannunsa sai kuka take, gefe guda kuma Otun da Agba Akin ne zaune suna masara addu'a tare dayi masa fifirta,
Daga can gefe guda sautin kukan Bola ne tashi a hankali, Zama Mai Babban ɗaki tayi tare da kallon ɗan nata, a hankali ta sanya dai-dai kunansa ta shiga karanta masa addu'a, ta nayi tana kalmar shadda,
Jin yadda Mai Babban ɗaki take nanata Kalmar Shahada ne ya sanya Salimerh gigice wa, tare da sanya kuka tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir Arjun, Dad!! Dad!!"
Ganin yadda Salimerh ta gigice take neman ruɗa MALEEK dake kusa da King Tunde Muhammad Jalal daya riƙe hannunsa sosai yana jin tamkar Zakinsa ne kusa dashi,
Ya sanya Oumuu-Ayman ta riƙe Salimerh tare da rungome ta sosai, tana faɗin.
"Just pray for him, ita yake buƙata Salimerh"
Kuka Salimerh tasa tana rungome Oumuu-Ayman tare da faɗin.
"Oumuu!! Oumuu Dad!! I'm going to lose my Dad Oumuu, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Sosai Oumuu-Ayman ta rungome Salimerh a jikinta, ganin tana neman ficewa daga cikin hayyacinta.
"In sha Allah, noting will happen to him sai abinda Ubangiji ya tsara Salimerh, just pray kiyi masa addu'a"
Ta ƙare maganar tana juyar da idanunta saboda hawayen daya cika mata idanu,
Da sauri Salimerh ta miƙe tana faɗin "Oumuu Zaki?? Shakiru, Sharefddeen, babu kowa Oumuu yaya za mu yi?"
Sai kuma ta juya da sauri ko ganin gabanta ba tayi yana fita, taci karo da Junaid tana ganin ta nufi inda yake, runtse idanunsa yayi saboda wani mugun mugun! Tausayinta da yaji, tana zuwa ta faɗa jikinsa tare da riƙesa sosai tana faɗin.
"Junaid, My Dad! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un zan rasa farin ciki na Junaid yaya zanyi? Yaya Zaki zaiji idan ya dawo ya samu babu Dad? Wayyoooo Allah, Ubangiji ya dube mu, ka kawo mana sauƙi akan abinda yake shirin samu mun ba, Ubangiji ka dubi idanun mu ka tausaya mana ka barmu da mahaifin mu, shine jin daɗin mu, shine farin cikin mu, shine garkuwan mutanan Kanzaf, La'ilahaillahu Muhammadur Rasulullah S.A.W"
Ta ƙare maganar tana sakin kuka sosai, tare da riƙe Junaid, idanun Junaid yayi jaa sosai, a hankali ya sa hannunsa ya rungome ta a jikinsa yana so da ƙaunar ta na ƙara nunkuwa a zucyarsa, ga kuma wani tausayinta daya gama mamaye zucyarsa, a hankali ya shiga bubbuga bayanta tare da faɗin.
"It's okay My princess, In sha Allah Dad zai miƙe zaici gaba da zama damu, Kiyi masa addu'a please wifyna"
Ya ƙare maganar yana ɗan bubbuga bayanta, kafin ya janye ta daga Jikinsa, yana kama hannunta tsayawa tayi tana girgiza masa kai alamar ba zata shiga ciki ba.


Girgiza kai kawai yayi kana ya shiga ciki, yana barin wajan Salimerh ta nufi Part ɗin ta, tana zuwa ta samu wayarta na ringing da sauri tai answering daga cikin wayar akace.
"We are on our way Ranki ya daɗe?"
Wasu zafafan hawaye ne suka sakkowa Salimerh kafin tace.
"Ina Zaki na?"
Daga cikin wayar akace "we're all together Maaahh!"
Jinjina kai tayi cikin tsananin farin ciki da kuma jin daɗin Dawowar JULALUDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL, kafin tace.
"Ka shigo ta ƙofar baya"
Daga cikin wayar aka amsa mata da "In sha Allah" kashe wayar tayi a sanyaye kuma tace "Allahamdulillah"


Oumuu-Ayman ce tsaye da Salimerh suna nan tsaye kuma suka hango motar na shigowa ta can ƙofar baya, wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Oumuu-Ayman ta sauke, yayinda wata nutsuwa ta sauka a zcyarta, tun bayan tafiyarsa bata da wata nutsuwa kullum cikin damuwa take,
A hankali motar take tafiya harta iso inda suke Oumuu-Ayman suke, a hankali kuma Oumuu-Ayman ta nufi back seat tare da sanya hannunta ta buɗe motar, Idanunsa dake lumshe ya ware a hankali tare da sauke su akan Oumuu, tashin hankali daya a cikin ƙwayar idanun ta ya sanya ya tsorawa mata narkakkun idanunsa,
Zame idanun ta tayi daga cikin idanunsa saboda kallon da taga yana bata, a hankali kuma idanun ta ya sauka akan Julde wacce take kwance bakinta a ɗaure tana bacci juyawa tayi ta kalli Salimerh tace.
"Shiga ciki ina zuwa"
Tayi hakan ne kuma saboda bata son Kowa yaga Julde, hannunta ta miƙa wa Jalaluddeen alamar ya kama,
Ƙara ware idanunsa yayi a kanta kamar bazai magana ba dai kuma yace.
"Dad????"
Ya tambaya kai tsaye domin shine kawai ya faɗu masa, musamman yadda yaji ko'ina shiru hakan yasa jikinsa yayi sanyi,
Girgiza Kai tayi tace "Yana ciki, Zaki baƙuwa mukai?" ta ƙare maganar tana ƙara kallon Julde wacce taji nan take so da ƙaunar ta ya shiga zuciyarta, taɓe baki yayi tare fitowa daga cikin motar, yana fitowa daga motar sweet ta diro ita ba, ta shiga tsallan murna, har yayi gaba sai kuma ya tsaya tare dayin baya,
Cikin motar ya koma ya jawo Julde fuskarsa a ɗaure kuma ya ɗauki Julde a hannayensa kamar Jajiriya,
Kallonsa kawai Oumuu tayi tasan Abu Maleek bazai taɓa aikata abinda ba shike nan ba, hakan yasa bata zarginsa ko kaɗan,
Bayansa tafi kai tsaye kuma ya nufi wajan prvt bedroom yana zuwa ya cilla Julde ciki wacce tayi ɗan ƙara sai kuma taci gaba da bacci abinta,
Oumuu-Ayman dake bayansa sanin halinsa yasa tai masa shiru, tsayawa yayi tare da sanyawa Ƙofar passward, kana fuskarsa babu walwala ya kalli Oumuu-Ayman yace.
"Where's my Dad?? Ina Daddyna Oumuu??"
Idanunta ya kawo ruwa ganin haka yasa a gigice Abu Maleek yayi waje ta cikin ƙofar cikin family side ɗin ɗasu, kai tsaye kuma ya nufi Sashin King Tunde Muhammad Jalal, babu wanda bai mamakin dawowar Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal a wannan lokacin ba, yana zuwa ya amshi King Tunde Muhammad Jalal a hannun Mai Babban ɗaki tare da rungomesa, jikinsa na rawa tace.
"Dad! Dad!! Dad!!! Open your eyes please Daddy!!!!!!"
Ya faɗa yana Rungome Mahaifin nasa, wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya King Tunde ya sauke lokacin da yaji ɗumin jikin Zakin nasa, tare dajin sautin Muryar sa, bisa mamaki a kaga King Tunde na motsawa tare buɗe idanunsa ya riƙe hannun, Jalaluldeen ganin yadda bakinsa ke rawa yasa Abu Maleek sunkuyawa, ya ɗauka wata magana zai faɗa sai yaji yace.
"Allah yayi maka albarka, Allah yayi riƙo da hannayenka, Jalaluldeen ga Khaleluddeen nan, ga Zubaida nan, Oumuu-Ayman zata faɗa maka komai, zan tafi ciki farin ciki da kuma salama a Zuciyata, Zakina ka kula da kanka dan Allah ka sani ka girma ka daina wannan shagwaɓar, ka zauna cikin Kanzaf ka maye gurbina a Cikin Alaafi, kada ka yarda da kowa face Oumuu-Ayman, Mai Babban ɗaki Sai Zubaida, ko ƴan uwanka maza kada ka amince masu, akwai wani haske da zaizu a duk sanda ka kusance sa, za kaji faɗuwar gaba kada kaji tsoro wannan shi ne mahaɗin Wanda zai zame maka ɗan uwa wajan gudanar da Mulkin Kanzaf, Allah yayi maka albarka Zakina, Ka faɗawa Maminka ta na tafi cike da so da kuma kewarta a cikin zuciyata, kada ka Amincewa kowa Jalaluldeen kada ka yarda da kow......"
Wani irin tsayawa numfashin sa yayi wanda ya tilasta masa tsayawa da maganarsa, duk abinda yake faɗa babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login